Showing 18001 words to 21000 words out of 84595 words
zuboma kofar ido harna karasa ina gaida mom,
"Abin mamaki saida na ta'bata ta d'ago firgigit.
Kuma ta amsamin harda tambaya ta yasu ummi,
Amsa wa nayi ina gaida yah safwan shima dai amasa wa yayi tare da cewa ina kishiga ne safiyyah?
"Naje gidan ummi ne .
"Oooh shiyasa abincin ma sai anga dama akeyi a gidan kenan?
Bance komai ba na tashi na nufi anty Waleeda na rungume ta, duk da tana tureni amah ban damu ba dan ba karya nayi kewar su.
Yadda nai tsam mani hakan ce ta kasance Dan parlour dai sai addu'a wallahi.
Ina mamakin san jiki irin na mom da anty Waleeda.
"Bedroom nashiga na barsu da mamakin dawo wata, dan itafa mom batai tsammani zan dawo ba.
To shima dai bedroom din sai addu'a dan yama fi parlour datti,
Jaka tana ajiye ina Mai leka bathroom wayo Allah, na furta ina mai fitowa da sauri.
Parlour na fito na wuce kitchen na dauko kayan shara, bedroom din na share tare da yin mopping.
Na koma bathroom shima share shi nayi abin takaici ga pad nan haka duk na hada na share kana na wanke bathroom din.
"Saida akira magrib na gama aikin, yah safwan nata min sannu da yake shi ba halin mom ya biyo ba.
"Around 4:00
Natashi, raka'a atul fijir nayi kana nai sallah asuba tare da azkhar, nafara karatun alQur'ani ban wani dau lokaci ina yiba natashi nafara gyaran gidan kafin karfe 7:00am nagama komai har girki,
Wanka nayi har na fito anty Waleedah bata tashiba bare tayi sallah tashinta na kumayi, me hali baya fasa halinsa dan yauma masifa ta hauni da ita kyaleta nayi na cigaba da kintsawa.
"Tsaf na shirya cikin less pink wanda amai ado da fararen duwatsu, dinkin riga da siket,
simple makeup nayi dan kuwa daga fouda, sai kwalli, da lips gloos, and maskara, da na taje eyelashes dina dashi aifa ya fito gadar-gadar Masha Allah, kalba na hade na daure da ribom,
Parlour na fita dan na karya bakowa a parlour sai yah safwan, gaisawa muyi tare mu karya dan shima zai fita gurin aiki,
Jeki dako mayafi na ajeki,
Tom yah safwan.
Gogagen milk hijjab nasaka da face mask da eyeglasses sai plate shoe shima pink waya ta nadauka nasaka a hand bag na fita,
Su anty Waleeda suna ta sharar bacci harna mu tafi
Muna zuwa ya bani 1k godiya na mai ina karasawa ciki.
Yauma Isha ta rigani zuwa ban dade da zuwa ba mu fita gabatar da program din ranar Thursday da ba muyiba.
"Bayan mun gama mukhtar yake cemin MD na kirana,
Kai tsaye office din nashi na nufa ina shiga,
PA dinshi da sai cin magani take ta min iso gurin shi,
ban damu da kallon da take minba na karasa da sallama.
"Tsaye na ganshi sai zagaye office din yake,
Nima tsayawar nayi ina furta,
good afternoon sir!
Nuna min gurin zama yayi shima yana kai zaune.
Jin ya kafeni da ido ya sani na dago daniyar magana dan nifa na tsani kallo, shikuma ya kware indai gurin kallo nane.
Yah jikin naki?
Ya jefomin tambayar da saida na dago na kalleshi.
Ai naji sauki! Nafada ina kasa da idona .
Masha Allah!
Dama dalilin da yasa na kiraki ina son magana dake ne,
Uhm inajinka na fada cike mamakin wacce magana zaiyi dani.
"Cikin bazata matukar bazata na d'ago ina kallon shi jin maganar da banta b'a tsammani daga gare shi ba.
"Wallahi safiyyah ina son ki ina burin ki zamo uwar y'a'yana tun randa na ganki naji ina sonki wallahi, tinanin ki ya hanani bacci, har gidan ku naje acemin Wai banan bane gidan, ko sawa nayi yau tayi please kar kicemin aa.
Ya karasa maganar kamar zaiyi kuka idon shi na tara kwalla.
Ni wallahi dariya ma yabani da tausayi gami da kunya.
"Na baki lokaci safiyyah kije kiyi tunani da kyau, Insha Allah duk abinda kika yanke zan amsa da hannu biyu, amah kimin adalci please.
Ya 'karasa maganar cike da magiya.
Kai kawai na gyada mishi na fice daga office din,
Kai tsaye office din mu na nufa, mu cigaba da abinda muke,
gabaki daya tunanin maganar nake. to ya akai ma yasan gidan mu, haka dai har atashi takardun dazan kaima ma cewa nayi Isha takai mu hadu a mota,
Koda ta tambayeni cewa nayi bakomai na wuce.
Da ta dawo take sake tambaya ta, meya faru naji MD yace intaya shi rarrashin ki?
Bakomai! Na fada irin banson wata tambayar,
Amah safiyyah baki da wata aminiya data wuce nida buhaisa, haka nima bani da wata aminiya sama dake, kinsan bana boye miki damuwa ta. amah some time kina boye min damur ki bana takura ki da dole saina ji, shikenan.
Ganin taji haushi kuma nima fa banyi adalciba, hannun ta na kama, kiyi hakuri kinji sis wallahi ba haka bane, nafad'a mata duk yadda muyi da shi.
"Uhmm safiyyah ta kira kinsan menene?
"Aa saikin fada isha"
"Wallahi ki amince ta ko ina MD ya can-can ci a soshi.
Don mutum ne nagar tacce wanda yasan ya kamata mai ilimi.
A taikaice wallahi koni MD yace yana so tuni zan amince ba kiga yadda PA ta mutu akanshi ba amah bata gaban shi.
Please kidai kara tunanin amah wallahi kun dace da MD sosai.
"Murmushi nayi tom sisy nah nagode sosai muje to"
"Itama murmushin tayi never mind sis nidai fatana ki amince wa bawan Allah nan,
Tafad'a tana tada motor,
Har kofar gida takawo ni kana ta wuce tana kara rokona murmushi kawai nayi na shiga bakina dauke da sallama.
Mom ce da anty Waleeda kawai a parlour, ko firar mai suke ina shigowa suyi shiru dan ko sallamar basu amsa ba,
To nasan hali tunda basu san mahimmanci taba.
Gabanta naje ina fadin good evening mom, murmushi kwance a fuskata.
Sanin ba amsawa zatai ba yasa na mike na wuce bedroom.
Tom dama yaudin fa gaskiya na gaji. kasancewar program biyu nayi ga kaina har juyawa yake.
Bathroom na shiga na wanke kana nayi wanka tare da dauro alwala,
Bed nafada ina sauke ajiyar zuciya ga yunwa na kwakular cikina, amah nasan ba abinda zan samu a gidan nan,
nikuma bazan iya girki ba dan kaina ciwo yake.
Ganin fa zan cutu yasa na tashi, mayafi na daura akan towel din na fito kai tsaye kitchen na nufa.
"Kamar yadda nai tsam mani hakan ce ta kasance dan kuwa bakomai hattana miyar basu rage ba,
Garin kwaki na jika da Madara na zuba gyada, na fito duk da kallo su bini anty Waleeda na dariya kasa-kasa har nashige"
________
*Abuja🤍*
Motocin shi ne su shigo gidan kai tsaye parking lot su nufa ajere su tsaya, kasancewar parking lot din akwai girma.
Da sauri Samuel ya Kara so ya bude mai motar.
yadau tsawon lokaci kafin ya fito gaba daya kamewa suyi har ya bargun youseef beye dashi,
Kai tsaye ta babban parlour yabi.
Aikuwa gaba daya 'yan matan gidan suna zaune,
wasu sunyi group din fira, wasu waya, wasu chat, wasu koma iya su biyu ne, wato zaituna da azima kenan dan yanzu ma riga da wando ne ajikin ta.
"Da sallam ciki-ciki ya shiga dan inba kallon bakin shi kayiba ba zaka ce yayi magana ba.
Gaba ki dayan su nutsuwa suyi,
Barka da dare yah Aj su hada baki gurin fada.
Da kallo ya bisu daya bayan daya,
"Ke"
Ya furta tamkar mai ciwon hakori,
Zaituna da tasan da ita yake tace Na'am yah Aj tana nufo inda yake tana wani rangwa d'a.
Tom bema san metake ba dan hankalin shi bashi gareta,
"Karna dawo na ganki a haka.
Yafada yana haurawa upstairs,
Me feenah zatai itada aynah inba dariya ba har da shewa.
Zaituna da ranta yayi ko loluwar baci itama b'angaren granny ta nufa dan ta gane nufin shi ta cire kayan jikinta kenan.
"Shiko kaitsaye dakin Ammii ya nufa.
Haka yayi ta zuba mata shagobba san ransa saiki rantse shine auta kamar ba Wanda gaba daya yaran gidan ke tsoro har ma manyan shakkar sa suke.
"Zakai dinner ne yau ko aa?
Tafada tana kallon shi.
"A'ah auta ta amso min Madara a gurin granny ita zansha"
Tom dayake itama tasan halin nashi baya son cin abinci bare kuma na dare ya gwamace yasha Madara ko coffee.
"Saida safe yayi mata yabi ta wata kofa da Kai tsaye part din shi zata kai shi............✍️
🌹 RAYUWATA 🌹*
*Story and written✍️*
*Bilkeesu .S. Aliyu*
_💞(Billy pinky)💞_
*🤝 Amanar nazari writer's association📚🖊️*
*[07070260240]*
_WhatsApp number or call_
_📚N.W.🖊️_
*Book 1 📖*
*Page 20&21*
"Yanzu zakaje ka gaishesu ne koh sai ka dawo?
"Saina dawo yanzu time ya kure"
"Allah yah tsaremin Kai ya dawo da kai lafiya Allah yabada sa'a"
"Ameen yah Allah cewar Addah, shima Ameen yace yana sunbatar goshin ta kana ya fice cikin nutsuwa, dolene inka kaleshi ka 'kara kallo .
Tunda ya fito compound din gidan tight security d'in dake zagaye da harabar wurin suka wani irin kamewa tare da sara mishi,
Had'i da gaishe shi"
"Hannu kawai yadaga musu tare dace wa kun tashi lpy?
Cikin harshen turanci.
Bai jira amasa warsu ba ya nufi"
"Gurin shegun manyan car's d'in dake jibge wuri guda su nufa shida security d'insa.
Zu'ke'kiyar ba'kar motar da juseph ya fiddo,
Wanda ko makaho ya shafa yasan eh lallai kudi yayi aiki wurin siyenta. Dan sai wani irin kyalli da sheke take mai daukar ido.
Gatan dai bata cika hayaniya ba kuma Bata mamaye waje ba. Tsaf take kala da yanayin matasan zamani irinsa dake gara kan nera bisa ga damar da ubangiji ya basu."
"juseph ne ya bude masa motar ya shiga sanan Yuoseef ya shiga suma sauran security d'in shiga nasu suyi su fita a jere susa motar da Aj yake a tsakiya juseph ke driving"
"Kai tsaye company su nufa"
"Ganin katon company dasu zo yasani furta masha Allah gaskiya company ya hadu ga girma, a saman company dauke yake da wani tambari Mai kamar tauraro irin tambarin dake jikin motocin shi"
"Har ciki su shiga guys d'insa su bude Mai motar,
Saida yadau tsawon lokaci kafin ya fito gaba daya ma aikantan sai girma mashi suke."
"office din danake kyautata zaton nashine, dan yafi ko ina tsaruwa, kuma security's ne aciki da wajen shi. ya shiga youseef beye dashi"
✨🤍✨
Uhm dan Allah meye ai bin wanan shigar granny? bama wannan ba ace yah majeed ya dawo amah baki gayama mummy ba?
"To ban fada ba kinga daga ke har uwar taki inbaku rabu dani da zancen Abdulmajeedu ba wallahi zan saba muku.
Kedashi kwata-kwata baku dace da juna"
"Kamar zaituna zatai kuka tace granny kina nufin nida yah Aj bamu daceba?"
"To banda abinki inake ina Abdulmajeedu?
jikifa yara ba tarbiyya, jifa shigar dake jikin ki da sunan wayewa, shiyasa yaran 'kauye sufiku hankali wallahi.
Takare maganar tana cigaba da damun furar ta,"
"Zaituna nashirin sake magana, granny ta zuba mata wani kallo, wuce ki bani guri kin wani tsayamin aka"
"Harara itama tazuba ma granny tana wuce bedroom din ta,"
"Kwafa granny tayi tacigaba da abin da take tana mita"
"Tana shiga ta danna ma mummy kira wayar na fara ringing ta fashe da kuka.
Aikuwa mummy na dauka taci karo da kukan zaituna, nanfa hankalin ta ya tashi an ta'bamata shalele.
Kinga ya isa haka fadamin meya faru?
Nanfa ta shirya karya da gaskiya tafada mata, kuma granny ma wai nida yah Aj bamu daceba takai karshen maganar tana sake fashewa da kuka"
"Kinga ki kwantar da hankalin ki, wallahi indai ina numfashi a doron kasar nan bamai auren majeed sai ke,
Inko kiga baki aure Shiba to saidai bana numfashi wallahi.
Bari Yaya ya dawo"
"Yauwa mummy na shiyasa nake kara sonki wallahi sosai Allah ya barmin ke"
____🤍💗
"B'angaren Ammii kuwa bayan Aj ya fita ne take karaba addah hakuri.
A'ah aminiya bakomai Nima jiya basma take sanar min ya dawo, kuma yau ina Shirin zuwa saiga fennah tashigo raibace, nake tambayar basma wai fada suke da zaituna.
Yaushe zaituna nan tazo gidan nema?
"Saida Ammii taja numfashi kana ta bude baki tamkar Bata son