Showing 78001 words to 81000 words out of 84595 words
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION ✨*
*T.M.W.A✍️*
*Amanar taurarin marubuta writer's.......✍️*
*TEAM HAZIKAI BAKWAI 💪✨*
Page. 4️⃣8️⃣➡️4️⃣9️⃣
~AMMEII~
..............Zaune take a makeken bedroom din na dady a wata kujerar da ke cikin ɗakin wanda ajesu dan hutawa kawai, yadda ta zuɓe dady da kallo dake kire-kiren waya yana sanar musu da bikin Majeed ɗin gobe ne yasata a mamaki. Duk abinda take hankalin sa na kanta kuma yana kallon ta, saida ya gama ya dawo da hankalin sa gaba ɗaya zuwa kanta, hannun ta ya kama kana cikin sayin murya da kwantar da hankali yace.
"BILKISU!"
A hankali ta ɗago da idanun ta tana kallon sa fuskar ta ta ƙawata da murmushi kana cikin sayin murya ta amsa da, "Na'am ASADI" Saida ya sauke ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa. "Please inason ki kwantar da hankalin ki akan batin auren nan nasan ki Bilkisu nasan ki da hakuri gami da kawaici Please Bilkisu ki daura a yadda na sanki, Auren nan anyi shine bisa wasu dalilai nawa da Ni kadai nasan su kuma insha Allah bazata bamu kunya ba. Dan haka Inaso ki kwantar da hankalin ki Ni nasan tunanin ki akan wacece wacce na aura ma ɗan ki ya take? wannan tambayar nasan itace a cikin zuciyar ki toh ki ajeta zuwa gobe insha Allah zaki sani, kuma nasan zaki mutukar farin ciki haɗi da jin daɗi dan haka ki kwantar min da hankalin ki kinji Bilkisu nah". Dady ya idda maganar murmushi kwance a fuskar shi yana kallon Ammei, itama da murmushin a fuskar ta tace, "Tabbas hakane tambayar dake a cikin zuciya ta kenan kuma Ni nasan bazaka zaba mishi wacce bata dace da shiba sai dai ina tsoran halin Majeed Dadyn su kasan shi, kasan yadda ya tsani mata sai naga kamar bazai amince ba".
Saida dady ya nisa kana fuska ɗauke da murmushi yace "Bilkisu kenan amincewa kuma ta nawa kinsa Majeed da biyayya balle kuma wannan umarni na ne wanda tun yana ƙaramin shima baya tsallake wa balle yanzu daya girma na tabbata koda ace Youseef nama auran nan zai amsa da hannu bibbiyu balle Majeed".
"kayi hak'uri Alhaji bahaka nake nufiba wlhy, ina farin ciki da umarninka, ALLAH kuma yasanya alkairi, wlhy tun kafin naga yarinyar ma tashiga raina, kuma naji k'aunarta. Allah Ubangiji ya shige mana gaba Allah kuma yasa alkairi bari na kira su Ammah na sanar musu, dan su fara shirin tahowa zuwa gobe domin tarbar amarya".
"A'a ai tuni na kirasu tun bayan ɗaurin auren na sanar musu ƙalilan ne wanda ban sanar musu ba yanzu kuma nake kiran su, hatta yan Kano yau da shirin su zasu kwana gobe da safe zasu sauka insha Allah". Murmushi kwance a fuskar Ammei tace .
"Lallai Dadyn su da shirin ka kake tafe kace Ammah tama rigamu ji kenan?" Yar dariya dady yayi kana yace, "Toh ai kinsan ance da zafi-zafi ake dukan karfe balle bikin Majeed guda, Jika Namiji ɗaya a familyn AA SARAKI a dolene bikin shi kowa yasan dashi, koya kikace? Sannan abinda yasa Ammah bata kiraki ba Ni nace ta kyaleki saikin kirata da kanki tukun na". Dariya itama Ammei tayi kana cikin farin cikin da idan ka kalli fuskar ta zaka sheda hakan tace, "Kwarai kuwa amma mu ai yan kallo ne sai dai mu zuba ido".
"Ba wani zuba ido dan Allah tashi ki ɗauki wayar ki duk wanda ya dace ki kira ki kira ki sanar musu, duk da nasan wannan aikin su Ammah ne kuma yan Kaduna nasan duk zata sanar musu duk da Ni na kira wanda naga zan iya, sauran saita ƙara sa, toh amma kema ai aikwai wanda zaki kira, sannan kuma batun abokansa tun a ɗazu wasu daga cikin su su sani, Sannan kuma nasan wannan aikin Youseef zai ƙara sa shi ai, zuwa gobe duk wani abu da aga ya kamata sai ayi dan maybe sai yamma yan kawo amarya zasu ƙara so".
Sosai Ammei ke mamakin mijin nata inda su zauna suyi shawara sosai akan yadda bikin zai kasance gobe dan shirin zuwa gurin granny ma take bayan magrib.
~ZAITUNA~
Sosai daka kalli Zaituna a daren nan zaka sheda tana cikin tsantsar tsagoron tashin hankali wanda ya kasa boyuwa a fuskar ta, dan tun ɗazu ta tasa mahaifiyar ta tana kuka akan alƙawarin datai mata na auran Majeed kuma ita kadai ce zata Aure shi dan ita kaɗai zai zauna. Sai gashi ɗazu Dady ke sanar da yama Majeed ɗin aure da wata ba itaba, wannan wacce irin masifa ce. Ita kanta Mummy Hankalin ta bashi a jikin ta tunda Dady ya gama maganar sai dai wayar datai da ƙawarta ce tasa ta ɗan ji daɗi, akan koma wacece aka aurama Majeed ɗin zuwa safiya zata sani dan zatasa a mata bincike ne akanta. Yaron da bata da wani buri daya wuce ya auri yarta dan koda ace Zaituna bata son sa toh fa dolene ta aure shi saboda wani dalilin ta, sai gashi wata can zata rusa mata shirin data dau shekaru gana yi. Meyasa ma Yayan nata ya mata haka? Meyasa ya aura masa wata bayan ta sanar dashi 'yarta tana son shi? Wacce ma wacce a aura ma Majeed ɗin? Waɗan nan tambayoyin sune cike da zuciyar ta wanda batada mai amsa mata.
Ganin yadda Zaituna ta tasata a gaba sai uban tambayoyi take mata da kuku yasata kora ta waje dan ita kaɗai tasan meke damun ta. Tanaji duk tashin hankalin da Zaituna ta shiga na rashin Majeed baikai rabin wanda ita take ciki ba a yanzu, dan shirine data daɗe tana yi na tsawon shekaru su gashi cikin kuni ɗaya ana neman kaita ƙasa, "Impossible Wallahi". Ta faɗa da ƙarfi kamar wata zararriya.
Koda Zaituna ta fito a ɗakin Mummy ɗakin ta tashiga inda ta tarar da Azima zaune ta zabga uban ta gumi alamun itama ta faɗa duniyar tunani. Jikinta ta faɗa tana sakin wani sabon kukan kana cikin kuka take cewa.
"Shikenan na rasa shi Azima wallahi bazan juri rashin Yah Majeed ba a cikin RAYUWARTA bazan iya juraba Azima, duk son da nake mishi kuma yasan da inason shi amma harya bari Dady ya aura masa wata bani ba?". Kuka ya sarke ta inda Azima tayi shiru tana sauraren ta kana cikin kwantar da murya tace. "Zaituna dan Allah kiyi hakuri kisama zuciyar ki salama kwarai nasan da ciwo kuma da mamaki danni kai a cikin mamakin nake, kuma Yah Majeed ai baki rasa shina Zaituna dan yayi aure bashi ke nufin kin rasashi a RAYUWAR kiba Zaituna ki kwantar da hankalin ki mana".
"Na kwantar da hankali kafae kice Azima kinsan me kike faɗa kuwa, wallahi hankali na bazai taɓa kwanciya ba saina san wacce a aura mishi wacce ke shirin rabani da RAYUWARTA, sannan naga na fitar da ita Ni kuma na shiga shine hankali na zai kwanta Azima". Mamakin Zaituna ne ya kama Azima sosai dan ita har dariya take idan taji ta nace saita auri Yah Majeed d'in. Cikin ƙasa-ƙasa da murya tace da Zaituna.
"Humm Zaituna kenan toh ke taya zaki san wacce dady ya aurama Yah Majeed d'in? Ke nifa tunda naji batun auren nan nace maybe wacce ya aura masa ba 'yar ƙasar nan bace, nifa badin yaran Uncle Kabeer ba 'yan mata bane da sainace a cikin sune tunda kinga su a Saudiya suke, dan nifa a ganina Yah Majeed ya wucce a Aura masa 'yar Nigeria kuma a masa irin wannan auran inba ZAƁIN saba bace, kinga fa Dady daga ƙasar waje ya dawo kila acan ya samu 'yar abokinsa ya aura mas...". Tsawar da Zaituna ta dakama Azima ce tasa tayi shiru tana kallon ta, "Ya isa haka dan Allah Azima ya nazo miki da kukana kuma kina min wata maganar banza, wato nufin ki harni ma Yah Majeed ya wuce ajina bankai ya aureni ba kome ne"?
"A'a kwantar sis ba haka nake nufi ba ina nufin ita wacce a aura mishi sai dai ba yar Kasar nan ba amma in yar ƙasar nan ce nace ya wuce ajinta. Keko wazai ce baki mishi ba kina da komai na matar manya gashi kin fito daga babban family ga class a kinkai Yah Majeed ya aure ki". Shiru dai Zaituna tayi bata sake cewa komai ba sai tashi da tayi ta koma ƙarshen gado ta kife kai ta cigaba da rera kukan ta, yayin da Azima ta taɓe baki murmushi kwance a fuskar ta ta tashi ta fice a ɗakin.
~FINNAT~
Kwance take a gado sai raira kuka take Basma dake gefen ta sai aikin rarrashi take, "Dan Allah anty Finnat ki kwantar da hankalin ki akan auran nan na Yah Majeed duk kin wani daga hankalin ki, auran na fa da yayi bashi ke nufi kin rasa Shiba, aa indai Allah ya hukunta zaki aure sa ai saikin aure sa dan haka Please ki kwantar da hankalin ki. Kuma mafa ni abinda yake bani haushi daku yadda ku mace akansa batin shi sam baya nuna alamun yasan kuna yi, sautari a gaban ku yasha sanar damu cewa yadda ba aure a tsakanin sa da Auta haka ya ɗauke mu ba aure a tsakanin mu dashi, Amma ku dukun mace akansa bamai iya danne sonda yake masa a cikin ku why?".
Finnat na shirin magana Addah ta shigo hakan yasa ta fasa maganar da tayi niyar yima Basma. "Barka da dare Addah". Basma ta faɗa kai kawai Addah ta jinjina ma Basma kana tace.
"Tashi ki zauna Finnat".
Ba musu Finnat ta tashi ta zauna tana share hawayen dake fita a idanun ta, cikin daure fuska Addah ta fara magana.
"Meyasa kike son maida kanki shashasha ne akan wanda sam baisan kina yiba idan ma yasani bai ɗauki abun serious ba?" Shiru Finnat tayi b tare da tace ma Addah komai ba sai ajiyar zuciya da take sauke wa. Addah ce ta cigaba da magana cikin taushin murya. "Toh inaso ki kwantar da hankalin ki indai mijin kine zaki Aure shi dan yayi aure bashi ke nufin bazai Aure kiba, a'a Aure nufin Allah ne, sannan kuma bazan ce ki cigaba da son shiba ba kuma zance ki dena son shiba Saboda dan uwan kine. Amma fah ki sani duk sanda son shi ya miki wata illar ke kijama kanki. My son ya ɗauke kune a matsayin kannen sa wanda su fito ciki ɗaya amma wai ke son shi kike wannan wanda irin abune haka Finnat? Toh Daga yau karkice ban gaya miki ba ba ruwana, kuma duk wacce ta kawomin wata matsala a sha'anin bikin nan wallahi zan mugun saɓa mata, koba alaƙar dake tare dani da Majeed aishi yaron Aminiyata ne, dan haka wllh ku kiyaye nasan ki Finnat nasan halin ki a haka kina a sanyi-sanyi amma bakida ragi ko kaɗan dan haka wannan kashedine".
Daga haka ta mike ta fice rai a bace yayin da Basma ta bita da kallo, shiyasa Addahn tasu ke birgeta sam batada son zuciya akan wani komai nata tanayi ne iya gaskiyar ta gashi tana mutukar son Aminiyar tata. Yayin da Finnat ta koma t kwanta ta cigaba da kukan ta daga Yadda ta tsaya, baki Basma ta taɓe ta fice a ɗakin itama inda kai tsaye part d'in Ammei ta nufa dan tana son su gana da Auta kasan cewar duk yaran gidan ɗakunan su a part d'in iyayen su yake.
___________________
A wannan daren duk wanda ya kamata yaji bikin Majeed kam yaji harma da wanda bai kamata ba, wasu tuni sunji dan tun bayan ɗaurin aure dama dady ya kikira mutane da yawa ya sanar musu sai Alhaji Ahmed daya tayashi, dan familyn sane kawai bai sanar musu tun a waya ba saboda surprise d'in dayaso musu, kuma tabbas ya musu yaga masu so dama wanda basa so. Yan Kano kuwa tun a yammar su so tahowa sai dai yace su bari sa iso gobe tunda, su sai gobe za suyi nasu taron zuwa jibi amaryar ma sai zuwa goben zata iso. Ba musu suka barshi a sai goben yayin da duk wani shirin su sunyi zuwa gobe sai tahowa. Haka ɓangaren yaran gidan da suyi aure, su anty Hauwa dake a Legos a lokacin da Mama ta kirata ta sanar mata ba ƙaramin murna tayi ba, a kuma lokacin ta kira Majeed ɗin dan da kyar ya samu tabarshi dan saida ma ya kashe wayar. Ita kadai ce ke masa wasa harya biye ta kasan cewar ta sakuwar sa.
Youseef kuwa tun barin sa part d'in Dady ya fara kiran friends din nasu yana sanar dasu bikin Majeed ɗin, inda suyi mutukar mamaki tare da jinjina wannan lamari akuma daren su fara kiran Majeed suna masa murna masu shakiyanci na masa, Yayin ji yake kamar ya kodesu saboda takaici. A ranar fah yasha amsa waya dan daga bayama kashe wayoyin nasa yayi ya kwanta zuciyar sa cike da alwashi iri-iri akan yarinyar da'a aura masa.
Lokacin da Youseef yake sanar mada yaran Majeed ɗin su muktar ba ƙaramin mamaki su shigaba tare da jin daɗi, inda a lokacin Joseph ke cewa. " Haba no wonder naga Boss yau yayi wani kyau Allah na rage karya har wani haske ya ƙara duk kasan cewar sa fari". Dariya muktar yayi yace, "Humm nima da naga har wani kyalli yake ashe kyallin angoci ne". Dariya suka sa gaba ɗayan su harda Youseef dake sauraren su dan shima kanshi yaga Boss d'in ya Kara kyu yau ashe ango yake. Yayin da su cigaba dama Majeed ɗin shakiyanci tare da godema dady dan sun kosa suma suna matar Boss d'in haɗi d yaransa dan su nuna musu gata kamar yadda mahaifinsu ya nuna musu dan Boss d'in nasu fa na musamman ne. Anan ne Youseef ke cewa, "Nima maza-maza zanyi na samo matar aure kafin Dady ko Abba ya dawo kaina, dama shi Boss d'in muke jiran yayi toh yanzu ko dole muma mu shigo layi".
Dariya sosai su Jabeer suke yi inda Jabeer yace, "Toh ai kai saidai ka zaba badai ka nemo ba kaida kake King of love". Duka Youseef ya kaima Jabeer ya kauce yana dariya, yayin shima Youseef dariyar yayi ba tare daya sake cewa komai ba. Daga nan kuma hira su cigaba da shirye-shiryen su.
Toh a ɓangaren yaran gidan kowa sai murna dokin bikin Yah Majeed d'in suke, dan Auta ma ita kadai tasan farin cikin d take ciki dan a duniya bata da burin daya wuce ace taga Yayan nata yayi aure, kamar yadda sauran kawayen ta nasu suyi, sai dai kaji ana ina gidan anty ko munje anguwa da anty, amma ita shiru kasan cewar shi kaɗai ne namiji a familyn nasu, gashi tun bikin su anty Hafsah da ayi ba'a sake yin biki a gidan ba, kuma wasu daga cikin duk basu da wayo shiyasa suke mutukar son ayi biki a gidan nasu. Toh yau ga bikin Yah Majeed dan itafa tun barowar ta part din dady ta fara kiran friends dinta tana sanar dasu haka Basma tazo ta sameta su ɗaura daga yadda ta tsaya. Daga nan su fara shirye-shiryen yadda goben zata kasance.
*WASHEGARI 🤍*
A washe garin ranar FRIDAY wato asabar, gidajen rediyo dana television suka tashi dama mutane Albishir da auran na AA SARAKI wanda kowa yafi sani da *Abdulmajeed Abubakar Saraki* sosai sanar wa taba mutane mutukar mamaki dan jin abin suyi kamar a mafarki babban abun mamakin ma shine wacce aka faɗa cewa itace Amaryar. Sosai mutane su tayashi murna yayin da gaba ɗaya ƙasar ta ɗauka kasancewar sa Babban mutum da Nigeria keji mutukar ji dashi, dan yayi gadone daga Uban har kakan ana damawa dasu a Nigeria kasancewar su sannan nu a duniya dan ko a ina akace SARAKI FAMILY toh fa ansan da zaman su a ƙasar. Yayin da garin na Abuja harma da Kaduna yayi mutukar amsa kuwa da labarin bikin Majeed ɗin da amaryar tasa wacce itama ta zama sannaniya a tsakanin garuruwan saboda ba yadda prograns dinta baya zagawa. Mutane da yawa sunji mutukar mamaki na canjin Auran da aka samu a maimakon wanda akan tun farko shi zata aura, koya zancen yake? Wannan tambaya itace cike a bakin mutanen harma da 'yan uwanta 'yan jarida da suke son sanin wannan amsar.
____________🖤🤍
* AA SARAKI HOUSE*
Misalin 12:00am na rana gidan a mugun cike yake da yan uwa da abokan arziki na kusa dana nesa. Duk da bikin jiya sukaji wasu ma sai dare bai hana su sauka yaudin ba, kunsan abu na jirgi awa ɗaya ne zuwa biyu ya kawo ka. Musamman 'yan Kano da tun 10 suka iso sosai duk parts ɗin gidan ke ɗauke da baki haka zalika ko wacce mata itama da tata tawagar, dan sosai part din granny ke cike da baki haka na Ammei dan tuni Ammah ta iso. Tuni fah gida ya cika da baki alabarshi SARAKI FAMILY wanda daka gansu kasan sune dan fa suna mutukar kama da juna ga auran zumunci da yawancin su shi