Showing 9001 words to 12000 words out of 84595 words

Chapter 4 - RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

15 Nov 2025

1134

akoye,
Shima bukar din shida azma take ko azima sun zubama ido tunda karfin su kafi koh,
Yaro sai shagobba tsiya kaje ka kanan nade mata ajiki kamar Kaine auta, umm kwafa tayi tana kallon shi a dole an'bata mata rai.

Karo na farko da yasaki wani murmushi har hakoransa su fito masha Allah shine abin da furta,
Har granny saida tasaki baki tana kallon shi,
Tashi daya ya gintse fuska, yana wani kan_kance ido to granny ina ruwan kine uhm kinemo matar mana kiga inba'a aure taba,
Ke tsohuwar nan saisa ido, yafada yana Kai kofin furar bakinshi,
Baki tasake tana kallon shi wato nice tsohuwa mai sa ido, koh?
kai badin 'yan matan gidan nan basu da ta ido ba ai acikin su zan zabama, amah na kauyen sunfi ta ido,
Aciki zan nemoma zakuma kagani,
Saida ta kai aya tashaki nufashi tana mai zuba mishi harara.
Bai karacewa komai ba batun uhm.
Yacigaba da shan furar shi hankali kwance,
To ya dubai din komai lafiya?
Lau!
Sallama akayi daga kofa shigo mana
Tafad'a tana gyara zamanta, wani dattijo ne kimanin shekara 50 ko sama da haka ne yashigo,
Fuskarsa kwance da murmushi,
Au audullahi kaine da ranan nan? saida yakai zaune yace nine hajja barka da rana!
Yauwa barka!
Majeed andawo kenan?
Eh uncle dazu nadawo! Okay ya hanya andawo lafiya?
Lafiya!
Yafada yana tashi aa ina zuwa kuma granny tafada tana kallon shi,
Lokacin sallah, yafada yana nuna agogon dake daure a tsin-tsiyar hannun sa.
Ajima zaka dawo ne?
A'ah! Madarar kafa?
Akawomin part dina,
Baijira amsarta ba ya fice daga part din,

Ta wata kofa yabi saigashi a b'angare shi,
Bathroom yashiga baifi minti talatin ba ya fito jikin shi da laima,
Alamun alwala yayi close d'insa ya shiga ya fito sanye cikin riga da wando blue.
Ko waya bai dauka ya fita kai tsaye, masallacin dake gidan ya nufa,
Bayan ya fito daga masjid dine suka fara gaisawa da uncle's d'insa,
Uncle abdallahi
Uncle sulaiman
Uncle kabeer
Bayan sun gama gaisawa, kai tsaye part din granny su nufa shikuma ya nufi part din "Ammii"

Na farko ba kowa aciki Dan har tv akashe yake,
Dama kai tsaye main parlour ya nufa shiko duk 'yan matan gidan suna ciki,
Kasancewar yafi ko ina tsaruwa da 'kawatuwa, yasa sunfi zama a cikin shi kowa na harkokin sa wasu na waya, kafin lokacin dinner yayi,
Da sallama yashiga ciki_ciki ba wanda ya lura dashi a cikin su, Saida yazo tsakiyar parlour hankalin su ya dawo kanshi, gaba daya kowa ya shiga tai_tayinsa, har masu wayar denawa suyi,
Barka da dare "yaya "Majeed su hada baki gurin fada,
Saida ya gama binsu da kallo sannan yace ina "Ammii"
Ya fada yana tsare auta da ido, yaya tana sama, okay!
Kai tsaye sama ya nufa,

______________
_________
___-_-

Kaduna...

Harzan kirashi na fasa dan nasan ina fada mishi zaice na koma,
Shi zaizo nikuma bansan ya baro aikin shi ya tahonan,
Wai dan Allah sis meye tsakaninki da MD ne?
Umm sis kenan idan akwai ai kinsani maybe ma kin fini sani!
Ni bawata alaqa tsakanin mu face na matsayin sa MD, da muke a karkashin sa,
Umm haka dai kice sis amah wallahi MD sonki yake, da kan shifa yazo duba ki Dan ance bakida lafiya,
Umm ni rabudani dazancen MD can mishi,
Dariya "Isha tayi tace can muku dai ke dashi".
Nima murmushi kawai nayi ban sake cewa komaiba har muka iso anguwar rimi,
Abakin get ta tsaya au bazaki shiga bane ko gaisa da buhaisa?
Eh gobe idan nadawo gurin aiki zanzo!
Tom kigaida min momy,
Nafada ina fita daga motar hannu na daga mata, ina kara sawa bakin get din shiga nayi bayan baba mai gadi ya budemin.
Aa malama safiyya ce yau a gidan namu?
Murmushi nayi tare da gaishe shi ina karasawa cikin parlour da sallama, anty hajara ce kawai aciki,
Waya take batama lura daniba saida naje kusa da ita nazauna ina mai daura kaina acinyarta,
Wayar ta aje cikin mamiki tace, "Safiyya meya faru?
gurin aikin fa?
Anty kaina ke ciwo!
Umm wacce matar dai ko?
bance komaiba, itama haka, sai kama hannuna tayi muka nufi sama,
Muna shirin shiga bathroom ummah halima ta fito,
Wanake gani kamar safiyya? itace wallahi ummah, ato gurin aikin fa?
Ummah kinsan halin dai waccen shegiyar mata ai,
Eh kuma hakane kuje dakina inazuwa,
Kitchen tashiga ta hado tea mai zafi sanan tashigo dakin.

Sakko kisha tea din saikisha magani, kadan nasha, maganin ko saida naga bacin ranta sannan nash,
Dan a rayuwa natsani magani da allura, kwanciya nayi anty hajara tafita,
Haka bacci ya daukeni.

________
____
A b'angaren MD kuwa bayan yatashi daga office kaitsaye gida yanufa,
Mommy ce kawai a parlour ganin yadda ya shigone yasata cewa suraj lafiya kuwa?
Mom lafiya lau kawai dai ba najina dai_dai ne,
Amah wani abu ya farune?
Aa mommy bakomai!
Tom shikenan kaje Kai wanka kafito muyi dinner,
Da tom kawai ya amsa ya wuce dakinshi,
Wai metasa bazaki
Fahimta bane ina sonki,
Wata zuciyar tace kawai kafada mata,
Aa bazata amince ba
Yarinyar akwai zafin Kai,
To ya zanyi yafada a hankali alamun zancen zucine ya fito fili,
"Yaya ya zakayi mene?
mineet da mommy ta aiko takirashi,
sunji shi shiru tafada tana karasawa kusa da Yaya nata,
Bakomai!
Haba yaya ya zakace bakomai batin naji kana tambayar zakai,

Mineet nace bakomai aa yafada cikin tsawa Kai yaya Allah yabaka hakuri kazo mommy nakira,
Tana fadar haka tafice,
Zuciyarta na tunanin meya batawa yaya "Suraj raine,
Shiko MD tana fita shima yatashi yayi wanka, sannan ya fita
Parlour,
Dad dinshi sai mommy da mineet ne kawai a dinning area din,
suma da alama sun kusa kammalawa,
Barka da dare dad, yauwa barka Suraj yau baka fito dinner da wuriba,
Dad nadan kwanta ne shiyasa,
Amah da magrib dinan zaka kwanta Suraj,
Kinga kyaleshi maybe baya jin dadi ne kisan daga gurin aiki yake,
Okay hakane,
Yauwa mommy kawai kaina ke ciwo,
Okay gama kasha magani kawanta tom,
Mineet dai kalon su tayi dan tasan ba ciwom kai bane,
Amah koma mene zata tayashi addu'a

(Ayya MD fa yakamu ga safiyya💃 mu bata masan meyake ba)

_________
_____

B'angarena kuwa tunda natashi ba kowa adakin,
dan haka wanka nayi kozan ji karfin jikina,
Nama manta dakin ummah halima nake, saida nabude wardrobe zan dau kaya,
Natina fita nayi kaitsaye dakin buhaisa na nufa, ina shiga ta rungume ni sis kin tashi kenan?
Tun dazu zan tasheki ummah tace kar wanda yatadaki,
Umm ciwon kaine fa kuma ya sauka,
Haka dai kice sis kije kishirya ki fito mi dinner,
Okay!
Doguwar rigar buhaisa nasa dayake tsawon mu daya,
Tayi min dai_dai amah takama ni kasancewar nafita kiba,
Sallah nayi na danyi karatun alQur'ani sai a azkhar,
Buhaisa ce tashigo Tom ustaziya inkin idda kifito ke muke jira,
Hararar ta nayi wace ustaziya?
Kemana tanada fada ta fita dagudu tana dariya,
Murmushi nayi nima na bita,
Duk ahalin gidan na zauna a dinning area amah banda dady,
Tun daga nesa Yaya saif ya zubeni da ido ko 'kiftawa har naja kujera na zauna,

Ina dagowa naga niyake kallo,
Nasan za'a rina dan naji alamun ana kallona,
Harara wasa na mishi ina turo bakina cikin shagobba naceYaya
uhm!
kallon fa,
Murmushi kawai yayi yacigaba da cin abicin shi,
Kasancewar ba Wanda yajimu sai buhaisa da naga tana dariya kasa_kasa,
Har ummah halima tace lafiya buhaisa ko duk murnar ganin safiyya ne?

Kai tadaga tana kallona nikuma na harareta,
Haka dai mu gama cin abicin,
Mu dawo parlour ana fira,
Waini "safiyya meya hadaki da matar can ne?
Duk abinda yafaru na fada mata har dukan da abba yamin,

Waikina nufin har yanzu malam ibrahim na dukan ki,
Ato gaskiya bazai yiwuba bazata saboba ya karyamin 'ya a alhaji yadawo,

Matar nan dai batada da Imani tarabani da yar uwata kuma so take tarabani daku,
Sai kuka,
Ya Allah duk inda 'yar uwata take Allah yasa tana cikin koshin lafiya,
Allah ka baiyana Mana ita,
Da ameen duk muka asa danni yanzu nasaba,
Kinzo gidannan kenan in Allah ya yarda,
Kuje ku kwanta dare yayi kusan zaku fita aiki,
Saida "Safe muyi mata mutashi mu fita Dan anty hajara ma ta tafi daki,
Muna zuwa nayi alwala kwanciya bacci,
ina addu'a buhaisa kecewa waike meye tsakaninki da Yaya saif ne?
Saida na shafa nace ikon Allah wani Yaya saif din?
Yaya saifu
mana kokina nufin bakiga irin kallon da yake miki bane,
Ummm nashiga uku ni safiyya waikeda "Isha meke damun kune wai,
Nafada ina kallon ta............✍️

_(😎 To ga yayah saif ga MD da alamufa Yaya saif naciki koya zata kaya🤔)_











https://chat.whatsapp.com/CiFQHB3CNkRJ8gmX6banlC

🌹 RAYUWATA 🌹

Story and written✍️

Bilkeesu .S. Aliyu
💞(Billy pinky)💞

🤝 Amanar nazari writer's association📚

[07070260240]

WhatsApp number or call

📚 NAZARI WRITERS ASSOCIATIONS📚

EPISODE🌷1️⃣6️⃣▶️1️⃣7️⃣🌷


Meye na kirawa kanki shiga uku?
Dan ance yaya saif din na sonki,
Umm bazaki gane bane wallahi sis,
Me Ishan tace mikine?
Barzancen kawai!
Wallahi baki isaba saikin fada,
Murmushi nayi tare da cewa,
San gulma to basai kinji ba,
Haba sis please kidafamin mana,
Umm wai MD take cewa sona yake,
Dariya tayi inma hakane_inma-bahaka bane munriga shi ehhee,
Tafada tana fari da iddo,
Nima murmushi nayi tare da addu'a konciya bacci,
naja blanket na rufe har fuskata,
Saida safe, Allah yakaimu lafiya,
Wai kin kira yaya Ansar kuwa,

Ohh my God nafada ina fitowa daga bargon,
Waya nadauka zankira shi dare yayi sosai,
Sis kibari kikirashi gobe maybe ma yayi bacci,
Umm hakane kuma Allah yah kaimu goben lafiya.
Ameen!


______--------______

Zaune take a kujera bedroom din nata alamun waya take,
Koda majeed yashiga Bata yankeba,
Shima da alamu yagane dawa take wayar,
Zama yayi kusa da ita yana daura kanshi a cinyarta,
Wayar ta cigaba dayi tana shafa sumar kanshi,
Sallama take da Wanda suke wayar, yazare wayar yana kaita kunne shi,
Barka da dare papa yafada kasa_kasa,
Banji abinda nacikin wayar yake fada,
Naga dai yayi murmushi wanda inba ka kura mishi iddo ba bazaka gane yayiba,
Papa Allah yakaimu lafiya,
Shine abinda ya furta basu wani dade ba ya ajiye wayar gefe,

Muje kayi dinner!
"Ammiii ya Kirata cike da shagobba,
"Na'am"
Auta taje ta amsomin Madara ta aguri granny,
Yau bazakai dinner bane?
Uhm zanyi wani aikine,
Tom Allah yabada sa'a ka kwanta da wuri kagaji dayawa,
Insha Allah,
Yafada yana gyara kwanciyar shi acinyar ta tare da lumshe ido,

Yana haurawa sama azima tace auta yaushe yaya Majeed yadawo ne?
Dazu taba ta amsa lafiya!
Ooh a'ah bakomai!
Okay,
Auta nabarin gurin ta dakko waya,
Can gefe takoma da alamu waya zatayi,
Hello zaituna,
Banji me aceba daga can b'angare ba,
Tace albishirinki,
Shiru tayi,
Can kuma ta kyalkyale dariya,
Yaya majeed fa yadawo,
Shiru tayi alamun tana sauraren ta,
Ke nima ban saniba yanzu na ganshi nake tambayar auta,
Ki kwantar da hankalin ki sai goben kyazo,
Shiru takuma yi tana murmushi,
Tom Allah yah kaimu goben,
Daganan ta yanke wayar takoma parlour,
Su cigaba da fira,
Majeed ne ya fito alamun masjid zashi Dan isha'i ake kira,

Barka da fitowa yaya Suka hada baki gurin fada,
Hannu kawai ya daga musu ya fita a parlour,
Kai tsaye masjid ya nufa,
Kasancewar masjid din acikin gidan yake,
Bayan ya fito kai tsaye part din shi yanufa,
Kamar yadda yabarshi haka yake saidai da alamu angyara shi dan kuwa sai kamshi yake,

Bai tsaya parlour ba yawuce bedroom yadade sannan ya fito parlour,
Hannun shi ri'ke da waya da laptop,
Zaune yakai kan sopa yana daura laptop din asaman cinyarshi,

Lasa keypads din laptop din yake, cike da kwarewa, da alamu wani aiki yake Mai mahimmanci,

Wayar sace tafara vibration alamun shigowar kira,
Kamar bazai dauka ba can kuma maiya tuna yadaga,
Shiru yayi,
Okay,
Subari ma hadd'u gobe,
Shine abinda ya furta yana ajiye wayar,

Yayi nisa a aiki saiga auta nan,
hannun ta rike da karamin tire mai d'auke da jug, sai mug da cukali karami

Da sallam ta'karasa parlour bai d'agoba yadai amsa mata sallamar ciki-ciki har tak'araso,

Tabble din dake tsakan kanin kujerar dayake ta dari tire,
Barka da hutawa yah majeed,
Hannu kawai ya daga mata,

Guri tasamu ta zauna tana kallon wani Indian film da akeyi,
Zubamin madara ya fada batare da ya d'agoba,,
Mikamai tai data zuba akaramin mug tabashi,
Kana takoma tacigaba da kallon tana satar kallon shi kadan_kadan,
Tunda yaga ta zauna yasan akwai wata kasa,
"Auta Na'am" yayah,,
Mekiki bukata ne? uhm,
Kusa dashi tamatsa tana murmushi,
"Yah majeed waya nakeso asanja min,
Uhm saimai?
Account dina yayi kasa tafada cikin shagobba,
Uhm saime?
Shikenan!
Okay kifada ma "Yusuf kalan wacce kikeso kudin kuma zan miki transfer,
Thanks yayanah,,
Madara takara mishi ta fice daga part din,
Fuskarta dauke da murmushi,

Shima murmushin yayi ya cigaba da akinshi,


________---------_______

💗💗💗
Kaduna


B'angaren ummah halima kuwa,
Koda dady yadawo tafada mishi cewa yayi,
Ganina bai kamata safiyya tadawo gidan an yanzuba sbd yanzu ta girma ta mallaki hankalin ta, dole bakomai za'a sassauta mata bakamar daba,

Kuma dudu saura kwana nawa tai aure,
In Allah yakawo nagari,
Baikama ki ri'ka Sagar mata da gwiwa ba,

Yarinyar akwai hankali da hakuri kinsan kuma duk mai hakuri a RAYUWAR Nan bazai taba faduwa ba,
Kikara kwantar mata da hankali kinji,

Hakadai ummah halima ta hakura dan taga hakan shine dai-dai,

Around 8:30 safiyya ta farga kasancewar dama ta tashi tayi sallah komawa tayi,
Gefen ta takalla ba "Buhaisa kana takai kallon ta ga agogo,
Ido tazaro tana durowa,

Kai tsaye bathroom ta nufa,
Sanye ta fito daure da towel,
Da karami a hannun ta tana goge gashin kanta,
Dan Safiyya batasan kitso kwata_kwata
Wardrobe ta nufa ta dakko bakar jallabiya,
Tasaka,
Kana takarasa gaban mirro lotion, kawai ta shafa sai kwalli, da lips gloos,

Fita tayi kanta ba dan kwali sbd ta wanke kan tanaso ya bushe,

Ummah halima ce kawai a parlour ganin yadda tafito ne yasata sakin baki,
Wato ke safiyya har yanzu baki dena barin kannan naki ba kitsoba,
Kuma bana hanaki zama ba dan kwali ba koh,
Ummi wanke kan nayi shiyasa nabarshi yasha iska,
Okay bari buhaisa ta dawo saikuje kitso "Ummii" tafada cikin shagobba,
"Na'am please basai naje ba tana rausayar dakai,
Shikenan jekiyi breakfast kannan ya bushe sai na tufkemiki,
Uhm kawai tace tanufi dinning amah badin taso ba,

Bayan tagama tafara tufkemata ummi please kimin kalba next week sai buhaisa tarakani amin kitson Dan Allah,
Uhm Allah yashirya ki da wanna halinaki
bari na miki kalba
Amah ki tabbata anmiki kamar yadda kifada,
Insha Allah ummi!
Har tagama mata suna fira,
Takuma fadamata yadda suyi da dady,
Ai bakomai ummi nifa nasaba da halinsu,
Hakadai takara kwantar mata da hankali da sake yimata nasiha..

kitchen su shiga ta tana tayata aiki kasancewar masu aiki basa musu girki,



_________

B'angaren MD kuwa Koda yaje gurin aiki da murnar ganin safiyya amah sai ya tuna ya bata hutu fah,
Hakadai ya aikin ba nutsuwa Allah yasama dai taji sauki, yafada yana shafa fuskar shi,
har sutashi gurin aiki yana tunanin ta dan haka kai tsaye gidan su yanufa,
Daya dade da sanin sah,
Ya dade bakin get din kafin ya aika yaro akirata,
To inta fito me zance mata uhm meyasa yau bakizo gurin aiki ba, kai aa kawai nazo dubaki ne yesss shikadai yake surutun shi har yaron ya dawo wai gatanan,
1k yaba yaron shikuma yatafi kusan 20 minutes saiga anty Waleeda ta fito acin mayafi da da dauri,
Bai lura da fitowar taba saida ta kwan-kwasa glss din motar,

Budewa yayi tare da fadin baiwar Allah lafiya,
Cikin yau'ki tace bakai ace kana kirana ba,

Ooh sorry safiyya nake nema,
Dan inkin shiga ki turomin ita,

Kallon sama da kasa tamai mai ooh ka Bata ai banan bane gidansu,
Kallon rashin fahimta yabita dashi ai naga kuma nan gidan,
Kai malam nacema bannan bane haba tafada tana kama hanyar koma gida rai a bace,

Mamaki yakama shi to amah ai naga dai Nan ne gidan yafada yana kara kallon gidan,
Hakadai yaja mota ya tafi badin yaso ba,
Zuciyar shi cike da kewarta,



__________
Yayah saif ne yafara dawowa sai anty hajara,
Buhaisa karshe lokacin tuni sunyi dinner itada ummi Dan har baccin rana ma tasata tayi,

Bayan kowa ya shirya su fito parlour suna fira yayah saif shima yadawo daga massalaci,
Shima zama yayi ana hirar dashi,
Buni_buni kadan yana kallon safiyya,

Har anty hajara ta lura dashi ummi ce ta fito Dan haka dinning area suka nufa,
Safiyya ce tayi saving nasu tana zuwa buhaisa ta zauna,,
Dariya anty hajara tayi sufara cin abicin,
Itama buhaisa batai magana ba ta zuba tana hararar ta,

Parlour su dawo ana Hira har dady yadawo motsi kadan tayi idon yah saif akanta,
har dai ta gaci tace yah saif please kallon fa tafada tana harara shi,
Ka badaya kallon shi sukai kanshi ya sun kuyar cike da kunya, daga bayama tashi yayi ya koma ciki......................✍️


(Waishin 🧐dawa azima take waya ne komai zai faru tsakanin anty Waleeda da md🤭)


Kudai kawai saimun hadu a page 18&19 danjin yadda zata kaya🥰





*🌹 RAYUWATA 🌹*

*Story and written✍️*

*Bilkeesu .S. Aliyu*
_💞(Billy pinky)💞_

*🤝 Amanar nazari writer's association📚*

*[07070260240]*

_WhatsApp number or call_

*📚N .W .A🖊️*

*EPISODE 🌷1️⃣8️⃣⏪1️⃣9️⃣🌷*




*Abuja____--___*


B'angaren yah majeed kuwa Koda auta ta fita aikin shi ya cigaba, bayan ya gama ya maida hankalin shi a tv yana kallon film din da sukeyi yana shan madarar sa kamar baya so.
Har saida film din yakare sannan ya shige ciki.
Maimakon kwanciya bathroom ya wuce ya hada ruwa mai d'umi cikin bathtub tare da zuba kayan kamshi kala_kala.
Sanan yashige ciki Saida yayi minti ashirin cur ruwan na ratsashi ya sanan ya shiga gurin wanka ya dauraye jikin shi.
Bayan ya fito shafa'i da wutiri yayi sanan ya shirya yayi kyau sosai cikin shigar tasa kamar wanda ba kwanciya zaiyi ba .
Ga wani uban kamshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login