Showing 45001 words to 48000 words out of 84595 words
d'aya bata kalleshiba wlhy bare tasanma kalarsa.
“humm aiko wlhy inabata kalleshiba anyi babu ita kuwa, ruwa ta shata kuma, yo kobabu komai aina bada koda labarine nace nata6a ganinsa ido da ido ko”. ‘cewar Ihsan’.
Dariya kawai Buhaisa tayi, su cigaba da firar su inda suka tsaya.
inda ni ciki ma nashiga na kwanta dan kaina wani irin ciwo yakemin dama tunda na tashi yau nakeji gabana na faɗuwa.
*Washegari*
Muyi sallama da Abuja inda dakyar aka ɓanɓaremu ajikin anty Hajara dan haka mu barota tanata kuka danma Yah Ahmad yana gidan, toh mumu dai haka muke shiru kamar kurame har mu isa Kaduna. Dan Isha ko gidan Ummi bata shigaba tace wallahi gida tayi to muma bamu takura mata ba muyi sallama mushige ciki. Inda mu samu duk bakin sun tafi sai ƙalilan na nesa nima dai yau maso tafiya amah Ummi ta hana tace na bari sai gobe. Kasan cewar gaba da magrib mu dawo sallah kawai nayi sai karatu ina zaune akan sallaya har a kira isha'i na tashi na gabatar daganan ƙasa na sauka muyi dinner inda su Yah Saif su dawo musha fira daganan mu wuce mu kwanta.
*In the evening*
Sanye take saukowa cikin abaya pink sai mayafin ta White da nayi rolling ƙaramar hand bag pink ce a hannu na sai plate shoe pink mai gashi-gashi asaman sa waya kare a kunne ta tana waya da Isha. Buhaisa riƙe da ƙaramin akwatin ta a hannu fuskar nan a haɗe Safiyyah zata tafi ta barta. "Eh kijirani yanzu in zamu wuce da Yah Ansar zan biyo muyi sallama" shiru tayi na wani lokaci kana tace. "Okay saina zo" dai-dai suna ƙara sawa parlour inda Yah Ansar ke zaune shida Ummi suna fira yana jiran ta fito su tafi.
Zama muyi muna gaisawa da Yah Ansar Ummi ce ta kalli Buhaisa data haɗe rai tace. "Ikon Allah Safiyyahn zakibi ne dakike niyar sakin kuka" cikin tura baki gaba tace "yanzu fissabilah anty Hajara ta tafi itama Safiyyah danake gani take ɗebe min kewa itama zata tafi ni Allah Binta zanyi".
Dariya Ummi tayi tace. "Aikuwa baki isaba nikuma kibarni dawa Saifu da inya fita aiki sai an ganshi baki ba Hajara to bazai yiwu ba. Indai Safiyyah ce tama kusa dawowa nan da zama tunda bikinta ya taho nanda wata ɗaya ne dan bazan barta agun waccan matar ba wallahi dan ba uwar da zata tsinana mata". Takai ƙarshen maganar ranta bacce.
Mudai shiru muyi batare da munce komai ba har ta gama sai Yah Ansar ne ya bata baki sallama muyi mata mu tafi Buhaisa kam harda hawaye tonima dai yau ta sani kukan. kai tsaye gidan su Isha muje da take jirana.
Har ciki na shiga nabar Yah Ansar a mota yana jirana, koda na shiga mu gaisa da Momyn ta inda tashiga ta kiramin ita, bangajiya na mata muyi sallama nace. "Kinga Isha bari na tafi Yah Ansar na mota yana jirana kizo muje ku gaisa". Murmushi tayi kana tace "a'a ki gaidamin da shi ba saina fita ba" galala nayi ina kallon ta kana nace. "Lallai ma wai ni dan Allah meke tsakanin ki da Yah Ansar ne naga sai wani kunyar sa kikeji anya kuwa Isha". "Uhmm kinga tashi muje dan Allah karkimin wata fassarar Mrs Md"
Sallama nayima momy kana mu fita saida na fita nake cewa. "Can muku dai intai wari maji". "Bama zatai ba ai balle kuji". Dariya kawai nayi batare dana ce mata komaiba har mu iso inda motar sa take, tunkan mu ƙarasa ya zubeta da kallo dan saida ta gaishe sa kana ya ɗago yana amsawa murmushi kwance a fuskar sa. Nidai murmushi nayi na shiga ina jiran su gama gaisawa yazo mu tafi. Gida ta koma mukuma mu dau hanyar gida.
Koda mu isa gidan nayi a haukace yake kamar wanda yayi wata ba gyara sai can daga gefe akwatina ne dasu sweet, dasu alawa, da drinks, harda su biskit, a watse a ƙasa dukkan alamu kayan sa ranane da'a kawo shine aka wulaƙanta su haka. Yah Ansar ya buɗe baki da niyar yin magana saiga baby nan da gudu tazo ta rungume ni. Tana min oyoyo shine take cewa ai kayan sarana nane da'a kawo shine mom Bata taɓa ba ta barsu a gun, bance mata komai ba sai Yah Ansar ne ya fice na leka ta window naga motar shi ta fice a gidan. Nima kota kansu banbi na shige bedroom,
"Yah rabb" shine abinda na furta ganin bedroom ɗin kamar anyi danbe a cikin sa kaina har juyawa yake saboda na tsani naga guri da datti koya yake. Dama nasan za'a rina amah banyi tunanin dattin zakai hakaba.
Kitchen na nufa na ɗauko kayan shara, da bedroom na fara kana nazo parlour jin gidan shiru yasa nace koh mom bata nan ne, bayan nagama share gidan gaba ɗaya bathroom na shiga shima na wanke shi abin haushi wai hatta pad ankasa d'auke wa saidai duk sanda na dawo na ɗauke. Haka na gama wanke wa tsaf na fito na fara mopping ina cikin mopping ɗine saiga su mom nan itada Anty Waleeda kodaga ina suke oho. Ko gaisuwar danake ma mom bata amsa bamin sai ciki su shige abinsu duk su batamin mopping din dana gamayi ga bayana ya gaji ga ciwon kai banbi takan gunda su bata ba nashige bedroom wanka nayi tare da dauro alwala. Inda anty Waleeda ta shigo sai habaici take zubarwa ban kalleta ba na tada salah.
Bayan na kintsa cikin kayan shan iska na fita parlour saiga Yah Ansar nan shida Mama Hadiza ashe wai can yaje ya ɗauko ta. Kakace a wajenmu, dan ƙanwar kakarmu ce, mahaifiyar su Abba kenan. Ba sosai take zuwa gidan ba saboda wulaƙancin da Mom ke musu. Mu kuma Abba baya barinmu zuwa wajenta, garama Yaya yanzu daya mallaki hankalin kansa yana zuwa abinsa. Nayi murna ƙwarai da ganin mama Hadiza. A take na shiga hidima da ita dan naga alamun mom ko ruwa bata bata ba. Duk da hararar da Mom ke mun banbi takanta ba na shiga hidima da kakarmu. Bayan sallar isha'i kuma Yaya ya sayo mata kayan ƙwaɗayi yazo ga zauna muka sha hira. Dan dole Abba ma yazo ya zauna akayi da shi shima. Mom da anty Waleeda kuwa kowa yay shigewarsa ɗaki sai baby kawai a wajen. Bamu tashi a falon ba sai sha biyu. Abba ko tun sha ɗaya matarsa tazo ta tasashi suka shige ko kunyar mama Hadiza bata ji ba balle mu ƴaƴa. Gado nabarma mama Hadiza su kwanta itada Anty Waleeda Ni kuma na shinfiɗa bargo na kwanta. Sabuwar hira muka buɗe da ita har sai ɗaya sannan barci ya kwasheta. Niko alwala na tashi nayi nai nafilfilina kamar yanda na saba sannan na kwanta. Hakan kuma bai hanani tashi uku da rabi ba na shiga ayyukana. Kafin kace mi na kammala, dan har abinci naima mama Hadiza na saka mata a kula nakai ɗaki dan nasan ba lallai da rana a bata na kirki ba. Gashi ban dawoba lokacin. Kalacin ma isashe na ɗiba mata. Itako tanata mitar yanda nake wannan uban aiki ga fitar safe kuma. Ni dai bance komai ba face murmushi kawai. Yau kam Yah Ansar ya shigo gidan domin gaisheta. Ya ajiye mata kayan shayi da ƙaton bread ɗin ta harda soyayyan ƙwai. Albarka ta dinga saka mana sannan mukai mata sallama muka wuce dan kar mu makara.
◾Mama Hadiza itace ta raba komai na kayan sa ranar nan. Har maƙwafta sai da tasa Baby ta kai ma kowa gida-gida. Sannan dangin su ta ƙulla na kowa daki-daki. Wanda ke anan cikin Kaduna ta saka Yah Ansar ya kaita ta kai ma kowa. Na dangin Ummah kuwa har gida tasa Yah Ansar yakaita ta kaima Ummi. Yah Ansar ma da Yah Safwan ta ɗiba musu. Nima komai sai da ta ɗiba min. Hakama jama'ar gidan kowa da nashi. Kuma kowa zai iya rabama abokan arziƙinsa idan yaso. Amma sai Mom tai biris da nata anan falo har Yah Ansar ya maida Mama bata ɗauke ba daga ita har ƴaƴanta. Abba dai ganin mama Hadiza yasa shi zama ya ƙuƙƙula ya fita dasu wai zai rabama abokansa da ƴan wajen aikinsu. Ya raba ko bai raba ba oho masa.
◽A ranar da nakai ma ƴan office ɗinmu kowa ya sake sanin alaƙata da Suraj wato MD, dan wasu basu ɗauka gaske soyayya muke ba saboda yadda muke taka tsan-tsan dan shi yama rigani rabawa dan iya yan officer ɗin mu kawai ni na bama.
*Abuja🤍*
........"Dama Mummy turaren da kika bani ba mai kyau bane ba batin kince ina sawa indai yaji ƙamshin shikenan zai fara sona"
Zaituna ce ta tasa Mummy a gaba tana tambayar ta kamar zatai kuka.
"Me kike nufi ne Zaituna kina nufin baku haɗu bane ko baki sabane eye".
Tai maganar cikin zaro idanu, itama Zaituna cikin taɓe baki tace. "Wallahi Mummy nasa dan saida naga fitowar sa ma nima nasa kuma daga gun kaitsaye gurin sa na nufa amah Mummy karkiga irin wulaƙancin da yamin" ta kai ƙarshen maganar tana fashewa da kuka.
"A'a wallahi da sake dan nasan Sakeenat bazata min karya ba akan turaren inma ya kasance karya ne wallahi tamu ce nida ita jeki dakko min turaren dakisa nagani". Ba musu Zaituna ta nufi ɓangaren su domin ɗauko turare, saboda yanzu Mummy ta bar part ɗin granny ta koma part ɗin ta.
Koda ta kawo mata wata ashariya Mummy ta mulmulo tana sakin turaren ya faɗi ƙasa ya tarwatse, cikin hargagi ta ɗago kamar zata daki Zaituna. "Uban wa kika nuna ma sanda na baki, kinsan kuɗin dana kashe kuwa akansa kanna same shi shine zaki bari har a canza da wani?". Zaituna data ji tsoro ganin Mummy a haka dan koda wasa bata taɓa zagin taba sai yau aikuwa tasan ba ƙaramin kuɗi ta kashe ba dan Mummy bata da hakuri akan kuɗi. "Mummy Allah sanda na ajiye shi bakowa a ɗakin kuma Allah ba wanda yasan na ajiye shi". Mummy cikin sauke ajiyar zuciya ta zauna a gefen gado tayi shiru na wani lokaci tana kallon Zaituna kana tace.
"Kibari zanyi bincike akai duk wacce naga da hannun ta aciki wallahi zan dau tsatstsaura. Mataki akanta. Nasa an kawo min shine saboda naga Yaya ya share magana ta kamar suna tsoran Majeed ɗin shiyasa nake so nayi maganin sa da kaina dan duk sanda yazo hannu na humm". Takai ƙarshen maganar tare da sakin makirin murmushi. Zaituna ba tayata.
Azizat dake bakin ƙofa alaɓe tana jinsu tai wani shumin murmushi tare da cewa. "Ai Wallahi muddin inanan bazan bari ki auri Yah Majeed ba" tana gama faɗa ta wuce part ɗin granny....
⚫ Ɓangaren Majeed kuwa tun da subar Mall gurin meeting su wuce inda dukkan tunanin shi yana gun wannan yarinyar daya rasa ina ya taɓa ganin ta. Daya ga yana takura ma kansa dan shi mutum ne wanda bai shiga abinda bai shafesa ba dan haka ya fige tunanin ta arai har su isah gida amah jefi-jefi takan faɗomai arai dan har Youseef ya lura da hakan. Bai zarce ko inaba sai part ɗinshi dan bebi ta babban parlour saboda yasan yanzu parlourn cike yake da 'yan matan gidan. Youseef biye dashi hannun sa riƙe da wasu Golding din leda mai dauke da tambarin Mall ɗinshi har su isha parlourn sa na kasa. Zaman su ba daɗe wa bayan ya sallami Youseef akan yaje ya ɗan huta saiya dawo shima ya tashi ya nufi bedroom, Kai tsaye bathroom ya shiga ya dau kusan 40 minutes kana ya fito sanye da bathrobe blue color hannun sa ɗauke da ƙarami yana guge kwantar ciyar sumar sa dake kwance har gadan bayansa. Bayan ya gama komai na al'adar rayuwar sa haka zalika ya shirya cikin kayan bacci farare tas ga ƙamshin dayake kamar ba dare ba ya fito parlour saboda yau bazaiyi dinner ba. Waya ya ɗauko ya shiga kiran granny bugu ɗaya ta dauka. Jin shiru yasata cewa. "inbaka da abin faɗa ne zan kashe waya ta kana cinye min kati ehe"
Yanda tayi maganar saida yasa shi sakin ƙaramin murmushin gefen baki kana ya motsa bakin sa kadan kamar mai tsoran ajishi yace. "Please granny kiba wani ya kawomin madara" yakai ƙarshen maganar da alamun ya gaji dan da gani bayasan doguwar magana. Granny data taɓe baki daga can tace. "kasan banson wannan turancin naka dan Allah meye wani filis kace ne komai nifa in bazaka fito kayi magana ba zan datse kirana". Tana wani ballama wayar harara kamar yana gaban ta. Zaituna dake kusa da itadai sai kunshe dariya take ga wani farin ciki da take ciki na zataga rabin ran nata dan yau tun safe bata ganshi ba. Daga ɓangaren Majeed kuwa hannu yakai kansa dake dan masa ciwo kaɗan-kaɗan tare da jinjina rigimar granny da sarai yasan ta gane me yake nufi amah ta basar. "Humm in bazaki bani bane nasa anemo minla wani wajen ke komai sai kin ma mutum gori". Kasan cewar yasan hakan ne kawai zaisa ta kyale sa shiyasa, aikuwa granny cikin zaro idanu tace. "Rufamin asiri ni Maryamu ace na hana jikana guda ɗaya madara yo Allah na tuba meye wata madara? Bari nasa a kawo ma yanzu". Ba tare data jira me zaice ba ta yanke kiran. Murmushin gefen baki yayi kana ya jawo wayar sa yana da nawa.
..........Zaituna ce tace. "granny kawo na kaima Yaya madarar dan nasan yana can yana jira yau koda ya dawo bai shigo babban parlour ba". Tunda Zaituna ta fara magana har ta gama granny kallon ta take cikin taɓe baki ta fara kwalla kiran sunan Rabi'ah". Cikin nutsuwa mama Rabi'ah ta fito daga kitchen ta ƙarasa gurin granny. "Dama zance ne kiɗan zuba ma Abdulmajeedu madara ni kafar nan ta matsamin basan tashi dan Allah a kula sosai".
Da "to" mama Rabi'ah ta amsa tana wuce wa kitchen, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama haɗa ta ta kawo granny, Zaituna ta umarta data Kai masa tare da zuba mata gargaɗi.
Kai tsaye part din ta nufa yana zaune a kujerar yayi crosing ƙafarsa ɗaya akan ɗaya da ganin sa duniyar tunanin ya faɗa. Dan saida ta ajiye a ƙaramin table ɗin dake tsakiyar kujerar da yake takai zaune ƙasa kusa da kafar sa tare da kure kyakkyawar fuskarsa da kallo. Jin kamar motsi kusa dashi yasa shi buɗe idanun sa a hankali yana binta da kallo dan bata masan ya buɗe idon ba dan ta lula duniyar tunanin. Tsawar daya daka mata ne yasa ta firgigit ta dawo daga tunanin data fada tana kwabe fuska, ta buɗe baki da niyar magana ya daura hannun sa asaman labban sa tare da nuna mata kofa. Sanin halinsa da baya son musu yasa ta fita da sauri hawaye na zubowa a idanun ta, kai kawai ya girgiza kana ya haura sama domin wanke bakinsa sbd zaisha madara. Bai dadewa ya dawo ya zuba a ƙaramin mug yana sha a hankali, cikin lokaci kaɗan ya gama sha ya koma kan laptop yana danna wa kafin Youseef yazo. A hankali yake jin bakon yanayi a kansa tun yana daure wa ya daiji abin bana wasa bane ya tashi a hankali zai nufi bedroom jiwa ta kwashe shi ya zuɓe a ƙasa.
Matar dake labe a bayan kofa ta saki wani makirin murmushi da sauri ta bar part din.................................✍️
(Toh fah🤔🤔 inji mai tallan totuwa a birnin totoh🤨)
*Taku har kullum da koh yaushe*
*Billy pinky💞*
Typing📲*
_WhatsApp channel_ 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0
_WhatsApp group_👇
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*
*T.M.W.A.✍️*
✨✨✨✨✨
💪😊
*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*
✨✨✨✨✨
💪😊
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_CREATED AND WRITING BY_
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞
*Amanar taurari writer's asso..✍️*
Page 3️⃣2️⃣➡️3️⃣3️⃣
................ Youseef ne ke shigowa part din shida Samuel kasan cewar neman da boss ke musu tunkan su ƙaraso cikin parlour su hango kamar mutum kwance a ƙasa. Cikin tashin hankali su ƙarasa inda su tarar da Majeed kwance a ƙasa ga wata kunfa dake fitowa a bakin sa danko motsi bayayi.
Cikin tashin hankali Samuel ya nufi shi yana kiran boss, shiko Youseef da kingan sa yana cikin tashin hankali ya shiga kiran doctor ɗin gidan ring biyu tayi ya dauka.
Ba tare daya jira mai zaice ba ya fara bashi ummarni, doctor fadil jin yadda Youseef ke magana cikin tashin hankali yasan ba ƙaramin abu bane ya sami Majeed.
.........cikin ƙan-ƙanin lokaci saiga su doctor fadil da gadon nan da ake daukar marasa lafiya, shida sauran doctor's din. Sunyi shiga ɗimuwa ganin halin da Majeed yake ba ɓata lokaci su nufi hospital din dake cikin gidan dashi, babban hospital ne acikin gidan dan koh wani asibitin ma albarka ga kwararrun ma aikata masu jajayen kunnuwa Hausa wan kaɗan. Kai tsaye Emagency aka nufa dashi domin bashi temakon gaggawa dan tuni gabar ta fara aiki ajikinsa kasan cewar ta