Showing 72001 words to 75000 words out of 84595 words
fara min da nasiha mai ratsa jiki. Kafin sauran ma su dinga karɓa ɗaya bayan ɗaya. Daga baya suka koma faɗa da gargaɗi, yayinda ni kuma nike sharɓan kuka ta cikin gyale. Dan babu abinda ya tadamin hankali sai jin muryar Yah Ansar na rawa alamar karaya sanda yake min addu'ar zaman lafiya a gidan aurena. Abba ma dai yamun tasa a taƙaice, daga baya kiran wayarsa da akai ya nema excuse ya fita, da alama kuma kiran da akai masan nada matuƙar muhimmanci ne. Dan naga sai da ya fara magana da Kawu Bala suka miƙe tare suka fita. Fitar tasu bai hana iyayena cigaba da mun nasiha ba, sai da suka gamsu sun min yanda suke buƙata kafin suka sallaman Inna Binta ta kamani ta maidani ciki, dan mazan zasu wuce massalaci ne daga can kuma za'a ɗauro aure. Dole sai da aka sake min kwalliya bayan nayi sallar azhar saboda na ɓata fuskar dan kukan da nasha. Kaya na canja zuwa wani fitinannen less Green daya ji uban ɗinki dan uban su doguwar riga. Ga ƙamshi irin na amare ƴan ƙwalisa ina zubawa. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar nan. Lokacin da ƙarfe biyu ke cika maza suka fara dawowa alamar an ɗauro auren gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri. Wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da jijiya har ina jin wani kalar sanyi-sanyi duk da kuwa uban zafi ake zugawa a gari. Ƙawayena sun shiga min shaƙiyanci da buɗa a saman kai, dan Buhaisa da uban gudu ta shigo bedroom din tana kwalla kiran sunana harga Allah na ɗauka wani abun ne ya faru aiko cikin sauri na mike ina tambayar ta meke faru wa, ai bata tsaya bani amsa ba sai rungume Ni da tayi tana faɗin "Sisy nah an daura" sai kuma ga Isha dasu Yasmeen gaba ɗaya sai suka haɗa ni su rungume ni suna murna, sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba. Shin murna da farin cikin mallakar matashin saurayi ƙyaƙyƙyawa ɗan ƙwalisa mai cikar kamala da dattako irin Suraj ne, ko kuwa fargabar rabuwa da ƴan uwana ne. a lokacin sam na kasa ganewa. Na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa. Sai ma wani sabon bugun zuciyar da na sake ji sakamakon shigowar aunty Fatima kamar a firgice tana kiran Ummi data shigo tana miƙamin fura a kofi da aka dama wai na sha. Koda Ummi ta tambayeta lafiya, sai tace mata su Kawu Bala ne ke kiranta kuma sunce tai sauri dan kamar dai akwai wata matsala. Da saurin kuwa ta fita alamar itama tana a cikin ruɗanin ne..
Na cigaba da zama kamar butun butumi a tsakkiyar ƙawayena daketa hotuna abinsu batare da su sun fahimci kamar akwai abinda ke faruwa ba. Danni su Buhaisa harsum isheni da hotuna dan tun ina biye musu harna koma na zauna. Muna nan dai hayaniyar gidan na sake ƙaruwa alamar mutane na sake cika gidan ƙananun magana suka ɗan fara fitowa. Sai dai anƙi a fito da komai a fili ana ta son basar da mutane dai. Abinda ya ɗan fara tsayamun a rai shine rashin zuwan Suraj gidan. Dan a burikan mu akwai zuwa hotuna bayan ɗaura aure da yace zasuyi shi da abokansa da kuma ni da ƙawayena da ƴan uwana. Amma dai zuciyata nata tausata akan masa uziri, dan maybe mutane sun masan yawan da hakan bazai yiwu ba ya cika wannan alƙawarin. Wannan tunanin yasa na danne zuciyata na ajiye wannan batun a gefe.
Isowar masu kiɗan ƙwarya karfe 4:00pm bayan hotunan da aka gama yi tsakanin duka family na mu. yasa Anty Fatima zuwa ta fita dani a ɗakin ni da ƙawayena. Sosai gidan ya cika da mutane har sai da naji ƙwalla ta cika min ido. Dan tunowa da nayi da Ummah. Ko a wajen kiɗan ƙwaryar ma duk da ba rawa nake ba tsaye kawai nake tsakiya ƙawaye na da su Buhaisa ƴan uwana masu rawar zagaye da ni sai da dinga shigowa ana min liƙi, wasu kuma sukanyi hoto dani a waya harda masu video. Kusan karfe Biyar sai ga Ummi riƙe da hannun Yah Saif da Yah Ansar wai sai sun min liƙi. Kallo ɗaya na musu su duka biyun na fahimci sunyi kuka. Dan idanun Yah Ansar jajur suke. Na Yah Saif kuwa har sun kumburo saboda fari ne kamar Buhaisa. Hankalina ne ya tashi a take nima idanuna suka ciko da ƙwalla ina binsu da kallo. Amma sai suka ƙi yarda mu haɗa ido sai liƙi da sukemin kawai ana ihu kawunansu a ƙasa suna murmushin da ni kaɗai na fahimci na yaƙe ne. Duk yanda naso riƙe kukan nawa hakan ya gagara, bamma san sanda na riƙo hannayensu su duka ba cikin nawa. Dole suka kalleni a tare. Kukan na sakar musu kawai na faɗa jikin Yah Ansar. Shima sai Yah Saif ya rungumemu mu duka biyun yayin da Ummi ta haɗe mu duka ta rungume aiko a tare mu saki kuka mai tsuma zuciya. A take wajen yay tsitt, wasu na ganin mun birgesu da fassara abin namu da tsananin shaƙuwa ne da soyayyar juna. Wasu ko da suka san wani abu dake ɓoye sai suke jin tsananin tausayinmu da jin karaya suma. Nan take aka ringa tuno alkairan Ummah gare su nan masu share kwalla nayi kukan zuci nayi da musu addu'a. Dole dai Yah Ansar ya jamu muka fita daga filin Saboda gaba ɗaya kuka ya sarke Ummi dan ba abinda take tunowa sai yar uwar tata. Nan Mama Hadiza ta jamu zuwa ɗakinsa ta dinga lallashinmu da mana nasiha. Haka kawai maganganun nata sai suke ta min kai da kawo dan na gagara fahimta da fassara wasu nikam. Kiran Yah Ansar da akai a waya ne ya sashi miƙewa ya fita. Babu jimawa ya dawo yay kiran Yah Saif suka fice..
Acan ƙasan zuciyata kam ina jin babu daɗi saboda rashin ganin duk jama'ar gidan a cikin sha'anin bikin nawa. Dan yaran duka babu wanda na gani har Baby da su Yah Safwan Gara ma ita Mom ɗin bayan ɗaura aure sanda Yah Ansar yazo ya fita dani ɗin nan zuwa falon baƙi na ganta ita da wasu ƙawayenta a tsaye sunata faman dariya da alama akwai abinda suke tattaunawa a tsakaninsu...............
___________🤍🖤
*Abuja*
..........A hankali mutocin nashi ke dai-dai parking a parking lot din dake gidan, cikin sauri Muktar ya fito tare da buɗe ma Boss din nasu kofa. Bai ɗau wani lokaci mai tsayi ba ya fito a motar, kamar yadda ya fita cikin kayan nasa irin na larabawa duk da shima tamkar balaraben yake haka yanzu ma cikin su ya dawo duk dama masallaci Jumma'at suka je. Kamar ɗazun dai haka ma yanzu fuskar tasa take a tamke kwata-kwata ba fara'a a cikin ta. Amma duk da haka baka isa gane cewa yana da damuwa duk dai da haka yake ko yaushe fuskar sa ba fara'a, su kansu yaran nasa sun lura Boss din nasu bashi a yana yin walwala yau kasan cewar sun sanshi kamar yunwar cikin su. Dan yau ko gaisuwar da suke mishi bai amsa ba illah hannu kawai ya ɗaga musu.
Muktar ne dake wannan tunanin a zuciyar sa ya dawo ganin harma ya nufi kofar main parlour yayin da Youseef ke biye dashi. Kofar ya buɗe da kansa kana ya tura kansa ciki tare dayim sallama ciki-ciki. 'yan matan gidan ne kawai zaune a parlourn ko wacce da abinda take yi, kamshin turaren sane sai kuma sallamar Youseef dashi yayi da karfi ya fargar dasu cewa sun dawo. Duka ido su zuba ma Yayan nasu ko wacce a cikin su da irin tunanin da take. Sannu da zuwa su masa inda tunkan dama ya iso ya gama ƙare ma kowa a cikin su kallo hannu kawai ya ɗaga musu yayin da su shiga gaida Youseef daya samu guri shima ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun parlourn. Amsa musu yayi da kula wa yayin da Majeed ya haura upstairs part din Ammei.
Zaune ya same ta a bedroom din ta kan abin sallah da alama addu'a take dan ita Ammei haka take idan tayi Sallah kafin ta tashi a gurin sai ta dau lokaci mai tsayi. Zama yayi harta idda addu'ar kana ta tashi ta zauna a kujerar da yake, ƙasa ya zamo ya zauna dabas akan lallausan cafet ɗin dake shimfide a ɗakin kana ya ɗauki ƙafarta ya daura akan cinyarsa yana mata tausa. Murmushi kwance a fuskar ta a hankali ta ɗaura hannun ta akan lallausar sumar kansa me kama data larabawa kasan cewar tun shigowar sa ya cire naɗin dake kansa. Jin hannun nasa sanyi kanshi kuma zafi yasa ta tabbatar har yanzu da sauran ciwon, shiru suyi na wani lokaci ba me magana a cikin su. "Abdulmajeed" Ammei ta kira sunan sa cikin nutsuwa, jin yadda mahaifiyar tasa ta kira full name ɗin sa dan zai iya rantsewa tunda ya girma bai taɓa jin ta kira full name ɗin sa ba. Tashi ɗaya ya dena mata tausar kana ya juya gaba ɗaya yana fuskantar mahaifiyar tasa tare da maida Hankalin sa gaba ɗaya kanta. Kana ya amsa da "Na'am" yana zuba mata rikitattun idanun sa dasu kade su koma jajur.
Saida ta sauke ajiyar zuciya kana. tace. "Meke damunka ne haka har wannan ciwon ke ƙoƙarin kama ka Majeed?". Saida ya sauke ajiyar zuciya kana ya ɗauke idanun sa akan ta, shidai harga Allah bai iya karya ba sam dan baima san yadda ake yin ta ba dan haka ya zaɓi yayi shiru. Jin yayi shiru alamun baida ta cewa kenan yasa ta sake cewa. "Majeed dakai fah nake". Kai ya langabe kana cikin silent voice din sa yace "Ammeiii". Ya idda maganar yana langab'e kai alamun baya son maganar, dama tasan da wuya ya faɗa yasa ta sake cewa. " Answer me Majeed". Fuska ya bata kana yace "Please Ammei tell me meya ce miki?". Shiru tayi tana kallon sa ba tare da tace komai ba hakan ya bashi tabbacin ba zata ce wani abuba kenan, shiru shima ya sake yi na wani lokaci yana tunani kana yace,
"I swear to God, but I don't know what's wrong with me." Ajiyar zuciya kawai ta sauke tare da ce komai ba "Okay bari Dadyn ku ya dawo dan ɗazu yake cemin zasu taso yanzu na kirasa wayan sa bata shiga. "Tom Allah ya sauke sa lafiya". Da "ameen" ta amsa kana ta bashi maganin sa daga nan kuma downstairs su sakko domin yin lunch. Bayan gama lunch din ya wuce part d'in sa Youseef kuma ya fice.
Ammei ce zaune ita da Auta suna tattaunawa akan batin ciwon Majeed, cike da damuwa Ammei ke cewa. "Wllh sam na rasa meke damun Yayan naku har wannan ciwon ke ƙoƙarin kama shi". Ajiyar zuciya Auta ta sauke kana itama cikin damuwa tace, "Ammei abinne abun tunani amma fah kinsan me nagani ɗazu kuwa a ɗakin sa?" Kallon ta Ammei tayi kana ta girgiza kai alamun a'a, "Humm Ammei kinsan hoton wa na gani akan screen ɗin system ɗin shi?" kai Ammei ta girgiza tana kallon Auta kana tace "Hoton wa ki gani?" Saida Auta ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "Wallahi Azim Ammei hoton Safiyyah na gani a jiki sanye da hijjab da facemark da eyeglasses". Shiru Ammei tayi tana tunanin wacce Safiyyah kuma dan ita harga Allah bata gano Safiyyahn da Auta ke nufi ba. Kafin itama cikin sauke ajiyar zuciya tace, "Wai Auta wacece kuma Safiyyah kin sani a duhu?". Fuskar Auta cike da damuwa tace, "Ammei Safiyyah fah ta Haske TV wacce ake bikin ta yau". Shiru Ammei tayi kamar mutum mutumi tana kallon Auta cike da mamaki a zuciyar ta koh tunani take, meye haɗin sa kuma da Safiyyahn batin tasan shi sam mata basa gaban sa?. Taɓa ta da Auta tayi ne yasa ta kauda kanta a kallon ta kafin tace, "kin tabbata Auta?"
"Wallahi Ammei kafin nazo kiran kune ma na kashe ta kinsan matan gidan nan da yan sa ido". Kai kawai ta gyaɗa ma Auta ba tare da ta sake cewa komai ba a zuciyar ta tace ai aikin gama ya riga daya gama tunda ta zama matar wani. Daga nan shiru ta biyo baya Ringing din wayar tane ma ya katse mata tunanin data tafi. *ASADI* sunan dake rubuce akan screen ɗin wayar a lokacin da Auta ta miko mata dan tasan Dady ne, ita wancan tunanin ta ture kana ta maye fuskar ta da murmushi kana ta ɗaga. Sanar da ita cewa gashi a gida yasa tunkan ta mike Auta ta fice da gudu kamar wata ƙaramar yarinya. Murmushi kawai tayi kana ta aje wayar itama ta nufi downstairs.
Dai-dai isarta cikin parlourn shi kuma yake shigowa yayin da dagudu Auta taje ta ɗafe shi. Cike da farin cikin da ya kasa ɓoyuwa a fuskar Dady yake shafa kan Auta yayin da su Basma ma suzo su rungume shi, cikin parlourn ya ƙaraso kasan cewar yau ba wasu mutane a mai parlourn sai ɗai ɗai kun yan matan gidan ne a ciki sai kuma Hajja Mummy da dama ita ta fison zaman Main parlour kodan tayi sa idonta yadda take so. Kasan cewar duk wanda zai shiga ɗaya daga cikin part d'in gidan saiyabi ta nan parlourn.
Cike da farin cikin ganin ɗan uwan nata ta dan dama dakon jiran dawowarsa take yi ganin tuni tama Yayan nata magana akan haɗa auren Majeed da Zaituna amma shiru takeji kamar ma Yayan nata ya manta da maganar, shiyasa yanzu jira take zuwa anjima taje ta sake samun sa da maganar dan taga alamun inba da zafi-zafi tayi ba sai abun ya gagare ta dan yaron nan sam baida mutunci. Kuma tunda tama 'yar ta alqawarin auren sa dole ne saiya aure ta, dan baida matar data wuce Zaituna. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta dawo daga duniyar tunanin data tafi tamishi sannu da zuwa, yayin da shi kuma ya haura sama domin watsa ruwa.
Bayan gama kintsawar Dady dan yace shifa baya jin yunwa a koshe yake. Ya shirya Meeting a babban parlourn dake part d'in sa. Jin batun meeting d'in da Dadyn ya shirya kuma bama a part d'in granny ba a nashi parlourn yasa kowa hallara da wuri dan dagaji magana ce mai mahimmanci kuma gashinan yace dukan su harma da yaran. Granny ma tuni ta kintsa ta nufi part d'in Dadyn kasan cewar suma mazan gidan na nan wato su uncle Abdallah Dan tun Around 4 suke dawowo daga gurin aiki ranar FRIDAY.
Gaba ɗaya parlourn na Dady a cike yake dan fa kowa ya hallara harda Youseef inka cire masu aiki kawai sai kuma Majeed da dama shi sai yayi African time. Dan har uncle Kabeer dake Saudiyya saida a kira ta video call a babbar system ɗin dady dake parlourn. Saida Dady ya gama bin kowa da kallo yaga ba Majeed kana ya ɗaga wayar sa yayi kiransa, ba'a wani dau lokaci mai yawa ba ya iso sanye cikin t-shirt fara tas sai Black Jen's, sumar Nan tasha gyara danko ta kwanta luf a bayan sa, babu abinda yake sai kamshi turaren nasa mai saka nutsuwa. Gurin zama ya nema ya zauna ɗan nesa da Dady kana ya gaida iyayen nasa cikin girmamawa, suma su amsa mishi da kulawa tare da masa ya jiki, dama tuni Dady yasan Majeed ɗin bashi da lafiya kasan cewar Dr Fadil ya kirasa ya sanar mishi.
Bayan buɗe taro da addu'a Dady ya fara magana. "Abdulmajeed!" Kowa jin yadda dadyn ya kira sunan Majeed ɗin yasa wasu da yawa ɗago wa suna kallon dady dan abune dabai saba faɗa ba. A ɓangaren Majeed ma haka take dan shi zai iya rantsewa da Allah tunda yake bai taɓa jin mahaifin nasa ya kira wannan sunan ba sai yau, dan haka ya tabbatar da maganar mai mahimmanci ce, a hankali ya ɗago kansa dake masa ciwo ƙasa-ƙasa ya zuba ma dady idanun sa tare da amsa wa da, "Na'am dady" saida Dady ya sauke ajiyar zuciya kana ya cigaba da magana yayin da gaba ɗaya parlourn ya sake ɗaukar shiru.
"Menene matsayina a gurin ka?"
Yadda dady yayi magana fuskar sa sam ba alamun wasa gashi ya kafe Majeed da ido, yayin da cikin tsananin mamaki kowa ke kallon Dady bare Majeed daya d'ago yana kallon dady, cikin sauke ajiyar zuciya yace. "Dady kai mahaifinane wanda bani da kamar sa aduk faɗin duniyar nan".
Dady ya jinjina kai tare da sakin murmushin gefen baki kana yace, "Masha Allah Toh a matsayina na mahaifin ka na zartar da umarni akanka yanzun nan". Zuciyar Majeed na luguden daka cikin sanyin murya da a yanzu ta sake komawa ƙasa-ƙasa yace, "Toh dady wani umarni?". Kai Dady ya jinjina kana ya cigaba da magana.
"A matsayina na mahaifin ka na tabbatar ko wanne irin hukunci na yanke a kanka yayi, dan na tabbatar kome na kawo maka na baka zaka riƙemin shi amana, ka kula dashi kuma ka tattale shi saboda abun daga gareni yake, Toh a yau aka ɗaura maka Aure".
Gaba ɗaya parlourn ɗago wa suyi cikin tsananin kiɗima suna kallon dady, musamman Majeed da kirjin sa yayi tsawar hadarin gabas na tsakiyar ogosta😂
Atsorace Majeed yake kallon dady yayinda zufa keta ambaliya adukkan sassan jikinsa, ya daure cikin rawar murya ya ce, "dady aurefa kace?"
Dady ya ce, "kwarai aure nace Majeed, kuma ina fata amatsayina na mahaifinka zaka yimini biyaya, zaka