Showing 63001 words to 66000 words out of 84595 words
yake amma Suraj ya ruga saidai hakuri. Toh a bangaren Ummi ma hakan take dan tuni ta gano son da Yah Saif yake ma Safiyyah ita kanta zata so yarinyar 'yar uwar ta ta dawo kusa da ita toh amma me haka Allah yake ikon sa sai dai suyi fatan Allah yasa alkairi amma komai ya kare kuma.
Around 4:pm Yah Ahmad yabi jirgi ya koma Abuja inda yabar anty Hajara anan dan ita tazo kenan sai kuma bayan biki shima dai yace insha Allah zai shigo ranar bikin. Adaren kuwa munsha hira da anty Hajara dan har Abba ya dawo muna hira daga baya kowa ya nufi gurin kwanciyar shi.
________★
Washegari Suraj yazo kawo min kayan da zansa a gurin dinner da walima da kamu dan nace nifa bana son wasu events iyakacin walima, kamu, sai dinner da yace abokan sa sun shirya ma za'a yi hadin naso ba na yarda dan Buhaisa har haushina tasoji itada Isha, acewar su su kadai su san yadda su shirya ma bikin nan amma wai na musu cikas nidai bance komai ba sai hakuri dana basu. Da kyar Luba ta yadda tabarni zanje gunshi saida Ummi tasa baki kana ta yarda.
Nayi kyau sosai cikin abaya k'irar Saudia baka daga ciki nasa wandon Jen's Blue da farar riga data min kyau. Dan kwallin abayar kawai nayi rolling a kaina dan ko turare ban saba saboda kamshin daya gama maye jikina ga wani irin glowing da fata ta take.
babu jimawa ta fita. Tunda ta fito ya zuba mata ido, sai ya zam tana takune tamkar da bugawar zuciyarsa. ALLAH ya jarabcesa da son wannan halittar ƙwarai da gaske. Yana kuma fatan mallakarta nan da kwana uku kacal. Safiyyah ta tsani kallo, dan haka sai da ta masa tsogumi akan kallon ƙurillar da yake matan. Baice komai ba face basarwa yana sakin murmushi. Itama sai ta bata ce komai ba kawai ta shiga gaishesa. Ya amsa mata da kulawa, kana su shiga ciki bayan sun gaisa da Ummi dan bai wani jima ba ya bata kayan daya kawo mata yama Ummi sallama yayin da ita kuma ta fita raka shi.
Juyowa yayi a hankali yana kallon ta kana cikin sayin murya yace
"Babe" da "na'am" na amsa kana na ɗago aiko idanuna su faɗa cikin nashi da shima kallo na yake yi, kallo muke ma junan mu mai wuyar fassarawa. Nina fara janye nawa idon tare da yin ƙasa da kaina, murmushi yayi kana ya katse shurin namu ta hanyar faɗin.
"Please babe ki kulamin da kakin sosai Please". ya haɗe hannun shi alamun roko🙏🏽 , kai kawai na daga mishi tare da cewa "insha Allah". Ba wani hira mukaiyi mai yawa ba dan time ɗin da Luba ta dibamin bashida yawa dan haka bai wani daɗe ba ya tafi. Har bakin get na rakashi dan saida yama motar sa key sannan na shigr ciki cike da kewar sa.
Kodana shiga ciki matsamin Ummi tayi akan sai mun shiga parlourn Abba naga kayan lefe na, ba yadda na iya na tashi mu hau sama harda su anty Hajara dan itama bata gani ba. Toh ba abinda za'a ce saidai ace Masha Allah dan tabbas MD sunyi bajimta sosai dan sun zuba kaya sosai dan wannan fa shi ake kira da akwatin yar gata. Kayan da ya kawo min na events Buhaisa ta shigo dasu suma dai komai yayi sai dai ace Allah ya kaimu lokacin. Ba wani daɗe wa mu kayi a parlourn Abba ba mu fito kasan cewar ni Luba na nemana dan gobe nema Walima.......................✍️
*Typing📲*
_Follow my WhatsApp channel_ 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0
_Follow my WhatsApp group_👇
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_CREATED AND WRITING BY_
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*
*T.M.W.A.✍️*
*Amanar taurarin marubuta writer's....✍️*
*TEAM HAZIKAI BIYAR✨*
Page. 4️⃣0️⃣➡️4️⃣1️⃣
.....................Ina ciki Isha tazo can na jiyo hirar su itada Buhaisa ji nayi kamar na fito amma ba dama, dan tunda bikin nan y rage saura kwana ki kaɗan Luba ta kara kaimi akan da duk da da dinma anyi amma fa na 'yan kwanakin nan yafi na da.
Dan Sosai take min gyara na fitar hayyaci, ciki da waje ga wani uban ƙamshi na bala'i a dukkan motsina. Ko guri na gitta saika ji kamshi ya zauna kaman nice zaune agun. Fatata kuwa wani irin santsi da take da walƙiya abin ba'a magana. Gaba ɗaya ji nake a jikina komai ya canja. Hatta gashina, ƙafafuna da tafukan hannuna gyara Luba ke musu na musamman Dan hatta baki da lips ba'a bari ba..
________________🖤🤍
A bangaren gidan su Suraj kuwa koda yan kawo lefe su koma sun faɗi irin karrama sun da ayi a gidan su Safiyyah sai kuma maganar ta Mom data tsaya ma ƙanwar maman Suraj a rai. Da take cewa, "ai saurayin yar tane ayi mata kwace da asiri" koda ta tambayi yayar tata saita Bata amsa da. "bakin ciki ne kawai Zubaidah kinsan halin kishi irin n mata, kuma ita Safiyyah maman ta bata a gidan dan wayar gari ma ayi aga bata a gidan kuma dai zargin da ake itace ta koreta, toh kinga kuwa ai komai zata iya faɗa".
"Wallahi kuwa yaya shiyasa tunda muje tana kace a kujera sai habaice-habaice take".
Murmushi kawai mumy tayi tare da cewa, "shiyasa nake mutukar son yarinya nan wllh, gata da nutsuwa dan duk wanda ya same ta a matsayin mata kam ya dace,"
da haka su rufe hirar Safiyyah da samata albarka yayin da
sosai suke shirya biki na ƙerewa sa'a dan daga uwar angon har uban agon wannan shine zasu fara aurar da ɗan su na fari shiyasa kowa ka gani yana cikin farin ciki da kuma shirin bikin. Daga Mumy har anty zubaidah basu da wani lokaci na kansu dan sun shiga busy sosai akan bikin. Itama dai Mennat ba'a barta a baya ba, gurin shirye-shiryen bikin yayan nata dan jefi-jefi take samu ma ta tabo amarya. dan ita kanta ta maida kanta busy ne a cewar ta ai daga shi ba wani biki da za'a sake yi a gidan sai nata.
Toh ta ɓangaren Suraj ma shirye-shirye suke ba kama hannun yaro shida abonka sa. dan har wata yar ƙwarya- ƙwarya walima su haɗa mishi bayan daurin aure sai kuma dinner da duk sudin ne dai su haɗa. Dan acikin abokan nasu kusan shine baida aure shiyasa suke a shirye a harkar bikin dan su Al'ameen babban abokin sa nema yaso rako shi gurin Safiyyah lokacin da zai kawo mata kayan events din Amma fir MD yace aa dan shi akwai shi da kishi acewar sa zasu gama kalle mishi mata tun kafin ta shigo, haka su gama zolayar shi su hakura.
_______________🖤🤍
............Gidan Abba fah abu ya musu yawa dan gaba ɗaya Mom itada ɗiyar tata hankalin su a mutukar tashe yake ganin biki ya matso kwata-kwata saura 2 days ga gaiyata ta walima da a aiko musu daga gidan Ummi gobe in Allah ya kaimu. A lokacin da invitetion ɗin ya iso ga Mom bayan gama karan tawa da tayi, wata irin a Shari'a ta lailayo ta dire ma ɗiyar kawu Bala Kafin ta yaga shi tai mishi gutsi-gutsi ta watsa mata, tare da zuba mata gargaɗi akan ta fice mata a gida kafin ta fito ta same ta.
Itako Bahijja cikin sauri ta fice tana dariya da hali irin na Mom dan su kam ba abinda zai hana su zuwa gurin walimar harma da kamun, karo su kusa yi da anty Waleeda da duk ta rame a tsaye dama ita abu ba aukiba duk ta kara zabge wa dan Allah ya jarabce ta da mugun son Suraj gashi ana shirin ɗaura mai aure da ƙanwar ta ƙanwar tata ma wacce tafi tsana sama da komai a duniyar nan dan yanzu wata irin tsanar Safiyya take ji dan ji take ko wuka a bata ace ta kashe wani a duniyar nan kai tsaye Safiyyah zata daɓa ma dan yanzu haka ji take kamar ta bita gidan Umma Halima ai duk wacce za ayi toh amma ba dama dan ko gidan bata sani ba tasan dai suna a anguwar rimi ne shi kadai kawai ta sani game da su.
Tana a wannan tunanin ne har ta bangaji Bahijja bata sani ba da kallo kawai Bahijja ta bita har ta shige cikin parlourn. Kai kwai ta girgiza tare da furta. "Allah ya shirya". Kana ta fice a gidan.
Kamar wacce a jefo cikin parlourn anty Waleeda ta shigo inda ta sami Mom zaune sai uban huci take, da gudu ta karasa ta faɗa jikin ta tana sakin wani marayan kuka, hankalin Mom duk ya tashi haka take rarrashin yar gwal ɗin Tata da mata alƙawaruru ka iri-iri da rantse-rantse akan batin fasa auren nan. Ita abun haushin ma tunda Safiyyah ta bar gidan bata sake dawowa ba, toh amma tasan dai iya wuya sai dai a dawo gidan ubanta ayi bikin koh, toh anan zata nuna mata ainihin ta dan saita sa an batar mata da ita a duniyar kamar yadda ta battar da mahaifiyar ta. Fatan dai Allah yasa kar suzo da wannan ƙanwar uwar tata Halima.
Haka su cigaba da tsine ma su Umma Halima har Yah Safwan ya dawo gidan shigowar sa baisa sunyi shiru ba, saida ya kai zaune kana yace,
"amma Mom bikin yarinyar nan Safiyyah yazo ban saniba kuma baki faɗa min ba?". Ya tambaye ta yana kafeta da ido itama cikin fusata tace, "Ban faɗa ba idan ƙanwar uwar kace kota ubanka sai inji". "Kai Mom ƙanwata cef.....a".
Tsawar data daka mishi ce yasa shi ɗago wa yana kallon ta dan shi sak Abba ya dakko bashi da faɗa ko kadan, itama cikin tsawa tace, "karka sake kiranta da ƙanwar ka dan duk duniyar nan Baby ce kawai ƙanwar ka sai kuma Waleeda antyn ka amma inba suba baka da wasu kanwa ko yaya". Baki ya buɗe da niyar yin magana ta katse ta hanyar cewa, "bace min da gani shashasha mara kishin kanshi dana uwar sa". Bace komai ba cikin sanyi shi ya wuce dakin shi, su kuma su raka bayan shi da harara kamar ido zai fado.
A ɓangare Abba ba wani shiri da yake yi na mahaifi zai aurar da ɗiyar shi, saida su kawu Bala su mishi tatas tare da kawo mishi invitetion ɗin bikin dasu bugo a matsayin su na iyaye, kwarai da gaske Abba yaji daɗi sosai dan har fuskar shi ta nuna toh shine fah harya fara raba ma abonkashi na kasuwanci invitetion ɗin dan sai yanzu ma yake ji a jikin sa na zai aurar da ɗiyar tashi. Rabon ma daya ganta tun da tazo tace mai zata gidan Umma Halima da rabon da ya taka Kafa yaje tun sanda yaje amso Safiyyah bayan batar mahaifiyar ta da Umma Halima ta ɗauke ta. Saidai jefi-jefi suna haɗu wa da Abban su Buhaisa. Shi sai yanzu yake jin rashin kyauta warsa na watsar da Umma Halima toh amma wataran tasa gane kanshi yake kwata-kwata.
Toh shima ya Ansar gobe yake saran shigowa cikin garin na Kaduna dan duk wani abu daya kamata mahaifin yayi toh yayi shi ba tare da shi kansa Abban ya sani ba harma dasu Safiyyahn. Dan yadda zai aurar da Yar ƙanwar tasa da yake mutukar kauna.
_______________🖤🤍
Washegari Laraba walima ce ta yamma ce, ƙarfe huɗu za'a fara
Gaba ɗaya gidan na Ummi cike yake da baki kasan cewar yau ne walima, Safiyyah nacan cikin bedroom din Ummi Luba tazo damai kwalliya domin yima amarya, duk dai yau ba mai yawa za ai mata ba. Amma kafin ayin ma tasha turare harda na tsiya, kai Luba tasan sirrin ƙamshi, tsaf aka kwalliyeta aka sakata ta shirya cikin wata fitinanniyar shadda yar uban su wacce ta kasan pink color kai da gani kasan an kashe kuɗi sosai gurin ɗinkin ta. Matuƙar ƙyau Safiyyah tayi kam kamar ka saceta ka gudu. Ga wani ƙamshi mai azabar daɗi tana bulalawa. Anan harabar gidan aka shirya walimar, dan tabbas gidan su Ummi babbane matuƙa ta yanda basa jin ko ɗar idan sabga ta tashi. Dan koda bikin Anty Hajara duk wani events anan akayi inka cire irinsu dinner. Sosai walima ta ƙayatar dan iya mata ne kawai, dan Ummi akwai jama'a tun daga kan kawaye harma da dangin Abban su Buhaisa dan suna mutukar son ta sasai. sai malamai magada annabawa da aka gayyata suka zuba lectures masu ratsa jiki da saka nutsuwa musamman akan ma'aurata da shi kansa ma zaman auren da daɗin dake cikinsa da ƙalubale.
Alhamdullah walima ta kasance cikin aminci, amarya Safiyyah tasha kuka jikinta yayi sanyi sosai, dan har su Isha dake kusa da ita dasu tasa ta da tsokana shiru sukai dan suma fa nasihar ta ratsa su, dan idan ta haɗa da lectures na nasihar iyaye da gargaɗi da wannan ya sake tabbatar mata da aure ba wasan yara bane. Dan duk abinda akace IBADA ne to lallai dole ne ka shirya da shiri na musamman. Dole ne ka yarda da dariya a cikinsa da kuma kuka a wasu lokutan, ita aljanna bata samuwa a kwance, kamar yanda kasan baka samun kuɗi a cikin mafarkinka sai ka motsa ka nema. Idan har duniya da take ba komai ba bata samuwa a garemu cikin sauƙi, taya zamu yi tunanin aljanna samunta zai kasance mana mai sauƙi. (ALLAH kasa mu ɗin ƴan aljanna ne🙏🏽.)
Ba lectures ce kawai ta gudana a wajen ba, anci ansha tare da raba souvenirs masu ƙyau da ɗaukar idanu. Bayan kammala walima amaryar jibi Safiyyah ta koma ciki, yayin da ƙawayen ta yan islamiyyar su harma dana gurin aiki su fara shirin tafiya kasan cewar magrib tayi. Sallama suyi ma Ummi da Amarya kana su tafi sai kuma Allah ya kaimu gobe Kamu, suma 'yan dangin su Abban su Safiyyah tafiya suce zasuyi Ummi tace a'a suyi zaman su sai gobe tunda akwai kamu, amma ina Mama Hadiza tace gida zasu tafi sai koh 'yan matan irin su Bahijja su zauna. Hakan da Mama Hadiza ta faɗa baima ƙanwar Mom daɗi ba dan taso taga kwal uwar daka. toh amma ai goben ma ƙafarta ƙafarsu ta samu naba wa yar uwar ta labari dan ko yanzu saida ta ɗauki hotuna a cewar ta gani da ido yafi labari.
______________🖤🤍
Washe gari Alhamis kuma ana gobe ɗaurin aure Kamu ne, na rana ne ƙarfe 3:00pm za'a fara. Tunda gari ya waye su Buhaisa basu koma bacci ba dan Isha ma nanta kwana sai su Bahijja. Kasan cewar yau ne ana gobe ɗaurin aure gashi kuma yau za'ayi Kamu, dan ma bikin ba anan gidan Ummi za ayi ba can gidan su Safiyyahn zasu koma bayan an gama kamu. Bayan gama duk wani aiki daya kamata suyi subar ma masu aiki su ƙarasa sauran su kuma su dungu ma zuwa gurin wankin kai da lalli.
Kusan ƙarfe 12:30pm su Mama Hadiza su iso da tawagar ta harda ƙanwar Mom da Yayar ta guda ɗaya umma Rabi, dama wasu daga cikin 'yan matan jiya anan su kwana. Da Hibbah, da Bahijja, sai Salma anan su kwana dan tare ma su tafi gurin kunshi dasu Buhaisa. Zuwan su ba daɗe wa saiga anty Fatima nan ƙanwar Abba dake aure a Abuja itama da yaran ta uku biyu sa'ar Safiyyah ne Nabila kuma taɗan girme su, dan daga Abuja nan ta taho tunda Mama Hadiza tace mata suna can, kuma dama suna mutumci sosai da Ummi dan har bikin Anty Hajara taso zuwa amma lokacin sunyi tafiya ne. Nabila, Ikram, Yasmeen, sune yaran ta sai babban namiji. Sosai Safiyyah tayi farin ciki, dan ba wasu ƙawaye bane da ita dan ma 'yan gurin aikin su sunada kara sosai suma kuma ba duka ba. Kamar wasa saiga Yah Ansar da baby wai ta maƙale saita biyu shi shi kuma ganin Mom batanan kawai yace ta shirya yazo ya kawo ta. Aiko zabar farin ciki haɗe su nayi duka na rungume ina murna. An musu tarba ta mutun tawa dan Ummi ba daga nan ba gurin karrama bako yayin da su kuma su shiga saka mata albarka.
Gurin karfe biyu saiga dangin su Buhaisa nan sunzo ma Ummi kara kace bikin Anty Hajara harda yaran su dan duk ƙawayen su Safiyyahn ne su kuma saba sosai kasan cewar tana zuwa suma kuma suna zuwa nan su haɗu. Sai wasu daga cikin kawayen Ummi wasu kuma sai zuwa anjima zasu shigo. Kai saidai fa ace Masha Allah dan gida fa ya ciga da dangi tako ina.
Hummm kunga Safiyyah kuwa, nace kuga Safiyyah kuwa tayi ƙyau harta gaji, ga ƙunshi ja da baƙi an zuba mata. Karku yadda kunshi nan ya zauna raɗam akan farar fatar ta da sai sheƙi tana wani glowing