Showing 54001 words to 57000 words out of 84595 words

Chapter 19 - RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

15 Nov 2025

1144

a nan duniya, haka nan ma a wajen Ubangiji Mai Girma da Buwaya.
Kwarjini: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya zama mai kwarjini.
Matakan Bayar da Tarbiyya
Akwai matakai ko hanyoyi da ake bi wajen bayar da tarbiyya da suka haɗa da nuni, lura, umarni da kuma hani.

Nuni: Abin da ake nufi da nuni a nan shi ne aikata aiki a aikace, wanda daga nan shi wanda ake tarbiyantarwa zai gani ya koya. Tirƙashi, masu iya magana sun ce; “Idan mutum ya ce zai baka riga, to duba ta jikinsa”. Wannan magana ta zo daidai da faɗin Larabawa cewa; “Maras abu baya bayar da shi”. Saboda haka dole ne mai bayar da tarbiyya ya zama mai tarbiyya.
Wannan hanya ta bayar da tarbiyya ita ce mafi tasiri da kuma muhimmanci wajen bayar da tarbiyya. Saboda haka dole ne masu bayar da tarbiyya; iyaye, malaman makaranta da sauran jama’a suma su zama masu tarbiyya.

Misali.

...... dole iyaye su zama masu tsafta a aikace, kafin su dasa halin tsafta a zukatan ‘ya’yansu. Idan yaro ya tashi ya ga iyayensa suna share gida tsaf-tsaf, basa barin kwanon abinci da dauɗa, basa jefar da sutura ko’ina a ciki da wajen ɗaki, to a haka shi ma zai girma mai kula da tsafta. Kuma zai tashi shi tsafta ya sani bai san ƙazanta ba. Saboda haka da zarar ya fara zuwa makaranta malaman makaranta ba za su wahala da shi ba.

Umarni da Hani (Kwaɓa): Umarni shi ne a riƙa gaya wa yaro yi kaza. Misali, idan yaro ya tsoma hannun hagu cikin kwanon abinci, ko ya riƙe abinci da hannun hagu zai kai bakinsa, sai a gaya masa cewa, wannan ba shi ne hannun cin abinci ba, ga na cin abinci nan. Da haka zai gane hannun dama dana hagu.
Shi kuwa hani shi ne kore abu. A wannan gaɓar kuma yana nufin kare ko dakatar da yaro daga aikata aikin da ba mai kyau ba. A cikin wannan misalin dana kawo a sama, akwai gaurayen hani da kuma umarni. Yaro ya tsoma hannun hagu domin cin abinci, sai aka hana shi; wato aka dakatar da shi daga cigaba da amfani da hannun hagu. Sannan aka gaya masa; wato aka umarce shi da amfani da hannun dama.

Lura/Kula:

Lura ko kula, suna ɗaukar ma’anar saka ido a kan kai-komo na yaro; wato zirga-zirgar yara. Wannan hanya ta lura, cikamakonta shi ne kwaɓa. A nan, iyaye za su saka ido sosai game da zirga-zirgar ‘ya’yansu, duk lokacin da suka ga wata baƙuwar halayya maras kyau, sai su yi maza-maza su ɗauki matakin da ya dace tun kafin ta zama jiki.
Da zarar yaro ya fara fita wajen gida domin zuwa makaranta; wato daga shekaru uku zuwa sama, to fa dole iyaye su riƙa lura da shi sosai, saboda yanzu kuma ya je ya gwamutsa da sauran yara daga gidaje barkatai. Saboda haka idan iyaye basu saka lura ba, to tarbiyyar ‘ya’yansu sai ta koma barkatai.

MUHIMMANCIN TARBIYYA

Tarbiyya tanada matuqar muhimmanci. A duk lokacin da dan adam bai samu tarbiyya ta musulunci ba to lallai zai iya komawa mai dabi'a kamar ta 'dabba'.

ANNABI S. A. W yana fada a hadisi cewa:

ﻣﺎ ﻧﺤﻞ ﻭﺍﻟﺪ ﻭﻟﺪﻩ ﻣﻦ ﻧﺤﻞ ﺃﻓﻀﻞ ﻣﻦ ﺃﺩﺏ ﺣﺴﻦ

"Uba bai bawa Dan shi/Yar shi kyauta mafi falala ba fiye da kyakykyawan ladabi/tarbiyya".



........... Zuciya da gangar jikin sa ba abinda take so sai kwadayin son ganin fuskar ta a hankali cikin ya sauke idanun sa dake farare tar akan TV a kuma dai-dai lokacin Safiyyah ta d'ago domin sallama da masu sauraro.
Aikuwa akan kyakkyawar fuskar ta ma abociyar kyau da kwarjini idanun sa su sauka.
Yadda zuciyar sa tayi wani tsalle a girjin sa kamar zata fito cikim mamaki yake sake kallon ta yayin da ita kuma ta cigaba da sallama da masu sauraro.
"Yah rabb" shine abinda ya furta wani tari yana sarƙafeshi jin yadda zuciyar sa take masa.
"Lafiya Majeed meya faru".
Cewar Ammei duk ta ruɗe da sauri Auta ta dauko ruwa tare da balle bakin gorar tana Shirin tsiyaya masa ya amshi gorar inda ya kafa bakin sa saida ya shanye kana ya koma kujera ya lafe dan ya bar jikin Ammei ma. Sannu suke masa yana ɗaga kai inda ya maida idanun sa kan TV, a zahirin gaskiya baza kace TV yake kallo ba dan sam idanun sa ma a lumshe suke amma a baɗini tar idanun sa suke akan kyakkyawar fuskar Safiyyah yara sa me ke shirin faruwa dashi ne akan wannan yarinya. Yanda take motsa dan ƙaramin bakin ta dake ɗauke da lipstick mai kalar pink yake kallo gaba ɗaya ya faɗa duniyar tunani dan duk firar dasu Ammei suke baima sani ba haka yayi luf kamar me bacci. Yanda su Ammei keta yabon Safiyyah da sa mata albarka kasan cewar duk family suna mutukar son program ɗin ta dan baya wuce su. Ba abinda Ammei take fata da addu'a sai Allah yaba Majeed mai irin halin wannan yarinya dan yanzu *RAYUWAR* sai a hankali. Hankalin t mayar kan Majeed daya labe kamar me bacci amma ita tasan ba baccin yake ba.
"Majeed yaushe zaka fito da matar aure ne".

Jin maganar yayi a bazata don haka cak ya dawo daga duniyar tunani daya tafi yana d'ago rikitattun idanun sa dasu dan surka sai su bada wata kala daban yana kallon Ammei dasu. Hararar wasa Ammei ta bishi da ita tare da cewa. "Bar kallo na da wannan idanun naka".
Fuska yaɗan kawar tare da shagobe ta yana kallon ta batare daya yi magana ba.

"Kaga Majeed ya kamata ka farka a baccin da kake tuni ka girma ka isa aure sa'oinka kowane gasu nan da yaran su ba ɗaya ba ba biyu ba amma kai ka tsaya mene?".
Yanda ya wani shagobe fuska kamar ba shiba kana yace. "Nifa Ammei Allah cikin matan banga wacce tamin b..a". Ya ƙarasa maganar a rabe jin zuciyar sa ta tuno mai da Safiyyah.

"Toh tun wuri kasan abunyi dan mun gaji da ganin ka haka in kuma dadyn ku ya samoma da kasan to ko a cikin ƙannin kane ai yayi koh".

"Uhmm Ammei jan raini ne ai, nidai ku barni insha Allah na kusa kinji Ammei nah".
Ya ƙarasa maganar yana kwantar da kanshi a kafadar Ammei.

Murmushi kawai tayi tare da girgiza kai dan tasan indai ta halin Majeed za'abi tofah bazai ba.

"Nadai na faɗa ma tukafin dadyn ku ya waigo gareka kasan abun yi".
Auta da tunda afara maganar ba tace komai ba sai yanzu tace.
"Allah yah Aj nima na kosa nayi anty amma ka ƙi yin aure yaya".
Kamar zatai kuka ta idda maganar dan Auta cikakkiyar yar shagobba ce. Harara ya zuba mata tare da cewa. "Yaushe na zama abokin wasan kine habibat harda ana min magana kina samin baki?".

Dan shi baya ce mata Auta dan yace har yanzu shine Auta shiyasa duk shagoɓɓar Auta indai yanan bata yi sai dai tabar mai.

Kamar zatai kuka tace "Yaya nah Allah ba haka bane am very sorry".
Batare daya ce komai ba ya girgiza kai kawai tare da zame wa ya kwanta a cinyar Ammei yana kafe TV da ido. duk da tuni Safiyyah ta gama program ɗin ta dan wani shirin ma suke.
gani yake kamar zai ganta amma shiru a hankali ya lumshe ido yana faɗa wa duniyar tunani Safiyyah. Time ɗin daza ta faɗi a shopping mall ya taima keta yanda fuskar ta tai bayyana tsoro ƙarara da yanda ta runtse idanun ta sai ƙaramin bakin ta datake motsawa kamar mai addu'a yake tuna wa. A hankali murmushi ya subuce mishi.

Ammei da tunda ya kwanta take binshi da kallo ganin sai murmushi yake yasa ta ƙara kallon sa dan tasan abune mai wuya yasa Majeed murmushi. amma yanzu haka kawai sai murmushi yake kamar wanda abashi kyautar wani abun tunda bayi yake ba.

"Majeed lafiya naga sai murmushi kake kodai ka samomin suruka ne wannan murmushi haka".

Saida gaban sa ya faɗi jin Ammei tace yana murmushi dan baima san yana yiba, kasan cewar sa namijin duniya bai nuna mata ba sai kallon ta da yayi tare da lumshe ido cikin shaguɓe fuska yace.

"Ammeiiii".

"Na'am".

"Bafa murmushi nike ba kawai wani abu na tuna shine".
Yayi maganar yana sauke numfashi alamun ya gaji da maganar.
"Humm wai nikam Majeed kaje kuwa Kaduna ka gaida Amma?" .

"Yah rabb" ya fad'a yana dafe koshi kana yace. "Sorry Ammei banje ba amma insha Allah zani"

"Yaushe?".

"Cikin week din nan insha Allah".

"Allah yasa"
Shiru suyi na dan lokaci sai Auta da Ammei ne ke fira can Majeed ya tashi ya wuce wani bedroom din shi dake part din Ammei, da kallo su bishi har shige kai kawai Ammei ta kada su cigaba da hira da Auta.

Koda ya shiga kan bed din shi dake lailaye da white bedsheet ya fad'a tare da lalubar wayar sa number Youseef ya fara kira bugu biyu ya ɗauka cikin girmama wa yayi sallama. Bayan sun gaisa Youseef yace, "boss akwai wani abu da kake bukata ne?".
"Hmmm dama wani bincike nake so kaimin kuma kai da kanka nake so basai wani yayi ba".
"Okay inajinka".
"Akan wata yarinya dake aiki a gidan TV haske a Kaduna ".
Ya idda maganar yana lumshe ido, daga can ɓangaren Youseef tuni ya gane wace boss ɗin nashi kuma aminishi yake nufi amma sai ya basar tare da cewa.
"Okay boss meye sunan ta"

Saida ya sauke ajiyar zuciya kana yace. "Humm S.... Sohfeeyarh". Ya idda maganar yana lumshe ido.

Saida Youseef ya saki ƙaramin murmushi jin yadda boss ya faɗi sunan, kana yace
"insha Allah bani nanda anjima".

Sallama suyi yana gyara kwanciyar sa tare da lumshe ido ya faɗa duniyar tunani.............





____________

*Kaduna ✨*

.............. Shirye-shiryen tafiya gidan Umma Halima nake dan ta matsa kasan cewar bikin saura 2 week's ne inda a ɓangaren MD ma shirye-shiryen suke da mama Hadiza taso naje gidan ta tamin amma kasan cewar umma Halima ta riga ta sai ta hakura.
Nikam tsakanina da Abba muna nan yadda muke in batin gaisuwa dake haɗani dashi, haka su mom da anty Waleeda ba abinda ya ragu saima abinda ya karu, dan kwata-kwata yanzu ba abinda yake haɗani da anty Waleeda saboda biki nata matsowa su kuma sunyi sunyi dai sunga ba abinda ya sauya na daga biki saima shiri da ake yi dan haka sun zuba ma sarauta Allah ido kawai baby ce sai Yah Safwan dan shi bama zaman gidan yake ba.

Kasan cewar yaya Ansar ya dawo shiyasa yanzu sai dai dana dawo gurin aiki ko Islamiyya ina gurin shi wataran ma har fita muke shaƙa tawa.
Yayin da tsakanina da MD soyayya muke mai tsafta da tsayawa arai haka ahalinsa suna nuna min so dan wataran ma da Mennat yake zuwa dan kawai tazo guri na, dan haka shakuwa ce sosai a tsakanin mu.

Tsaf yau na shirya bayan na gama duk wani aiki na gidan dana saba cikin blue Black ɗin abaya na shirya da mayafin ta fari dan yah Ansar yana waje yana jirana. Hand bag d'ita na ɗauka da waya ina shirin fitowa naci karo da anty Waleeda sai cika take tana batsewa tabbas naji zafi sosai amma haka na daure tare da cewa.
"Sorry anty Waleeda bansan kina gurin ba".
Yanda ta bini da wani kallo tsana tare da jan wani shegen tsaki kana tace. "Okay da kike shirin tafiya yawon naki uban wa ki barma yayi miki girki".

Danne zuciya ta nayi kana nace "sorry kin ɓata ba yawo zaniba ziyara zani girki kuma ku bari dana dawo zan dafa muku ku ci tunda ba daɗe wa zanba just 2 week's ne fa". Na idda maganar ina sakin murmushin rainin hankali.
Ba tare dana Jira me zata ce ba na raba ta gefen ta na wuce wata na barta tsaye baki sakeke tana kallo na.
Ina fita dama yaya Ansar na mota yana jirana dan haka kai tsaye mu dau hanyar anguwar Rimi...........✍️


*Taku har kullum da ko yaushe*

🤝*Amanar taurarin writer's association📚*

_*Insha Allah book one ya kusa sauka kuyi hakuri plzzzzz da jina shiru kwana biyu amma insha Allah ko farkon azumi ne zanyi ƙoƙarin karasa muku book 1 bayan sallah in Allah ya nufemu da kaiwa lpy sai a daura da book 2 ina gaya maku yanzu fa za'a fara wasan kudai ku kasan ce dani cikin littafin*RAYUWATA* _Billy pinky✍️*





*Typing📲*

_WhatsApp channel_ 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0

_WhatsApp group_👇




*🌹 RAYUWATA 🌹*

_CREATED AND WRITING BY_

*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞


✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

*T.M.W.A.✍️*



*Amanar taurarin marubuta writer's....✍️*

*TEAM HAZIKAI BIYAR✨*




Page 3️⃣6️⃣➡️3️⃣7️⃣



................horn ya danna baba mai gadi ya buɗe mana mu shiga inda kai tsaye a parking lot a tsaya. Bayan gama dai-dai ta parking fitowa yayi tare da buɗe min kofa. Muka jera gunin ban sha'awa sai cikin parlour bakin mu ɗauke da sallama. Ummi ce sai Buhaisa tare da wata mata fara tar da ganin ta 'yar kwalliya ce, zaune a parlour suna fira cike da farin ciki.

A tare su ɗago suna amsa mana sallama yayin da Buhaisa tazo da gudu tana rungume ni. Murmushi nayi jin tana niyar kada ni, a hankali nace. "Sake Ni kar ki karasa ni dan ba karfi garen ba".
Sakin nawa tayi fuskar ta kwance da murmushi kana tace.
"Kai amarya a hakane har zan kada ke guda nawa nake".
Batare dana ce mata komai ba jin ta ambaci amarya sai ma hannun ta dana kama tare da ƙarasa wa kusa da Ummi. Shikam yah Ansar tuni ya zauna suna gaisawa dasu Ummi, kusa da Ummi na zauna ƙasan lallausan cafet ɗin dake malale a parlour tare da gaida su ita da matar dake zaune a kujerar kusa da ita, inda tuni Buhaisa ta shigar min da kayan dana zo dasu.

Yah Ansar bai wani daɗe ba yama ummi sallama tashi nayi nabi bayan sa domin muyi sallama. Ina fita ya kalleni tare da marairaice fuska. Cikin mamaki nace.

"Yaya nah maiya faru nagan ka haka?"
Kai ya kawar tare da cewa. "Zo ki rakani".
"Amma Yaya nah ina?"
Harara ta yayi tare da cewa. "Bazaki ba dai kenan?" Kallon sa na sake yi kana na shiga dan bana son masa musu.

Bai tsaya ako inaba sai a kofar gidan su Isha. inda tsabar mamaki nama kasa magana saima kallon sa nake inda shi hankali sama yana kan waya da kuma dukkan alamu da Isha yake waya yana shaida mata gamu a waje. Ban dawo daga mamakin dana tafiba saida naga Isha ta fito inda kai tsaye motar da muke ta nufo.

Tafin da yaya Ansar yamin a fuska ne ya dawo dani a tunanin dana tafi tare da cewa. "Kallon fah?"
Kai kwai na girgiza ina sakin murmushi tare da cewa. "Ba komai". Shima murmushin yayi tare da buɗe motar dan tuni Isha ta iso, tare mu fita cikin murmushi ta rungume ni tare da faɗin. "Amarya ce da kanta". Hararar wasa na mata tare da cewa kodai ke.
Murmushi akwai tayi tana gaida Yah Ansar amsawa yayi tare da binta da kallo da ita ma shi take kallo, Inda ni Safiyyah na saki baki ina kallon ikon Allah.

Gyaran murya nayi tare da cewa. "Toh mudai zamu tafi dan yaya kasan halin ummi".
"Sis bazaki shiga ki gaida momy ba?" Isha ta faɗa tana marairaice fuska.

"Kiyi hakuri daga gidan ummi fa muke saboda yaya ya kosa ya ganki ya dakko ni Ko ummi bata san munzo ba amma insha Allah zanzo ki gaidamin ita".
"Tom shikenan sis saina zo". Cewar Isha yayin da yah Ansar dai sai kallon mu yake. Sallama mukai mata kana mu shiga mota dan ya maida ni.

"Hmmm yaya yaushe akaimin wannan ɗan waken zagayen?" Na faɗa ina kallon shi murmushi yayi tare da cewa. "Allah sarki lili sis surprised naso na miki". Ya faɗa hankalin sa nakan titi.

"Wow Yaya naji daɗi sosai kuma hakan shine burina kuma ka cikamin shi nagode sosai".
Murmushi shima yayi dai-dai lokacin da mu iso kofar gidan sallama muyi kana ya tafi ni kuma
Na shige ciki. Inda ummi ke tambaya ta nace mata fita muyi kana take cema matar dake zaune kusa da ita da tun da mu shigo Mu gaisa da ita.

"Toh luba ga tanan zaku iya farawa yau ko sai gobe".
Kallon ta takai kaina tare da cewa.
"Ai ina ganin Hajiya yau kawai zamu fara saboda lokaci, yau saura two weeks kice kuma baza mu kai haka ba kinga kam saidai a fara yau". "Eh hakane Allah ya bada sa'a ke Safiyyah sai kije ki kintsa zuwa anjima zaku fara".
"Tom Ummi"
shine kawai abin da na faɗa na tashi na shiga ciki inda Buhaisa ta tasani a gaba tana min tsiya.
Labari na bata tsakanin soyayyar Isha da Yah Ansar.
"Haba biri yayi kama da mutum danni tuni wallahi na harbo jirgin su tom Allah yasa alkairi saura Yah Saif".

"Ameen yah rabb Allah sarki Yah Saif mun rabu da gaisawa".

"Hmm kedai kawai ki bar Yah Saif inda kika ganshi wallahi".

"Saboda me meke da munsa?"
"Wallahi sopsy ban sani ba amma kamar yana cikin damuwa saidai mu taya sa da addu'a kawai".
Saida na sauke ajiyar zuciya kana nace. "Allah ya yaye mishi abinda ke damun sa". Buhaisa ta amsa da "ameen" kana mu cigaba da wata firar.





_________

*Abuja🤍*

*A A SARAKI HOUSE*


................."Hajiya ya kamata fa mu sauya taku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login