Showing 57001 words to 60000 words out of 84595 words

Chapter 20 - RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

15 Nov 2025

1141

dan wallahi komai ya kusa kwace mana ke ya kike gani da an bari anyi binciken nan dafa shikenan kashin mu ya bushe?"
"Humm bazaka gane bane wallahi Ni kadai nasan irin tashin hankalin dana shiga lokacin ga wannan rigimam miyar tsohuwar da anbiye ta ta a da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, amma dai mun tsallake sai mu sake shiri".

"Toh yanzu ya kike gani za'a yi?"

Dariyar mugun ta tasaki tare da cewa. "Yaron ya cika taurin kaine inaga kawai mu tafi plant B shima in bai samu ba sai mu tafi plant C Dan shi dai da wuya ya tsallake ko waye shi kuwa".

Shima dariyar yayi yana kallon ta tare da cewa. "Daɗi na dake kema muguwa ce kanki akwai kawo wuta, dan haka plant B din kawai za'a tafi kinga kafin ya bar ƙasar nan kawai sai a gama komai idan kuma bai samu ba sai a tafi plant C din kwai".
Dariya su sake saki a tare, tare da tafawa kamar ba mace da namiji ba sannan su cigaba da tsara shirin su.


✨🤍✨🤍✨


..........Gaba ɗaya idanunsa da ƙyaƙyƙyawar fuskarsa na kan screen ɗin laptop ɗin cinyarsa da takardun hannunsa. Fuskar nan ciɗin-ciɗin babu alamar sassauci kamar wanda ke cikin ɓacin rai. saman Centre table ɗin daya ajiye ƙafafunsa masu tsananin tsafta da haske. Gashi cas babu wani girma sosai irin na maza. Dan wata macen ma sai ta fishi girman ƙafa. Youseef ne ya shigo bakin sa ɗauke da sallama inda kai tsaye kujera ya samu ya zauna tare da cewa.

"Barka da hutawa boss".

Kai ya jin jina ya cigaba da aikin da yake a laptop saida ya dau kusan 20 minutes kana ya maida hankalin sa kan Youseef tare da cewa. "Friday zamu je Kaduna". Shine kawai abin da ya faɗa ya maida hankalin sa kan laptop. Inda shikam Youseef ya ɗago yana kallon boss din nashi kuma Aminin sa kana yace.
"Amma boss me zamuje yi Kaduna?"

"Oooh kasan bani da dangi acan koh".
Majeed ya faɗa yana zuba ma Youseef hararar wasa. Inda shiku ma Youseef ya saki murmushi tare da cewa.
"Allah sarki Ammah zatai baki kenan ranar Friday". Ya faɗa yana ɗan kasa da kai, Majeed ne yace.
"Okay kaida mekake nufi"
Yar dariya yayi tare da cewa.
"Na ɗauka....s".
Hararar da Majeed ya wasa masa ce yasa shi kasa ƙarasa wa yana dariya. Cikin silent voice ɗinsa yace .
"Youseef Allah ka fita idona ".
Murmushi kawai yayi tare da cewa.
"Boss fatan ka duba bayanan akan binciken da kasa nama dan tuni na turama?"

"Yes"

"Toh amma boss nayi mamaki da ace bikin ta yazo".

"Ba abun mamaki bane ai hakan"

"Toh Allah ya zaɓa abinda yake alkairi".
Da "ameen" Ya amsa a saman labba inda Youseef ya cigaba da faɗin. "Boss yaufa kana da meeting 11:00pm dan tun 5:30pm suke a cikin garin Abuja".

"Na sani kaje kuyi kawai dan yau banjin zani ko ina".
Cikin mamaki Youseef ke kallon sa kana yace.
"Amma boss kasan fa muhimmanci baƙin nan dan zasufi jin daɗi idan kaine".
"Kawai kuyi dasu ɗin dan bani a yanayin haɗu wa da kowa yau".

"Okay Allah yah karoma lpy da kwanciyar hankali, nabar ka lpy".
Cewar Youseef dan yasan tunda yace yaje ɗin tofa baza Shiba, dan dagani ran sa ma a ɓace yake amma ya dangan ta ɓacin ran a akan waccan dalilin.



✨💞✨💞✨


............"amma Alhaji ya kamata fa akan wannan matsalar dake tsakanin ka da Majeed ta wuce yanzu dan wallahi abun na damu na, ka duba fa shakuwa da kaunar dake tsakanin ku a da amma yanzu zama guri ɗaya ma ku gaisa ya gagara balle aje ga hira".

"Hajiya bilkeesu kenan baikai ga yadda nikeji ba a zuciya ta ba, nayi iya yina amma abu yaci tura da kamar yayi sauk'i amma yanzu gaba ma kawai abin yake ƙarawa. Kuma yana shan maganin?"

"Toh a cewar sa dai yana sha amma lokacin daya dawo nan da zama gaskiya kamar ba'a amfani dashi, Tom amma ni kafin ya bar part din nan nasa yayi amfani dashi sosai duk da dai sai nayi fama dashi yake sha".

"Tom Allah ya kawo sauki dama akwai maganar dana ke so muyi dake akan Majeed ɗin".
" toh Alhaji ina sauraren ka".

"Daman akan batun nan ne".

"Màsha Allah an samu nasara?"

"A'a kam dan anrigamu sai dai hakuri".

Cike da damu Ammei ke kallon dady kana cikin sanyin muryata Mara hayani ta fara maganar dani kaina banjin me suke cewa, dan haka ne tattara alkalami ✍️📝na nace bari mu leƙa Kaduna muga halinda mom suke ciki.





_________________

*Kaduna✨*


A ɓangare mom fa abu gaba ɗaya ya cabe mata dan dawowo gida tayi ta tarar ba Safiyyah inda anty Waleeda ke sheda mata ta tafi gidan ummi halima, anan fa hankalin mom ya tashi dan taga alama wannan abun fa ba fasa shi za ayi ba. Gashi gaba ɗaya ta gaza gane kan ɗiyar tata ga nakan kwari yace abu bazai tabbata ba amma gashi yana niyar tabbata dan haka bataga ta zama ba.

Zaune take ta zabbaga uban tagumi inda parlour yake kaca-kaca kamar anyi dambe a cikin sa, gefe guda kwofu nan tea din dasu Shane baje a gurin amma har yanzu ba a kwashe suba sai kudaje ne keta binsu. Tana wannan tunanin har Umman ta tashigo bata sani ba dan ba kowa a gidan sai ita kaɗai, anty Waleeda kuwa tunda ta karya ta fice a gidan bata dawo ba, shiko Abba ko karyawa baiyi ba ya fice wai yana da aiki a office.
Saida umman ta ta gama ƙare mata kallo kana tashigo har ta zauna a kujerar kusa da ita bata sani ba saida ta kai hannu ta taɓa ta aikuwa firgigit ta d'ago tana kallon mahaifiyar tata.

"Ikon Allah ni A'i tunanin me kike yi ne haka Zuwaira tun ɗazu sai sallama nake amma hankalin ki bashi a jikin ki".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da kallon mahaifiyar tata fuska ɗauke da damuwa tace. "Umma wallahi gaba ɗaya na kasa samun sukuni akan maganar auren yarinyar nan ki duba fa umma har yanzu shiru, bayan kuma anyi aikin nan amma abu yaci tura ga Waleeda kullum cikin min maganar take".

Ajiyar zuciya umma ta sauke kana tace.
"Daɗi na dake rashin hakuri ai tunda kiga na kwantar da hankali na kema ya kamata ace naki ya kwanta, dan nakan kwari baya magana biyu ballema irin kuɗin da muke zuba mishi ai dolle asamu biyan buƙata, dan haka ki kwantar da hankalin ki aure baza ayiba inko anyi toh bazamu barta ta zauna lafiya ba".

A hankali mom ta sauke ajiyar zuciya fuskar ta ɗauke da murmushi tace. "Shiyasa nake yinki umma nifa inson samune aure ne bana so naga tayi, nafiso ta ƙare a meyi min bata dan ko kaɗan bana so naga jinin Amina yana hutawa.
Yanzu umma Bama wannan ba intai auren wazai ringa mana gyaran gida, da girki, dan itafa Waleeda ba iyawa zatai ba shiyasa na fison ko auren zatai akaita gidan da yake da maiko".

Saida umma tayi murmushi kana tace "toh baga su Safwan ba in suyi aure matan ba sai suyi miki bauta ba".

"Hakane kuma fa umma Waleeda inta dawo zan turo miki ita sai ake can ɗin da ita". ta faɗa tana dariya.

Da haka su cigaba da tattaunawa itada mahaifiyar tata inda kisan ba uwarta ba anayi ana dariya.




🤍💞🤍💞🤍💞


Shirye-shirye biki ake ba kama hannun yaro daga ko wanne ɓangare, musamman ma daga family ango dan shine auren dasu mumy za suyi na farko dan daga Suraj sai Mennat. Dan haka ita kanta Mennat ba'a barta a baya ba dan ta shirya ma bikin Yayan nata sosai dan ma ta wani ɓangaren tana gun amarya.
Haka ɓangaren Ummi ma shirin aurar da ɗiyar yar uwar tata take, dan duk wani abu daya kamata uwa tayi a bikin yar ta toh Ummi tayi shi saidai fatan Allah ya kaimu ranar lpy.
Batun aiki kuwa tun ranar data zo gidan Ummi tai sallama da gurin aiki sai kuma bayan biki angama shan amarci.
Yayin da tuni mai gyaran jiki ta fara nata aikin tun ranar datazo.
Wani irin gyaran jiki mai ban mamaki luba ta fara min ɗan gaske. Tunda na shiga bedroom din Ummi ko falo an haramta min fita, hakama wayata an kwace gyara kawai nake sha ciki da waje, ni kaina abin har tsoro yake bani. Abubuwan da ake danna min ina sha kuwa kamar zasu sanyani amai nake ji. Shiyyasa dana faki ido sai na zubar. Ga wani irin mahaukacin ƙamshi da ko yaya na motsa sai kaji waje ya buɗe. Fatata yayi wani irin ƙyau na tashin hankali. Sau ɗaya Luba ke bani damar yin waya da RK a rana. Shima na minti goma kawai. Duk wani abu na bashi damar yaje su tattauna da su Buhaisa, ga Isha, ga Nusaiba yarinyar uncle ɗin su Buhaisa, harma da Mennat ƙanwar sa.

_______★


A ɓangaren ango wato MD shiri yake dan kai tsaye zance yafi amarya ƙaguwa, dan gurin aiki tuni ya mishi ƙaura kace shine amaryar daka kalleshi ko da yaushe yana cikin farin ciki. Komai ya kammala saidai jiran ranar kawai.
inda yaune gidan su ango ke shirin miƙa lefe gidan su amarya.

Kasancewar lefen gidan Abba za'a kaishi dan haka Ummi tuni tayi shirin tafiya gidan dan ita rabon ta da gidan ma ta manta. Tsaf ta shirya dan tuni tasa masu aiki da Buhaisa harma da ita kanta sun shiga kitchen domin shirya ma yan kawo lefe a abinci, dan tasan indai ta Mom Za'abi tofa za'aji kunya dan haka komai tasa an fita dashi ansa a motar Yah Saif danshi zai kaita.

Daga ita sai Maman Isha suka tafi dan tasan dole za'a samu wasu mutumen daga dangin Abba zasu zo, dan Aminiyar tace baji ba gani, sai Buhaisa data maƙale saita bita dan ita anty Hajara sai satin biki ya shiga zata zo. dan haka daga Safiyyah sai Luba dake mata gyaran jiki sai kuma masu aiki aka bari a gidan yayin da su kuma Yah Saif ya tafi kaisu.
Koda suje gidan ilai kuwa yadda Ummi tai tsammani ba kowa acikin sa sai Mom da anty Waleeda sai wata ƙanwar mom ɗin da mahaifiyar ta dan da alamu zuwa gidan yar Tata baya mata wuya, tun kafin agama shigo da kayan dasu zo dashi saiga dangin Abba nan suma sunzo a mota, batare da Ummi ta tsayaba kai tsaye suyi sallama acikin parlour, dan gaba ɗaya angama shigar musu da kayan dasu zo dashi.

baki mom su saki suna kallon yaran dake shiga da kayan cikin parlour kafin Mom ta jefoma yaron tambayar. "Wannan kayan daga ina".
Amsa yaron ya bata dacewa. "Wata Hajiya ce tace a shigo dasu".
Ba tare da ya gama basu amsa ba su Ummi su shigo bakin su ɗauke da sallama.

Wani kallo aka shigarma juna tsakanin Mom da Ummi batare da sun amsa musu sallamar da suyi ba, Ummi ce tai janye idonta akanta tare da sakin wani miskilin murmushi tana ƙarasa wa cikin parlour su Buhaisa da Maman Isha biye da ita inda kai tsaye kujera su samu tare da karka ɗewa dan tayi datti ba lefi, su zauna kowa bakin sa ɗauke da bisimilah. Shirune ya ratsa parlour sai kuma kana nun tsaki dake tashi ƙasa-ƙasa daga ɓangaren su Mom yayin da ko daga ido su Ummi basuyi ba saima hankalin su dasu mayar kan waya sai Buhaisa dake bin parlourn da kallo dan a mutukar har mutse yake tako ina.
Zaman su ba daɗe wa saiga dangin Abba nan su Mama Hadiza da anty Maryam yarta dake aure acan kawo harma da matan su kawu Bala sun shigo.
Aikuwa tuni parlourn ya dauka aka fara gaishe-gaishe tsakanin dangin Abba dasu Ummi yayin da Mom ko ido bata daga ta kalle suba saida mahaifiyar ta ta zun gureta dan koba komai ai itama dangin tane.

Sai lokacin ta gaishe da dangin Abban koma ince dangin ta tunda auran zumunci ne tsakanin ta da Abban. Tunda kuma su gama gisawa ta tsuke bakinta tayi shiru batare da ko tayin ruwa tayi musu ba, anty Waleeda kuwa ko kallo basu isheta ba saima tashi da tayi tana harare-harare tare da taunar cungum ta shige bedroom din su.
Duk da kallo su bita yayin da Mama Hadiza ta kada baki tace.

"Oooh ni yar nan kace kema A'i nan kuka yo".
Saida ta tabe baki tare da cewa.
"Eh munzo taya ku amsar lefen yar tamu ne".
Itama Mama Hadiza saida tayi murmushi kana tace.
"Anko gode".
Daga hk bata sake cewa komai ba sai kan Ummi data koma tana tambayar ta.

"Wai ni mai babban suna bata nan ne nasan data nanan da tuni an cike mana gaba da kayan shaye-shaye dana ciye-ciye".
Murmushi Ummi tayi kana cikin girmama wa tace.
"Ai Safiyyah ta kwana biyu a gurina ko zata dawo sai biki ya rage kaɗan"

"A'a màsha Allah dama ta faɗa min lokacin dana ce Maryam zata mata ɗan gyaran jiki tace ai tana gidan kima. Toh Allah Ubangiji ya saka miki da mafificin alkairi amma tabbas kinyi hallaci dama wannan shine zumunci ai".

Da "ameen" dukka suka amsa inka cire mom da komatsen ta da sai baki kawai suke tab'e wa.

"Au Niko nace Zuwaira fatan dai abincin ya kammala?, dan nasan bakin nan na gab da isowa".
Mama Hadiza ce ta kuma faɗa tana mai kafe mom da kallo. Cikin ya tsina mom tace.
"Mama wanda abincin kuma?.
Ta sake jefa ma mama Hadiza wata tambayar itama fuska haɗe take bata amsa da.
"Abinci mana na yan kawo kayan lefen Safiyyah koh shi Ibrahim ɗin bai faɗa miki bane".
Saida ta wani taɓe baki kana tace.
"A gaskiya ba'a faɗa min ba, dan haka ni yau koh girki banyi ba gari ma mu jika mu s....".
Tsawar da mama Hadiza ta daka mata ce tare da ɗaga mata yasa tayi shiru tare da cewa.

"Wato kedai Zawaira bazaki canza wannan baƙin halin naki ba?, aiko ɗin ki fitar da mijinki kunya kyasa y'ar taki da ƙanwar taki su tayaki ayi girki nan amma tsabar is...".

Ummi ce ta katse ta ta hanyar nuna mata abincin dasu zo dasu harma da drinks da duk wani abu daya kamata aba baƙi na fita kunya. Aifa nan mama Hadiza harma da matan su kawu Bala su shiga da mata albarka ita da zuri'arta, inda mom rai bace ta tashi fuuu tashiga daki zuciyar ta na kuna inda ƙanwar tata yabi bayan ta. Duk abin nan da ake ko sau ɗaya umma mahaifiyar mom bata ce ta tafi a sauke ba, Dan jitake kamar ta tashi ta bar gidan toh amma ta riga tace sunzo amsar akwati ne. Dole ta cigaba da zama badin taso ba...........

To lefen dai Safiyyah ya iso gidan Malam Ibrahim. Gida fa cike da ƴan gulma musamman ta fannin mom dan harda kawayen ta kace bikin Anty Waleeda dan wannan dai badin Allah suzo ba, anzo ne ayi sa ido. ga akwatina jerarru na kece raini da ƴar gata kawai ake kaima set biyu shaƙe da kayan alfarma na gani na faɗa. Babu wanda zaice lefen nan bai birgesa ba. Sai dai anga tsagwaron hassada daga Mom dan ta kasa haɗiye komai. Harda zage-zagenta wai ai saurayin Anty Waleeda ne na kwace da asiri. Kuma ba kowa ke kawo min asirin ba sai Ummi. Ba tare da koh daga kai Ummi tayi ba ta kalleta saima Buhaisa ce datai niyyar magana Ummi ta dakatar da ita ta hanyar harara. Ai kuwa ta sami amsa dai-dai da ita dan Mama Hadiza da matan kawu Bala saida suyi mata tatas.........

kowa na shirin kama gaban sa dan Mama Hadiza cewa tayi kawai Ummi su ɗauke lefen ta tafi dashi can gidan ta, dan yanzu itace ai mahaifiyar tata. Batare da Ummi tayi mata musu ba aka ɗauke lefen daga gidan sun wuce da shi can gidanta. Acewarsu barinsa gidan Abba bazai yiwu ba su Mom zasu iya salwantarwa saboda basu da isashen mutunci. Ashe ko hasashen su Mama Hadiza yay dai-dai. Dan su Mom sun shirya mummunan ƙudiri kuwa akan lefen nan aka ɓata musu shiri............✍️








*Typing📲*







_Follow my WhatsApp channel_ 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VauF15RLNSZvrEQHsL0


_Follow my WhatsApp group_👇


https://chat.whatsapp.com/EKFnHpoI54t1MvodB5HgYB









*🌹 RAYUWATA 🌹*

_CREATED AND WRITING BY_

*Bilkeesu Sa'eed Aliyu*
💞*Billy pinky*💞










*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

*T.M.W.A.✍️*






*Amanar taurarin marubuta writer's....✍️*



*TEAM HAZIKAI BIYAR✨*













Page 3️⃣8️⃣➡️3️⃣9️⃣



..................Su Ummi sun dawo lpy da kaya niki-niki dan mota biyu ma su kayi, inda ni abin ma yaɗan so ya bani mamaki amma ba abun mamaki bane sanin halin mom. Na tarbe su cike da fara'a inda kai tsaye Ummi tasa su Rabi shiga mata da kayan can parlourn Abba ita kuma ta haura sama domin hutawa.
Buhaisa ke bani labarin duk yadda akayi naji baƙin ciki kwarai da gaske da abun da Mom din takeyi, koba komai aini ɗin a matsayin ɗiyar ta nake amma bakomai Allah ya ganar da ita inme gane wace.
Ina shirin magana waya ta tafara haske alamun shigowar kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login