Showing 6001 words to 9000 words out of 61103 words

Chapter 3 - MARAINIYA CE​ (1 to End) Complete by Anty Ruky ( Maman Abduljalal.)-.txt

cewar Hafsa.
Ni kam Ku daina min wannan fata ko mafarki nayi sai nayi sadaka.
Kutt..... Mariya ni din.
Eh kaidin .
Zanyi maganin ki ya fada yana kokarin mikewa.


In dedication to Halima Auwal.


08161594233 for cmmt.


FASAHA WRITERS🖊🖊
👛👒MARIYA👒👛



30-35


By Anty Rukie ( Mmn Abduljll)




Tun kan ya karasa mikewa ta ruga a guje ta nemi hanya.
Karo taji tayi da abu saura kadan ta fadi aka taro ta.
Dago kan da xatayi suka hada ido da ya Salim. Sakinta yayi da sauri tabi gefensa ta wuce tana mai addu ' ar Allah yasa bai ji hirarsu ba.
Mai da dubansa yayi kan Sadiq daya ke tsaye yana da murmushi yace " Sadiq wai har yaushe zaka daina irin wnn wasa da yarinyar nanne.
Nasha gaya maka ka daina. Ita ma ta nuna maka ba ta so.
Da gaskiyarta Kuma tunda mu ba muharramanta bane bai kamata muna tabata ba.
Ko ma ba wannanba idan ka saba mata irin wannan wasan ko wani ya mata a waje baxata jishi kamar sabon abu ba don ta riga ta saba .
A cikinsu kuma duk wacce hakan ya kasance da ita baxa muji dadi ba.
Gaskiya ne Big bros za a gyara ba xa a kuma ba in sha Allah.
Allah yasa yace ya juya yana jin wani daci a makogwaronshi , shi kanshi bai San me yasa ba idan yaga Sadiq yana wasa da Mariya ranshi yake baci ba.

1 week later.
Xaune yake a kofar gida a kan plastic chair, buta ne a gabanshi yana shirin yin alwala, kamar an ce masa daga kanka , yana dagowa kuwa ya hango Fa'iza, Mariya, da kuma Hafsa suna zuwa ga wani saurayi yana binsu a baya . ga dukkan alamu kuma mgn yake musu.


Tsura musu idanu yayi yana tunani wannan wa ya biyo a cikinsu.
Mariya ce ta fara ganinsa, a ta tsorata ganin irin kallon da yake musu.
Dafe qirjinta tayi tare da cewa mun shiga uku ga ya Salim.sai kuma juya ta kalli saurayin tace , Dan Allah mal. Ka rufa mana asiri ka juya ga yayanmu wlh idan ya kamamu baza muji dadi.
Saurayin kuma sai cewa yayi yauwa muje ma Na gabatar da kaina tunda kunki saurarata.
A gigice ta sake kallonshi , tab... Wlh idan ya wanka ma mari sai fuskarka ya qaura. Dariya mgnar ma ta bashi . yana dariya yace ya qaura ya je Ina? Ohon maka ta fada tana Jan hannunsu Hafsat da tsoro da takaici ya hana su motsawa.
Shi kuma tsayawa kawai yayi yana kallonsu yana murmushi har sukayi nisa .
Kafin su iso ya fara alwala Dan jin Kiran sallah da akeyi.
Sannu ya Salim fa' ixa tace , ina yini ya Salim cewar Hafsa.
Ko kallonsu be yi ba balle su sa ran zai amsa.
Sum sum suka shige cikin gida.
Yau da wuri suka shiga bacci gudun haduwa da ya Salim, da safe ma basu yarda sunyi breakfast tare da sauran mutanen gidanba. Ko da mami ta tambaye su sai cewa sukai haka kawai sukayi sha'awar yin brkfst a kitchen.
Sadiq kasa hakura yayi yace " ban ganewa ' yan matanki ba , jiya ba' ayi hira da su ba yau kuma basu fito brkfst ba".
Shi dai Salim yana jinsu bai ce komai ba Dan yasan rashin gaskiya ne ya boyesu.


Gaisuwa mai tarin yawa ga masoya Mariya , Allah ya barmu tare.




In dedication to Halima Auwal.


08161594233 for cmmt.






FASAHA WRITERS🖊🖊
👛👒MARIYA👒👛



36-40


By Anty Rukie (Mmn Abduljll)




Saida sukayi kwana uku cur suna wasan buya, ganin bai kulasuba suka ci gaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.



5 dayz later.


Hankalinshi ne ya gagara kwanciya gani yake kamar kullum suka fita sai samari sun musu mgn .
Dabara ce ta fado mishi ya aika sageer ya kira Mariya ta sameshi a garden.
Zaune yake a kan plastic chair ya daura kafafunshi a kan dayan kujeran dake gabanshi.
Gaisheshi tayi bayan ta tsuguna.
Minti uku yayi yana kallonta, har ta fara tsarguwa Dan jikinta ya bata kallonta yakeyi sbd kasa take kallo.


Tsinkayo muryarsa tayi yana mgn.
" ke me yasa idan aka tambaye Ku sunan Ku kuke Karya"
A raxane ta dago kanta kafin tace dashi. A INA?
A hanya mana ya bata amsa,
Su waye suke tambayanmu?
Su waye suke tareku a hanya.? Ya sake jeho mata tambaya.
Mukam babu me tare mu ahanya.
Har a hanyan islamiyya ma? Ya tambaya.
A take ta tuno incidence Na rannan tayi saurin sadda kai tana tunani a ranta wato sai yau yaga damar yin maganan Kenyan, to amma me yasa ya kira ita kadai ko yana tsammanin saurayinnan ita ya biyo.
Baki amsamin tambayataba me yasa kuke musu qarya bakwa fadan sunan Ku Na gaskiya.
Wlh ba wadda muka taba yiwa qarya. OK Na gaskiyan kuke fada kenan. .
A ah mu babu wadda ya taba tambayar sunan mu.
Shi wancan da Na ganku dashi rancan fa.
Mgn yake mana kuma bamu kulashiba. Wani irin Baku kulashiba bayan Na ga kina masa mgn.
Ce masa nayi idan ya biyo mu xaka bashi mari sai fiskanshi ya qaura.
Zaro ido yayi, Na taba marinki? Kayi hakuri Yaya. Baki ban amsaba Na taba marinki?
A ah. Wa kikaga na mara fiskanshi ya qaura. Babu kayi hakuri.
Shi kenan tashi kije . sai yanxu yadan samu relief tunda ba sauraran samarin sukeyiba.


Bikin su Atika ne ya taso Nenne ta matsa dole Mariya taxo bikin ' yan uwanta Hurera, da atika.
Saida mami tayi da gaske Mariya ta yarda xataje a hakan tare da Hafsa domin duk a tsorace take.


Sadiq yasa ta a gaba da tsokana, ni dai Mariya kada ki manta da maganar mu idan Baba ya tambayeki kice kina da wadda kike so, ehe Na gaya miki Kenan.....yana mgn yana dariyan tsokana.
Bakinka ya sari danyen kashi , tace tana harararsa.
Mariya kyaleshi ke sai kinyi karatu yadda kike so zakiyi aure. Yawwa mami Na Allah ya bar minke.
Sun gama shiri yau dai sageer ne zai kaisu Dan ya jima baije ba karatu yakeyi yanxu kuma ya samu hutun makaranta.
Dai dai xasu shiga mota sadiq yace" matas karfa ki kula kowa kuma ana tambayanki ki fadi sunana"
Murguda mai baki tayi . ya sa hannu xai murda bakin tayi saurin kaucewa, cafko hannunta yayi tana kokarin kwacewa .
Sai jin muryarshi sukayi yace " Sadiq respect urself and maintain ur personality"
Saurin sakinta yai yana Sosa kai " sorry bros" yace.
Yana tunani a ranshi ko me yasa ya Salim ya sa mishi ido akan Mariya.

Shi kanshi Salim yana mmkin yadda ya tsani ya ga ko mgn mariya nayi da wani.
Wata xuciyar tace masa to kodai sonta kake. No..wannan karamar yarinyar nida nake da fadila.
Fadila 'yar kawar mami ce. Tana yawan xuwa gidansu anan taga Salim tunda ta dora ido akanshi taji ya kwanta mata, daga nan ta dinga shisshige mishi tun yana sharewa har suka daidaita Kansu suka kama soyayya.
Fadila yarince kyakkyawa, fara ce mai mulmulallen jiki da ka ganta kaga yar Hutu.ta gama secondary sch.
Yàñxu ta yi applying tana Neman admission sai dai fatan Allah ya bada sa a.
Fadila tana tsananin son Salim saboda ya mata ko ta ina .


Salim baki ne saidai ba wul ba yana da Dan Haske, kyakyawane , mai sanyin Hali Dan bai cika hayaniya ba .


Yana yawan sa manyan kaya . yana sakananama amma ba sosai ba.
Yanxu haka yana 27 yrs yan aiki ministry of finance.
Fadila Sam basa shiri da Mariya Dan acewarta tacika yawar mgn ko mai ta gani sai tayi mgn.
Tun wata rana da taxo suna Palo dukkansu Salim ya dawo daga aiki ta tashi xata je wajensa,
Mariya ta ce mata anty fadila Dan Allah in tambayeki. Tace ina jinki , ke bakya jin kunya kixo wajen saurayi .
Tace wa ya gaya miki wajensa nake xuwa tun kan kixo gidannan ina xuwa.
A a ba gidannan nake nufi ba yanxu da kika kama hanya xa kije wajansa me xaki ce masa ai abin da kunya a kya ji kunyar idanunmu ma balle Na mami.
In nice ke wlh idan mun hadu a gidansu daga gaisuwa baxan nuna alamar akwai wani abu tsakaninmu bama.
Kai wlh wasu mata ma basu da kunya , Allah yasa Ku gane , wai Ku nan a dole wayewa ko.
Ta fada tana wani tabe Baku.

Kunya, haushi, takaici, su suka lullube fadila, ji tayi kamar ta shako Mariya ta wawwanka mata mari , ji yadda yarinya karama ta kunyatata a idon mutane.
Dàga ranar ta rage zuwa gidan Dan haushin Mariya takeji koganinta bata son yi.




Luv u all








In dedication to Halima Auwal.




FASAHA WRITERS🖊🖊
👛👒MARIYA👒👛




41-45




By Anty Rukie ( Mmn Abduljll)




Sun isa da kwana biyu aka fara biki ba zama sai xirga xirgan biki suna cikin kawayen amarya atika da yake itace karama itace kusan sa'ar su.


Sun fita daban acikin 'yan matan , abokan ango da sauran samari sai kokari shigar da Kansu sukeyi su kuma duk a tsorace suke kasancewar basu saba tsayawa da samari ba. Bama kamar ita Mariya da take gudun kada babanta yaji labari yace xai aurar da ita tunda ya aurar da ' yan uwanta.


Ranar da xa'a kai amarene suka ce xa su leka Nenne kafin axo tafiya da amare xasu fita kenan suka ga wasu yara biyu suna fada ga yara an xagayesu ana kallo. Cikin sauri ta isa wajen tana kokarin raba su . sai ta samu sun rabu tana juyawa sai su ci gaba .
Bulalanta ta samu lafiyayye ta fara tsarga musu ihunsu ne ya jawo hankalin matan dake ta harkokinsu wasu hiran duniya sukeyi wasu girki wasu wanke kwanuka kowa dai da abinda yakeyi,.
Wasu daga cikinsu ne suka xo jin me yake faruwa daidai lokacin da Mariya ta dakawa yaran da suke wajen tsawa , kai duk Ku watse anan tunda Baku iya rabon fada ba saidai ku tsaya kuna kallo.. Sum sum yaran suka watse , watace daga cikin matan tace . ikon Allah lallai Mariya kin canza har kina wa yara fada basu raba fada . ta fada tana dariya tunowa da halin mariya. Watace acikinsu tace wlh kam mariyan da idan ana fada ita ke zigawa tana wakar Ku doku ba mai rabaku.ko ta mikawa masu fada kasa tana ga Na fada ga Na wasa , Wanda ya fasa yaji tsoro. Haka dai suke ta fadin abinda Mariya takeyi da ana ta dariya.
Kamo hannun Hafsa tayi, zo mu tafi ke kuma kin tsaya kin hangame baki da hanci kina kallonsu. A a Mariya barni naji ba labari akeyi ba .
Toh yi taji nikam nayi nan ta tafi tana mita kaji min mata kamar an tambayesu.
Hafsa dai biyo ta tayi tana dariya , Ai na tsaya nayi recording ma ya Sadiq ne bari mu koma zai sha labari.
Sai kuma kiyi Mariya tace mata.




Sati daya sukayi suka koma , suna isa gida suka fito da gudu suna oyoyo mami , jin muryoyinsu mami ma ta fito tana Oyoyo yaran mami suna rigerigen isa ga mami sai ganin sadiq sukayi ya nufo su guje yana dariya duk yadda Mariya taso kauce mishi saida ya sha gabanta yana oyoyo sisters.
Kauce wa tayi da sauri tana wa xai maka oyoyon kafin ta isa Hafsa ta rigata . kankame mami tayi , mami munyi missing dinki . mu fa ?
Kai ya sadiq ka damen, to banyiba asali ma mantawa nayi dakai , karya kike wlh. To shikenan gwara ma fa'iza nayi missing dinta kadan👌, amma kaida ya sageer kam lala lala ta fada tana tabe baki.
Toh ya Salim fa, cewar fa'iza . shikam sosae nayi missing dinshi banda su o' o ta fada tana wa Sadiq gwalo.
Xan kama kine yarinya, amma dai naga ya Salim ya hana .......bata gama fada ba sukayi 4 eyes da Salim din daya kafeta da idanu tayi tsit kamar ba ita ke surutu yanxunnan ba.
Karasa mana me ya hana , kaga Sadiq kyale min ' ya ta huta daga isowarta ka tsareta da surutu ko gaisawa bamuyi ba. Ta jata sukayi dakinsu jekiyi wanka kuci abinci Ku huta mariyata. Toh mamita.


Ya Sadiq ina xuwa haka? Wani abunne? Ya tambaya.
Eh naga kamar fita xakayi , eh kina bukatar wani abune? A hakan xaka fita, dubi shigarka fa. Me shigar tayi ,
Tab amma kana da matsala 3quarter da vest kasa ka fita kamar ba musulmi ba.
Matsalata dake kenan kauyanci kayan shan iskanne zaki wani ce kamar ba musulmi ba? Wa xai ganni yace ni ba musulmi ba , xa' a fada da wannan suma da katara, kumatu kamar Na inyamurai.
Ba wani nan kedai kishi kike kada wata ta kwace miki ni kada ki damu mariyata Sadiq nakine ba me kwace miki.
Mtseew kanka akeji. Kema xa'a ji naki idan na fada ma Abba ya daura mana aure kinga sai kiji dadin hanani sa kayan da bakiso nasaka.
Mtseew wlh kiran mami xanyi taga da kayan da xaka fita.
Saurin ficewa yayi yasan yanxu mami tazo sai tace magnar Mariya gaskiyace.





In dedication to Halima Auwal.




FASAHA WRITERS.🖊🖊
.
👛👒MARIYA👒👛




46-50


By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)




Bayan kwana biyu Mami ta ce Mariya ta kaiwa Salim abinci a dakinsa yayi bako. Hafsa xo mu kaiwa ya Salim abinci , Hafsa da take sallah maza kai musu kafin su fito masallaci.


Tana isa kofar dakin tayi sallama kasa kasa Dan batayi tsammanin da mutum acikiba tasa kai ta shiga.


Turus tayi ta tsaya tana kallonshi baki bude, ajiye mana Salim din yana masallaci.
Ajiye abincin tayi sannan ta dago tana kallonshi wayanshi yake dannawa hankalinshi kwance kamar bai San da mutum a dakin ba.
Har ta juya ta fara tafiya sai kuma ta dakata ta juyo kai kuma to xaman me kakeyi?
Kamar ya ? Ya tambaya.
Gani nayi ana maxa sun tafi masallaci sallah kai kuma kana xaune lafiyanka qlau, da hankalinka a jikinka kai kuma ba mace ba balle kace kana da lalura.
Dago kai yayi ya kalleta,
" so, what concerns u."?
Ya tambaya. Kallonshi tayi da kyau sannan tace
" sorry wlh Na dauka kai musulmine"
To da wa yace miki ni ba musulmi ba ya fada yana binta da mugun kallo.
Yi tayi kamar bata ga kallon da yake mata ba.
To nidai a matsayina Na musulma ' yar uwarka nake baka shawaran kaji tsoron Allah Kuma ka rike ibada. Allah da kansa yace ban hallice kuba sai Dan Ku bauta mini.
A yadda kake yanxunnan Baka bauta wa Allah ba sai yaushe xaka bauta mishi.
Shidai kallonta yake da mmkin irin karfin halinta.
Toh naji Malama jeki.
Zakayi sallan? Ta tambayeshi, ikon Allah wai me ya damekine.
Xama tayi a kujeran da ke kusa da bakin kofa,
Mlm ina guje maka mutuwar baxata, mutuwa bata sallama ba kuma sanarwa lokacinka nayi xata daukeka ko ka shirya ko Baka shirya ba, ina maka tsoron axabar qabari ina maka tsoron wutan jahannama gamuwanka da ubangiji da ya halicceka ya raya ka, ya axurtaka da ni,imominsa ya Baka lfy ya maka dukkan gata amma ka butulce masa ka gagara bauta masa.
Mu dauki misali da d'an da ka Haifa a cikinka kayi masa dukkan gata ya girma karshe ya za ya kasance marar biyayya marar jin maganan ka fi sabilillahi ya xa kaji.
Zata ci gaba da magana..yayi saurin katseta... Naji kuma Na gode insha Allah xan gyara kanwata.
Yawwa yayana Allah ya sa,nima Na gode ta tashi xata fita.
Ya sunan malamar? Ya tambaya , Mariya tace. To Na gode Mariya.


Tana fitowa sukayi kicibis da ya salim , a take ta tuno abinda yace mata rannan, Na shiga uku tace a xuciyarta amma a xahiri sai tace sannu ya Salim, baice komaiba sai kallonta da yakeyi, ganin haka sai kuma ta tsargu.
" ya Salim ko banyi dadai ba nidai gsky Na fada masa ko" ta karashe mgnn da fiskan tausayi. Gyada mata kai kawai yayi yana kuma tunanin wato ita Mariya wannan Hali AJININTA YAKE. Dan tun dazu ya dawo ya ke jin duk abinda take gayawa abokinsa.


Ko da ya shiga bai nunawa mansur yaji abinda sukayi da Mariya ba. Sai cewa yayi "mansee yane "? Ajiyar xuciya mansur ya ya sauke duk ta gama kashe masa jiki abin kunya yarinya karama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login