Showing 69001 words to 72000 words out of 84595 words
bane" ta ai faɗa a zuciyar ta ai cikin sauri ta diro a gadon tai kofar fita. Kome ta tuna oho sai kuma ta dawo ta kashe system ɗin kana ta rufeta kafin ta sake fice wa a ɗakin.
Cikin sauri take sakkowa a down stairs tunda kafin ta iso yadda su Ammei su hangota ya basu tabbacin babu lafiya ai basu ma bari ta ƙaraso ba su tashi subiyo ta. Amma banda Mummy Dai-dai tana karsowa ta faɗa jikin Ammei tare da sakin kuka. Cikin tashin hankali Ammei ke tambayar ta "lpy meya sameshi?" Cikin kuka take ba Ammei amsa da, "Ammei yana kwance cikin duhu da alamama baya numfash.....i" kasa ƙarasa wa tayi saboda sakin ta da Ammei tayi ta bi bayan su Zaituna dan sune a farkon fara wucewa jin batun Auta.
Yanda Auta tabar shi haka su same shi aikuwa ko numfashi bayayi cikin tashin hankali Ammei ta haye kan Royal bed din da yake kwance kansa dake a pillow ta maida kan cinyar ta tana hura mishi iskar bakin ta yayin da tuni Addah ta nufi compood domin kiran doctor Fadil dan bata majin yana cikin gidan. Cikin Sa'a kuwa ta same shi dan shigowar sa kenan ɗaukar wasu takardu daya manta dasu zai wuce ai nihin hospital din da yake aiki suci karo da Addah. Ganin ta cikin tashin hankali ya nufi ta yana tambayar ta lpy ita cikin sauri take bashi amsa yazo Majeed ba lpy.
Baima tsaya wata magana ba ya koma cikin hospital din dan dakko kayan aiki bai ja wani dogon lokaci ba yabi bayan ta zuwa part ɗin nasa ta wata kofa inda kai tsaye can zaka nufa. Koda su ƙarasa lokacin Mummy ma tashigo dan shirin nasu yayi yawa shiyasa ta biyo su, umarni ya basu dasu ɗan fita su bashi guri zai duba shi, babu musu su fito har Ammei da kansa ke a cinyar ta. Ya kai kusan 1 hours sannan ya fito fuska da damuwa Zaituna da Auta ne su fara shiga ɗakin kana sauran yan matan subi bayan su. Ammei ce tace, "ya jikin nasa Dr Fadil". Cikin sauke ajiyar zuciya yace, "Hajiya ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane amma dai zamuyi magana da Alhaji insha Allah, zan aiko da magungunan da zaisha yanzu na masa injections tare da drip. Daya kare sai a cire mishi insha Allah zai samu sauki". Shiru tayi tana kafeshi da kallo na wani lokaci kafin tace, "Allah yasa inajin yau ma zai shigo". Daga haka cikin ɗakin nasa ta koma inda ta tarar dashi kwance hannun sa sanye da drip irin babban nan da alamu ya samu bacci dan sai ajiyar zuciya kawai yake sauke wa fuskar nan tayi fayau irin na mara lpy. Daga can gefe ta koma ta zauna dan su Addah da Mama duk suna a kusa dashi ne inda cikin dattakon ta tace ma Auta' "Auta maza kije ki faɗa ma Hajja Yayan ku bashi da lpy dan kar ayi lefi" da "toh" Auta ta amsa kana ta tashi Basma tabi bayan ta su fice a ɗakin.
____________🖤
A ɓangaren granny kuwa tana can tana faɗa wai yau kwata-kwata Majeed bai shigo ya gaishe ta ba Mama Rabi na bata hakuri amma bata fasa ba, shigowar su Auta da Basma baisa ta dena ba sai ma harara data bisu daita. Gaishe ta su fara yi kana su gaida Mama Rabi inada granny ta amsa tana ɗauke kai kace Majeed ɗin ne a kusa da ita. Kana cikin faɗa tace, "Lafiya kuzo ku zauna fuska ba annuri gaba ɗayan ku? Atoh ni kunsan bana son wannan ɗan iskan miskilancin da wancan yake neman ya koya muku, inba hira ya kawo kuba ku tashi ku bani guri kafin na fatatta ke ku". Ta idda maganar tana kwafa cikin sanyin murya Auta tace, "Kai granny Yah Majeed nefa yau kwata-kwata bai fito ba toh shine Mama tace naje naga ko lafiya toh d nake sai natarar dashi baya numfashi.....".
"Innalilahi wa'inna ilahiri raji'un nashiga uku ni Maimunatu sumafa kice abdulmajidun?" Granny ta jehoma Auta tambaya Basma ce tace "Eh granny amma doctor ya duba shi yanzu haka ma yasa mishi drip maybe Around 11 ya kare." Granny da tayi shiru tana sauraren su Basma saida takai aya kana cikin sanyin jiki tace ma Auta "jeki ɗakko min mayafina naga halinda jikana ke ciki". Da "toh" Auta ta amsa kana ta shiga cikin bedroom din Bata fi 3 minutes ba ta fito ruke da mayafin granny sawa kawai granny tayi kana ta fice su bita a baya.
Koda su ƙara sa kuka granny taso farawa Addah ta lallashe ta tare da cewa su fita su dan bashi guri yasha iska kar motsinsu ya tashe shi, hakan kuwa akayi dan gaba ɗaya ma parlourn su koma yayin da Mummy ta koma ɗakin ta ya zama saura Mama da Ammei da granny sai su Zaituna Addah kuma taje kitchen domin haɗo masa abincin kafin ya tashi. Jefi-jefi Auta ko Zaituna kan leka wa koya farka amma dai har lokacin bai farka ba ana haka saiga Youseef yazo, dan tunda yaji boss din shiru yace maybe tafiyar nan bazata yiwu ba gashi yaita kiran wayan sa ba'a picking. Aikuwa koda Ammei ta sanar masa bashi da lafiya ba ƙaramin tashi hankalin sa yayi ba dan sam bai kaunar wani abu ya taɓa masa boss ɗin nasa. Shiga yayi har lokacin bacci yake bai farka ba dan haka bai wani daɗe ba ya fito.........................
_________________🖤🤍
*Kaduna ✨*
...............A gidan Ummi fah kowa ya kama gaban sa sai ƙalilan na 'yan matan da basu tafi ba suma kuma shirin tafiya gidan su Safiyyah suke yi, hatta Ummi itama can zataje dan da tace ita bazata waccan gidan ba a gidan ta zatai na taron a matsayin ta na uwar amarya. Toh amma Abba ya zaunar da ita ya mata nasiha mai ratsa jiki da nuna mata mahimmancin yin bikin acan tunda hatta ma ɗaurin auren ta acan yake. Tabbas nasihar ta shige ta dan ta gano duk abinda mijin nata ya faɗa gaskiya ne, da isha'i Yah Saif da Yah Ansar zasu maida su can.
Ta ɓangaren Amarya kuwa tun bayan tashi a Kamu ciki ta koma itada Luba domin shirin tafiya gidan su Safiyyah. Bayan gama shirya ta cikin wata bak'ar abaya da ama kwalliya da fararen stones haka shima takalmin ƙafarta baƙi ne sosai tayi kyau sai uban kamshi take yi kamar ba dareba. Gurin Abba Ummi ta kaita aiko Abba ya mata nasiha mai ratsa jiki dan ba abinda take sai kuka dan jin Abban su Buhaisa take kamar nata Abban, bayan gama mata nasiha kana ya ɗaura da kwantar mata da hankali da nuna mata muhimmanci aure da kuma hakuri, danshi aure sai anyi hakuri komai ma a RAYUWAR nan sai kayi hakuri kawai zaka ci ribar zaman duniya.
Yayin da tuni Yah Ansar yazo dan haka shida Yah Saif suka kwashe su sai gidan su Safiyyah. Dama tun bayan gama Kamu su mama Hadiza su tafi can gidan ɗin aikuwa suna zuwa da kanta ta buɗe ɗakin Ummah (maman su Safiyyah) su gyara shi tsaf kamar da mutum dan komai na Ummah ya nan ba abinda a ɗauka amma saidai ba mai shiga ɗakin dan ko Mom tayi mitar amma ta hakura shi kanshi Abban ba shiga yake ba. dan tace anan su Ummi zasu zauna da Amarya. aiko abin yama Mom zafi dan sai habaice-habaice take yarwa, su kuwa suyi kunnen uwar shegu da ita su fara shirin ɗaura girki dan tarbar su Ummi a cewar su yanzu basu da lokacin ta sai an ɗaura tukun na.
Aiko anan aka sauke su Ummi har hawaye ta share dan kace yar uwar tata tana a gidan ne. Kasan cewar dakin two bedrooms ne a ciki sai parlour dan har dakin Mom shima haka yake, hakan da mama Hadiza tayi kam yasa Ummi jindadi dan dakin zai ishesu yadda suke so kasan cewar itama nata bakin na nan tafe gobe yanzu daga ita sai anty Hajara ne sai Luba sai kuma ƙawayen su Safiyyah sai su Isha da Buhaisa. Abinci a kawo musu mai rai da lafiya yayin da Safiyyah take jinta kamar ba ita ba dan komai ji take ya sauya mata wai yau ita ce amarya ita abun ma saitaji sa kamar wani al mara toh amma wannan kaɗan daga cikin hukuncin ubangiji. Sanda Mom taga Safiyyah saida zuciyar ta ta motsa, dan sak yarinyar ta koma uwar tane aiko ko gaisuwar da Safiyyah take mata bata amsa ba tai waje fuuuu kamar zata tashi sama.
Number Murja ta nemo tare da danna mata kira bugu biyu t dauka hira suke ƙasa-ƙasa dani kaina banjin me suke cewa kana ta yanke tana sakin wani makirin murmushi..............
_________________🖤🤍
*Abuja 🤍*
Around 11am Majeed ya farka lokacin drip ɗin saura kaɗan ya ƙare, a kuma dai-dai lokacin suke shiga gaba ɗayan su dan ganin ko drip din ya ƙare, ganin yadda yake buɗe ido tare da lumshe wa ya tabbatar masu daya farka, aiko cikin farin ciki su ƙarasa gare shi kowa na jera masa tambayar ya jikin nasa. Ido kawai ya lunmshe kana ya buɗe ba tare da yace komai ba ya yunkura, jin kansa yake ya masa nauyi dan har yanzu yana jin ciwon kan ƙasa-ƙasa. Youseef ne ya jawo fillo ya jingina da fuskar gadon kana shi kuma ya jingina bayan sa. Hannu yakai zai fizge drip din Ammei ta rike hannun tare da girgiza masa kai, fuska ya shagoɓɓe kamar zaiyi kuka Mama ce tace "haba Majeed Please ka barshi ya ƙarasa". Ba tare da yace komai ba ya koma jikin fillon ya lafe tare da lumshe ido.
Cikin yan mintuna drip din ya ƙare bayan Youseef ya cire maa drip ɗin taimaka masa yayi ya mike domin watsa ruwa yayin da tuni Addah tasa Finnat haɗa masa ruwan wankan, kai tsaye bathroom ɗin su nufa a dai-dai kofar bathroom din Youseef ya tsaya yayin da shi kuma ya ƙarasa da kansa.
Gaba ɗaya fita suyi a bedroom din su koma parlourn ƙasa yayin da akabar Auta tana gyara masa ɗakin sai Zaituna da taki fita a cewar ta zata taya su. Harsu gama bai fito ba dan haka Auta ta kama hannun ta su fice.
Fitar su ba daɗe wa ya fito sanye cikin bathrobe ash color inda kai tsaye colose ɗin sa ya nufa. Tsaf ya fito cikin jallabiya fara tar sai wannan farin mayafin Irin na Larabawa da suke sawa musamman in sun sa farar jallabiya. Tsaf ya fito kam gaban mirror ya matsa bayan ya gama ma kansa barin fitinannun turarukan sa masa masu mukar daɗi ga sumar sa datasha mutukar gyara ta kwanta a gadon bayan sa kace balarabe ne tsaye a gaban mirror. Fuskar sa tayi fayau irin na mara lafiya. Kai tsaye parlourn ƙasan shima ya nufa zaune ya samu su a parlourn inda tunda ya sakko shi su zuba ma ido fuskar su fal mamakin shi, mutumin da bashi da lafiya ne ke cikin shirin tafiya masallaci, duk dai da shi dama haka yake komai ciwon da yake mutukar zai iya tashi yayi tafiya toh fa ba abinda zai hana sa zuwa masjid.
Sannu su ciga ba da jera masa inda hannu kawai ya ɗaga musu kai tsaye kusa da Ammei ya nufa tare da ɗaura kansa a kafadar ta inda yake magana ƙasa-ƙasa dan shi kowa yasan indai yana ciwo toh fah a zumin magana yake. Ammei ce ta umarci Auta data haɗa masa abincin saboda ko karya wa baiyi ba. Nuni tayi masa da dinning area akan yabi bayan Auta fuska ya shagwabe kamar zai kuka inda ita ma ta daure tata fuskar tare da ɗauke kanta, dolle yasa yabi bayan Auta shidai Youseef na boye dariya. Koda ya gama cin abincin sallama ya musu domin ta fiya masjid addu'a sosai Ammei ta bishi da ita inda dai-dai zai fita yaci karo da granny. Baya taja tana ƙare masa kallo daga sama har ƙasa kana ta fara tambayar sa shida bashi da lpy ina kuma zashi amsa Youseef ya bata da masjid zasu aiko fah nan ta fara faɗa yadda ta shiga ba nan take fita ba shiko Majeed tuni yayi gaba abin sa. Shima Youseef bayan wayan daya mata yabi bayan sa inda tuni driver ya fito da dalleliyar sabuwar motar da zasu tafi da ita.........................✍️
Typing📲*
_Follow my WhatsApp channel_ 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0
_Follow my WhatsApp group_👇
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_CREATED AND WRITING BY_
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION ✨*
*T.M.W.A✍️*
*Amanar taurarin marubuta writer's.......✍️*
*TEAM HAZIKAI BAKWAI 💪✨*
Page. 4️⃣4️⃣➡️4️⃣5️⃣
...............*RANA BATA KARYA INJI MASU IYA MAGANA SAI DAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA* Na yarda da batun masu hikimar zance. Domin kuwa nima da kaina na yarda wannan rana tawace kam. Sannan in har Mom na amsa sunan uwa a gareni to taji kunyar kuwa. dan ko yau take Jumma'at ranar da donbin mutane da yawa ke so da jinkirin jiran zuwan ta toh yau fah gashi Allah yayi. Kowa ka gani na dangin na wannan ranar ya tashi ne cikin farin ciki inka cire Mom da ita da maƙaraban ta dan a kallo ɗaya zaka mata ka gano tsantsar tsagoron hassada a shimfide a saman tam fatsetsiyar fuskar ta da kwata-kwata a cikin ba alkairi.
Misalin ƙarfe 10 daka shigo anguwar dole ka shaida ana biki danfa ta fara cika, dan ma ɗaurin auren sai bayan an saukko daga sallar juma'a za ayi. Amma duk da haka anguwar ta cika haka gidan ma ko ina cike da mata. Ɗakin Ummi aiko cike yake da baki manyan mata wanda daka kalle su kasan eye lallai nera tayi kuka a jikun nan su dan yadda Ummi take yar gayu yar kwalisa haka mutane nata suke.
Daga can tsakar gida kam taro yay taro gida ya kacame da hayaniya irin ta biki, anan ɗakin ƙawayena na zagaye dani. Wasu na hotuna wasu na kwalliya, dan yan gurin aikin mu su min kara sosai wasu daga cikin su duk sun zo, wasu na hirarsu akan batun dinner da za'ayi bayan an kai amarya. Dan can gidan su Suraj ɗinne suka shirya. Luba ce da Mamy (maman Isha) su sani na shirya bayan wanka dana sake sha da wasu turaruka Allah ni kaina na fara gajiya da kamshin nan yayin da su Buhaisa sai yabawa suke. Tsaf a shirya ni cikin wata fitinanniyar shadda Read color dataji uban aiki ga wasu stonos sai walwali suke yadda ɗin kin ya zauna daram a jikina zaka tabbatar da eh lallai nera tayi kuka, dan ko kusan yadda Jan abu yake ma fara fata kyau. Ga wani fitinannen ɗauri da ta kashe minshi mutukar zaunuwa ɗaurin ya zaunu, fannin sarka da 'yan kune da bangles ba'a magana sai plat shoe da shima ya kasance Ja mai shegen kyau da tsada dana sa aiko ba karamin kyau ya sake yiba kasan cewar jan lallin dake zane radam a ƙafa ta sai bakin daya kasance kadan, wani irin mayafi ne shima daya kasan ce Ja mai shara-shara sai fararen Stones dasu mishi ƙawanya inda kai tsaye a kaina a ɗaura min shi amma bai rufe fuska ba andai sakaya minshi ajikin ɗaurin da akai min. Aiko na fito fes dani kamar fure a tsakiyar lu'u lu'u. nan take hasken Camera na waya ya shiga kaikawo akaina hatta mai kwalliya tamin pics iri-iri nikam araina ji nake kamar na fisge wayar na goge su. Nan take wasu suce sai sun tura ma ango ciki koh harda Buhaisa ban tanka musu ba sai murmushi kawai d nake yi dan lokacin tuni su Mamy sun fice da gani sai ƙawaye na dasu sani a tsakiya tabbacin daka shigo zaka sheda amarya sai kuma mai makeup da itama sai gobe zata koma Abuja saboda Luba ta dakko tane har sai bayan an gama biki zata koma. Shiyasa itama tana cikin jerin ƙawayen Amarya kafin lokacin kuma dinner.
Kiran da Yah Ansar yazo yamin ne ya sakani saka gyale na rufe har fuskata. Shine ya kama hannuna har falon baƙi. Tunda muka fito kuwa gidan ya sake ruɗewa da buɗe-buɗe. Ni dai kaina na ƙasa a cikin gyale dan haka kawai sai naji ina jin kunya kowa.
Ban ida daburcewa ba sai da muka isa falon baƙi. Dan ganin kaf kawunaina na ɓangaren uba harda Abba da Abban su Buhaisa. Sai gwagganni da innoni suma dai duk suna nan na kusa sosai, saboda a gaskiya ta dangin Abba muna da family sosai. A tsakkiyarsu Yah Ansar ya zaunar dani ƙasan carpet. Shima sai ya nema waje ya zauna.
Kawu Bala ne ya