Showing 12001 words to 15000 words out of 84595 words

Chapter 5 - RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

15 Nov 2025

1153

da yake kamar kanfanin hada turare kamar ba dare ba.
Sumar nan tasha gyara hakama kwantaccen gashin sajan sa sai wal'kiya yake ya kwanta luf-luf ya sake fidda taswirar duguwar fuskar sa.
Saida ya tabbatar ya gama komai sanan ya nufi bed wanda a lailayeshi da farin bedsheet.
(Kirari nayi ga ubangiji mahalincin wannan hallitar kaskiya dole aso mai kyau dan shi mutum ne da yasan ha'kkin tsara ado. ya iya saka sutura ta zauna tsaf ajikin sa kuma ya haskata tamkar dan shikadai ake saka kaya irin su)
Addu'a konciya bacci yayi sanan ya kwanta,

*Washegari....*
Sanye yake cikin riga da wando gajeru da alamu daga gorin mutsa jiki ya fito jikin jike da gumi gafen shi karanshi ne ke biye dashi wato cucu.
Yusuf ne ya karaso da sauri yana mika mishi towel amasa yayi yana goge zufar data jikashi ruwa Hafiz yake niyar zuba mishi a karamin mug hannu yasa ya amshi goran ruwa ya kafa abaki kadan ya rage yana zubama cucu abaki,

Kaitsaye kofar da zata sada shi da baban parlour shi yanufa da alamu gurin ma a part din shi yake,
Dan gurin motsa jikin ma kanshi abun kallone koda yashiga Yusuf biye dashi ciki yashiga kana ya fada bathroom ya hada ruwa mai d'umi cikin bathtub tare da kayan kamshi kala-kala sanan yashiga.
Bayan ya fito close d'insa ya nufa fitowa yayi cikin shigar riga da wando rigar mai kamar rigar sanyi dan har hula tana da ita agaban rigar anyi zanen heart da pink din zare sai kyalli take shikuma wandon dogo ne daga kasa anmishi wata zuga ga wani uban kamshi da yake kamar kanfanin hada turare kamar ko yaushe sumar nan tasha gyara. (Masha Allah shine abinda nafurta🤫)
Kaitsaye parlour ya fito
"Yusuf yace barka da fitowa ranka yadade"

hannu kawai yadaga mishi kana ya zauna a daya daga cikin sofa.

Gaisawa suyi da shi kana yake bashi bayanin duk abinda yafaru lokacin bashi, kasancewar badashi sukai tafiyar ba da "Taheer ne"

ranka yadade auta tayimin maganar waya jiya dan har nasa zuwa anjima za'a kawo mata.

"Wai harta fadama?

"Eh rankaya dade tun jiya takirani ai.

"Okay"

Wayan shi tafara Kara dauka yayi kasancewar ringing din dayasa ma "Ammiii na daban ne shiyasa.
Majeed kana inane breakfast ya kamalla Kai ake jira.

Ammii yanzu zan fito insha Allah,

"Okay" sai kazo tana fada tayanke kiran.

Ga badaya 'yan matan gidan suna dining area suna breakfast,
Bako sallama tashigo parlour.
Sanye take cikin riga da wando wanda su kamata sosai,
Fuskarta tushe da wani tan fatsetsen glass, wanda baka iya ganin idon ta,
Tayi rolling da wani karamin mayafi,
Haka takalmin kafarta shima mai tsini, sai taunar cingam take yana kara kas-kas
Hannun ta rike da karamin akwatu.
Gaba daya 'yan matan kallon ta suke masu Jan tsaki nayi, masu murmushi nayi. azima ce ta taso da gudu ta rungume ta.
Welcome sis tafada tana rike mata hannu,
Sai ayna dake zaune itama tace welcome!
Tana dauke kanta.

Dukan su da kallon rainin hankali ta bisu tana karasawa tsakiyar parlour,
Wato ace har yah "Aj ya dawo ba wacce ta kirani ta fadamin saboda ba'kin ciki. to gani nazo,
Tafada cike da masifa.
feenah ce taja tsaki tare da cewa wace ke agurin shi da har sai ankiraki dan ya dawo?
Cike da rainin hankali tayi maganar batare da ta dago ta kalleta ba.
Wacce ni kike tambaya?
Ido feenah ta kashe mata alamun eh.
Wacce zai aura!

Oooh ai basai anfada Miki ya dawoba kina matsayin wacce zai aura.
Ai saidai muji agurinki yah majeed zai dawo koh?
Tafada cike da rainin hankali ta na kallon zaituna.

Auta dake jinsu takaici duk ya isheta.
sai hauka suke akan Wanda sam besan sunayi ba.

Ayna ce tai dariya tacigaba da danna wayar ta.
Takaici ne ya ishi zaituna ta dago daniyar yima feenah masifa azima ta rada mata magana akune.
Ke kikama kanki bansan rashin kunya
Sonki ne bayayi besan ma kinayi ba.
Zaituna tafada cike da masifa.
Oooh ashe ke yasan kinayi fa tunda har maganar aure anyi koh.

Tafada suna fashewa da dariya itada aynah,
Aifa zaituna ta harzuka parlour ya cike da hayaniyar su bakajin komai sai zage-zage suna tona ma juna asiri.

Ammiii ce take sak kowa daga upstairs, ta hade cikin wata hadda'd'iyar shadda sai kyalli take.
Wacce tasha dinki irin na zamani.
Aa hayaniyar me nake jine tun dazo?
Ba wanda ya dago ya kalleta,
saima Kara kami da sukai har ana shirin fara dambe.

A nutse yake sa'kkowa daga upstairs d'in cikin nutsuwa gami da nagarta sai zuba 'kamshin mayun perfumes d'insa yake.

'Kamshinsa ne ya shiga rige-rigen shiga 'kofofin hancin su,
Azima dake kusa da zaituna tai saurin tsungulin ta,
Gaba daya ido su zuba mishi tunkan ya idda saukowa.

Ammiii murmushi kawai tayi ta wuce dinning area din. Wanda autace kadài akai sai basma,

Wani kallo ya watsa musu dan saida hantar cikin su ta kada.
Kana ya wuce dinning din ba tare da yasake kallon suba.
Yana karasawa ya rungume Ammii tare da cewa,
good morning first love!
Morning handsome I hope katashi lpy
Alhamdulilah! Ammiii nahh!
Yafada yana kaiwa zaune kusada kujerar Ammii.
Kuma tunsa taja bazaka saki wannan fuskar bane.
Murmushin gefen baki yayi yana kallon ta,
Kai Ammii nah!
Aiko kamar zuciyar zaituna da feenah zata fado.
Ba masuba har su auta,
Dan murmushi gawan da bai sabayi kyau yake mai.

Suma kujera suja suna sinne kai ita ko zaituna har zuma take gurin gaishe shi,
Morning kawai yace ya fara cin abicin shi
Suma sauran gaida shi suyi
Kai kawai ya daga musu kasancewar in yana cin abicin baya magana




___________
*Kaduna🌸*

"B'angaren mom kuwa jiran safiyya kawai suke ta dawo su ci ubanta.
dan gyaran gidan ma basuyi ba jira suke ta dawo tayi,
Amah shiru kamar an aiki bawa garinsu.
Anty Waleeda ce tace mom kinga yarinyar nan ba dawowa zatai ba,
Kuma kinsa Abba ya daketa maybe tana gidan wannan kanwar uwar tata.
Hakane wallahi kinga
Har na manta da halima ai uban nata zai dawo da kafarta zata dawo dan ubanta,
"Har kwana biyu shiru safiyyah Bata dawo ba"
aiki na neman gagarar mom dan anty Waleeda cewa ma take bata iya aiki ba.
Yaune ma mom ta zage tadan gyara gidan azuciyar ta tana tsinema safiyyah da tanan ai da ita zatayi har hango irin dukan da zatama yarinyar nan take inta dawo"

"Kasancewar Abba bashi agarin ne da tuni tasa ya dawo da ita "

"Mom ce zaune a parlour ta daura kafa daya kan daya tana dana waya"

Yaron ya shigo wai ance safiyya tazo a waje.
Injiwa? wani ne mai mota.
Okay kace gatanan"
Wani murmushi makirci mom tasaki tana Kiran anty Waleeda"

"Haka ta karaso dawata fingilar riga iya gwiwa ta tsaya mata aka tana wani 'bata fuska mom gani"
Kije ana kiranki a waje kuma ki sanja wanan kayan kidan fesa turare.

"To kawai tace ta fice saigata anci doguwar riga da mayafi sai kamshi take kai tsaye wajen ta nufa gurin MD"

"Shigowa tayi ranta a 'bace mom dama waccan yarinyar yazo nema akace ni"

"Yakuyi dashi?
Duk yadda suyi da MD ta fada mata kuma ni wallahi mom yamin ina son shi"

"Kwantar da hankalin ki zanyi bincike akanshi in yayimin yadda nake so shikenan"

"Amah fa mom nidai gaskiya yayimin sosai k kingan shine ga kyau ga aji da kingan shi kisan daga gidan madara ya fito"

"Niji bari yarinyar nan ta dawo tafada mana ko waye shi"

"Uhm mom"

"Na'am"

"Wallahi kamar safiyyah yanzu tafara rainaki fa, kinga da komai dukan daza amata ba inda take zuwa, amah yanzu har tasamu zarrar maida Miki martani inkina mata magana mata"

"Shiru mom tayi nawani lokaci kamar mai nazari,
kuma fa hakane amah ban nida ita zanje asake mata wani sabon kollin ne"
yauwa mom koh kefa ni wallahi na kosa abba ya dawo ya dakko ta dan nagaji da cin garin kwaki, da fara da mai"

________________

"Around 8:00
Sutashi kasancewar yau ba aiki,
Safiyyah cema ta tashi buhaisa, wanka tafara shiga koda ta fito saida tasake tashin buhaisa kana tashiga, ita kuma tafara shiyawa"

"Tare su fito waya ma'kale a kune ta Tana waya da yah Ansar har su iso parlour yah saif na satar kallon ta kadan-kadan.
Ita tama saba da wannan kallon nashi Dan haka bata nuna alamun tasan yana yi,
Zama tayi su cigaba da waya har yake cema ta Sunday ta koma gida shima wanan week din yaso dawowa amah yanzu sai next week,
Amah yah maiyasa bazaka dawo din ba?
baki a gida nikuma basan ciwon kan wanan matar!
Please yah Ansar ka dawo mana.
Tafada cikin shagobba,
a'ah kibari sai next week din insha Allah.
Tom yaya nah Allah yah kaimu
Da haka sukai sallama"

"Gaisawa suyi da yah saif da anty hajara wace take zaune tana danna waya,
Fira suke har Ummah halima ta fito itada Abba gaishesu suyi cikin girma mawa kana su wuce dinning area"

Bayan sun kammala ita da buhaisa su kwashe komai su gyara,
kana su koma parlour suna fira anan nema Abba yake cewa gobe za'a sa ranar anty hajara dan haka yah saif kar yaje ko ina,
Haka dai safiyyah itada buhaisa suke ta murna da tsare-tsaren biki kamar ansa har yah saif nasaka musu baki anty hajara da kunya ta isheta tashi tayi takoma sama tana murmushi"

"Dariya buhaisa tayi uhm waifa kunya taji meye na kunya anan wallahi da nice ba kunyar da zanji tafada tana fari da ido,
Ungo taki nan wato da kece ba kunyar da zakiji koh ai dama tafiki kunya.
Ummah ce tafada tana ma buhaisa da kuwa,
dariya suka sa gabaki dayansu,
Kai ummi nifa bahaka nace ba tafada tana turo baki"
Allah dai yashirya minke cewar Abba yana murmushi,
Da ameen duk suka amsa, ana murmushi"

"Har abba ya fita suna hira itama anty hajara daga baya ta fito a cigaba da ita,
yah saif please yau ka kaimu shopping wallahi kayan kwalliya na sunyi kasa.
Sai dai safiyyah ce tafada sai muje ya fada yana kallon safiyyah,
Uhm a lallai yah saif to gaka gatanan ita take cewa tana so taje shopping wai turarukan ta sunyi kasa.
Koba haka bane? tafada tana kiftama Safiyyah ido da rausayar dakai,
Eh hakane!
Dariya anty hajara tayi tace gulman mu kawai,
Ku gama gulmar ku kuzo ku same ni,
Kai anty hajara mune gulman mu Safiyyah tafada cike da shagobba"

"A'ah kugama zaku dawo ku sameni ne ai"

"Duk dariya suyi su maida hankalin su kan yah saif,
Kar anty hajara tai musu gwabi,
Itama bata sake cewa komai ba dan tasan halin 'kannan nata.
tom shikenan ku shirya sai muje after asahr preyer.
Yauwa yah saif su hada baki gurin fada.
Daga baya ma kan anty hajara su koma suna mata tsiya tun tana samu su baki har ta koma saidai tai musu murmushi"

"Tsaf ta shirya cikin doguwar riga ta material red, Kayan sun mata kyau, ta dauko fari hijjab tana niyar sawa buhaisa ta turo kofa"

"Kan bala'i menake gani haka?
Wai gowa tayi tana dubawa a ina?
Bata rufe bakiba taji buhaisa ta kwace hijjab din wallahi baki isah kinsa hijjab ba.
Tsaki Safiyyah tayi tana cewa uhm sai kiyi Dan Allah ni bani,
Banza tayi da ita ta nufi wardrobe duk hijaban ciki ta kwashe tana niyar ficewa.
safiyyah tace ina kuma zaki?
ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login