Showing 81001 words to 84000 words out of 84595 words
sukeyi.
Gaba ɗaya Majeed mamakin ganin bikin da suka shirya yake yi, dan Ammei kanta da su Ammah su Addah da komai da ita ake ko lokacin kansu basu da. Shi sai abun ya fara bashi mamaki bikin da kwata-kwata sai jiya bayan ɗaurin aure su san dashi amma shine har an mishi wannan shirin. Granny kam ai ba'a ganin ta sam, dan tana can cikin yan'uwa da ya'ya da jiko dan can na hango ta cikin wani fitinannen les da amishi ɗinkin bubu ga wani uban ɗauri daa coka mata kace itace Amaryar, Dan fah ita baki har kunne Dan musulta muku irin farin cikin da take ciki bata lokaci ne, kasan cewar yau ne zata aurar da Jikan nata ɗa ɗaya tilo Namiji dake gare su da duk duniya bata da burin daya wuce taga wannan ranar, ai ita ko iya auran sa ta gani ta mutu taji daɗi.
Al'amarin Ammei ɗin tashi bai gama girmar kansa ba sai da Youseef ya kaisa masaukin da suka tanadarma abokan nasu, yaje ya samesu harma da wanda baiyi zaton gani ba. Aifa nan suka tasashi gaba da mitar rashin sanar musu auren nasa, dan sai da suka iso suke jin ai an rigada an ɗaura aure tun jiya, Bashi da bakin bayani sai kawai ya bar Youseef da musu sharhi. Yayinda shi yake jinsa wani iri dan shifa sam ya kasa gane kan wannan lamari na Auran dolen da aka mishi, shifa bai taɓa tunanin rashin Auran nasa ya dami Dady ba da har zai masa Aure da wacce bai sani ba. Shi a yadda ya tsara sam ba Aure a ra'ayin sa yanzu dan har yanzu baiga wacce tamishi ba. amma kwatsam sai gashi Dady ya rusa mishi wannan shirin nasa ya nasa auren dolen da ba yadda ya iya dole ya amsa, amma fah shi amsar da yake jira itace shin wa Dadyn ya aura masa? wacece ita? a ina take?. Waɗan amsar yake jira toh amma koyasha kwaya bai isa yaje ya tambayi Dady ba.
Shakiyancin da Abokan nasa suke masa ne yasa shi jin kamar ya tashi ya basu guri dan harda Youseef, dama tun ɗazu ya isheshi sai da ya masa jan ido kana ya samu yabar shi amma yanzu tunda yagan sa da sauran friends d'in nasu shine ya daura a inda ya tsaya. Kasan cewar kusan duk abokan nasu sunada mata wasu ma ba ɗaya ba, dama shi suka tasa a gaba garashi Youseef yana shan love da yan matan sa amma shi ko yan matan ma baya kallo balle ya kula wannan dalilin yasa suyi mutukar samasa ido da son ganin matar dazai aura.
Ji yake kamar ya tashi ya basu guri toh amma ba dama, dan tun farar safiya Dady ya turo masu gyaran dan har yanzu suna can suna gyaran part din shi abun mamakin ma wai badai a part din sa za'a sataba. Wata zuciyar tace "Toh inba nan ba part din Ammei za'a kaita?". Hannu yakai yaɗan shafa gashinsa dake kwance luf a gadon bayan sa tare da lumshe ido kana ya buɗe a lokaci guda.
Dariya sosai Youseef su saki inda Khalid yace, "Wooo my friend anan can ana tunanin amaryar tamu ne?". Harara daya wulla masa ce tasa shi sakin dariya inda Taheer ya amshe da faɗin, "Ganemin hanya mutumina sai wani shafa kai yake da Lumshe ido". Dariya suka kuma saki a tare inda Faruq yace,
"waini yaushe ma mutumin nan ya fara soyayya ne?". Abdul ne ya amsa da, "Abinda na gani kenan kaga yana wani sanfewa shiba ruwan sa da mata". A tare suka kuma sakin dariya irin ta shakiyancin inda Sadeeq ya amshe da cewa, "Kaga yana wani muzurai shi har yanzu baiga wacce tai mishiba". Dariya sosai suke yayinda Sameer yace, "Ai yanzu gashi yaga wacce ta mishi a Kaduna koh". Dariya suke keyi iya iyawar su dan yadda gogan ya wani haɗe fuska zai baka tabbacin a kusa yake, su kuma sanin hali yasa basu barshi ba su cigaba da yanda su tsaya. Tun yana jinsu har abun ya fara isarshi ya fara maida musu martani.
Toh a ɓangaren 'yan matan gidan kowa da irin nata shirin da take yayin da irinsu Auta, Basma, Ihsan, Salma, sai sauran yaran SARAKI FAMILY dasu iso ɗazu Sa'a ninsu kansu ke a haɗe danfa yan matan family kashi-kashi ne. Su sai masu mugun jiji dakai wato su Zaituna da Azima, Asfad, bathool, saina su Finnat da Aynah, Sarah, Ashfa. Sai nasu Auta dake ƙasa dan su yan ba ruwan sune. Gaba ɗaya 'yan matan sun haɗe kowa ya kama nashi ɓangaren dan ma yaran uncle Kabeer basu zoba kuma Dady ne ya hana yace bayan bikin idan sun samu hutu saiya taho tare da iyalen nasa idan kafin nan ma shi Majeed ɗin yazo masa da tasa iyalin toh, wannan dalili ya hana zuwan ahalin uncle Kabeer din.
Sosai ko wacce taci wankan ta Dan fah wanna bikin ba ƙaramin tanaji da dakon jiran sa suke ba sai gashi Allah ya kawoshi. Yayinda ta fanni Zaituna fah ko alamun tashi ta fara shiri batayi ba dan tana kwance shambar a gado kuka ma ta gama yi.
Mummy ce ta shigo dakin inda ta samu kusa da Zaituna ta zauna, tashi tayi ta faɗa jikin ta tana sake sakin kuka. Cikin dacin murya tace.
"Ya isa haka mana baby ki kwantar da hankalin ki wallahi wallahi wallahi indai Abdulmajeed ne kisa a ranki ki same shi dan kota halin ƙa-ƙa saikin auri Majeed ni na miki alƙawari dan wallahi yanzu za'a fara wasan. Dan haka maza tashi ki fara shiri kamar yadda sauran yan uwanki keyi, dan kema nan gaba kaɗan naki taron bikin za'a dawo tare Abdulmajeed wannan alƙawari nane Zaituna dan sam bazan yadda akaini ƙasa ba".
Ina ita Zaituna yanzu tama dena fahimtar Mummy dan farin cikin alƙawarin data mata, shiyasa bata wani damu da zance baza'a kaita ƙasa ba dan ita burinta kawai shine mallakar RAYUWARTA wato Majeed. Kuma tunda Mummy ta mata alƙawari tasan bata da haufi akan mahaifiyar Tata, dan haka cikin kankanin lokaci ta fara shiri. Yayin da su Azima su shigo cikin nasu shirin da tabbas ka kallesu dole ka ƙara dan fa sun dau na agwagwa kowacce ta baza capacity yadda ya kamata. sun sameta tana shiri, mamaki sosai ne ya kama Azima ganin wacce su bari tana aikin kuka ce zaune tana shirin shagalin bikin abun son nata fuska ɗauke da murmushi toh meya sata farin ciki haka kamar wacce ace itace Amaryar? Koma dai itace Amaryar? Kai inna abinda bazai ma yiwuba kenan.🤔
A ɓangaren Finnat kuwa tuni tashi tayi shirin ta dan tun faɗan datasha jiya agun Addah haka yauma tasha, shiyasa ta dake ta shirya inda tasa aranta tunda taga Addah bata goyon bayan ta da Majeed ɗin toh fah ba hakan ke nufin zata hakura ba, dan dolene itama ta fara nata shirin basai ta jira wani ba. Shiyasa ta kuduri fara nata shirin dan daka kalleta baka isa gano akwai damuwa a zuciyar taba, dan tsaf fa ta zauna ta dau wanka da itada yan Team ɗin nata wato su Ayna dan anko suyi sun baza cafacity iya cafacity fah ba karya 💃😂.
Huu huu huu😂🤣 yaufa akeyin ta bikin Big Bro watoh Yah Majeed koya zata kaya wacece amarya shin kodai Zaitunan ce🤔, toh fah nima ban sani ba 🤷 Readers ku biyo alƙalamin BILLY PINKY ✍️ Dan jin yadda zata kaya.💃😂
Nidai nayi nan 🏃🏃🏃🏃🏃
*Typing📲*
_Follow my WhatsApp channel_ 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0
_Follow my WhatsApp group_👇
https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB
*🌹 RAYUWATA 🌹*
_CREATED AND WRITING BY_
*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞
✨*TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION* ✨
*T.M.W.A✍️*
*Amanar taurarin marubuta writer's.......✍️*
*TEAM HAZIKAI BAKWAI 💪✨*
*END OF BOOK ONE*
Page. 5️⃣0️⃣
.............Kamar yadda a gidan jiya FRIDAY ayi yinin biki yau Saturday ta kama cikar biki, sosai Yau ma nasha kyau Kamar ka sace ka gudu. Sosai yau tunda na tashi nake jin gabana na faɗuwa na rasa dalili yayin da kuma haka kwai naji sam bana son yau ɗin akaini gidan su Suraj ɗin kamar yadda ace sai yau.
___________★
Bayan gama walimar da Ummi ta sake shiryawa anan gidan Abba da safe inda a tashi gurin sha biyu. Sosai walimar ta kayatar dan ba karya.
Sosai Mom taji mutukar bakin ciki na walimar da Ummin tayi a gidan dan fa duk wani abu da ayi a gurin kamu ba wanda 'Yan uwanta su boye mata, acewar suma gani ya kori ji dan dakko mata suyi a waya su nuna mata, aiko bata iya ta ƙarasa kallaba tace a kashe dan ita anty Waleeda ma tashi tayi ta shige ɗakin Mom d'in tana kuka, wai Safiyyah ta gama kwace mata Suraj d'in. Toh yanzu mafa shine ganin wannan walimar da Ummin ta shirya yasa bakin ciki ya cika Mom ɗin itada maƙaraban ta.
_______★ *Around 4*★______
Bayan nayi sallar La'asar kamar yanda Ummie ta faɗa aka haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito sai uban kamshi nake, dan da alama wannan ɗin yafi sauran da ake min amfani dasu. ace a fara shirin shiryani
Sai kawai na sakin musu kuka anty Hajara tace "ƴar shagwaɓa". Dan wlhy jinake tamkar kar a kaini. Haka dai aka gama shiryani cikin atamfa datai matuƙar ƙyau ta kuma samu ɗinki na nutsuwa.
Kawu Bala, Abban su Buhaisa da ya zo ɗazu, da sauran uncle's d'in nawa sai Abba nah su Yah Ansar, Yah Saif, Yah Safwan, sai su Mama Hadiza, su Ummie ne sukai min faɗa da nasiha mai matuƙar ratsa jiki da ɓargo. Daga ƙarshe suka sanya min albarka da fatan alkairi a rayuwar aurena.
Sosai nake kuka mai tsuma zuciya dan zuwa yanzu nikam na fara karyewa. Duk da jiyama sun min nasihar hadi da faɗa amma nayau ɗin sai naji yafi najiyan.
Karfe biyar saura mintuna saiga haddadun motoci masu matukar kyau da ƙyalli bakaken Prado da G-Wagon suka shiga unguwar cikin natsuwa da tsari. Unguwa ta tsaya cak. Kowa na kallon jerin motocin kamar faretin gwamnati.
Ya subahannallah tsarin ya matuƙar haɗuwa, motar amarya a tsakkiya tasha flowers. Wasu na ɗaga waya suna ɗaukar bidiyo.
Shigowar Anty Fatima tana cewa ga motoci sun zo. Sai a lokacin kuma naji duk na rikice. Nanfa na saki musu kuka, haka dai aka ƙara shiryani tare da chanja min atamfar zuwa wani fitinannen les ne komeye dai ban saniba sai wata irin alkyaba mai mutukar kyau, tsaf kuwa kayan suka tsayamin ga wani uban kyau dasu min duk da ba make-up ko ɗaya a fuska ta.
Duk yanda akaso na miƙe naƙi nai hakan har sai da Kawu Bala da kansa ya shigo yana faɗa sannan. Kuka nake sosai har numfashina na shiɗewa. Amma babu wanda ya saurareni, sai ma gaban Mom da aka kaini na roƙi yafiyarta. Cikin taɓe baki tana wani fisge-fisge ta ce, "ALLAH ya yafe mana baki ɗaya sai aje aita haƙuri, dama ita rayuwa ai haka take babu tabbas..." ganin tana neman sakin layi Mama Hadiza ta kamani muka fito dan Ummie sam bata biyomu gurin Mom ba.
Abba ma an sake kaini na masa sallama. Yah Ansar kam ya rufe kansa a ɗaki yaƙi yarda. Nasan kuka yake, dan haka nima na ƙara ƙarfin nawa kukan ina tutturjewa, sosai Ummie ta riƙeni kasan cewar tace saita kaini har ɗakina yayin dani sam bamga su Buhaisa da Isha ba. A rikicen da nake yasa bamma san kala ko adadin motocin da suka zo ɗaukata ba. Ni dai kawai Ummie ta sakani a motar da take ɗauke da wani irin ƙamshin. Mama Hadiza da Ummie ne tare da ni, sai gaba da ban san waye agun ba danni fa, tunda La'asar tayi gaba na ya tsananta faɗuwa ji nake kamar wani abune zai sameni. Sosai gurin yaɗau buɗe-buɗe yayin da masu ɗaukar video da hotuna sai faman ɗauka suke. Yah Saif kam tun bayan gama min faɗa ban sake sashi a idona ba harmu tafi.
Mamaki kwance akan fuskata ganin mu a tashar jirgin ƙasa sosai gaba na ya cigaba da faɗuwa yayin da nakai kallona ga Ummie da niyar tambayar ta. Hannu tasa abakinta alamun karnace komai daga haka ta kama hannu na itada Mamy su nufi cikin jirgin dani, sosai nake son magana da Buhaisa akan sanin ina kuma za'a kaini, bayan nasan Suraj a Kaduna zai zauna amma ana shirin barin garin dani, zuciya tace ta tsinke tuno Suraj da nayi, Yayinda su Buhaisa suma su take mana baya su biyo mu cikin jirgin.
Jirgin ya fara motsawa da ƙaramar ƙara. Gwaninta da kyau ya bayyana a tsarin komai – daga lafazin ma’aikata, zuwa ƙamshin sabbin kujeru. Amma a zuciya ta ba komai sai shiru mai nauyi, da tunanin da ke kewaya kamar hayakin jirgi.
Ina zauna a wajen taga dan anan Ummie ta zaunar dani, ina kallon fitilun titi da ke wucewa da sauri. Ina jin kamar duniya ce ke kaucewa daga gareni, ina barinta da tambayoyi da ba su da amsa.
Wani murmushi mai rauni ya leko a fuskata ba don farin ciki ba, sai don ƙoƙarin ƙarfafa kai. Ina tunanin
“inane inda za'a kaini kuma? Me yasa suke boyemin bazasu faɗa min ba? Kuma me yasa Suraj sam bai nemeni ba?"
Wadannan tambayoyin sune narke acikin zuciya ta da sam banda me amsa min su saboda tun jiya na fahimci akwai abinda ake boyemin, ga Ummie taƙi bani damar yimata tambaya, gashi ba wayana a hannu na, gashi basu Buhaisa a kusa dani,
A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da kwantar da kaina a kafadar Ummie ina lumshe ido.
___________★
*Abuja 🤍*
Jirgin ya iso tashar Idu da ƙarfe Bakwai 7:00pm na dare. Fitilun tashar suna haskakawa cikin daɗin gani, amma a idanuna, duhu ne kawai da sabuwar rayuwar da ke gabana.
A wajen fitowar fasinjoji, manyan motoci ne na alfarma jere masu mutukar kyau da ɗaukar ido. Wata fitinanniyar mota ce ƙirar Mercedes Maybach mai sheƙi. Fara tas tasha flowers. Kamar a Kaduna yanzu ma motar ɗaukar Amarya ce a tsakiya datai mugun haɗu wa. fuskata dake rufe cikin alkyabar datake shara-shara tanan nake ganin komai yayin da tuni zuciya ta ta sake tsinkewa gabana ya cigaba da faɗuwa a kuma dai-dai lokacin su Ummie da wata mata da bansan taba suka sakani a cikin wannan farar motar Mercedes Maybach cikin nutsuwa.
Yayinda sauran motocin kowa ya debi iya adadin mutanen da zai iya, a jere manyan motocin suka bar tashar Idu motar amarya a tsakiya gaba da baya jami'an tsaro ne. Inda kai tsaye a bakin wani irin gida gidan daya amasa sunan shi gida, haka kuma gidan da kyawunsa yadarama dukka gidajen, duk dacewa gidajen naka mancece niya da juna, amah duk yafisu tsaruwa,
Idanu nasake warewa tabbatar da cewar, glass din danaga yana budewa get ne ko akasin haka,
Batare da nagama tinanin ba,
Motocin suka kutsa kansu ciki,
Wanda hakan ya tabbatar min da cewa get ne.
*WELL COME TO THE AA SARAKI HOUSE*
Shine ke rubuce asaman makeken gidan "Dammm" gabana ya bada sautin dan wllh Billy ji nayi kaina yana neman kwance wa dan gaba ɗaya duk wata nutsuwa da kuzarin dana dan samu sun gudu, ba abinda zuciya keyi sai gudu acikin girjina. Wai meke shirin faruwa dani ne Ni Safiyyah?" Wannan kalma dana furta a hankali da sam banma san ta fito fili bace ta dawo da Ummie da Mama Hadiza daga sumar wuccin gadin dasu tafi na ganin wannan fitinannen gidan. A hankali ummie ta sake damke hannu na cikin nata tare da furta "Ki nutsu Safiyyah". Shiru nayi ba tare dana ce komai ba sai bin komai dana keyi da ido.
Ajere motocin duk suka shiga makeken compound din da Sam bai da iyaka ga Mai kallo, kowace ta tsaya a muhalin da akeson ganinta,
*AA SARAKI HOUSE*
A tsaye AA SARAKI FAMILY suke suna jiran isowar amarya wacce tunda ta ƙaraso cikin garin Abujan suka sani, Inda duk da ɗunbin mutanen nan dake cike da SARAKI house da wanda sukayo ma amarya rakiya hakan bai hana Granny da ke fama da tsufanta ba fitowa tarbar amarya ita da su Mahmah. An fara kaita sashen Ammei, Ammei ta rungume abarta tana share hawayen farin ciki, wai yau itace rungume da matar ɗan ta guda ɗaya tilo ALLAH ya cika mata burinta. Yayin da Ammah ta rungume Safiyyah daga baya kuma ta koma kan Ummie mamaki kwance akan fuskar ta. Bayan addu'oi aka fito da ita aka nufi sashen Granny da ita Anan kam dai cike da bariki Mummy ta tarbesu, addu'oi duk da basu kai ciki ba. Yayinda Granny ta rungume Safiyyah tsam tana samata albarka, Daga nan aka dawo da Safiyyah sashenta. Bayan an sakata tayi alwala aka shiga da ita ciki bakinta da addu'a. Anan bedroom ɗin ƙasa suka ajiyeta bisa umarnin Ummie
Gaba ɗaya dangin Mom sun gama sumewa a tsaye. Karo na farko na rayuwarsu suka fahimci ashe inda Safiyyah ta shigo ba ƙaramin guri bans, dan wlhy a dukiya irin ta wannan gidan da ginin kawai suka gani Suraj d'in da suke hauka akan su bakomai bane. Dan wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa.
Su Buhaisa kam sumar wuccin gadi suyi daga baya kuma su cigaba da kallon gidan tare da yabawa. Buhaisa mayyar hoto itada su Yasmeen ai tuni su fara aikin nasu.
Sosai ahalin Safiyyah sunji daɗin tarbar da akai musu. Tun daga kan shimfiɗar fuska har zuwa ta wajen zama da abinci dana sha komai