Showing 36001 words to 39000 words out of 84595 words

Chapter 13 - RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

15 Nov 2025

1139

ni,
Cikin tsoka na doctor fadil yace.
"Safiyyah allura fa zan miki itace kawai zatai saurin saukar da zazzaɓin nan.

Jin ya ambato allura nai rau-rau da ido, ina kallon yah Ansar daya haɗe fuska, Please doctor ka bani magani kawai.

"A'a Safiyyah nasani ko maganin abaki basha zakiyi ba, inma kinsha to ba bisa ƙa idaba, kuma allura itace kawai bani hannun ki na miki.

ƙin karasawa nayi saima tsayawa da nayi kamar zanyi kuka ina kallon yah Ansar.

"Doctor fadil yimata ina sauri ne"

Badin nasoba na runtse idona har a gama hawaye na zuraromin. Saida yah Ansar yayi murmushin gefen baki kana yace.
"Allah ya shirya minke safiyyah"

Doctor dai ya amsa da ameen daga haka muyi sallama ya biya ya ciri kuɗi, ya mubiya ya siyamin kaza, kana mu wuce. Gida

Yanzu yaya haka zaka bata kuɗin?

"To ya za'ayi Safiyyah bafa yau tasaba irin wannan abun ba.
nidai abinda nake so dake duk inda RAYUWA zata kaiki ki kasance mai hakuri, domin me hakuri ne keda ribar zaman duniya.

"Insha Allah yaya"

Koda muje tana zaune a parlour tana jiran dawowar mu, daki na shige shi kuma yah Ansar ya bata kuɗin ya wuce daki.

Gaba daya yau kowa na gidan da yunwa ya kwana, to baiwar tasu bata da lafiya bare naje na daura musu. nikam yah Ansar ya siyamin kaza ita naci na kwanta. Bayan munyi waya da MD.

______

Yah Ansar yaje ya sami su kawu Inusa da kawu mansir sun. Sunta faɗa dan me za'a takura ma marainiyar Allah, dan kowa ya yabari ummah ta rasu, to har yanzu bata ba labarin ta. daga baya su amince da za suzo su same sa.

*Washe gari*

Suzo don mun tafi aiki ma har Abban basu same shiba sai office ɗinsa. Su tattauna duk da dai da farko taso tayi tsami a tsakaninsu.
Kasancewar Abba yana ganin girman yayan nashi. Da kyar dai ya amince da batin Suraj..


A lokacin mani ina office ɗin MD naje kaima sa aikin daya bani ranar Friday. Kamar kullum yauma sanye nake da hijjab har kasa, akwai mark a fuskata har da eyeglasses. To dama shigar tawa kenan. Indai ka ganni da gyale to ɗan kolin abaya nasa nai rolling.

Miƙa masa nayi na maida hankali a wayata,

"Masha Allah yayi kyau sosai baby yanzu saura printing. tom ki kasan ce cikin shiri kinji"

"Insha Allah"

Daga haka na koma office na koma mu cigaba da aiki.

*In the evening*

Har gida yauma ya kaini. Dan har na fita na manta da jakata, shine ya dakko ya fito ya bani nadan jingina da motar shi.

"Amarsu ta ango" daya faɗa yasani dauke kai ina murmushi. Shima karamar dariya yayi yana dawo ta inda na maida kan nawa. Karamar harara nasakin masa ina sake dauke kaina. Yace

"Tab irin wannan harara haka amarya ai saiki sa na zube a ƙasa wallahi. Kinga adanamin ita sai nanda 'yan watanni kawai. Kinga inma suma nayi dai kya farfaɗo dani da kanki ba wanda yaji konya gani koh?

Dariya ya bani amah kasancewar ba'a ganin bakin nawa sainai murmushi kawai nasake dauke kaina.

________

Anty Waleeda da dawowar ta kenan daga yawan ta. Taci karo da Safiyyah da MD suna shan soyayya zuciyar ta data buga lokaci ɗaya ta dafe tare da furta.

"Na shiga uku na Ni Waleeda me nake ganine?
Ganin ba me amsa mata tambayar ta kuma intaci gaba da kallon su zuciyar ta zata iya bugawa. Ta faɗa gida hankali tashe tana kwalla kiran.

Mom! Mom!

"Waleeda lafiya kike kwalla kirana kamar ance miki na mutu ko Abban ku?

"Uhmm mom bazaki gane bane wallahi jinake kamar zuciya ta zata fashe"

Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka. Tuni mom ta rikice sai jerama ɗiyar tata tambaya take. amah anty Waleeda sai kuka take kamar. ko wacce ace mom ta rasu.
Dai-dai ina shigowa parlour dan basu masan na shigo ba. Mom ta daka mata tsawa tare da cewa.

"Ki faɗamin meya faru, me amiki, wani abune ya faru?

"Mom safiyyah!

"Meya faru da Safiyyah har kike kuka kamar ance ta mutu?

"Wallahi mom da zata mutu danafi ko jin daɗi. Wallahi da har sadaka sainayi"

Tsabar yadda maganar ta dakeni bansan sanda zafafan hawaye su zubomin ba. Dama tsanar da anty Waleeda tamin har ya kai haka.
Mom ce ta katseni tare da cewa

"sai jamin rai kike kifadami abinda ya faru"

"Wallahi mom ganin ta nayi da wannan wanda yazo gidan nan neman ta. kuma mom kisan tsananin son danake masa mom. Jin zuciyata nake kamar zata buga"

takai ƙarshe maganar tana zubewa akasa.

"Banza yaushe kizama shasha-shane Waleeda akan namiji kike zubda hawayen ki?
To wallahi ni Zuwaira nayi rantsuwa da Allah. indai baki same saba itama bazata same shiba. saidai bana numfashi a doran kasa.
(Tofa🤔 ana wata ga wata wai inji masu iya magana)

Ban bari mom tasake cewa komai ba na share hawaye tare da sallama.
Gaba ɗaya ɗagowa suyi suna kallo na.

"Barka da gida mom"

Bata amsa ba nima na wuce ciki zuciya tana suya.
Dama ƙiyayyar da anty Waleeda take nuna min har takai ace kona mutu saitai sadaka saboda farin ciki. Innalilahi wa'inna ilahiri raji'un wannan wacce irin rayuwa muke ciki. Allah yasa mu dace,,


◼️Alƙawarin Allah yah cika. yau dai iyayen Suraj wato MD sun kawo kuɗi gidan mu. inda naga baƙin halin mom muraran. Dan zage-zage ta dingayi dayima Abba masifar wai an munafunce ta. Ashe bai gaya mata ba sai ganin su kawu Inusa tai. Shine take tambayar sa meya kawosu. Yace mata iyayen wanda yake neman aure nane suka zo yau. Takaici ya hanata sake cewa komai sai ido data zubamishi. Dai-dai shigowar baki saiga abinci da ruwa da lemo yah Ansar na shigowa da su da batan san ina yasame suba. Shiko yah Ansar sanin halin ta yasa ya faɗa ma ummi ta dafa musu.
Aikuwa ranar munga tujara. Dan nima da bansan meke faruwa ba ina gurin aiki ina dawowa saida na amshi rabona. Anty Waleeda kuwa kuka take tana zage-zage. Uffan bance ba musuba. An wajen yah Ansar naji komai iyayen Suraj sun kawo dubu 300k suna gun Abba.

Bance masa komai ba muciga ba da fira dan bana ma sha'awar shiga cikin gidan. Sai gurin sha ɗaya nashiga anty Waleeda kawai na samu a parlour taci kuka idon nan yayi hulu-hulu. Bance mata komai ba na kama hanya bedroom. Jinayi kawai an shaƙemin wuyan hijabi na tabaya tare da sakin mun duka hannu bibbiyu. Jin numfashi na na barazanar dauke wa yasa na fusgo hijabin na yagaji sanan na waigo ina numfashi da kyar.
Anty Waleeda ce tsaye sai faman huci take kamar me shirin dambe. Na mata kallon sama da kasa kafin nace mata cikin mamaki,,
Lafiya kuwa baiwar Allah kin shaƙeni haka sai kace wacce na cimiki bashi?
Are You oky?

"A haukace nake dan uwarki. Wallahi kaɗan ma kigani dan wataran in shaƙe ki saikin dena numfashi zan barki. Dan haka ina gargaɗin ki inhar kina son ranki ki fita sabgar Suraj wallahi. Ki kuma bar ganin ya kawo kuɗi da sunan auren ki. Wallahi indai kiga kin aure sa saidai ina bana raye. Amah inhar ina raye wallahi yadda ban same saba kema wallahi bazaki same saba jaka yar dabba yar gidan mayya.

Murmushi kawai nayi mai fadi. wallahi ni dariya ma tabani da tausayi, na wucce ɗaki na barta tana ɗaura min zagi kamar ba dare ba.

Bathroom na shiga nayi wanka kana na dauro alwala nai shirin bacci, ba abinda nake sai ƙamshin humura.
Sama-sama najiyo maganar Abba ita kuma tana kuka. Baki kawai na taɓe na gyara kwanciya ta ina karanto addu'oi kwanciya bacci dan gobe zanje gidan ummi bikin anty Hajara saura one week. Sai dai kamar kullum saida na tashi nayi ƙiyamul laili daya zame min jiki. Saidai idan banda lafiya, amah ko prioud nake saina farka.



________

*Abuja🤍*

Mummy nashiga ɗaki taci karo da zaituna data kafe hoton majeed dake wayar ta da kallo. Har takai zaune kusa da ita bata sani ba har ta amshi wayar kana ta ɗago firgigit. Ajiyar zuciya ta sauke dan har mummy saida ta jiyota kana tace.

"Wallahi mummy kin bani tsoro"
Tafaɗa a shagobe .

"Uhmm zaituna ki kwantar da hankalinki indai majeed ne kamar kin samu. Dan mun gama magana da yaya kuma nasan zai amince hajja ce matsalar amah nasan yadda zanji da ita".

Tsabar farin ciki zaituna rungume ta tayi tana zuba ma mahaifiyar tata addu'a.

Granny da duk maganar da suke tana jinsu kai kwai ta girgiza ta koma parlour. Dan tunda taga mummy tasan wani abun take kullawa shiyasa tasa mata ido sosai. Yanzu kuma tunda ta gano abinda take shirya wa ai tasan yadda zatai da ita.

_______

Yau majeed zai dawo dan haka Ammii dakanta tashiga kitchen tamishi girki sai auta da fennah dasu taya ta. Dan kwata-kwata baya son cin abinci masu aiki, bayan sun gama tasa mama Rabi'ah da auta suje su gyara mai ɗaki kasancewar mama Rabi'ah ke masa gyaran ɗaki.

*In the evening*

A hankali motocin nashi dasu taso daga airport ke shigo wa cikin gidan, youseef ne daya fito a cikin ɗaya daga cikin motocin ya nufi motar da ogan nashi yake ya bude masa. Saida ya ɗau minti biyar kana ya fito gaba ɗayan shi. Sanye yake cikin suite milk sai neck tie black, sai takalmin kafar sa da yake milk kwalliyar sa data kasance black, sumar nan tashi data sha gyara ta kwanto mishi har fuskar sa. Ga wani ƙamshi da yake me kwantar da hankalin me shaƙa.

Yanda su zaituna da fennah su zubamishi ido kamar zasu cinye shi. Zaituna ji take kamar taje ta rungume shi ko zataji sauƙin abinda take ji.
Ita dai fennah tana ƙoƙarin danne wa ba kamar zaituna da take nuna wa a fili ba.

Da gudu auta taje da niyar rungume shi itada basma tunda ya musu wani kallo su kame suna tura baki.

Murmushi youseef yayi kana a hankali yace.

"Sorry autar mu"

Yana bin bayan sa hannun shi dauke da laptop da wayoyin sa.
Sannu da zuwa su zaituna su mishi shi kuma ya wuce part ɗin Ammii.

_______

*Kaduna✨*

*In the evening*

Tsaf na shiya cikin abaya baka mai santsi wacce amah ado da fararen duwatsu manya da kanana. Gashina da tunda na tsefe kallabar da ummi tamini ban sake yin kitsoba na daure da ribbon nai acuci. Rolling nayi da mayafin abayar aikuwa na fito kamar balarabiya. Farin eyeglasses na saka kamar ko yaushe idona ya fito dara-dara, ko marks yau ban saba saboda yah Ansar, Plat shoe nasa kana na dauki jakar dana haɗa kayana, sai hand bag da phone na fice a ɗakin.

"Wow my Little sisi kinga yadda kiyi kyau kuwa kamar wata balarabiya?

"Uhmm kai yah Ansar kaima dai, ina ni ina balarabiya dan Allah"

Nafada a shagobe. Murmushi yasaki kana yace "ki adana abarki kyama Suraj danni yanzu na kusa hutawa da shagobarki"
Baki na taɓe kamar zanyi kuka na nufi gurin motar shi na shiga.
Shima dariya yayi y biyoni mu tafi.

Dai-dai wani shagon ɗinki ya tsaya yace min ina zuwa. Be wani dade ba ya fito hannun sa dauke da leda, ashe ɗinki ya mana nida buhaisa da Isha, kala bib biyu tsabar farin ciki bansan sanda na rungume shi ba.

Tun kan mu isa gidan yace min nakira Isha ta kintsa za muje shopping da ita, da to na amsa kana nakira ta, koda muje shiga yayi su gaisa da ummi, buhaisa da ta cika tai fam wai saboda banzo da wuri ba. Hakuri na bata na miƙa ma ummi kayan taitasa mishi albarka.Tafiya muyi mu ɗau Isha a gida. kai tsaye shop rite muje yace kowa ya dauki abinda yake so, kama daga kan takalma jaka da kayan kwalliya. Da turaruka iri ɗaya mu ɗauka. Daga nan ya maida mu gida muyi mishi godiya yace.

"Toni dai gobe insha Allah zan koma kuma munyi sallama da ummi sai minyi waya."

"Yah Ansar bazaka zo bikin ba?

"A'a buhaisa insha Allah zan dawo ranar Friday"

Isha da tunda a fara maganar bata ce komai ba. Sai yanzu ne cikin sanyin murya tace.
"Tom Allah yah kaimu yasa kaje lafiya kadawo lafiya"

Da ameen yah Allah duk muka amsa. Yanda yah Ansar yake bin Isha da wani kallo ita kuma sai ƙasa da kai take.
Murmushi nayi kawai dan abinda nake zargi ya kusa zama gaskiya na shida Isha na son junan su aɓoye. To da hakan zai kasance dana fi kowa murna. Sallama muyi mishi mushiga ciki.

Tunda mu shiga ɗakin da ake ma anty Hajara gyaran amarya mu tasata gaba da tsokana kamar sa'ar mu. Kamar zatai kuka take kwalla kiran.

"Ummi! Ummi! Kizo ki rabani da marasa kunyar yaran nan dan Allah. Wallahi kema Safiyyah kita biyema su buhaisa inadai aure ne kema ai kin kusa, zakiga iskanci wallahi".

Jin haka yasa ni zunbura baki cikin shagobba nace kai anty Hajara.

Dariya susa gaba ɗayan su buhaisa tsabar dariyar mugun ta harda rike ciki. "matsoraciya kawai ni kutashi kubani guri zanyi waya da my husband"
Dariya mu sanya gaba ɗayan mu kai anty Hajara har yazama miji ne ai saiki bari ashafa.

"To ko hana ashafa fatihar, kunga Safiyyah in baku wucce ku bani guriba wallahi"

Dariya mu sanya tunda muna shirin kara magana saiga ummi nan. Ai da gudu mu fice muna dariya. Tunda kuma mu koma ɗaki su buhaisa su sani gaba wai amaryar MD. Saida su kusa sani kuka kana su rabu dani. Muraka Isha gida mukuma mu dawo.

Gabaki dayan su suna parlour harda yah saif suna shan fira. Muna zama muyi anayi damu. anan yah saif ya bamu kayan fitar biki, dan haka muyi zaman tsara yadda komai zai kasance.......✍️




Taku har kullum da ko yaushe

🤝Amanar nazari writer's association📚🖊️
07070260240, WhatsApp number or call

Please🙏 comment and like and share fissabilah👏👏





*_Typing📲_*

_What's app channel👇_

https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0

_WhatsApp group👇_

https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB



*🌹RAYUWATA🌹*

_CREATED AND WRITTEN BY_


*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
_💞 Billy pinky💞_


*Nazari writer's asso....📚*

[07070260240]

_*WhatsApp number or call*_

_Amanar🤝 Nazari writer's✍️_



*Page2️⃣8️⃣➖2️⃣9️⃣*
Kaitsaye part ɗin Ammii ya nufa zaune ya sameta, murmushi kwance a fuskata har ya ƙarasa gareta ya rungume ta. Cikin shagoɓɓa yace

" Ammiii i miss you "

"Miss you so much my son. Ka dawo lafiya?

" Alhamdulilah "

" Ma sha Allah. Kaje kayi wanka ka huta saika fito kayi dinner "

Da "to" ya amsa kana ya fice cikin sassarfa, Youseef yana zaune suna fira da su auta. Fitowar sa yasa shi tashi yabi bayan sa, a parlour Youseef ya yada zango yana shirin shiga bedroom ya waigo yana kallon Youseef kana a hankali kamar mai ciwon baki yace.

"Youseef kaje kawai ka huta, zuwa anjima saimu fita"

"Okay sir baka bukatar komai?

" Babu kaje kawai "

Ya faɗa yana shigewa bedroom, ba abinda yake sai ƙamshi mai kwantar da hankali mai shaƙa. zama yayi a bakin tam fatsatsen bed ɗin nashi da a lailayeshi da lallausan bed sheet. Yanda yake bin ko wacce kusurwa ta ɗakin da kallo kamar me neman wani abu. fuskar nan murtur kamar bashi bane ya gama zuba ma Ammii shagoɓɓa, a hankali ya tashi ya nufi bathroom bayan ya rage kayan jikin sa.

kusan minti arba'in ya fito sanye cikin, bathrobe pink calour sabuwa dal, ƙaramin towel dake a hannun sa yana goge kwanta ciyar sumar sa.

Gaban mirro ya karasa yana ɗaukar hand dryer ya jona a socket cikin cikin ƙan ƙanin lokaci ya kammala gyara ta, lontion ya shafa sai sprays dinsa masu shegen ƙamshi. Kana ya nufi close ɗin sa, riga da wando ya dauko wacce rigar ta kasance mai hula a gaban ta an rubuta TIGER da manyan baki mai kyau da laushi sai dogon wando da boxer shima dai sabo, tsaf ya gama shirin nasa ya koma gaban mirror yayi wankan tsaddadun turarukan nasa masu ƙamshi kamar ba dare ba, ya fito parlour, Kai tsaye masjid ya nufa domin gabatar da sallah.

Tare su fito da dady da sauran Uncle's ɗin nasa bayan sun gabatar da isha'i, tafiya suke suna fira cike da Nishaɗi har su karasa babban parlour domin yin dinner. Lokaci-lokaci Majeed kan ɗan runtse ido da shafa gefen kanshi.

Gaba ɗaya family zaune suke a kan dinning area domin yi dinner inka cire granny dasu dasu shigo yanzu. Da sallama suka shiga aikuwa su zubo musu ido na ɗan wani lokaci suna dauke idanun su tare da musu barka da zuwa. Inka cire Zaituna data zube Majeed da kallo kamar wata sokuwa. mummy ce data lura da hakan ta zun guro ɗiyar tata tana balla mata harara baki taɗan taɓe saiku ma ta maida kanta kasa tana wasa da abincin dake gaban ta.
Gaba ɗaya zama suyi kana cikin girmama wa Majeed ya gaida iyayen nashi fuskar nan dai ba alamun fara'a a cikin ta. wani kallo mummy da umma amarya suke mai kowa datashi fassarar, ita mummy haushin ta tana matsayin uwar sa kuma tana niyar zama surukar shi amah bai nuna alamun ya ma ganta a gurin ba balle ya mata Tata gaisuwar da ban, dan koda ya gaida su Addah bata amsa ba.
Itako umma amarya ita tabar wa kanta sani.

Bayan sun gama kamar yadda su saba su nufi part ɗin granny domin yin hira. Gwanin ban sha'awa family suke fira, in kacire Majeed daya koma gefe ɗaya yana aiki a laptop kamar dole idonan ya kaɗa yayi jaa, Lokaci-lokaci yakan kai hannun sa kan shi alamun ciwo kan yake mai ko kuma gajiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login