Showing 3001 words to 6000 words out of 61103 words
Chapter 2 - MARAINIYA CEโ (1 to End) Complete by Anty Ruky ( Maman Abduljalal.)-.txt
Na shiga uku, tace a hankali.
Wata ' yar siririyar dariya yai. Me ya shigar dake uku ? Ba komai tace tana kallon hannayenta dake cikin nashi.
Na zaci za a cemin Dan iska ne Ai. A a Ai kai mutumin kirkine ta fada tana Jan hannunta.
Sakinta yai tare da fadin muje.
Tana tafiya tana kunkuni. Ashe kadai San kanka Dan iskane ba se na fadaba tayi kwafa. Me kikace . cewa nayi mun godewa Allah da ya kawo mu Lfy.hmm, Allah ya soki yarinya. Tana bude kofar gidan tare da sallama ta hango Nenne bakin kofar daki tana tambaya ya har yanzu Mariya bata shigo ba.
Da gudu ta karasa, oyoyo Nenneres take cew tare da rungumeta. Oyoyo Mariya . sallamar Sadiq ta katse su. A ah sadeequ kai ka kawo su ne . eh nine tsohuwa. Ya fada tare da kokarin zama.
Marabanku lale. Nan ta shiga hidima dasu kawo wannan kawo wancan tana farin cikin ganin jikokinta bama kamar Mariya .
Anya Nenne kinyi kewata Kuwa. Niko nayi kewarki mariya . shine kuma kika kara kiba kumatu kamar biredi.kutt sukace gaba d'ayansu suna kallonta.
Ja' ira har yanzu baki daina halin ki Na zagin halittan mutane ba ko. Wlh bata daina ba Nenne cewar Hafsa ko makaranta muka je haka takeyi sai takarewa mutum kallo tayi dariya ta zageshi. Ko muma Na gidan ba barinmu tayiba.
Allah ya shiryeki Mariya amma zagin halitta ba kyau ba amfani. Nifa Nenne ba zagi nakeyi ba iyakan gaskiyata nake fada idan banga abu a jikin mutum ba ai baxan fada ba.Allah dai ya duba miki Mariya.
Kwana biyu sukayi suna zaga dangi duk inda suka je sai anyi mamakin girman Mariya a cikin shekaru biyu ta canja. Su Mariya har an fara kirgen dangi๐.
Na ta'ala yasha mamki da ya ganta Dan bai ganeta bama saida tayi mishi halin nata .da yake ya bude shago harda yi musu kyautar su sweets, chewing gum da biscuit.
Kwanansu uku suka kama shirin komawa amma banda Mariya Dan tace sai an kare Hutu. Kuma bata gaji da ganin nennenta ba.
Sau biyu tana zuwa gidan babanta ta yini .Shi kansa babanta yaji dadin ganin yadda ta kara girma ta kara kyau.
Matsalarta dayace yadda samarin kauyen sukai mata ca. Wasu har gurin mahaifinta suke zuwa a dole su Mariya ta isa aure๐.
Kullum sai anyi sallama da ita a kofar gida ko ayi ta aiko mata kyaututtuka.hakan ba karamin bata mata rai yake ba.
Shi yasa ma tana cika sati biyu ta matsawa Nenne zata koma.
Haba Mariya ba ke kikace sai an kare Hutu ba." Na fasa Nenne ni dai ki kirasu kice azo a d'aukeni. Kin gaji dani kenan. " A a nidai ana wuce ni karatu a islamiyyane. To shikenan xan kira kawunnaki.
Washegari taje ta salami babanta akan gobe xata koma.ya bata tsaraba mai yawa harda kudin kashewa. Tana isowa gida ta dankawa Nenne kudin me xatayi da kudin tunda komai tana samu.
Sadiq ya zo d'aukanta wannan karon ma haka sukai ta fadan a hanya sai yaga ranta ya baci sosae ya lallabeta su shirya.
A haka suka iso gida yayi horn gateman ya bude gate. Yana parking tana fitowa ta runtuma a guje aiko sadiq ya mata halinnashi capp ya capkota yana wani yamutsa fuska.
Mtseew, gaskiya ne akace ko me akayi da jaki sai yaci kara.
Kallonsa tayi rai a bace naji ni jaka ce sakeni Na wuce.jikinsa ya danyi sanyi , ba fa kece jakar ba ina nuf..... Nikam ka sakeni nace, Mariya gudunne banaso kinayi.
Naji tace tana faman kwace hannunta daga rikon da yayi mata. " Saketa man Sadiq wai me haka ne wai" su kaji an fada. Atare suka dago sai ganin Salim sukai yana ya harde hannayensa a kirji fuskarnan a daure kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa.
Sakon gaisuwa gareku masoya musamman fasaha grp members, mun gode kwarai da kaunarku garemu.
In dedication to Halima Auwal.
08161594233 for cmmt.
Luv u all.
๐๐MARIYA๐๐
16-20
By Anty Rukie (Mmn Abdul)
Suna hada ido ya galla mata harara, tayi saurin dauke kai tare da magana kasa kasa, " Daga isowar mtm har an fara mai kallon banza " .
Ke, magana kike , Salim ya tambaya cikin bacin rai. Eh um cewa nayi Ai gwara da Allah ya kawoka .kaga rashin mutuncin da wannan yake min . ta nuna Sadiq da yatsa .
Tayi saurin wucewa ciki.mai da kallansa yai kan Sadiq da yake fiffitar da kaya daga booth din mota. Kaga Sadiq , ka rage irin wannan wasa da kakewa yarinyarnan. Ko dan iskan da take ce maka ne yake maka dadi. Yarinya karama sai Dan banxan raini.
4 days later.
Hafsa, Mariya kuzo Ku raka ni karban dinki. Kuje ni baran je ba . me yasa ? Haka kawai. Kinga Hafsa yi sauri muje mu dawo kafin mami ta dawo.
Cewar fa' iza.
Suna fita ta zamo daga kan kujera ta zauna a kan tiles Na palon sbd tun tashin ta da safe takejin ta wata iri. Ciwon kai, Mara , ga kasala kuma ji take kamar zatayi amai.
Tana zaune taji abun sai karuwa yakeyi .babu Wanda ya sani gashi duk sun futa sun barta.
Salim ne ya shigo kamar an jefo shi.ganinta yasa yai sallama. Ciki ciki ta amsa. Bai kula ba yace , ke, ina Mami. Ta fita tace dashi.har ya juya zai fita ya sake juyowa ya kalleta, ganin tana hada zufa yace. Mariya ya dai. Ba komai tace . wani irin bakomai ga sai hada zufa kike kina cije baki.
Shiru ta masa. Matsowa yayi kusa da ita yace magana fa nake ko bakya jine. Kalonshi tayi ta dauke kai.ke tashi ki shiga daki. Yace ta tashi ko zai fahimci matsalarta.
Tayi kamar zata tashi sai kuma ta fasa.kallonta ya tsaya yi yana kuma nazarinta. Mika hannu yayi kamar zai dagata ya fasa." Yanxu mutum ya tabata ta fassarashi mtseew" yace a zuciyarsa.
Lura da yayi kamar bata cikin hayyacinta ne yasa shi dago ta gaba daya tayi staining wurin.
Amma ke yarinyar muguwace. Idan ba mugunta kina jin ciwo kin yi shiru bara kiyi magana ba har kika bari aka watse aka barki mtseew.
Kwantar dai yayi akan 3 seater ya fita tare da rufo mata kofar palourn .magani ya sayo yana isowa saiga su Hafsa . tare suka shiga suka sameta tana ta sheqa amai tana Kuma rike da ciki. Sannu suka Shiga yi mata , Hafsa Na rike da ita har ta gama. Fa' iza ce ta gyara wajen. Shi kuma ya kawo ruwa tare da ballo mata magunguna ya bata ta sha yana mmkin irin qarfin halinta.
Ku shiga da ita ciki ta kwanta abinda yace kenan yana mikama Hafsa ledar hannunsa.
Maganine a ciki sai kuma always.
Bayan kwana uku Hafsa ma ta tashi da nata .kuka take tana birgima take tana kuka babu Wanda bai San halin da ta shiga ba a gidan saida aka kaita asibiti akai mata allurai.
Bayan taji zaukine suna hade ana hira .Hafsa sai zuba surutu take kamar ba ita ba. Mami tace jita Dan Allah kamar ba ita ta cika mana kunne dazuba
Salim ne yayi carap yace Ai gwara ita umma wata kam so tayi ta kashe kanta Dan mugun hali .ba Dan Allah ya kawo ni ba bansan ya zatayiba.
Ai ' yata jarumace dauriyace da ita na gaya maka, haka akeson mace.
Mami ke dai kina kare 'yarki dai.
Mariya tunda ta fahimci inda maganar ta dosa ta gudu daki Dan tun ranar da abin ya faru take jin kunyar Salim, sa ar ta ma daya ba Sadiq bane Ai da ta shiga uku.
Kwanaki sun wuce da dama yanzu Mariya da hafsa jss3 an zama 'yan mata Dan yanxu suna Neman 15 yrs.
Kawayen fa'iza yau suka zo gidan suna xaune suna ta zuba hira. Mariya da ta kawo musu abinci ta tsaya tana qare musu kallo,. Tace wa dayar , baiwar Allah yanzu fisabilillahi me ya kaiki aske girar ki bakisan hakan haramun bane? Kuma ni nasan yanzu haka kina wanke fiskarki zaki koma kamannin birrai( biri)
Ke kuma tace wa dayar kin wani dame jikinki wai kin sa kaya wannan ba takura kai bane waiku idan an barku kun waye ina wayewar kuna tafiya kowa Na kallon jikinku.
Wayewa duk idan ba ta addini bace wlh shirmece wani mutumin kirki zaku birge. Mhmm Allah dai ya shirya.
Fa'izar da take hararta ta gaji tace to munji ustaxiya fice ki bamu wuri .
Tabe baki tayi ta fice tana nidai Na fada muku gaskiya.
In dedication to Halima Auwal.
Missed u badly.
08161594233 4 cmmt.
๐๐MARIYA๐๐
20-25
By Anty Rukie( Mmn Abdul)
Kawayanta suna tafiya su mami a palo suna hira .mami kiyi wa Mariya magana gaskiya bana son shisshigin da take min da frnds dina.
Me kuma ta miki. Fa'iza ta labartawa mami yadda akayi.
Tana gama fada Sadiq yace. " kawar mahaukaciya kike Jim" ni ranar da nazo da kamil sai da ta kare masa kallo ta kwashe da dariya ni Na xaci ta kyasa nema.
Sai kawai yace , amma dai ya Sadiq kai mugu ne.
Kana kallon abokinka Na tafiya wandonsa Na faduwa amma baza kayi masa magana ya gyaraba wai don fa taga yayi ass down.
Sagir ne yayi kwafa yace nida nazo da Anas ranan ba cewa tayi ina abota da arna ba .wlh ranar ba karamar kunya najiba.
To wai me anas din yayi tace mishi Arne. Cewar Sadiq .
Tsaya kaji ya Sadiq kaga wani Dan banxan askin da yayi akanshine ga wani wando da ya saka daga kasa ya matse sosae fa sannan daga sama kuma yana zazzagowa ko kyaun gani babu bai yi kama da musulmi ba Sam. Mariya ta karishe tana yatsine fiska.
To ke ina ruwan ki da rayuwar mutanene? Sadiq ya fada yana harararta.
Duk Ku dakata , wlh duk abinda Mariya takeyi bana ganin laifinta domin gaskiya take fada , dama kuma mai fadan gaskiya bakin jinine dashi.
Kawar mahaukaciya:' da fadan gaskiya.to me, wan can lokacin yarinta ke dibanta. Saida ta dan saci kallon salim wadda yayi kamar be San me suke ba , amma a zuciyar sa yana mmkin abin nata har yakai haka. Har zata Iya tarar mutumin da bata saniba ta fadi abinda taga dama.
Fa'iza ce ta katse masa tunaninshi da cewa dama Goyon Kaka akwai Iya manyanyance.
Ba wani manyance sai sanin ya kamata gashi a sanadiyyan goyon kakan kun Iya girki da aikin gida . da da an tabo Ku kadan kuce Ku ' yan makaranta zakuyi latti.
Haka sukayi ta hira da yake weekend ne duk sun yini a gida.
Washe gari kuwa Mariya Na fitowa daga palo tayi kicibus da abokin sagir Na rannan da wani Dan banzan dressing.
Sai cewa tayi ikon Allah anya kai zaka samu matar aure ma kuwa?
Murmushi yayi gashi kuwa Na samu. Tabb tace amma zataga abin takaici.
Zata gani ko zaki gani . ni kuma ! Allah ya tsare in. To ya kika Iya nidai Na gani kuma inaso.
Kinga Na samu mata cikin sauki tunda kanwar abokina ce.
Ji tayi kamar ta kurma ihu .kafin tayi magana har ya shige dakin sagir Sadiq da yaxo wucewa ya jisu ya fashe da dariya tare da cewa " maganinki kenan uwar shisshigi .
Salim da tun fitiwanta yana tsaye a gun ya hade rai yace " ke , zo nan" ya juya yayi hanyar dakinshi.
A raxane ta kalle shi Dan ita bata ma lura yana wajen ba. Bin baynsa tayi a sanyaye. A kofar dakin ta tsaya tayi sallama. Shigo yace bayan ya amsa sallamar. Adarare ta tsuguna a bakin kofa kamar ace mata kat ta gudu. Daure fiska ya dada yi shigo ciki nace.
Haka ta shiga tana rarraba ido Dan bata taba shigowa part dinsuba.
Xauna anan ya nuna mata kasan carpet.
Xama tayi ta sunkui da kai. Jin yayi shiru tace ya Salim ina kwana , ai ina yini, dariya taso ta subuce mashi yai saurin kau da kai yana hadiye dariyarsa.
Wato ke baki da hankali ko , me nayi kuma ya salim . ina ruwan ki da wannan yaro da kika tsare kina gayawa mgn.
To ya naji ance musulmi ne. Idan yai ba daidaiba ya kamata a fada masa.
OK . kece ma uwarsa Kenan, iyayensa ma suka zuba masa ido bare ke.
To ya kasan ko a dalilin maganata ya canxa.
Ba xata dena bafa kenan ( ya ce a zuciyarsa) amma bari nayi maganin ta.
Mariya ko sonshi kike Na fadawa Abba ya aura mikishi. " Allah ya kiyaye " ta fada tana hawaye.
Kinsan Allah, kika sake ma yaronnan magana sai nasa an aura mikishi tunda yace ya gani yanaso.
Baxan sake bama in Allah ya yarda kayi hkr. Tashi kije yace.
Tana fita shima ya fito tare da kiran sagir ya masa fadan ya daina shigo da irin wadannan cikin gida.in so samu nema ya daina Hulda da irinsu dan zasu lalatashi.
Me ya sameki Mariya naga kamar kinyi kuka.
Xunburo baki tayi , ba ya Salim bane , ta labarta musu yadda sukayi.
Dariya suka hau yi. Daidai kenan ya Salim dinne maganinki.
Ahaf, wlh kyalesa nayi , ya Salim dinme wani kanshi kamar...sai ganinishi ya shigo yana kallonta, um um ya Sadiq din nace kanshi kamar kwakwa. Sai ganin Sadiq tayi abakin kofa. Ai ko ta runtuma da gudu tayi dakinsu.
Dukkansu dariya sukeyi. Sadiq har da buga kafa. Allah ya shiryeki Mariya Salim yace yana dariya.
In Dedication to Halima Auwal.
08161594233 4 cmmt
Luv u all.
FASAHA WRITERS ๐๐
๐๐MARIYA๐๐
26-30
By Anty Rukie( Mmn Abduljll)
Cikin ikon Allah suka ga junior WAEC, saura
jiran result. Fa,iza kuma ss2 take yanxu.
Babu inda suke xuwa sai islamyya shima da yamma ne 4-6pm. Aiyukan gida yanzu duk su sukeyi.
Mariya da Sadiq halinsu sai abinda ya qaru ayi fada a shirya . idan suka fara fada kamar xasu cinye junansu. Wani lokacin kuma ka samesu suna hira kamar basu ba.
Zaune suke a garden din gidan wadda yake gefen dakunan samarin gidan . Hafsa, Mariya , Sadiq da sageer.sai dai shi sageer bai cika samusu baki a maganarsu ba a ganin shi idan ya sake musu raina shi za suyi kamar yadda suka raina ya Sadiq . karatunsa yakeyi hankali kwance.
Sadiq yace wa Mariya.
" ke kawar mahaukaciya wannan karo bxa kije Hutu gun nenneres bane."?
Shiru tayi masa kamar bata jiba , mariya baki jini bane?
Au da dani kake, to da da wa nake tunda kinji nace qawar mahaukaciya. Mtsch , to wace qawar mahaukaciya anan ni ban ganta ba. ta fada tare da murguda baki.
Yi hakuri ' yar kanwata , nace yaushe xa a jewa Nenne Hutu.
Baxanjeba zaro idanu sukai dukkansu tare da cewa " wajen nennen "?
" Eh"
To me yasa? Ya tambaya.
Haka kawai, tace.
Qarya kike badai haka kawai ba.
Shiru tayi kawai.
Sis. Pls me yasa cewar Hafsa.
Hmm, ke baki sani bane, sai kuma tayi kwafa tayi shiru. Menene Dan Allah .
Kwafa ta sakeyi kafin tace.wacan lokacin da naje Hutu kin San yadda 'yan iskan nan suka kusa haukata ni?
Su waye suka fada har suna hada baki.
Hmm " wai ko wani Tom n jerry cewa yake wai yana sona , Nenne kuma harda cewa ai Na isa aure , haka kawai tsohuwa zata jawo min jidali ina karatu. Harfa wajen Babane wasu sukaje wai sunje Neman aurena.she gu mugaye kawai.
Wani dogo, dolo , tsiriri har da zuwa gaida nenne . wani katon ba...... Ke dakata mana inji Sadiq . me babankin yace to.
Cewa yayi sai anyi bikin su Hurera kafin yayi maganan nawa.
Tab, to ke akwai wadda kikeso acikinsu ne?
Kaga wlh bana son irin wnn magana ni da nake makaranta me ya hadani da wani so, wai ma ni a nawa nake har zaka wani yi min wannan tambayar.
Ta fada tana xumbura baki.
To ni meye laifi Na dan na tambayeki? Ina guje miki ne kada a aura miki wacan dogo, dolo, tsiririn.
Sai a sannan sageer yasa baki ai itama doguwa , doluwa , tsiriruwace.
Harararsa tayi ta kawar da kanta dan bata fiye son shiga sabgarsa ba shegen xuciyace da yanxu yace zai daketa ta raina shi, unlike ya Salim da Sadiq sun fishi saukin kai.
Sadiq ya katse shirun da cewa , " yauwa ga shawara sistona " tame? ta tambaya.
Idan Babanki ya tambayeki kice masa kina da Wanda kikeso.
Idan ya ce wanene kuma me xance masa.
Wa kuma zakice bayanni.
Wa ? Ta tambaya tana xaro idanu.
Ni Sadiq yace yana nuna kansa da yatsa.
Allah ya kiyaye, ni wlh kar kasa nayi kuka ma.
Kiyi mana wa yahanaki.
Haba ya Sadiq matar da xata aure kama tausaya mata nake wlh.
Lallai sai ki fara tausyawa kanki