Showing 48001 words to 51000 words out of 84595 words

Chapter 17 - RAYUWATA BOOK COMPELET BY BILLY PINKY.txt

15 Nov 2025

1146

mai karfi.

Kasancewar darene yasa a gidan ba wanda ya san Majeed na asibiti, sai ma'aikatan gidan dake kaikawone suga sanda a fito dashi cikin tashin hankali suka nufi part din granny dan sun san gaba ɗaya family yanzu suna can. Kuma ganin ba ko ɗaya acikin sune ya tabbatar musu da ba wanda ya sani, dan uncle Sulaiman ma bai daɗe da shiga cikin ba.

Aikuwa shigar ɗaya daga cikin ma'aikatan cikin parlour tare da sallamar sace ta dawo dasu daga firar da suke, hankali su mayar kan sa inda Mummy tayi ƙofa ta mike cikin daka tsawa tace. "Me haka kai kuma zaka faɗo ma mutane daki bayan hakan dokace?". Cikin in ina yace dama.. dama.. Alhaji.., tsawar data daka masace tasa shi kasa ƙarasa maganar jiki na rawa dan tsawar ta mutukar gigita sa. kuma kowa yasan halinta dan gaba ɗaya ma'aikatan gidan tsaron ta suke harma daga wasu daga cikin gidan kasan cewar yadda take shinfiɗa mulki a gidan.

Hannun data nuna masa ne tare da zaro masa ido alamun ya fice yasa shi dawowa daga tunanin daya tafi. Har yana yin tuntube gurin juyawa zai fita, Dady ya kira sa tare da tambayar sa meke faruwa, granny kuwa harara kawai takai ma Mommy suna maida hankalinsu kansa baki ya buɗe zaiyi magana kenan wayar dady ta fara ringing ganin Youseef ne yasa yasake tabbatar daba lafiya ba, hannu ya daga masa yana ɗaukar wayar. Batare da sun gaisa ba ya faɗa mishi suna cikin hospital Majeed ba lafiya. "Innalilahi wa'inna ilahiri raji'un" kawai dady ke maimaita wa, inda gabaki ɗaya family wasu daga ciki su shiga damu suna kallon dady dan son jin meke faru haka. Cikin tashin hankali dady ke tambayar Youseef meke damun Majeed ɗin dan yasan shine kawai dalilin dake sa Majeed ya kwanta a asibiti amma yanzu meya same sa. Daga can ɓangaren Youseef cewa yayi. "Gaskiya dady jikin ba daɗi dan har yanzu doctors na ciki basu fito b..". Dady baima Bari ya gama jin maganar Youseef ba ya fara ƙoƙarin fita dan tuni dama ya tashi a tsayema yake waya da Youseef ɗin.

"Haba bukar ina kuma zaka kuma meye faru ka barmu cikin kokwanto kuma kana shirin ficewa ba tare da kace komai ba?." Maganar da granny tayice tasa dady juyowa. "dan Allah ku gafarceni Hajiya wallahi tsananin tashin hankali ne yasa na manta ya cancanta kusani albashi Mahaifiyarsa. Majeed ne yanzu Youseef ya kirani wai suna asibiti bashi da lafiya". Yana gama maganar yabar ɗakin yayinda su uncle Abdullah su rufa masa baya.

Granny kuwa salati tayi ta sanar da ubangiji tare da cewa. "Nashiga uku ni Maryamu meke faruwa da Abdulmajidu har da kaiwa kwanciya a asibiti Ni Yar nan jikan nawa guda a'a wallahi ba Lafiya". Granny ke maganar cikin tashin hankali tana nufar kofa danko takan hijabi batabi ba ta fice.

Adddah ce ta matso kusa da Ammei data kasa cewa komai sai binsu take da ido. "Kinga Aminiya tashi muje muga ya jikin nasa ba zama zamuyi ba". Ta faɗa tana kama hannun Ammei ba musu tatashi tasaka hijjab suka fice, to dama Yan matan gidan tuni sun fice dan Zaituna da Auta dady na fita subi bayan sa cikin tashin hankali. Suma sauran sun tafi sai mama ce da Umma amarya suka bi bayan su Adddah.

...............A ɓangaren su Majeed kuwa tunda doctor's su shiga dashi suke ƙoƙarin ceto numfashin sa amah Abu ya faskara da kyar da temakon Allah suyi nasarar ceto numfashin inda kuma suka koma kan gubar dan ba ƙaramar poison ayi amfani ba gurin cutar dashi. Dan badin an fara masa temakon gaggawa ba kuma asibitin acikin gidan yake da komai zai iya faruwa.

Yayinda su dady hankalin su yake a tashe dan basu san halin da yake ciki ba, kowa na familyn ka gani kasan bashi cikin walwala dan ba'a gane cikin kowa acikin su. Yayin da granny ta daga musu hankali daga baya ma komawa tayi tana zagaye bakin kofar, ita kuwa Ammei na zaune kamilar mace kenan mai kawaici da hakuri bazaka taɓa ganin damu a fuskar ta ba saidai ƙasan zuciyar ta addu'a kawai take ma yaron nata dan tasan shi kuma Allah ya haɗa shi da jarabawoyi iri-iri acikin wannan a hali, sai dai kawai addu'a. Su Zaituna kuwa daka gansu kasan suna cikin damuwa alabashi Auta da Zaituna dan damuwar su tafi fitowa fili sai Fennah. Su Youseef kuwa da sauran yaransa suna zaune jigum-jigum kowa fuska ba walwala.

...........har dare ya tsala gidan gaba ɗaya ya dau shiru sai hasken daya haske gaba ɗaya gidan dan idan kana cikin sa bama za kasan dare yayi ba. Amma har lokacin shiri kake ji doctor's basu ce komai ba idan wannan ya fito yana share gumi anan granny dasu dady zaauje suna tambayar ya jikin nasa amma amsar ɗaya ce su cigaba da addu'a.

Umma amarya ce cikin ranta ke mitar gajiya da zaman gun datayi tashi tayi cikin daure fuska tace. "Toh Ni zan danje ciki Allah ya bashi lafiya". Yayin da uncle Sulaiman ke aika mata da wata harara tare da nuna mata ta zauna, sarai ta fahimci me yake nufi amma ta basar tana kama hanyar barin hospital din.
"Ke ke ina zaki haka?." Granny tayi maganar tana bin Umma amarya da wani mugun kallo, cikin jin takaicin wannan tsohuwar ta juyo fuska haɗe tace. "Hajiya zan ɗan shiga ciki ne Allah ya bashi lafiya". Ta ƙarasa maganar tana gafe da kanta dan tasan halin wannan kinibabbayir tsohuwar. Cikin zazzaro ido granny tafara managa. "Eyye wato ciki zaki shiga ki kwanta bakiji kunya ba ke? Jikana na nan rai a hannun Allah amma kina faɗin ciki zaki ki kwanta, kina ganin kowa na gidan anan dan nasan har masu aiki tunda su san bashi da lafiya suma bazasu runtsa ba dan sun san mahimmanci sa amma saike toh bari kiji tun wuri ki koma ki zauna dan muna nan daku har gobe idan dame niyar tashi bisimilah". Tana gama maganar takoma bakin kofa tana zagaye.

Cikin jin takaicin granny Umma amarya ta bita da wani mugun kallo ƙasa-ƙasa tana tura baki gaba haka ta nemi guri ta zauna gefe guda tana hare-hare. Murmushi kawai Mama tayi tana girgiza kai, shiko Uncle Sulaiman harara kawai yake aika mata dan yaji daɗi da granny ta hana duk shi bataji maganar saba.

A hankali doctors suke fitowa da Majeed dake kwance a gadon daukar marasa lafiya kai tsaye wani ɗaki na musamman suka nufa dashi yayin da granny tabi bayan su. Dr Fadil ne ya dakatar da ita kana su shiga dashi granny har tayi niyar yin tujara sai kuma tai ƙofa taja tunga a bakin kofa. Basu daɗe ba su fito dan sai share gumi suke su dady ne su nufeshi suna tambayar Ya jikin nasa, saida Dr Fadil ya nisa kana ya fara magana.

"A gaskiya Alhaji jiki da sauki amma fa da matsala". cikin tashin hankali granny tace. "meye matsalar meya sami jikana"
"Granny ki kwantar da hankalin a yanzu haka jikin nasa da sauki kuma mun shawo kan matsalar".
"Humm" granny ta sauke ajiyar zuciya kana tace. "Kaga fito ka faɗa mana meye matsalar meye same sa".

"Maganar gaskiya abun ya bani mamaki dan kuwa poison a samishi a wani abu yasha kuma yana da mutukar illa ajikin ɗan Adam dan zai ɗauke shi tsawon shekara yana kwance ko ɗan yatsa bazai iya ɗaga waba daganan kuma sai mutuwa dan kwata-kwata bashi da makari. Saboda haɗarin sa gaba ɗaya a hana saida shi a ko ina dan duk wanda agani dashi hukunci yake dauka mai tsanan...

"Nashiga uku na ni Maryamu" granny dake yashe a ƙasa ce ke maganar jin ana niyar kashe mata jika. "Yanzu wacce Yar iskar ce ke niyar kashe min jika? oo ni Yar nan me Abdulmajidu ya muku ne kuke niyar kashe min jika? kun haɗa shi da mahaifinsa amma hakan bai muku ba sai kun rabashi da duniyar wayyo Allah na bukar kamani kamani naje naga ɗan nan karsu ƙara sa shi". Ta ƙara sa maganar tana fashewa da kuka, shikuwa dady tsabar maganar ta dake sa ya kasa koda motsi a gurin Ammei dai nacan bata taso ba amma duk abinda ake cewa tana ji dan bata da tacewa saidai tai ta mishi addu'a dan wannan familyn nasu sai addu'a kawai.

Uncle Abdullah ne yace. "yanzu doctor kana nufin wannan gubar mai hatsari aka sama My son kuma a cikin gidan nan".
"Nima shine abin tambayar taya za'a sami wannan gubar a cikin gidan nan". Cewar Uncle Sulaiman yana kallon Dr Fadil, jinjina kai Dr yayi kana yace. "Toh wannan ne kuma ban sani ba amma zanso naji meyaci na ƙarshe kuma koh zan iya samun shi domin nayi goji akan sa nagani".

Zaituna dake shirinyin magana Granny dake kuka ta rigata, "maganar gaskiya Abdulmajidu madara yasha kuma madarar daga gurin na ta fito, dan tunda ya kirani nasan yace yana bukatar madara nasan ba abinda yasha kuma daga ita baya shan komai. Haka zalika madarar mai tsafta ce". Takai ƙarshe tana sake fashewa da kukan dayafi nada.

Tunda afara maganar har a gama acikin su Addah ba wanda baiyi jimamin hakan ba. amma sai dai mutum ɗaya dana lura tunda akayi maganar binciken akan madarar fuskar ta tacanja dan gaba ɗaya ta maida hankali akan wayar ta, tana danna wa kasan cewar dokar granny taba wanda zai fita agun.
Gefe kadan ta matsa tana waya ga dukkan alamu da mai aiki take waya cikin bada ummarni take maganar.
"Kinyi abinda nasaki". shiru tayi tana sauraren abinda ake faɗa, daga can ɓangaren ta ce. "Ranki ya daɗe komai done dan suna fita dashi na ɗauke komai".
"Okay". Kawai tace tana kashe wayar tare da sakin wani murmushi kana ta koma inda ta taso.
(Niko nace kin manta abu ɗaya akwai CCTV camera a part din 🤣) yayin da su Uncle Sulaiman da su Youseef su nufi part din Majeed domin ɗakko madarar da ace yasha domin ayi bin cike akan ta.

Koda suje an duba sama da ƙasa ba'a ga madara ba kuma dai doctor Fadil yace gubar bata daɗe wa ajikin mutum take fara aiki dan bata ɗaukar 10 minutes bare ace tun a waje ya sha, har sun fito zasu wuce Youseef da tun ɗazu yake ta waige-waige idonsa ya sauka akan mug din daya faɗi ƙasan table ɗin dake tsakan kanin kujerar daya zauna.
Tsaidasu yayi kana ya tsuguna ya dauko duk ga madarar nan ta zuɓe da alamu da'a zo ɗaukar wacan ba'a lura da itaba, "yauwa kawo wannan ɗin zaiyi bari a gwada". Cewar doctor Fadil ajiyar zuciya su sauke a tare kana su fice a part din su nufi hospital.




*Kaduna ✨*

..............Yauma kamar kullum tun kafin asuba na tashi duk wani aiki danake na gama shi kafin a kira sallah bayan nayi sallah tare da tilawar Alqur'ani. Tsaf na shirya cikin bakar abaya mai sulɓi an mata ado da fararen duwatsu ɗan kwalin abayar nasa nayi rolling dashi na fito tsaf kamar balarabiya. Yadda abaya ta ta kasance baka haka takalmin dake kafata ya kasance black mai dan tudu. haɗaɗɗiyar humura ta mai sanyin ƙamshin nakasa sai turaruka na masu sanyin ƙamshi irin na mata, kasan cewar niɗin ma'abociyar ƙamshi ce a ko ina akuma koda yaushe. Sai facemask black da eyeglasses white dana sa.
Dama tuni nayi breakfast dan haka bakar jakata na dauka sai phone na fice a ɗakin nabar anty Waleeda na sharar baccin ta dan banjin ko sallar asuba tayi.

Napep na tare mu wuce dan Yah Ansar ya koma shikuma Yah Safwan dama ba kwana yake a gidan ba. Koda muje kuɗin sa na ciro na bashi akuma dai-dai lokacin motar MD ta tsaya na ganshi amma sai nayi kamar ban gansa ba na nufi hanyar shiga ciki cikin takuna da mutane ke fassarawa da yanga wasu suce girman kai. Da haka har ya ƙaraso inda nake ya koma muna jerawa.
"Good morning" shine kawai abin dana furta batare dana kallesa ba.
"Uhmmm beb da shine zaki wuceni bazaki tsaya mu gaisa ba kohhh?".
Jin yadda yayi maganar ne yasani daga manyan idanu na da wasu kan kira da kamar na mage aikuwa su faɗa cikin nashi a hankali na janye nawa, kana nayi ƙasa da kaina ina sakin ƙaramin murmushi mai ɗan sauti ta cikin facemask ɗina kana nace.
"Humm bafa haka bane kawai daiii". Yanda ya tsireni da kallo ne yasa nayi shiru batare dana ƙarasa maganar ba.
"Kawai dai me?"
"Na tafine amma ai zamu gaisa".
"Uhmm beb kenan batin ma kona kiraki baki zuwa sai akan aiki".
"Sorry hakan ai shine dai-dai koh?". Na faɗa ina langabe kai tare da kallon shi, saida yayi murmushi kana yace. "Uhm hakane beb muje toh". Tafiya mu fara kaida ka ganmu kasan mun dace da juna, PA da tun farkon zuwa na tana kallon duk abinda ke faru tsakanina da MD haka take jin zuciyar ta kamar zata fito girjin ta dan a haukarta son shi take shikuma baima san tana yiba. Ta kusa da ita mu wuce muna cigaba da hirar mu irin ta masoya, dan saida ya rakani har office din mu kana ya wuce nashi cikin takunsa na nutsuwa, dan MD gayene Wanda ya san darajar gayu da iya daukar wanka gashi miskili shiyasa su PA su mace akansa. Tabbas idan nece muku bana son MD nayi karya dan inajin son shi acikin zuciya ta.

Sanda na shiga office ma acan na tarar da Isha inda members ɗin office din mu ketamin wasa wai gaba ɗaya na canja MD nidai murmushi kawai nayi ina kaiwa zaune a kujera marks ɗin fuskata na cire na aje gefe tare na sake gyara eyeglasses din idona na fara aiki a lap top dan akwai wani program da zamu gabatar yau. Isha kuwa fita tayi don kaima MD wasu takardu dan haka na fara aikina cikin nutsuwa.


_______ Mom____

"Mom yanzu fissabilah haka zamu cigaba da zuba ido akan yarinyar nan kince zaki gurin malam amma kinje yace baza ai bikin ba amma har yanzu shiru tunda gashi har anyi sa rana yanzu bikin fa kwata-kwata bai wuce 3 week's ba haba mom. in bazaki iyaba kubarni ni na dau mataki akan yar iska dan wallahi Suraj na wane ni kaɗai dan Ni akayi shi.

Mom data zuɓe anyi Waleeda da ido kamar wacce ta faɗa duniyar tunani ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa.
"Waleeda baki san irin ciwo da rad'ad'in dana ke jiba akan Auren yarinyar nan aini ba Suraj ba Auren ne kwata-kwata bana so tayi na fiso ta ƙare a gidan nan kawai dan tamin bauta, ai indai inada rai jinin Amina bazai taɓa samun Salama ba shima Ansar ɗin bakiga mu yake ma bauta ba komai na gidan nan ai yanzu akan sa yake ban da haka wallahi da tuni nasa an batar min dasu kamar yadda na ma uwar su Amina tana rayene ma kota mutu oho".

"Yauwa mom dan Allah duk yadda zakiyi kiyi akan auren nan, kuma kisan ma wata matsalar mom?"

"A'a saikin faɗa".

"MD mom zai kuwa amince dani dan rannan dana tare sa mom karkiga wulakanci da yayimin wallahi shiyasa zuciya ta ke rawa". Kamar zata fashe da kuka tayi maganar tana kallon mom.

"Kinji banza dama akace miki haka zamu barsa? Ke nida duk yadda zanyi ki mallake sa ai saina yi abin dama yasa kijini shiru da maganar akwai abinda nake shiryawa ne sai kuma Umma da tace na jirata banda haka ai da tuni an rufe babin".

"Wayo Allah mom gaskiya naji daɗi sosai momy nah shiyasa nake ƙara sonki".
"Kawo kunnen ki kiji shirin dana ke akan su" cewar mom ba musu anty Waleeda ta masa mom ta fara gwargwada mata maganar dani kaina banjin me suke cewa bale na fada muku.
Da haka 'ya da uwar suyita zance irin makircin da zasu kulla ma Safiyyah.



________🔷🔷🔹🔹🔷🔷______

Sultan ne yazo mu fita domin gabatar da program. Inda tuni ba kuwar mu tazo dan haka mu fara gabatar wa.

Ya ku matasa! Shin me ya sa ba sa faɗa muku sirrinkan nasararsu, sai ci dai su kawo muku Maudu’in Jayayya?

Ya ku Matasa! Shin me ya sa ba sa ware awa ɗaya ko a sati ne, su koya muku wani abu da zai kawo muku sauƙin rayuwar da mu ke ciki?

Ko kasuwanci kake ko dako, Ustaz ne kai ko Comrade, ɗalibin ilimi ne kai ko ɗan siyasa, ka ware lokacin nazari, bincike, karatu, da koyon sabon ilimi mai amfani na zamani da zai dace da ci gaban rayuwarka.

Ka daina yadda wasu suna kawo maka Skip to content.


Haqiqa abin alfahari ne da kuma birgewa yadda wasu zaqaquran matasanmu a soshiyal midiya suka dage ga ba da himma wurin canza tunanin jama’ar Arewa, musamman matasa ‘yan uwansu daga akasin wayewa zuwa ga wayewar a harsunan Turanci da Hausa. Alhamdulillahi kuma ana ganin alamun nasara a kan hakan. Wannan juyin juya hali ne na tunani, wanda kuma shi ne a’ala. Allah ya saka mu su da alheri.

Sai dai kuma an ce mutum tara yake, bai cika goma ba. A tare da wannan himma na wad’annan matasa namu, akwai buqatar sanya mu su linzami don jan hankalinsu game da sha’anin addini da kimiyya, cewa yayin da dukkan masu wayewa suke yabawa ci gaban da kimiyya ya kawo wa duniya, to kuma kada hakan ya sa a raina gudunmuwar da shi kuma addini ya kawo wanda ya ma fi na kimiyyar.

Ba wai don kawai Allah ya ce walal-aakhiratu khairun laka minal uulaa (lahira ta fi alheri a gare ka a kan duniya) ba, addini a qashin kansa, ba tare da la’akari da Musulunci ne ko Kiristanci ba, yana ba da gudunmuwa ga tarbiyyar d’an Adamu ta hanyar tsara masa rayuwa da d’ora masa dokokin mu’amala. Wannan tsari na rayuwa yana koyar da mutum ladubba, abin da ita kuma kimiyya ba ta ma sansu ba.

A warware, abin da nake qoqarin cewa shi ne, kimiyya na koya wa d’an Adamu yadda zai yi rayuwar jin dad’i ta hanyar qere-qere da zaqule-zaqulen bincike mai amfani da ma mara shi, addini kuma na koya masa yadda zai yi mu’amala da mutane ‘yan uwansa cikin tsari da rayuwa mai ban sha’awa.

Idan aka taqaita zance a hakan kawai, a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login