Showing 33001 words to 36000 words out of 84595 words
kallo zakasan tashiga mamaki ne.
"Mekike nufi ne Waleeda kina nufin safiyyah tafara karunwanci ne shine zan dau mataki?
aini dazata bi duniya dana fijin dadi wallahi. Dan yadda na tsani uwar ta haka na tsaneta, keni yanxu ma nafi tsanar ta akan kowa wallahi.
"Uhm mom kenan, ai Ni nafiki tsanar ta bakiga kanwata bace amah tafini cigaba kigafa aiki take niko ina zaune,
Kuma kinsan ustaziya ce shine har kike tinanin zatayi wani karunwanci, kedai kawai mom ki tsaya kiyi bincike akanta wallahi, tunkan abi ya Miki nisa."
"Ehh kuma hakane, to amah ai ustazan sunfi iya iskanci"
"To nidai mom nafada miki, kuma akan wanan wanda yazo neman ta, wallahi mom kullum son shi ninkuwa yake a zuciyata kisan abun yi"
"Ki kwantar da hankalin ki zansan abunyi jiyama gurin na kan kwari muje nida mama, to bamu sameshi ba amah asatin nan zan koma"
"Assalamu alaikum"
Buhaisa data shigo tun dazu take sallama su mom suna can kwaryar daki suna kullin su ta fito tanabin buhaisa da kallo.
"Ina yini"
"Daban wuniba kya ganni, kekuma daga ina ?
"Oooh sorry nashigo miki gida ba neman izni safiyyah nake nema"
Buhaisa tayi maganar da cike da rainin hankali tana wani murmushi, Dan tasan sarai mom ta ganeta kawai tsabar wulakanci ne.
"Tsaki kawai mom taja tashige bedroom.
Itama buhaisa tsakin taja kasa-kasa tashige bedroom din su safiyyah.
*Evening*
Koda nadawo islamiya a gidan nasami buhaisa, aikuwa tacika fam.
"Ke shine ki'ki dawowa kinsan wannan shegiyar matar daba mutunci ne da itaba tana gidan "
"Sorry sisi wallahi matsala asamu mun biya gaida wata 'yar ajin muce da bata da lafiya shiyasa, amah afwan"
"Shikenan ya wucce, waikin san ma iskanci da matar nan tamin ne?
Aa amah sisi please mubar zancen mom kinji,
Yasu ummi da anty hajara da yah saif?
"Uhmm duk suna lafiya sunce a gaishe ki, damafa anty hajara ta fito da anko ne, yah saif ma harya suyo mana, kinga yanzu saura dinki gobe zamuje mukai, because biki yazo.
Yayi tom Allah yasaka da alkairi ya kaimu lafiya, kuje kawai da Isha tunda ni nakusa zuwa ma gidan, kinga some time kaya ma kai daya akemana da kadan nafiki jiki"
"Ameen yah Allah sisi nah tom yayi, sauran shirye-shiyen kuma saikin zo saimu k'rasa koh"
"Eh hakam yayi amah meda-me yakamata ayi kisan nifa bansan wannan abun"
Eyye to wallahi baki isaba, kinga fige wannan ustazanci zakiyi gefe in mungama kya dawo dashi wallahi.
Haba sisi nah, kunyar wa zakiji, kauyawa day ne, sai bredal show, sai fulani, sai kamu, kawai za'ayi anan acan Abujan za'ayi dinner, bayan kai amarya.
"Hmmm Allah yakaimu lokacin sisi "
"Ameen yah Allah ki kefa"
"Murmushi kawai nayi mu cigaba da fira har yah Ansar ya dawo mu koma dakin shi muna fira, bayan magrib ya tafi kaita, nikuma nadan gyara mai dakin na nufi bedroom din mu.
Yauma mun dade muna fira kana na tafi na kwanta, har lokacin anty Waleeda kamar ma bata a gidan.
MD ya kirani musha soyayyar mu a waya, muna shirin sallama yace,
"Amm baby su alhajina zasuzo fa maybe next week din nan dan haka ina bukatar ganawa da Abba yaya za'ayi kenan".
Da sauri na d'ago kaina kamar yana kallona, cike da kunya ga kwalla ta tarumun a ido,
"Baby kinyi shiru?
"Uhm yakama kafara ganin yah Ansar dai first kafin Abba nake ga"
"Sosai ya sauke numfashi mai nauyi, kana ya amsa da, "okay hakan ma yayi, zan bari to sai gobe masamu yah Ansar d'in"
Daga haka mukai sallama"
*Monday morning*
Yauma kamar kullum around 6:00 am natashi bayan nayi sallah da azkhar da karatun alQur'ani. Nafara gyaran gidan, dan na makara, cikin kan-kanin lokaci nagama komai, saidai ban musu miyar ba, dan har yah Ansar ya kamamin wani abun. kasancewar indai yana gidan yana tayani saidai mom ta hana shi,
Tsaf nashirya cikin riga da siket dakin ya zauna min daram ajikina, simple Make up nayi danko iyakar fauda, sai kwalli, da lipstick, and maskara, da na taje eyelashes dina dashi ya fito gadar-gadar, sai girata da take a ciki na taje. Turaruka na nafesa masu mutukar kamshi, sai plate shoe danasa, gashina dana tsafe nake son zuwa gun kitso tunkan ummi ta ganni dashi atsefe na daure da ribbon, sai yayi kamar nayi a cuci dashu.
Goggagen Hijab nasaka har kasa danko d'an kwali bansa ba, sai face mask, da eyeglasses, na dau hand bag d'ita da waya ina ficewa a dakin, dan yau anty Waleedah ma ba'a gidan ta kwana ba.
Kamar ko yaushe yauma parlour tsit yake har mutafi,
Saida yakaini har kofar shiga kana ya bani 3k, godiya na mishi nace please yayah kabari nakira Isha ku gaisa.
Da "okay" ya amsa min nashiga da dan sauri dan kiranta, a hanya mu hadd'u nace Isha kizo ku gaisa da yah Ansar.
"Kai Quee hijjab da gaske?
"Dariya nayi nace kinsan zan miki karyane ai"
"Sorry ni wallahi kunyar yah Ansar d'in nan nake ji wallahi"
"Kinji kamar wani saurayinki anya Isha anya?
"Ke dalla basan iskanci muje"
Murmushi nayi muje su gaisa kana mu shiga ciki shi kuma ya tafi gidan ummi.
"A hanya mu hadd'u dasu mu'az dan yau ma tare zamu yi program, duk gaishe su nayi, cikin tsokana suke tono na.
"Kai Quee hijjab yau kin makara fa MD zaiciki tara gaskiya, dan baza'a yi san kai agaban mu atoh kiya kukace?
Yafada yana kallon su mukhtar.
Nida su isheni ma nace kwaji dashi wain Quee hijjab sabon sallo kenan mutafi mubar su, daga baya suma su shigo. MD da tunda na shigo ya zubamin ido na gaisar. kana mufara gabatar da program din.............
__________
*Abuja🤍*
Mummy na fita tasaki murmushin samun nasara ta wuce part din granny, dantasan ita kad'ai ce zata bata cikas, Bilkeesu ko zataji da ita dan ita irin maccen nan ce me kawaici.
Tunda ta shigo granny ke binta da kallo, ganin yadda tashigo sai murmushi take bata ma lura datana parlourn ba, a'a zakiyya daga ina haka naga sai fara'a kike kamar wacce za'asa a aljannah?
Firgigit ta d'ago tana kallon ta, kana ta sauke boyayyiyar ajiyar zuciya, abinka da goggagiyar 'yar bariki sai cewa tayi.
"Hajja bakomai kawai dai wani abu natuna" takai karshen tana zama kusada granny.
Kallon ta tayi cike da nazari sai kawai ta girgiza kanta ta maida hankalin ta kan program din da akeyi.
Ita kuma tashige daki domin sanar ma da d'iyar tata labari me dadi.
_______✨
Koda mummy ta fita dady nazari ya shiga, har Ammii ta shigo besani ba saida ta taba shi, yasauke numfashi zama tayi kana tace.
"A'a lafiya kuwa naga na barka k'alau na dawo na ganka kuma sai a hankali?
"Hmmm lafiya lau zauna muyi magan da "to" ta amsa kana ta zauna tace,
"nima dama inaso muyi magana"
"Okay to fara kawai"
"Maganar dama akan auren majeed ne. kaga hajja kullum cikin fad'a take wai mumu daure mai gindi akan aure saidai mu lalabashi, toni ma abun yana damuna, shine na yanke hukuncin a had'ashi aure da feenah, 'yar wajen Addah wato d'iyar sulaiman?
"Dogon numfashi ya sauke yana kafeta da ido, nad'an tsawon lokaci kana yace.
"Kema dai Bilkeesu?
Cikin mamaki take kallon shi sannan tace.
"Bangane nimaba alhaji wani abinne ya faru?
"A'a bakomai kibani Time zanyi tunani"
"Tom shikenan amah yarinyar tana mutukar son shine shiyasa, ma amah dai saina ji ta bakin naka"
" Okay shima inaga next week d'inan zai dawo "
"Eh haka yace Allah yah yadawo dashi lafiya"
Daga haka su cigaba da fira cikin nishadi da farin ciki alamun anyi kewar juna.
_________
*Kaduna✨*
Har kofar gida ya kaini yauma dai mun dade muna fira, yake sannar min sunyi magana da yah Ansar,
Cikin jin kunya na dukar da kaina ina shirin fita,
"please beb ki waigo mana nasake ganinki tunda rowar fuskar ma akemin, sarkin kunya nikam naga sanda zaki dena jin kunya ta"
Murmushi kawai nayi jin yadda idonun shi ke yawo a kaina, nadan waigo kana nace
"to ka budemin motar tukunna.
Shima murmushin yayi yana budewa kuwa nayi wuf na fice ina daga mishi hannu.
" Shima dagamin yayi har na shige kana yaja motar ya tafi "
Cikin sand'a nashiga Allah ya remake ni bakowa a parlour dan haka nai wuf nashige daki dan bana so muhadu da mom, banyi miya ba yau.
Anty Waleeda ce a dakin tana kallo tunda nashigo ta bini da harara har nashige bayi,
Ashe fita tayi,
fitowa ta daure da towel kenan ina gaban mirror, saiga sunan sun banka d'o kofar,
Hannun Mom dawata katuwar bulala ta nufo kaina waina satar mata kudi , tsabar mamaki tsayawa nayi kawai ina kallon ta, banyi auneba tasakin min ita agadan bayana,
"Ke Waleeda dubamin Jakarta ki gani"
Mom tafada cikin hargagi,
Anty Waleeda na dubawa kuwa saiga kudi sun fado dauri har biyu a jakata,
Mamaki yasani cewa wallahi karyane saidai wanine yasamin.
"Dan uwarki rufemin bakin ki nice zan miki karya safiyyah, kud'in nawa zaki dauka kinsan yawan su kuwa?
Tafada cike da tsawa tana kara lafta min bulala, wani zafine ya shigemi na kwalla kara. Dai-dai nan Abba ya shigo kamar an jefoshu,
"Haba Zuwaira lafiya zaki kama yarinya kina duka jikin ta bakaya, baki da hankali ne?
Yafada a hassale yana rike bulalar data daga da niyar sake tsulamin. Basuba hattani Saida nashiga shock, dan bayau bane kawai mom ta taba dukana agaban shiba, bama niba har yah Ansar da duka take, baby kuwa kuka kawai take tana bata hakuri.
Mom ce takatsemin tunani na Dan cikin hargagi take ma Abba masifa, dafada mishi kud'in ta na sata kuma wallahi saina biya, inba hakaba wallahi saita kaini kitu, saida takai har yafara bata hakuri da lallabata, Ni al amarin ma saiya nemi fasan kai, haka dai yajata da kyar su fice.
Anty Waleeda ta dallamin hara mayya kawai to kurwar uwata kur wallahi. Kadan ma kigani indai mom ce wallahi bari Abba ya fita dan ba kyaleki tayiba kiji mada da tsamin jikin ki, wallahi kuma saikin fito da kud'in nan duk idda kikaisu. Saida ta gama zageni tsaf sannan ta fice,
kamar iska zata dauke ta dan sam anty Waleeda bata da kiba.
Tana fita na dur kushe nasaki kuka maicin zuciya saboda rad'ad'in da ilahiri jikina ke min. Baby ce ta matso tana rarrashina kai kawai nadaga mata nace jeki baby,
Koda ta fita da kyar natashi na hau gado na kudun dune da bargo zazzabi me zafi ya rufeni da ciwon jiki, inaji kiran da yah Ansar kema wayata harya gaji ya dena, nasan cewa zaiyi nayi bacci..................✍️
_Taku har kullum da ko yaushe🫶💯_
*🤝 Amanar nazari writer's association📚🖊️*
_07070260240, WhatsApp number or call_
*_Please🙏 comment and like and share fissabilah👏👏_*
🌹 RAYUWATA🌹
Story and written✍️
Bilkeesu Sa'eed Aliyu
💞(Billy pinky)💞
🤝 Amanar Nazari writer's association📚🖊️
[07070260240]
WhatsApp number or call
📚N.W.A🖊️
26&27
*Washe gari*
Da zazzaɓi na tashi, kota aikin gidan banbi ba, nayi shirin tafiya aiki dan ko breakfast banyi ba,
Ina shirin tafiya na hau napep dan ko yah Ansar bana so mu haɗu, sai gashi ya fito,
Ƙasa nai da kaina tare da furta "ina kwana yayah?
Bai amsa gaisuwar ba sai kallo daya bini dashi, nakara ƙasa da kaina.
"Me yake damunki ne Safiyyah?
"Bakomai yaya"
"Amah naganki haka ko aikin gidan bakiyi ba kuma kisan halin matar gidan?
"Muje yaya zan faɗa ma a mota"
Na faɗa inayin gaba da kallo ya bini har na shiga kana shima ya shigo, mun fara tafiya dan na dauka ma ya manta cikin muryar shi da bawasa yace.
"Inajinki"
Duk yadda muyi dasu mom na kwashe na faɗa mishi, kuma wallahi yah Ansar ko sanda na dawo ba kuɗin a jakata, hasali ma saida na cire waya ta a ciki, na ƙare maganar hawaye na zubomin.
"Nasani safiyyah ki ƙara hakuri kinji, nawa tace kuɗin nata?
"Bata faɗa ba ai kasan saita ƙai yace kuɗin da zai isheta zata faɗa"
Murmushi kawai yayi batare da ya sake cewa komai ba har mu iso gurin aiki.
"Yanzu ya jikin naki zazzaɓin ya sauka ko har yanzu?
"Because basan shan magani nace mishi ya sauka"
"Sure"
"Yes"
"Allah yasa ba kawai kin faɗa bane,
Akan maganar ku keda Suraj kuma, nagama duk wani bincike naga ya can-can ta inbashi ke saboda halayen sa masu kyau, kuma ya fito daga gidan mutunci,
To Abba ne matsalar, na mishi magana wai mom ta fito miki da wani, kuma shi zai ba dan yafi gamsuwa da tarbiyyar sa dan haka shi baisan wata maganar Suraj ba.
In kuma ba hakaba saidai ki bar aikin ki dawo gida ki cigaba da musu bauta.
Kuma..
Kuka na sakar masa mai taɓa zuciya. hakan yasa yai shiru ya gagara cigaba da maganar. Ya tsuramin ido kawai, kana ya jawoni jikin sa shima hawaye na tarumai a ido.
Amah fa kisan bana son kuka ko Safiyyah.
Dagowa nayi a karo na farko ina kallon sa. kana nasake fashewa da wani kukan ganin yadda idon sa ya kaɗa yayi jajur.
Ya kake so nayi. Shikenan haka zamu lalace gurin ma wacce bata taɓa tausayin muba biyayya. Kullum burin matar nan wulaƙanta mu. Tun bansan kaina ba nake bauta a gidan nan. Amah ko sau ɗaya ba'a taba min adalci ba innai kuskure. A kullum a banyi ba nake. Ka duba anty Waleeda fa tana kwance. Yaya nagaji jinake kamar na gudu na bar gidan nan...."
Shiii!! Karna sake jin wannan maganar a bakin ki. Safiyyah ai wuya bata kisa dan data nayi da tuni bamu. Duk dacan baki kosa ba saida aski yazo gaban gishi.
Kwana nawa ya rage miki a gidan. Bama keba da kike mace zaki tafi gidan miji hattani nakusa tattara kayana mu bar musu gidan.
Amah dan Allah kar insake jin kinyi wannan maganar. Inki gudu ina zaki. Ki daure ki cigaba da musu abin da suke so. Wata rana sai labari. Akan maganar ki da Suraj kuma, yau zanje gurin Abban su saif na faɗa mishi, da kawu Inusa da kawu mansir kinsan dai Abba yana mutukar tsoran su, insha Allah komai zai tafi daidai"
"Ameen yah Allah yayah"
"Yauwa jeki karki makara kuma ki kula da kanki sosai, kar kisa wata damu kinji?
" Insha Allah saika dawo Allah ya tsaremin kai yaya nah"
"Ameen yah Allah lili sis"
Kana ya tafi ni kuma na shiga ciki.
*In the evening*
A parlour nasame su gabaki dayan su cirko-cirko suna jiran dawowa ta. Da sallama na shiga ba wanda ya amsa har ba daya cika yayi fam da alamu an fan fashine. Banyi aune ba naji saukar mari a fuskata. Anty Waleeda ce sai huci take tana bina da kallon tsana. Yadda ta shammace, ni haka nima na shammace ta na bata hagu da dama.
Cikin tsanani azaba ta dafe kuncin ta Ni kimara Safiyyah?
An mare kin. wallahi duk sanda ki ƙara ɗaga hannun ki da nufin kaishi jikina wallahi saina miki abinda yafi haka...
Kasa ƙara sawa nayi saboda marin da mom tamin hagu da dama, duka na take tako ina tana barauniya ki fitomin da kuɗi na dan uwarki. Duk dukan da takemin ban motsaba saida ta am bato min uwata, cikin kaushin murya nace
"Wallahi mom badai uwata ba.
Cikin fusata ta shakemin wuya. dan da kyar nake numfashi baby kuwa sai kuka take, Abba da tun ɗazu bai motsaba saidai daka kalle fuskan sa kasan baya jin daɗi. Yake kokarin kwata ta a gurin ta, haba Zuwaira ki saketa mana ta faɗa miki inda takai miki kuɗin. da kyar ya kwaceni dan saida tayi taga-taga zata faɗi, niko zube wa nayi a kasa baby ta kawomin ruwa, ina cikin sha domin shi nake buƙata. Ruwan anty Waleeda ta kaɓar ya zubomin a jikina. Ban ɗago na kalle ta ba.
sai Abba da yace kowa ya zauna.
Kamar mom zatai magana kome ta tuna tafasa ta tsaya a tsaye kamar doki sai jijjiga take. Kai kawai ya girgiza kana ya fara magana cikin ɓacin rai.
"Yanzu dan Allah kunfi so kullum maƙwota suna jiyiku kuna faɗa?
Twssss aikin banza ina ruwana da wasu maƙwota nidai kuɗina kawai nasani wallahi. Inba haka ba saina kaiku police station acan kwa fitomin da kuɗi na.
"Kuɗin naki nawa ne?
Yah Ansar daya shigo ya faɗa yana kafe mom da ido.
Saida ta diririce saboda kallon da yake mata.
"Duba dari da hamsin tunda naga wasu a jakarta"
"Okay transfer or cash?
"Cash nake buƙata tunda nima cash ta.."
Hannu kawai ya ɗaga mata kana ya jah hannu na, mu fice kasan cewar jikina ya dau zafi.
Ba wanda yace komai acikin mu dan ni ko hawaye babu a ido na.
Har mu iso wani p hospital, ciki mu shiga a gwada