Showing 75001 words to 78000 words out of 84595 words
kuma karb'i k'yautar da ubangiji yay maka da hannu biyu, natsuwarka nake buk'ata da farin cikinka". Shiru Majeed yayi girjin sa na ciga ba duka. Amma ya kasa magana.
Yayin da Mummy ta kafe dady da
Kallon kiɗima. Cikin kakkausar murya tace. "Aure kuma Yaya". Ta idda maganar cikin zaro ido tana kafe dady da kallo. Murmushin gefen baki ya saki tare da lumshe ido ya buɗe kana yace. "Kwarai kuwa Zakiyya Aure" ruf zancen na dady ya rufema Mummy baki Dan fah ta gagara cewa komai.
Ammei madai kallon dadyn kawai take amma bazaka iya tantance halin data shigaba na farin ciki ne ko akasin haka, haka zalika batai magana ba illah "Alhamdulilah alah kulli halin" data faɗa ƙasa-ƙasa. A zuciyar ta kuwa tana ai yawa shiyasa taga dadyn cikin farin ciki kenan.
Wata guɗa da granny ta ranɗa da saida yasa Majeed toshe kunnen sa tare da ɗago wa yana wasa mata harara, daga nan bata sake cewa komai ba sai alhamdulilah da take ta faman jerawa.
Youseef madai kur yama dady da ido dan abune yazo musu na bazata. Wai yau Boss amma auren dolle eh lallai akwai kallo🤭
Zaituna kam da Fennat da wasu daga cikin yan Matana a tare girjin su ya buga, yayinda daka kalli Zaituna data koma kamar wata mara hankali dan yadda take bin dady da kallo.😂 Danko wata zabura tayi tare da dafe girji.
Finnat kam tama kasa ƙwaƙwaran motsi saboda yadda maganar dadyn ta dake ta.
Addah ma shiru tayi kanta a ƙasa ba tare da tace komai ba.
Mama kam murmushi kwance a fuskar ta take kallon dadyn dan itama kanta zaman Majeed ɗin haka yana damun ta kwarai da gaske.
Anty Amarya kam wani makirin murmushi tayi tana kallon Addah, dan itafa da da dama tashi zatai ta rangad'a buɗa harma da taka rawa saboda murna..........✍️
Toh nima nace ba'a barmu a baya ba dole ne muma mu taka💃💃
Hummm☹️ inji mai ciwon hakori Readers yaufa ake yin ta🤭🤗 toh amma bari dai nayi shiru muje page 46 danjin yadda zatakaya masoya masu hanjin ligidi😂
*ONE LOVE GUYS ❤️*
*Typing📲*
_Follow my WhatsApp channel_ 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0
_Follow my WhatsApp group_👇
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_CREATED AND WRITING BY_
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION ✨*
*T.M.W.A✍️*
*Amanar taurarin marubuta writer's.......✍️*
*TEAM HAZIKAI BAKWAI 💪✨*
Page. 4️⃣6️⃣➡️4️⃣7️⃣
.................. Dady yacigaba da maganarsa yana nazarin kowannensu, dariya taso kubce masa lokacin da idonsa ya sauka kan yah Majeed d'in, amma saiya danne ya kauda kai yana murmushi.
"Zaman Majeed ya isheni hakanan, Dan haka Na yanke hukuncin masa aure da mace tagari, wadda Na yarda da ingancin tarbiyyarta, irin macce da kowane namiji ko Iyaye keso ɗan so ta zama matar sa, ban hanaka anangaba idan kasami wadda kakesoba ka k'ara.
Bawata bace dan koh itad'in ba kaman komai bace amma sai dai itad'in mai tarbiyya ce hankali nutsuwa gami kamun kai, kuma itad'in mace ta gari ce, dan haka saiku fara shirye-shiryen tarbar amarya".
Gaba ɗaya parlourn ya dau shiru kace wanda mutuwa ta ratsa na wani lokaci yayin da Yah Majeed yayi ƙasa da kansa kai tsaye inka kalle shi zaka gane tsantsar tsagoron tashin hankalin daya shiga. Amma kansa a kasa amma dolene ka fahimci yana cikin tashin hankali da wannan sabon al'amarin.
Mumy ko gaba ɗaya hankali yayi kaura daga jikin ta babbar tambayar ta anan wacece wacce aka Aura ma Majeed ɗin? kuma taya? Waɗan nan tambayoyin sune cike a cikin zuciyar ta kuma take neman mai amsa mata.
Zaituna kam kai tsaye da ka kalleta zaka gane hankali yayi kaura daga gare ta, wai ace Yah Majeed d'in nata Wanda take mafarki da muradin ya zama mijinta, nata ita kadai dan batajin zata iya share nashi da kowacce irin mace, shine yau ake sanar da ita cewa ya zama na wata, watan da batasan ko wacece itaba.
Wai wacece ma wannan? wacece ke ƙoƙarin rabata da RAYUWARTA? Wacece ke ƙoƙarin rabata da MURADINTA? Waye uban ta a ƙasar nan? harda take ƙoƙarin mallakar abu mafi muhimmanci a cikin RAYUWARTA?.
Ammei dai shiru tayi dan bata da tacewa amma itama aranta tunani take wacece kuma dadyn ya Aura ma Majeed ɗin, tayi farin ciki sosai yanda taji mijin nata na yabon yarinyar hakan na nufin ta dace da ɗan nasu kenan, Allah ya bashi irin macen da take addu'a akan Allah yaba ɗan nata, duk da Safiyyah tayi masa sha'awa toh ita yanzu ta riga da ta zama amarya.
Finnat dai baka isa gane ainihin yadda nata tashin hankalin ya tafi ba amma kai tsaye daka kalle ta kasan maganar ta taɓa ta ainun. Amma a baɗini zuciyar ta zafi take mata, haka kai tsaye tunanin ta irin na Zaituna ne akan shin wacece wacce aka Aura ma abun son nata? a kuma ina take? Waye uban ta a ƙasar? Wannan tunanin da amsar take jira ta samu, toh amma a ina zata samu kuma waye zai warware mata.
Toh suma dai matan gidan kowa da abinda yake sakawa a zuciya yayin da tun gama maganar dady bayan granny da su uncle Abdallah sunyi magana tare da addu'ar Allah yasa alkairi. Su mama dasu Addah suma suyi addu'ar Allah yasa alkairi. Amma har suka gama Mummy da gaba ɗaya kamar ma bata a ɗakin batace komai ba, yayin da Majeed ke zaune a inda yake dan koh ƙwaƙwaran motsi bayi yake ba, ya zaune kamar mutum mutimin da aka dasa, kanshi a kasa.
Auta ma dai suma sunji mutukar mamakin wannan magana kuma sun shiga tunani yayin da kowa a cikin su da irin tunanin da yake a zuciyar sa.
Youseef madai saida dady ya gama magana kana ya ɗauke idanun sa akan sa ya maida kan Yah Majeed ɗin gaba ɗaya kana kallon sa kasan yana cikin tashin hankali.
Dady daya gama nazarin kowa daga ciki ya ɗaura da cewa.
"Yan uwana ina mai neman afuwar ku akan shishigin da na muku akan ɗan ku, duk da kune keda alhakin hakan. Amma ku sani bawai nayi hakan bane dan na nuna muku baku isa ba, a'a nayi hakan ne sai dan bani da yadda zanyi, abun ne yazomin a mutukar bazata kamar yadda kuma yazo muku, toh amma bani da yadda zanyi kunsan ance dama sau ɗaya take zuwa ma mutum, shiyasa nayi amfani da damata kafin ta kufce min, duk da dai ance matar mutum kabarin sa kuma wani baya auran matar wani. Toh bani da yadda zanyi face kawai a ɗaura kasan cewar bazan iya bari mace mai tarbiyya irinta ta kufce wa Majeed ba sbd samun irin su a yanzu sai an tona. Alhaji Ahmad amini gareni shine wakilin Majeed kasan cewar baku kusa dani a lokacin. Ina fatan zaku fahimce Ni kuma zakumin uzuri, Sannan insha Allahu amarya zuwa gobe za'a kawota, ku kuma a matsayin ki na iyaye mata saiku fara shirye-shiryen tarbar Amarya, Allah Ubangiji ya bamu ikon rike amanar da Allah ya bamu Allah kuma yasa alkairi acikin wannan Aure. Sai kuma kai Youseef, a matsayin ka na aboki gare shi kuma ɗan uwa saiku fara duk wani shirye-shirye da kusan ya kamata akan auren da kuma abun da zakuyi sannan duk wasu kudi ko wani abu da ake bukata kamin Magana dan ban lamunce ayi komai ba inbada kuɗi naba, sannan inaso ayi bikin irin wanda kowa zai sheda auran na *Abdulmajeed Abubakar Saraki*".
Gaba ɗaya da ameen aka amsa har uncle Kabeer dake sauraren su ta video call da'a kirasa, kana su uncle Sulaiman suka ce, "Ai Yaya duk abinda kayi yayi dai-dai kuma shima Alhaji Ahmad ai tamkar mune dan ko auran waye daga cikin familyn nan yana da ikon amsa dan shidin ya zama kamar dan uwa. Dan haka komai ku yanke yayi muma kuma munji daɗi sosai Allah kuma ubangiji yasa alkairi yasa abokiyar arziki ce".
Nan ma ameen aka amsa sai granny d tayi magana na irin farin cikin da Dadyn yasa ta a yau tare da saka masa albarka kana ta juya gun Majeed tana mishi tsiya. Dashi a yanzu gaba ɗaya ya dena fahimtar komai da suke cewa dan nutsuwa ma tayi ƙaura daga gangar jikin sa. Youseef ne daya gama lura da abokin nasa ya matsa kusa dashi dan kamasa ya tashi dan tuni dady ya sallami kowa shima shirin shiga ciki yake.
Yayin da wasu harma sun fice cike da tashin hankalin da suke ƙoƙarin boye wa wasu kuma nasu ya gaza boyuwa, wasu kuma suna zaune darshan sun kasa tashi irin su Zaituna kenan da suyi sumar zaune.
Da kyar Youseef ya taimaka ma Majeed su fice a part din dadyn su nufi nashi kasan cewar ma da kofar da zata kaika har part din Majeed ɗin daga na dady haka na Ammei ma haka, kuma wannan ɗin duk tsarin Majeed ɗin ne.
Suna shiga part din nashi ya zame hannun sa daga na Youseef ya wuce sama, da kallo kawai Youseef ya bishi a zuciyar sa yace, "duk da irin tashin hankalin daka kalle sa zakasan yana ciki amma ba abinda ya sauya daga cikin yanayin tafiyar sa, dan inba farin sani kayi masa ba baka isa gane yanayin nasa ba, saboda shi ko yaushe dama mai tsare gida ne ga kwarjinin da yake dashi."
Dawowa yayi daga tunanin daya tafi kana yace, "Allah sarki ko wacece ke shirin shigowa gidan nan, harna tausaya miki". Ya idda maganar shima yana ficewa daga part din Dan bashi lokaci ya huta. Ko zai samu nutsuwa.
A ɓangaren Majeed kuwa koda ya shiga bedroom d'in sa kai tsaye bathroom ya shiga inda ya shige ƙarƙashin shower yana sakarma kansa ruwan sanyi, duk da yamma ce kuma da ɗan sanyi-sanyi a garin haka ruwan ke sauka tun daga kansa zuwa ƙafarsa. Ya daɗe a bayin kana ya ɗaura alwala ya fito, yafad'a saman gado yana dafeda kansa dake masifar sara masa🤦♀, jiyake tamkar zai rabe biyu Dan ciwo.
___________🖤🤍
*Kaduna ✨*
A hankali kana nun maganganu suka fara tashi a gidan, saboda shiru har gurin karfe 8:30 na dare ba'azo ɗaukar amarya ba. Nikaina shirun na Suraj ya fara damuna saboda gaba ɗaya kunin yau bai kirani ba duk wasu alƙawaruruka damuka daɗe muna shirya wa akan wannan ranar amma ba wanda Suraj ya cika. A hankali wasu hawaye su gan garomin na fargabar wannan halin da Suraj ya ɗauka, duk da ta wani fannin na zuciya ta na masa uzuri wani kuma ya kasa masa sam.
Hannu nasa na share hawayen kafin wani daga cikin su Buhaisa ya lura na sake gyara kwanciya ta ina sauke ajiyar zuciya.
★★Luba ce ta haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito da taimakon Ummi na kimtsa jikina. Ta kuma tsareni sai da naci abinci da wani nama na musamman mai romo a cikin kula. Naman yayi daɗi dan haka na saki jiki naci sosai, koda tace sai na cinyesa ma ban musaba na dage na cinye nasha romon. Hakan yasa cin abincin bai armashi ba garan sosai. Tun ina kallon agogo harna daina. Sai dai a raina inata mamaki, dan tara dai-dai ya kamata ace muna a wajen dinner. Amma gashi anan har taran yama wuce ba'a kaini gidan su Suraj ba balle ai batun zuwa dinner. Kayan da Ummi ta banine tare damin umarni dana sa yasa ni kallon ta, ganin yadda fuskar ta take a sani amsar kayan kafin nace komai tace, "Amshi kisa Safiyyah ba yau za'a kaiki gidan kiba sai Allah ya kaimu gobe". Daga haka ta raɓani ta wuce ba tare da ta bani damar tambayar taba. Da kallo kawai na bita harta fice a bedroom din kafin na dawo daga tunanin dana tafi, Buhaisa tazo tana min irin wasan damu saba tana kara tonona, "Kaga amaryar tamu wato ke dan ance zaki ƙara kwana ɗaya damu kafin a kaiki shine kike wani jin haushi koh? Toh bari inje in faɗa ma Ummi ko Yah Ansar ince kefa kin kosa alfarma ma da amiki bakiso, kinfi so kiji ki cikin jikin Angonk......". Dukan dana kai mata ne yasa ta kasa ƙarasa maganar ta fice da gudu tana dariya, binta nayi nima har parlourn inda su Ummi ke zaune suna hira. Bayan Ummi taje ta labe tana min gwalo. Cikin shagwaɓa nace, "Ummi kin ganta koh". Hannu na Ummi ta kamo ta zaunar kusa da ita tana faɗin, "zonan baby inji meke faruwa meya haɗa ki da bestien taki". Labari naba ma Ummi yadda mukai da Buhaisa itako Ummi cikin kunshe dariyar ta tace, "Kinji baby rabu da Buhaisa so take kiyi kuka maza jeki ƙarasa shirin ki kizo muyi hira". Cikin jin daɗi na daga mata kai kana natashi na shige ciki ina hararar Buhaisa data koma kusa da Mamy, Isha kuwa na gefa tana mana dariya, anty Hajara kuwa cewa tayi, "Dama ku ako ina saikun raba hali kwa karanta" baki itama na murguda mata na shige, na barta itada Buhaisadan nasan dama ba kyaleta zatai ba. Koda na shiga gaba ɗaya yan matan ko wacce da abinda da take masu chatting nayi masu waya da babyn su nayi. Ni gaba ɗaya mamaki ma nake ganin duk cikin su ba wacce tamin zancen rashin tafiyar mu yaudin a zuciya ta nace maybe sun sani ne, zancen na ture gefe na wuce na karasa shirya wa cikin doguwar rigar da Ummi ta bani. Bata da nauyi dan irin mai bin jikin nan ce, tsaf na gama shirya wa bayan nasa turaruka na masu shegen kamshi na fito parlourn inda na same su ana hira, toh nima zama nayi anayi dani cike da Nishaɗi.
Bamu farga ba hirar ta ɗauke mu lokaci mai tsawo dan sai kusan ɗaya da wani abu Ummi tace mu shiga ciki mu kwanta, haka mu tashi mu shige ciki kamar kar a dena danni yanzu kwata-kwata banson ma goben tayi dan haka kawai dana tuna da goben za'a kaini gidan su Suraj sai naji gabana ya faɗi na rasa dalili. Koda mu shiga cikin tuni wasu daga cikin su Yasmeen sunyi bacci ƙalilan ne masu chat, toh nan ma maimakon mu kwanta sai a dasa da wata hirar irin ta ƙawaye da yan uwa. Mun daɗe muna hira daga baya kowa yayi bacci yayin da nidai kawai na kwanta ne amma baccin ya daɗe bai ɗauke niba dan bayi ma nashiga na ɗauro alwala nazo na tada sallah, sai gab da asuba wani bacci mai cike da mafarkai kala-kala yazo ya ɗauke ni.
_____________🖤🤍
*Abuja 🤍*
.................Tsaye yake a cikin garden daga can gurin wasu irin flowers masu kallar green da white gaba ɗaya sun ma gurin ƙawanya dan komai girmanka kaje gurin la zauna ba wanda ya isa ya ganka koda kuwa ace da rana ne balle kuma ace da dare ne. Gurin kwayar yake da hasken wuta wanda itama ta kasance green mai dan duhu-duhu, ba abinda yake sai kaida komowa acikin garden din alamu sun nuna da wanda yake jira. Kusan 5 mintues saiga wani nan yana shigowa ta kofar baya, yadda take tafiya ne da yanayin suffar jikin ta yasa na gane cewar ashe macece. Sanye take cikin shigar bakaken kaya sai wani uban hijjab data sa shi tun daga sama har ƙasa ya rufe nata sai bakin facemark shima data rufe fuska, ga wani uban glass da komai sa idon ka baka isa gane wacece ba, dan komai na jikin ta baka iya gani har tafukan hannun ta a sakaye suke cikin safar hannu.
Tunkan ta ƙaraso gurin ya zuɓe ta da kallo harta iso, shiru suyi na wani lokaci alamun kowa da abinda yake sakawa a zuciyar sa kana ya fara magana cikin tsananin ɓacin rai haɗe da fushi.
"Haka mukai dake ya kike so komai da mu shirya yake ƙoƙarin kubuce mana batare dana shirya hakan ba? Ko kinsan wannan auran shine plant ɗinmu mafi mahimmanci daya kamata ace munyi amma yana ƙoƙarin kubuce mana?" Saida taja numfashi kana cikin dake muryar ta Hadi da sakaya ta tace.
"Musalta maka irin tashin hankalin da ɓacin ran dana shiga bata lokacine a wannan bakar ranar da naji cewa wancan makirin uban nasa ya aura mishi yarinyar da sam bamu san ma daga ina take ba. Ya ruguza mana gaba ɗaya shirin mu shiyasa nayi gaggawar kiran ka dan sanin mai ya kamata muyi kafin su ƙarasa ruguza mu".
Kafeta yayi da ido harta kai arahe kana shima cikin fushi yace. "kinga duk matsalar kice wannan inda ace tun wuri kin sanar dani meke faruwa a wannan gidan naku da tuni munsan me zamuyi. Kinga yanzu munyi plant A yayi kyau plan B ya ɓaci plan C ma haka toh kinga dole mu tafi plant D mutukar muna so mu cinma burinmu".
"Wannan haka yake Yash toh amma yanzu meye shirin namu na gaba?".
Wata dariya yayi kana yace,
"Matso kiji dan wannan sam bana wasa bane dan yanzu ne za'a fara wasan wancan duk wasan yara ne hhhhh". Ya idda maganar yana sakin wata dariya, dariyar itama ta taya shi.
Toh daga nan ban sake jin mai kuma suke cewa ba dan duk Yadda zanyi naji na kasa, haka na tattaro alkalami na nayo waje🤭😂.........................✍️
*Typing📲*
_Follow my WhatsApp channel_ 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0
_Follow my WhatsApp group_👇
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_CREATED AND WRITING BY_