Showing 51001 words to 54000 words out of 84595 words
awo irin na masu hankali, na qarshen ya fi alheri a kan na farkon. Domin dai shi ne ginshiqin rayuwa. Za a iya gudanar da rayuwa ko da babu ilimin kimiyya, amma ba za a iya gudanar da ita ba idan babu mu’amala mai kyau a tsakanin jama’a.
Da wannan nake ce wa matasan nan namu masu himma, yes, muna buqatar qara qaimi daga wannan jibgewar da muka yi, don mu ma mu zama aqalla qannan Turai a ci gaban qere-qere, amma kuma, bisa la’akari da irin gudunmuwar da addini yake badawa wajen ha’b’baka nagartar halayyar bani Adama, wanda shi kuma kimiyya ba ya yi, to bai kamata mu kuma mu fi karkata ga ra’ayoyin Turawan ba, wad’anda tsanarsu ga addini da kuma ganin birgewarsu ga ci gaban kimiyya, sun kitsa mu su yawaita aikin aibata addinin da kushe shi tare da kambama ilimin kimiyyar sama da komai duk kuwa da taqaitawarsa a komai d’in. Ma’ana dai kada azar’ba’bi ya kai mu ga biye mu su wurin kushe addini a kai-a kai tare da kambama kimiyya a samansa. Kowanne na da muhallinsa.
Na’am, gazawa wurin amsa tambayoyin qurilla na mufakkirai da kuma zaluncin Coci a zamanin daular Romawa, na daga cikin dalilan da suka sa Turai ta tsani addini ta kuma juya masa baya. To amma gare mu mu Musulmi fa? Shin haka abin yake? Sam ba haka ne a wurinmu ba! Daga cikin ilmukan Musuluncin namu ne aka samu na kimiyyar, kuma almajiran Musuluncin ne suka bunqasa shi har ma duniyar yau take amfana daga gare shi.
Ga wasu ‘yan misalai:
1- Duk da qoqarin sauya tarihin ilimin lissafi na Algebra da Turai ke yi wurin d’aukaka sunan Diophantus (Masanin Lissafi na Girka) a kan na Khawarizmi, zuwa yau d’in nan fomular da aka sani kuma ake amfani da ita a wannan ‘bangare na lissafi, ta Khawarizmi ce. Shi kuma d’aya ne daga cikin almajiran Musulunci. Cikakken sunasa shi ne, Muhammad Ibni Musa Al-Khwarizmi. Ya yi rayuwa a zamanin Ma’amun, d’aya daga cikin halifofin Abbassiyya, wajejen 820 Miladiyya. A wannan lokaci, Turai na cikin duhu.
2- Ibni Sina, wanda Turawa suka malkwad’a sunansa zuwa Avicenna, wala’alla don kada Musulunci ya yi alfahari da irin gudunmuwarsa ga ilmukan kimiyya da falsafa, uba ne ga ilimin likitancin zamani. An ce ya rubuta litattafai sama da 40 a kan fannin likitanci kawai wad’anda har zuwa yau d’in nan ake komawa gare su. Littafinsa The Canon of Medicine, kundi ne na ilmukan cututtuka da magungunansu (encyclopedia). Shafin Wikipedia ya ce shi ne littafin da aka riqa amfanin da shi a jami’o’in Turai a zamanin tsakiya na wayewar Turai d’in (Medieval Era), wajejen qarni na 15 ke nan. Kazalika shafin ya ce an sake wallafa littafin a shekarar 1973 a birnin New York. Ibni Sina shi ne, Abu Ali Al-Ḥusayn Ibn Abd Allah Ibn Sina. Ya yi rayuwa a zamanin daular Abbasiyawa. A wannan lokaci Turai na cikin duhu.
3- Shafin yanar gizo na Aljazeera ya wallafa wani bincike da ya yi a kan abin da ya kira “Science in A Golden Age” wato Ilimin kimiyya a zamanin shuhurar ilimi na Musulunci. Shafin ya nuna irin ilimin Physics d’in da Ibni Haytham ya fitar a littafinsa, Kitabul Manazir (The Books of Optics), wanda ya rubuta sama da shekaru 1,000 da suka gabata. Shafin na Aljazeera ya ce, littafin mujalladi bakwai ne, kuma ya ragargaji ra’ayoyin Plato da Euclid a kan wata matsala ta ilimin Physics da ta shafi haske da gannai, kuma ra’ayoyinsa ne gaskiyar da duniya take amfana da shi a yau. Ibni Haytham shi ne Abu Ali Al-Ḥasan Ibn Al-Ḥasan Ibn Al-Haytham. Ya yi rayuwa a zamanin daular Abbasiyawa. A wannan lokaci Turai na cikin duhu.
Ke nan ashe dai, mu a Musulunci, addini bai yi abin da masu kimiyya za su tsane shi ba, qarewa ma, Malaman Musuluncin ne suka fitar kuma suka bunqasa ilimin na kimiyya a zamunansu.
Ga hujja:
Kimanin shekara dubu d’aya da d’ari hud’u wata ayar Qur’ani daga cikin suratul Hadid ta ce:
“Kuma muka saukar maka da qarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani, kuma da amfani ga mutane…”
Wannan ilimin kimiyya ne. Domin da qarfe ake qera bindiga da takubba da nukiliya, kuma da shi ake qera mota, da jiragen qasa da na sama da na ruwa. Ke nan tabbas akwai cutarwa a cikinsa kuma akwai amfani. Qur’ani ya fara fayyace hakan.
Hatta ilimin yadda za a sarrafa shi qarfen da wasunsa na daga sinadarai a kimiyyance yana tattare da dai shi addinin ne ta hanyar ingantattun hadisan da aka ji daga Manzon Allah (sawa), ko shiryayyun halifofinsa da suka sha daga Manzon (sawa).
Wata ruwaya ta zo a Nahjul Balagha cewa: “Wata rana Imam Ali (as) yana ga’bar kogin Furat sai ya ce wa Sahabbansa: ‘Da na so zan iya fitar mu ku da haske da wuta daga wannan ruwan.’”
Masana sun fassara hakan da cewa wutar lantarki yake nufi, wato “Hydroelectricity.” Hakan ne ko ba haka ba, wannan dai ya nuna yana da masaniya a ilimin qere-qere mai wuyar fahimta tun a wancan zamani wanda mutumin yau ke kira kimiyya. Me kuma ya sa bai yin ba? Wala’alla domin gudun fitinuwar mutanen lokacin ne saboda tsukewar fahimtarsu a lokacin.
Kazalika an ruwaito shi (as) Biharul Anwar yana cewa: “Shin kuna jin cewa Allah bai yi wata halittar bayan ku ba ne? Wad’annan taurarin da kuke gani a sama suna da birane kamar yadda kuke da shi a wannan duniyar.”
Kafin a haifi Galilio da kusan sama da shekara dubu, Imam Ja’afar Sadiq (as) yana da shekara 11 ya tabbatar da cewa duniya ce ke kewayawa a nata tsarin da tsaikon. Ya kuma yi sauran d’imbin zantuka da sai bayan sama da shekaru dubu ne ilmukan kimiyya ke aminta da su.
Duk wannan yana nuna mana cewa a cikin wannan addinin namu na Musulunci, muna da komai, kawai dai mu ne ba mu sani ba, don haka muke yabawa na wad’anda suka sata daga gare mu kuma suka yi sa’ayin bunqasawa.
A kan haka nake qarqare zancena da jan hankalin matasan nan namu masu himma da cewa, idan addini a wurin Turai abin qyama ne saboda zaluncin da ya yi wa kakaninsu da gazawarsa a amsa tambayoyin masu zurfafa tunaninsu, to mu a wurinmu abin alfahari ne saboda ya zo mana da komai, har ma da wanda ba mu tambaya ba. Don haka kimiyya daga addini take ba kishiyar ta ba ce. Rashin sanin hakan gazawarmu ce ba gazawar addinin ba.
Allah ya qara wa wad’annan matasa himma da qwazo da basira wurin tattaunawa da fitar da abin da zai amfani al’ummarmu, ba abin da zai raunana mata imani ba......................✍️
*Taku har kullum da ko yaushe*
🤝*Amanar taurarin writer's association📚*
_*Yawan comments and like yawan typing*_ 😜
*Typing📲*
_WhatsApp channel_ 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0
_WhatsApp group_👇
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_CREATED AND WRITING BY_
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞
✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*
*T.M.W.A.✍️*
*Amanar taurarin marubuta writer's....✍️*
Page 3️⃣4️⃣➡️3️⃣5️⃣
................Bayan mun gama gabatar da program inda muyi sallama da bakuwar mu na koma office mu ciga ba da aiki. Kasancewar yau da wuri mu tashi aiki sallama muyi da Isha MD ya ɗauke ni mu wuce, a tunani gida zamu sai naga ya dau wata hanyar daban kamar bazan ce komai ba dan tunda mu fara tafiya ba wanda yayi magana tun bayan gaisuwar da na mishi.
Ɗagowa nayi da niyar kallon sa a dai-dai lokacin shima ya ɗago yana kallon na a hankali na ɗan juyar da kaina gefe ina murmushi inda shima murmushin yayi tare da cewa. "Wai duk kunyar nan ta meye da ake kasa hada ido dani uhm beb ? Nan fa da 3 week's kin zama tawa sai yadda naso nayi dake fah"
Murmushi nayi tare da cewa.
"Ai saika bari time ɗin yayi koh"
kureni yayi da kallo na wani ɗan lokaci kana yace
"uhm aiya kusa".
Murmushi kawai nayi tare da cewa.
"Tom Allah ya kaimu amma yanzu ina zamu naga ka dau wata hanyar da ban". Da "ameen" ya amsa kana yace.
"Saida ke zanyi". Ya faɗa tare da jiyowa yana kallo na murmushi kawai nayi batare da nace komai ba, kana yace. "Wasa nike miki kinji zan kaiki ki gaida momy nah ne dan ta matsamin nakai mata ke ta gani kinga yau kuma mun tashi da wuri shiyasa nace bari muje. Amma ya kigani?". Saida na danji wani abu a zuciya jin yace zani gaida mahaifiyar sa amma ban nuna maiba sai kai dana daga mishi ina lumshe ido. Murmushi yayi mu cigaba da tafiya cikin kankanin lokaci mu isa gidan.
"Màsha Allah" shine abinda na furta ganin irin kyau da tsaruwar gidan inda kai tsaye parking lot ya nufa tare da yin parking kana ya maido da hankalin sa kaina tare da cewa. "Babe muje koh". Kallon sa nayi ganin shima ni yake kallo yasa nai ƙasa da nawa murmushi kawai yayi yana fice wa daga motar, har inda nake ya zagayo ya buɗe min tare da matsawa gefe, ba musu na fito inda kai tsaye cikin gidan mu shiga.
Zaune suke a cikin babban parlour inda mu shiga bakin mu dauke da sallama shine a gaba ni kuma ina binsa a baya kaina a ƙasa har mu ƙarasa cikin parlour. Dattijuwar matar dake zaune a kujera mai ɗaukar mutum uku kamar su ɗaya dashi sak kamar an zana ga dukkan alamu itace momy, sai wata da baza mu wuce sa'anni ba zaune kusa da momy wato mennat ƙanwar sa kenan dan duk suna kama da juna sai dai ita mennat ba sosai suke kama ba.
Gaba ki ɗayan su fuskar su kwance da murmushi inda mennat tunkan mu idda shigo wa tazo da ɗan gudun ta ta rungume ni tana mun barka da zuwa tare da kama hannu na ta nufi kujera dani. Tana niyar zaunar dani a kujerar a hankali na zame na zaune a ƙasan shimfiɗaɗɗen cafet ɗin dake malale a cikin parlour mai taushe. fuska ta ɗan bata tare da nuna min kujerar alamun in zauna, ka faɗa na make tare da marairaice fuska alamun nanma yayi, ba musu ta barni itama ta nemi kusa dani ta zauna.
Momy da tun shigowar mu ba tace komai ba sai murmushi da take yi tana kallon mu nida mennat har mu zauna sai kana tace.
"A'a ɗiyata yada zama a ƙasa? Tashi ki koma kujera ai nan gida ne".
Murmushi kawai nayi ina ƙasa da kaina tare da cewa.
"Momy nan ma ai yayi". Murmushi kawai tayi tare da girgiza kai dan tasan ba tashi zanyi ba.
A hankali na matsa kusa da ita tare da gaishe ta cikin girma mawa, itama cikin fara'a ta amsa min tare da riƙe hannu na cikin nata tana murzawa a hankali.
"Oooh sai ance ki kawo mata ruwa kenan koh mennat kin zauna kawai kina zuba surutu". Cewar momy tana kai duban ta ga mennat data zauna sai jana take da hira nidai ina amsa mata da eh ko a'a dan gaba ɗaya kunya nikeji dan tuni momy ta maidani kusa da ita tana jana da hira.
"Sorry my mom wallahi gaba ɗaya murnar ganin tane yasa na manta ban kawo mata ko ruwa bane afwan antynah". Tana gama faɗar haka ta tashi, kai kwai momy ta girgiza tare da cewa. "Allah dai ya shirya min ke". Da "ameen" mu amsa harta kawomin ruwa da drinks har da abinci toh ruwan dai kawai nasha cox gaba ɗaya MD ya zuɓeni da kallo ganin sai fira muke da momy kamar dama mun saba. Nikam kasan cewar magana tamin akan aikina shiyasa na saki jiki da ita muna fira dan saida ta sani dole naci abincin kadan kana ta barni mu taho, inda ta haɗa min shatara ta arziki naki ashe shi ya amso.
Har kofar gidan mu ya kaini kasan cewar magrib ta kusa, sallama muyi kana ya zagayo tare da buɗen mi kofa sai da naja wani lokaci kana na fito, hannu na ɗaga mai tare da nufar get har na kai hannu kan kofar naji ya kira sunana. "Safiyyah" cak na tsaya da buɗe kofar tare da waiga wa ina kallon sa da shima ni yake kallo.
"I love You".
"I love You too".
Ina faɗa na shige gida da sauri, murmushi yayi tare da lumshe idanu kana ya shige mota ya bata wuta yabar anguwar.
____________
*Abuja🤍*
A ɓangaren Majeed kuwa jikinsa alhamdulilah dan yaji sauki sosai yanzu haka ma yana part din Ammei, dan dady ya hana ayi bincike akan gubar da asama Majeed yayin da hakan yayi ma wasu daga cikin su daɗi wasu kuwa sun so ayi binciken amma dady ya hana, dan da kyar granny ta yadda dan tace sai anyi bincike an gano wake son kashe mata jika. Haka dai granny tayi ta gama amma dady ya kashe maganar ba yadda su iya haka su hakura.
⚫Kwance yake akan cinyar Ammei sai shagoɓɓa yake zuba mata itakuma tana lallaɓa shi Auta dake gefe sai dariya take.
Gaba ki ɗayan su zaune suke cikin parlour Ammei inda suke kallon program ɗin da Safiyyah take gabatarwa akan Tarbiyya.
Tunda ta fara magana yayi shiru yana saurare yayin da Ammei da Auta gaba ɗaya hankalin su yana kan TV, shiru yayi nawani lokaci kamar mai nazarin maganar da Safiyyah take yi itada da abokiyar aikin ta.
Yanda take bayani akan TARBIYYA cikin nutsuwa kasan cewar yau ba facemask a fuskar ta iya kacin eyeglasses ne kawai yasa ake iya ganin fuskar ta tar. Bayan sallama da tayi tare da gabatar da bakuwar tata ta fara magana cikin zazzakar Muryar ta mai saka nutsuwa ga mai sauraro, dan Allah yayi baiwa agurin Allah ya bata murya mai cike da wani kalar sirri a ciki.
*TARBIYYA A ƘASAR HAUSA*
Kalmar tarbiyya, ararriyar kalma ce daga Larabci (التربية aka Hausantar da ita. Kalma ce magamaiya, wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta renon jikin yaro; hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa, tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a, a al’ummance da kuma ɗaiɗaiku.
Ƙololin buƙatar tarbiyya ita ce gina cikakken mutum mai amfanar da kansa da kuna waninsa.
Bisa la’akari da wannan faffaɗar ma’ana da wannan kalma take da ita, rubutun zai taƙaitu ne wajen yin magana a kan abin da ya shafi ruhi da kuma cuɗanya. Zai yi magana bakin gwargwado a kan ma’anar tarbiyya, manufarta, amfaninta, masu bayar da ita, jerin wasu kyawawan halaye da kuma yadda Bahaushe yake bayar da tasa tarbiyyar, da sauransu bakin gwargwadon iyawa.
*Ma’anar Tarbiyya*
Saboda zamowar kalmar tarbiyya mai tushe a Larabci, zan kawo ma’anarta a Larabce da cewa, “Ita ce ayyukan ɗaukakowar halittu, wato ƙarawa mutum mutumtaka domin ya samu kaiwa cikakkiyar daraja matabacciya a jiki da aiki da ruhi da kuma cuɗanya”, Abu Hamza (2013). Daga wannan ma’ana za mu iya fahimtar cewa, tarbiyya reno ce. Saboda dukkan abubuwan nan da aka ambata suna ƙunshe cikin reno. Shi kuwa reno ana yin sa ne mataki-mataki. Sai dai ya fi zafi a tsakanin ranar farko ta haihuwa zuwa shekara uku. A wannan tsakanin komai yi wa mutum ake yi. Ɗawainiyoyin suna fara raguwa ne bayan an yaye mutum wato daga watanni 15 na haihuwa zuwa shekaru 2. Daga wannan mataki yawancin yara sukan fara yi wa kawukansu wasu abubuwan kamar ci da sha da sauran ƙananan abubuwan rayuwa.
Daga wannan mataki na yaye kuma, sai a shiga kiwonsa, da ma’ana ta lura da zirga-zirgarsa ƙut-da-ƙut har zuwa kamar shekaru 5 ko 6, idan zai kai kansa mahallaka ko dai a ce da shi bari, ko kuma a je a ɗauke shi ko a janye shi da sauransu.
Idan ya haura shida kuma, to ya fara kai wa matakin da zai fara cuɗanya da wajen gida, sai kuma ya shiga makaranta. A makarantar ma renonsa ake yi, saboda a koyar da shi ne alaƙoƙin da suka shafi rayuwarsa ta duniya da kuma ta lahira, iya tsawon karatunsa da ma rayuwar baki ɗaya.
Saboda haka idan muka koma kan waccar ma’ana ta tarbiyya muka ciro kalmomin cewa, ayyuka ne da ke ɗaukaka halitta, za mu gan su cikin wannan ɗan taƙaitaccen bayani game da reno da na yi.
Ana kuma iya cewa, tarbiyya ita ce horas da yaro kyawawan halaye domin ya zama mutum nagari. Ko kuma a ce, hanya ce ta nuna wa yaro yadda zai tashi da kyawawan halaye ababen yabo a cikin jama’a.
*Manufar Tarbiyya*
Babbar manufar tarbiyya ita ce samar da mutum mai kyawawan halaye ababen yabo domin ya zama mai amfanar da kansa da kuma waninsa.
*Amfanin Tarbiyya*
Amfanin tarbiyya ba zai ƙidayu ba, amfaninta na ƙarshe; wato maƙurar amfanin nata shi ne mutum ya samu kansa a gidan Aljana a lahira, a nan duniya kuma ya zama son kowa, ƙin wanda bai samu ba.
Waɗannan gajiyoyi da za a ci; duniya da lahira, su ne maƙura, sai kuma wasu ɗaiɗaikun abubuwa da zan lissafo kamar haka:
Numfashi ta sauke tare da gyara eyeglasses din idanun ta, kasan cewar tabar facemask dinta a office a hankali ta cigaba da magana cikin nutsuwa gami da kamala.
Tsarkake Halaye: Tarbiyya tana tsarkake halayen mutum ya zama mai kyawawan halaye.
Sauƙin Rayuwa: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya rayu, rayuwa mai sauƙi. Saboda zamowarsa mai wadatar zuci.
Farin Ciki: Mutum mai cikakkiyar tarbiyya akan same shi cikin annashuwa a mafiya yawan lokutansa. Saboda koda wani abu can gefe ya ɓata masa rai, to yasan idan ya zo yin hulɗa da wani wanda abin bai shafe shi ba, sai ya danne wancan ɗacin a ransa shi kaɗai.
Girma da Ɗaukaka: Kyakkyawar tarbiyya tana ɗaukaka darajar mutum a idon mutane