Showing 66001 words to 69000 words out of 84595 words

Chapter 23 - RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

15 Nov 2025

1138

mai ɗaukar ido, hummm 😌 gaskiya ba'a magana dan kunshin yayi mutukar kyau yadda bakwa tsammani. Ga gashi yasha wanki yasha gyara tubarkallah Masha Allah, dan Allah yama Safiyyah baiwar gashi ga tsawo ga cika sai ɗaukar ido yake. Ƙamshi kam hmmm ba'a magana nace ba'a magana hajiya ko kina nesa da ita matukar ta gitta sai kin jishi.
2:00pm su Buhaisa suka dawo daga gurin kunshi da gyaran kai dan harda anty Hajara dan haka suna dawowa ciki su shiga kota kan amarya basu biba suma su fara nasu shirin inda ganin su Yasmeen dasu Tasleem yasa su rungume juna ana ihun murna.

A ɓangaren amarya fah ana can ana kintsa tane dan wata irin shegen kwalliya mai natsuwa akema Safiyyah, komai dai-dai misali ba'a cika shi da shirme ba. Dan mai kwalliyar ƙwararriya ce tun daga Abuja Luba ta ɗakkota dan komai daya shafi amarya itace keyi. Matar ta gogu da sanin takan duniya ne ƙwarai da gaske. Ƙarfe 2:50pm an gama shirya amarya Safiyyah cikin doguwar riga na lass pitch and white color daya tsaru mutuka ga wani ɗinki dan ubansu na doguwar riga Fitet gown. Tun daga sama zuwa gurin cinyar ta a matse take sai da aje dai-dai cinyar ta a saki rigar ta wani buɗe har ƙasa ta wani irin fidda ainahin surarta tamkar zane a takarda dan har ƙasa take jah ta baya. Ga wani fitinannen ɗaurin data kashe mata shi a kanta mutukar zaunuwa ɗaurin kan Safiyyah ya zaunu, ga wata tamfatsetsiyar Sarƙa da ƴan kunne zuwa bangles suma sun haɗu haɗu ta musamman. dan ƙareriyar sarƙa ce da akama ma wani irin adon fararen stones, sai wani irin mayafi mai net dashi ma akasa fatan ɗin less din ayi mai kwalliya dashi shima pitch color, ga wani hadadden takalmi mai shegen kyau bashi da tudu sosai data sa sai ya zauna mata dagwas a kafa ya rabba. Dole ka kalla wannan amaryar ka sake kallo dan takai zama abin kallon. Ita kanta sai take jin kamar ba ita ba. Lokacin da Luba da anty Hajara da itama tuni ta kintsa suka fito da ita falo. sumar zaune tawagar Mom suyi dan da zasu iya rantse wa da Allah badin sun san Safiyyahn itace amarya ba da kai tsaye zasu ce ba ita bace, aran su kuwa imagine suke inama ace Anty Waleeda ce a haka. su Buhaisa da zaman su kenan suma cikin nasu shirin aikuwa suka shiga faɗin, “Woowww!!“ Suna miƙewa. Kafin kace mi hasken camara ya fara hasketa tako ina.
kansu su anty Hajara sai hotuna suke zuba mata haka su Yasmeen. Sosai tai ƙyau komai ya fita da fitarsa, sai ƙamshi take zabgawa kamar a kamfanin turare.
Tuni dama dangin ango sun zo dan haka kai tsaye harabar gidan su Mami (maman su Isha) itada wata farar mata kyakkyawa itama makotan su Ummi ne kuma kawar ta ce sosai baji ba gani itada Mami Hajiya A'isha su fita da ita, dama tun kan a fita da ita bayan hotunan dasu gama sha aka rufe mata fuska da net ɗin dake a matsayin mayafi.
Tunda Safiyyah ta fito Ummi ta tsaya cak tana ƙare mata kallo gaba ɗaya kamannin yar uwar ta take hango a jikin Safiyyah, a hankali ta goge kwallar data gangaro mata a ido kafin idon mutane yakai kanta, sai dai ta makaro dan tuni Safiyyah da ake ma hoto tagani aida dan gudunta ta ƙarasa ta rungume ta itama tana niyar sakin kuka. Cikin sauri ta ɗago ta tare da girgiza mata kai alamun kartai kukan tana ɗauke mata guntun hawayen daya gangaro mata zuwa kumatu rungume ta ta sake yi tana raɗa mata magana a kunne dayasa ta sakin guntun murmushi. Gaba ɗaya gurin tafi ya ɗauka kama daga dangin amarya har na angon.
Sosai harabar gidan tasha decoration irin na gargajiya daya mutukar ƙawata gurin. Haka 'yan mata ne sosai a gurin kowa ce dana ta gayun, daga ɓangaren ango har dana amarya sun haɗe yayin da ba ɓata lokaci a fara abinda ya tara su.

Alhamdulilah an gama Kamu cikin aminci dan komai fa ya kayatar kayatarwa ta musamman kama daga dangin ango dana amarya kam an rabu cikin farin ciki da nishadi sai dai fatan Allah ya kaimu goben lpy. Toh kusan abu na social media ga Kamu ya tara manyan mutane harma da yaran kuma zamani na kowa wayar sa, TUNI KAMU NA SHAHARARRIYAR YAR JARIDAR NAN WATO *SAFIYYAH A IBRAHIM* TA GIDAN TV HASKE DAKE WAYAR DA KAN MATASA DA KUMA JAN HANKALI GA IYAYE AKAN TARBIYYA. ya shiga zagaye social media. Toh mudai sai dai fatan Allah yasa alkairi.






_________________🖤🤍

*Abuja 🤍*





..................gaba ɗaya familyn zaune suke a part din granny kasan cewar duk dare bayan gama dinner can suke zuwa wataran ma can suke yi inka cire Yah Majeed. Zaune suke cikin farin ciki da anna shuwa ana hira wasu kuma na wata sabgar tasu daban daka kalli granny kasan tana cikin farin ciki na haɗuwar familyn nata, inka cire uncle Kabeer dake can Saudiya da iyalan sa shima kuma ana waya dashi kullum. Hira tayi hira tsakanin mayan yayin da kuma yaran ko wacce ta dukufa kan wayar ta sai masu hirar suma jefi-jefi.
Cikin zaro ido Auta ta ɗago tana kallon granny ga dukkan alamu wani abun mamakin ta gani, har tana harɗewa wajan cewa, "laaaa granny kinga yau ake Kamun Safiyyah ta gidan Tvn haske". Gaba ɗaya ido su zuba mata suna kallon ta, cikin waro ido itama granny tace, "Na shiga uku na ni Maimunatu Kamu fah kice aure zatayi?". Kafin Auta tayi magan Basma ta amshe da faɗin, "eh granny aure zatai dan yadda najima gobe ne ɗaurin auren shirin faɗa nake ma Auta ta rigani". Kasa cewa komai granny tayi sai sallallami da take yi Azima ce itama cikin nata salon yangar tace, "kai granny naga duk kin tada hankalin ki saika ce wacce akace iskanci take, aure nefa dan gaba ɗaya social media ta ɗauka sai hotunan tane ke trending". Itama granny cikin hayayyako wa tace, "Ina ruwan kine dani". Kana ta koma kan Auta tare da cewa, "wazata aura" shiru Auta tayi alamun nazari kafin tace komai Azizat tace, "MDn gurin aikin su naji kamar ana cewa".
Haba granny ta sake riƙe wa tare da cewa, "Ooo Ni maimuna".
Zaituna kuwa a zuciyar ta cewa tayi, "kaji tsohuwar nan da fitinar tsiya ina ruwan ta nema oho saika ce tana da wanda zata aura mata ne". Toh ba iya granny maganar auren Safiyyahn ya taɓa ba harda su Addah.

A dai-dai lokacin da zai shigo parlourn na granny yaji kalmar Auta tamkar wanda a doka da guduma haka yaja ya tsaya cakk.....................✍️









*Typing📲*







_Follow my WhatsApp channel_ 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0


_Follow my WhatsApp group_👇


https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB









*🌹 RAYUWATA 🌹*

_CREATED AND WRITING BY_

*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞










*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

*T.M.W.A.✍️*






*Amanar taurarin marubuta writer's....✍️*



*TEAM HAZIKAI BIYAR 💪✨*













Page. 4️⃣2️⃣➡️4️⃣3️⃣




..............Kamar zai shiga ko me ya tuna sai kuma ya nufi part din shi Youseef dake biye dashi da shima yaji zancen nasu Auta kai kwai ya girgiza yabi bayan sa domin ajimai kayan shi. Kai tsaye upstairs ya haura nan ma bai tsaya ba ya shiga ƙoƙarin zame kayan jikin sa domin yadda kansa ke sarawa ba abinda yafi buƙata sama da ruwan sanyi. Towel ya ɗaura kana ya shige bathroom din, tsawon minti arba'in da biyar ya dauka kana ya fita sanye da bathrobe white color sabuwa dal, ƙaramin towel dake a hannun sa yana goge kwanta ciyar sumar sa.

Gaban mirro ya karasa yana ɗaukar hand dryer ya jona a socket cikin cikin ƙan ƙanin lokaci ya kammala gyara ta, ko mai bai shafa ba sai sprays dinsa masu shegen ƙamshi yasa. Kana ya nufi close ɗin sa, tsaf ya fito cikin jallabiya fara tar ga dukkan alamu sabo ce. tsaf ya gama shirin nasa ya koma gaban mirror yayi wankan tsaddadun turarukan nasa masu ƙamshi kace ba dare bane.
Duk wannan shirin da yake kana kallon fuskar sa zaka fahimci bashi da walwala sam, duk da dama ba ma'abocin murmushi bane amma yanzun fuskar sa a mutukar tamke take ba walwala sam. Tuna tare su taho da Youseef yasa shi dafe kai tare da addu'a Allah yasa bai tsaya jiran sa ba ya tafi dan shi ɓacin ran da yake ciki ne yasa ya manta bai tsaya ya sallame shiba. Dan shi mutum ne me mutukar mutun ta ɗan adam, ko ya yake koda kuwa wanda ke aiki a ƙarƙashin sa ne, bare kuma wannan da yake Aminin shi da bashi da wani amini sama dashi a faɗin duniyar nan inka cire su Dady.

Cikin nutsuwar sa da izza da koda ace yana cikin damuwa ba lallai ka gane ba yake sauko wa daga upstairs din nashi, aikuwa can ya hango Youseef kishin gide a kujera yana waya sai uban murmushi yake. Shi sai abinma ya nemi bashi mamaki duk da dama yasan Youseef king of love ne shi kuma ta yadda halinsu ya ban banta kenan da nashi. Ya daɗe tsaye a yana kallon Youseef da sauraron shi amma kwata-kwata bai san ma ya fito ba (danya yi nisa sosai a kogin love❤️😂) jin Kamar tsayuwar mutum a bayan sa ne danshi sai yanzu ma ya farga da kamshin turaren shi aikuwa yana waiga wa yaga Yah Majeed tsaye kikam kamar wani soja yana kallon shi. Dariya ce taso kufce ma Youseef sai kuma ya danne baiyi ba sai murmushi da yayi kana yace, "Sorry my beb bani 1 hours plzzz". Ban San me ace mai daga can ɓangaren ba yadai cire wayar a kunnen shi.
Ganin yadda ya kafe shi da ido yasa shi saurin miki wa tare da ƙame wa kamar wani soja, sun kuyar dakai yayi alamun jin kunya kana yace.
"I'm sorry Sir".
Sai kuma ya kwashe da dariya ya koma kujera ya zauna yana cigaba da dariyar shi. Majeed madai murmushi yayi mai sauti tare da kaiwa zaune kusa da Youseef ɗin, duk da cikin ɓacin rai yake saida Youseef yasa Nishaɗi dan ya tuna masa baya ne lokacin suna yara. Cikin silent voice ɗin sa dake fita da ɗan amo yace,
"Ina can ina jimamin nabar ka kai ɗaya ashe kai kana nan ana abinda a saba. Allah ya shirmin kai Youseef wata ka kuma samo wa kenan?".
Dariya Youseef yayi tare da amsa wa da "ameen" batare daya bashi amsar tambayar shiba, hakan ya tabbatar masa da watan ya kuma samu, kai kawai ya girgiza tare da cewa,
"Adai ringa jin tsoron Allah, in kana tunanin Amma bata da wata toh Ammei nada Auta".
Murmushi mai sauti Youseef yayi kana yace, "Allah boss bafa yaudara bane kawai dai fashion love ne".
" Ummm"
Kawai yace alamun karshen zancen kenan, shima Youseef ɗin murmushi yayi ganin boss din ya saki jikin shi akan ɗazu dasu shigowa part din. Shima cikin sanyin murya yace, "Boss Wai ya batun zuwa Kaduna ne?"
Shiru yayi na wani lokaci kafin ya buɗe baki kamar baya so yace,
"Bari muga zuwa gobe".
"Allah kaimu lpy"
ya amsa da "ameen" asaman labba ba wata hira suyi ba yamishi sallama ya fice shikuma ya haura sama domin kwanciya. Ya daɗe yana juyi a gadon amma baccin ya gagara ɗaukar sa dan ba abinda yake sai tunani daga baya ma bathroom ya shiga ya ɗauro alwala ya fara gabatar da nafila......


________________🖤🤍


Washegari ta kama Friday gaba ɗaya familyn suna a dinning area suna breakfast inka cire Dady da Majeed, shi dady bayama ƙasar shi kuma Majeed yana part din sa, har su gama breakfast bashi ba alamar sa, gaba ɗaya hankalin wasu daga cikin 'yan matan bashi a jikin su na rashin ganin abin son nasu musamman ma Zaituna. kuma shiru Youseef baizo ba alamun maybe yau bazai fita aiki ba. Addah ce cikin yar dumuwa tace,
"wai nikam ina my son ne naga kwata-kwata yau bai fito ba". Ta faɗa idon ta akan Ammei da itama duk ta damu dan gaba ɗaya hankalin ta na akan upstairs kozai sauko amma bai sauko ba harsu kammala breakfast din wasu daga cikin family ma duk sun fita aiki. Mummy ce ta taɓe baki tana cigaba da danna waya anty Amarya kam ta fita gurin aiki haka Mama itama bata a parlourn. Cikin danne damuwa Ammei tace,
"Nima dai naga bai fito ba gaba ɗaya yau banjin ma yaje masallaci inba kota kofar part din shi yabi ba". Mummy da takaici ya tirnike tace, "ikon Allah wai nikam Majeed ɗin ƙaramin yaro ne kome har dan bai fito ba zaku wani bi ku damu saika ce yaron da baisan kansa ba". Mama da fitowar ta kenan daga kitchen taba Mummy amsa da, "Eh Majeed ba ƙaramin yaro bane amma ko kece a matsayin ki na babar shi in kikai wannan lokacin baki fito ba dole a nemeki aji ko lafiya". Kafin ma Mummy data shaƙa ta bata amsa tace,
"Ke Auta maza jeki part din nasa ki duba mana ko lafiya ko zamu sami su kuni". Da "to" Auta ta amsa kana ta miki ta nufi upstairs zuciyar ta cike da sake-saken ko Yayan nata yana lpy kuwa. Kwafa Mummy kawai tayi ba tare daya sake cewa komai ba. Yayin da Addah ta sauke ajiyar zuciya, Ammei dai ba tace komai ba dan ita irin matan nan ne wanda sam magana bata dame taba dan zan iya cewa ma Majeed ita ya gado gurin mulki da rashin son magana dan shi harya ma fita. Zaituna kuwa ji take inama ace ita Mama tace taje taga ko yana lpy, amma ya zatayi.

A ɓangaren Auta kuwa koda ta isa part ɗin nasa haka yake tsittt dan kwata-kwata ba haske a parlourn saina hasken rana ɗaya fito, amma gaba ɗaya fitulin a kashe suke alamun ma bai sauko parlourn ba. Kasan cewar makunin a farkon shigowa yake yasa Auta danna shi aikuwa gaba ɗaya haske ya mamaye parlourn. Tsaf yake tamkar ba'a zauna a cikin shiba ga wani irin kamshi mai sanyi dake tashi, saida ta gama ƙare ma parlourn kallo kana ta nemi guri ta zauna a kujerar dan tasan halin yayan nata ba'a shiga mishi daki kai tsaye, kuma tunda taga bashi a parlour tai tunanin ko yana bedroom ne. Zama tayi na 5 minutes shiru bai fito ba a hankali ta nufi upstairs din nashi takai gurin 3 minutes a bakin kofar bedroom ɗin sa kafin ta fara knocking, Amma shiru dan ko motsi bata ji kusan 5 minutes ta tura kofar cikin sand'a ta shiga.
Dind'um ɗakin yake dan komai na wuta a kashe yake inka cire ehsin dake kune dan gaba ɗaya dakin ya dau wani irin sanyi mai shiga cikin jiki, saida Auta ta ɗan matse jikinta saboda sanyi cikin tsanani tsoron dake gudu a zuciyar ta ta fara ƙoƙarin kunna wutar ɗakin dan zaman yayan nata cikin duhu ga sanyi tasan me yake nufi. Can ta hango shi kudundune cikin blanket sai uban tsumar sanyi yake yi, ai da sauri Auta ta nufi gurin ehsin ta kashe dan ita kanta da shigowar ta kenan ɗakin sanyin ya fara damun ta bare shi daya kwana cikin sa. Kafin cikin sauri hartana harɗewa ta nufi gadon, bargon daya rufe jikin sa dashi ta yaye inda wani uban hucin zafi ya buso mata a da sauri ta saki bargon tana niyar barin ɗakin, cakk ta tsaya saboda tozali da tayi da hoton wata kyakkyawar baiwar Allah a cikin system ɗin sa dake ajiye a kan side drower. Kur tayi tana ƙare mata kallo inda take sanye cikin White hijjab face din ta sanye da facemark sai eyeglasses dan siriri fari tar shima. Yanda zuciyar ta ke tsillo a kirjin ta yasa ta koma wa dabas ta zauna tare da maida system ɗin kan cinyar ta tare da zoming ɗin photon dan sake tabbatar da wacce take tunani ce ko wata daban.
"Kwarai kuwa Safiyyah ce"
Ta faɗa a fili sai kuma cikin sauri da kama baki ta waiga tana kallon shi dan ita tsabar kiɗimar ma da tayi na ganin photon Safiyyah a system ɗin yaya Majeed ɗin yasa ta manta da bashi da lafiya, amma waiga War da tayi yasa tunanin ta ya dawo jikin ta. "Habibah ki nutsu yanzu ba lokacin tunani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login