Showing 12001 words to 15000 words out of 61103 words

Chapter 5 - MARAINIYA CE​ (1 to End) Complete by Anty Ruky ( Maman Abduljalal.)-.txt

a Mariya ke ma kinsan idan baki kulashi ba ba xai kulakiba.
Ni dai mu jira ya Sadiq din kawai ya dawo ya kaimu. Wannan Ai bata lokacine Mariya .muje kawai munsan guri dole se an kaimu ne?
Da dai yafi mana kam.


Ina xakuje suka tsinkayo muryar Salim lokacin da suke kokarin fita daga gate din gida.
Saida gaban Mariya ya fadi, dago kai tayi ta kalleshi amma ta kasa magana. Hafsa ce ya fada masa inda xasuje. Saida ya danyi jimm sannan yace Ku tsaya ina xuwa.


Fitowa yayi da car key a hannunsa ba tare da yace musu komai ba ya shiga motar, binsa sukayi suma suka shiga sannan ya tayar suka fice.


Surutunsu suke ta xuba ko uffan baice musu ba.
Har suka iso wajen saloon din, xasu fita ya dakatar dasu tare da mika musu dubu biyu.
Kallon cikin idon Mariya yayi wadda ya sata sunkuyar da kai suna mishi godiya, be amsa ba sai cewa da yayi " Babu ruwanki da kowa kiyi abinda ya kaiki " toh tace.
Hafsa, Duk abinda tayi ki fada min xan dawo an jima idan kun gama" toh sukace dukkansu.


Ko dasuka shiga ciki sun tarar da mutane uku a gabansu, Mariya kokarin kame bakinta take kada ta jawowa kanta.
Har aka gama ma wadancan, daya daga cikin masu saloon din taxo gun Mariya tana cewa me xa a miki, relaxer za a sa miki ko... Kafin ta karasa Mariya tayi saurin cewa, a a nikam musulmace xata taban gashi bake ba.
Sakin baki tayi tana kallon Mariya , wato ni ban miki kama da musulma bako?
Sai kin fada? Ai kowa ya gankima ya sani. Kai amma yarinyar nan kin cuce ina musulma yar musulmai jikar musulmai kice ban yi kama da musulmai ba, to me ma ya hanani kama da musulmai.
Ke wai kina nufin kice min ke din kina sallah? Da wannan zako2 farata da gashin doki?
To ya akayi iyayennaki da kakannunki basu gaya miki cewar hakan haramun bane. Ko basa rayene?
Galla mata harara matar tayi, ga dukkan alamu ke ba wayayya bace idan aka ganki kamar kin waye .
Kallonta Mariya tayi Allah ya hanani irin wannan wayewa, wayewa duk inba ta addini bace bana fatan yinta.


Ni kina batan lokaci kixo Na fara miki,
Ke bafa xan yarda Dan har yanxu ban yarda da maganarkiba.


Ganin Mariya ta dage ne yasa matar Jan tsaki ta kira wata tazo ta mata.


Gyaran yayi kyau ba kadan ba Dan dukkansu Allah ya hore musu bakin gashi saidai Na Hafsa ya danfi Na Mariya tsawo kadan.


Saida sukayi 20mins da gamawa Salim yaxo daukansu.
Sun fara tafiya Salim ya karkato da mirror daidai fiskan Mariya ba tare da ta sani ba a sace yake kallonta, gyaran ya dada fito musu da kyaun fiskarsu.

Hafsa ina assignment din Dana baki ? Ya tambaya.Take Mariya ta fara rarraba ido, ita shaf tama manta da ya yi warning dinta.

Hafsa dake fa nake, marairaicewa Mariya tayi tana yiwa Hafsa alamar ta rufa mata asiri.
Salim da be bar kallonta ta mirror ba yace, tunda kin hanata fadi da bakinki
Ni ba abinda nayi. Xaki Iya rantsewa? Shiru tayi , ina jinki yace.
Dago kan da xata yi suka hada ido ta mirror tayi saurin sunkuyar da kanta tana tunanin kodai daxu yaga rokon Hafsa da idon da tayine.
Bata gama tunani ba taji yace" uhuum ina jinki Mariya. Kallonshi tayi taga hankalinshi Na kan driving din da yakeyi ta kalli mirror ta tabbatar ba ita yake kalloba.
Ta juya ta kalli Hafsa da take dariya kasa2 suna hada ido Hafsa ta mata gwalo aiko ta galla mata harara.
Kallon gefen hanya tayi sannan ta fara mgn a snyaye.
Ya Salim waifa wata arniya ce taxo xata wanken kai shine nace mata banaso ta kira min musulma yar uwata.
To sai akayi Yaya? Ya tambaya . shine tace min itama musulmace nikuma ban yarda ba. To me yasa baki yardaba.


Gashin doki fa tasa akanta, meye kuma gashin doki?
Karin gashi tayi da attachment .
OK Na fahimta shine kika hau yi mata wa' axi ko malama?
Kayi hakuri baxan karaba, Ahab sedai inba keba Mariya so nawa kike fadin hakan. Nasan maganinki .Hafsa mutane nawa tayiwa wa'azin?
Mutum dayace. OK , sai kina fitane xaki rika wa mutane wa' azi ai.
Dan Allah kayi hakuri. Bai kara cewa komai har suka isa gida.
Ko da suka dawo suka hadu da Sadiq yake tambayansu ina sukaje, Ya dawo yana nemansu be gansuba Hafsa ce kawai ta tsaya yin bayani ita ko Mariya wucewarta tayi.

A ranar akayi kamu shiga iri daya da kawaye ,Riga da skate suka saka Na material lace colourn purple da touches Na whites a jiki. Dinkin ya xauna musu das a jiki kayan yayi matukar karbarsu daurin dankwali sukayi ya musu kyau matuka.
Amarya kam fadan kyaun da tayi ma bata bakine, kamu yayi kyau an cashe an dauki hotuna.


Washegari akayi walima yaukam shigan Arabian gown sukayi , walima ya kayatar , acikin gidan akayi, anyi rabon abinci da soveniers. Aka watse ana tasa albarka.


Dinner akayi a karshe a wani babban hotel,
Yau kam gown sukasa Na light blue lace dinkin ya kama su cif cif.
Tunda sukasa rigar Mariya ta kalli jikinta ta kalli Na Hafsa ta kyalkyale da dariya, tambayanta Hafsa tayi, dariyar me take? Budan bakinta se cewa tayi, ammafa telan nan Dan iska ne bashi da mutunci, yaushe ya karewa jikinmu kallo har ya mana dinki cif cif da jikinmu mu da muka je wajensada hijabi, jifa ta fada tana jujuyawa , kamar ya gwada.
Mtsew Mariya kinada matsala Dan ya mana dinki daidai jikinmu sai ya xama Dan iska.
Au ke abin bema baki mmkiba ? Ai wannan dinki gani xa ayi kamar tsayawa ma muka yi ya gwadamu.
Kuma a haka xamuje ga kuma gwagwaro mu kima a kanmu kamar mune amaren. Ke idan baxakije ba kisha xamanki ba dole.
Mtseew to ya xanyi.kafinsu fitoma an fara watsewa xuwa dinner .
A kofar gidan motocine suke ta diban jama a, ganin abokan ango yawancinsu sunxo daukan mutane yasa Mariya juyawa xata koma.
Hafsa ce ta rikota , ina xaki ? Mu nemi ya Sadiq ya kaimu baxan iyashiga motan mutanennanba, dagewa tayi ita xata koma ciki Hafsa Na riketa, sai ga Salim sun fito tare da fadila.


Cak ya tsaya yana kallon abin mmki , mariyace wannan ko kamace, ba karamin kyau tamasa ba Dan be taba ganinta da makeup haka ba.
Kallonta yake ba ko kiftawa saida fadilà tayi mgn ya dawo hayyacinsa.


Kai kuxonan kokuwan me kukeyi?
Hafsa ce tayi masa bayani, idanunsa akanta ya harareta sannan yace me nace miki rannan, ko kin manta Na hanaki fita.


Kanta a kasa ta juya simi2 xata koma gida tama gagara bada hakuri sbd tsattsareta da yayi da idanu.
A sanyaye ta shiga gida.
Binta yayi da kallo shima duk jikinsa yayi sanyi.


Ina xuwa ya cewa fadila tare da bin bayanta.




Wayyo typing wuya...


In dedication to Halima Auwal.


FASAHA WRITERS🖊🖊?
👛👒MARIYA👒👛




76-80


By Anty Ruky ( Mmn Abduljalal.)




'Yan uwa ina baran addu'a daga gareku, kanwata bata da lafiya tana hospital satinta biyu a kwance, Allah ya bata lafiya ya kuma raya 'yar da ta haifa.


Ameen.






Da sassarfa ya biyo ta da yake ba sauri takeyi batayi wani nisa ba.
Jin kamar taku a vayanta yasa ta daga kafa.
Bata Ankara ba sai ganin mutum tayi ya tare mata hanya.
Kamshin turarensa sane yasa ta gane shi Dan duk zatonta Sadiq ne.
Langabar da kai tayi tayi rau2 da ido kamar zatayi kuka.


Kanwata kuka xakiyi? Girgixa tayi alaman a'a, kasancewar akwai hasken wuta ko ta ina yana ganin fiskarta tarrr.
Tsareta da yayi da idanune yasa taji kamar ta ruga , sai sussunkuyar da kai take snn tana kokakarin maida hawayen da yake shirin xubo mata.


Girgixa mata kanshi yake alamun kar tayi kuka, sannan yace " kinyi kyau sister pls kada ki b'ata kwalliyar, "
Xuge zip din purse dinta tayi, ga mmkinsa se yaga ta fito da hnkchf din daya bata ranar da suka kaisu sch.
Share Dan guntun hawayen da ya Dan sauko tayi, ta rab'a ta gefensa xata wuce.
Ya sake tare ta tare dacewa " zo muje " kamar tace ta fasa , ammafa kuma ya Salim ne baxata Iya masa gardama ba da dai ya Sadiq ne.

Har sun fara tafiya sai kuma yaja ya tsaya, tare da kiran sunanta, kinyi kyau, ya sake ce mata.
Kunyace ta kamata ta gagara cewa komai, " kimin alk'awarin baxa ki kula kowa ba Mariya "
" In sha Allah tace"
Idan kinsan baxa ki iya ba gwara ki fasa xuwa dan mgnar gaskiya wa'axin ki shi ke attracting mutane xuwa gareki, xaki Iya ? Ya karishe da tambaya.
" xan Iya ya Salim" Allah yasa yace.
Shiru tayi , "bakice amin ba sweet sis."
Amin tace tana kokarin bude gate.
Suna fitowa Sadiq Na isowa wajen. Wow , yace, Allah ya nuna mana namu Mariyata, Ya fada yana murmushin xolaya ,
" kin ganki Kuwa" kamar in sure ki in gudu dake.
" ka kaini ina? Ni kam kwalelenka "
Sadiq blacky' n ne kake ta gwadawa kamar ba 'yanmata a gari. Cewar fadila, wani kallo Salim ya watsa mata tayi saurin hadiye sauran mgn.


Matsawa ya danyi kusa da ita ya sauke Murya."wannan wani irin Neman rainine , yanxu idan ta amsa miki kice ta raina ki ko"
Juyawa yayi gunsu " kuxo Na kaiku"
Dukkansu suka shigo , fadila a gaba su suna baya.


Sadiq ne ya leqo yana cewa " yanxu xan biyo Ku kada wani yamin snatching" Salim ne ya bashi amsa da kada ka kuskura kaje ka takurawa yarinya.


Kusan tare suka iso tare da motar Amarya da ango. Suna fitowa aka fara sanarwa ango da Amarya zasu shiga.
Hafsa ce tacewa Mariya subi ayarin Amarya su shiga.

Har sun fara tafiya Salim ya Dan daga murya ya kira mariya , wani kululun bakin cikine ya tokare Fadila.
" wai ni meye damuwar ka da yarinyar nanne"
Wani kallon mmki ya bita dashi, " kamarya meye damuwata da ita ko kin manta Mariyace kanwata"
Dadai nan Mariya ta iso ta leko, gani ya salim .
"Ina alk'awarinmu "? Yace da ita. Saida ta rausayar da kai tace yana nan ban manta ba. " idan kika karya na miki me?
" kai ya Salim baxan ma karyaba insha Allah"
" Toh ustaziyata Allah yasa" amin , tace tayi saurin bin bayan su Hafsa. Yayin da fadila kuma take binta da kallon tsana karara Dan bata taba xaton kyan yarinyar yakai hakaba , bayan haka kamar akwai abinda ta hango a idon Salim game da mariya . in hakane ne kuma babanta ya cuceta da ya hana aurensu da wuri.
Sauke ajiyar xuciya tayi tare da maida kallonta ga salim .Abin takaici taga shima din kallonta yakeyi yana murmushi, tabb , lallai idan xarginta ya xamo gaskiya ya xatayi. Lallai babanta ya jawo mata.ko ba komai Mariya ta fita kusanci dashi a yanxu.


Sassauta muryarta tayi tace , " Dear, wani alk'awarine wai kuke mgn."?
" wannan be shafe ki ba tsakaninmu ne da 'yar uwata"
" yar uwa indeed, wait yaushe ka canxa hakane?
'Daga mata hannu yayi , " dakata Malama, bana son haka, kuma ina dad'a jaddada miki ki fita harkar Mariya kada ki jawa kanki reni , dmn idan ta raina ki abin baxaiyi kyauba, bakisan wacece Mariya ba " Niko nasan wacece Mariya , tace a xuciyarta. A fili kuma tace , shikenan , sai yaushe,
" Idan Na samu dama may be Na dawo Na maida Ku gida , idan an gama Baku ganni Ku biyo amare Ku dawo"


Tunda ya kama hanyar komawa gida yake ta tunanin mariya . yadai San Mariya black beauty ce amma dai bai taba tunanin takai hakaba, Ashe mansur yasan abinda ya hango yake ta hauka, Dan har yanxu be bar mgnr ba, kuma shi kanshi ya tabbatar mansur ya shiryu ya xama mutumin kirki , wannan abin alfaharine ace ta sanadiyyar ' yar uwarsa abokinsa ya shiryu. Saidai kuma a ganinsa ba lallai bane Dan ta xamo sanadi yace xai aure ta indai har tsakaninsa da Allah yashiryu.


Kasa hakura yayi bayan ya dawo gida, dakyar yakai awa d'aya da rabi yayi ya tashi ya zari key yayi waje.


Abinda yake gudun shi ya tarar Dan Mariya ya hango jingine da jikin wata mota ga wani tsaye kusa da ita , ga dukkan alamu mgn yake mata. Duk da baiga fiskarta sosae ba ya tabbatar itace.
Tsurawa gurin ido yayi yana tunanin me ya fito da ita.
Hangoshi da tayine yasa xuciyarta bugawa. Da sauri tabar wajen ta nufo inda Salim take.
Tsareta da idanu yayi wadda yasata tsarguwa.
" sannu da xuwa ya salim " bai amsa ba kuma be daina kallontaba. Kanta sunkuye, tama rasa yadda xatayi. Juyawa tayi ta fara tafiya. Ina xaki? Ya tambaya.
" Hafsa xan kirawo.
"Dawo " yace tare da bude mata murfin mota. Tana shiga ya shigo yaja motar a guje. Har suka isa ba wadda ya kara mgn duk ta gama tsurewa.


Ta kama murfin mota xata bud'e ta tsinkayo muryarsa.
" Tun yaushe kuke wajen"? Wlh wlh...." Ba rantsuwa nace kimin ba amsa xaki bani"
" Bamu jima ba"
Waye shi?
"Ban sanshiba"
Ban gane hausar baki sanshi ba, ba tare Na gankuba?
"Sun dameni da kallone Na gaji Na fito shine kuma ya biyoni ya wage min wagajejen bakinsa wai yana dariya"
Dariya kawai ya miki ?
"Wai cewa yayi wai sona yake kuma- kuma." Se tayi shiru.
Uhum kuma me?
" kuma wai da aure" ta fada tana goge k'wallar dake kokarin xubo mata.
Ni bance kimin kukaba amma Na rokeki ki taimaki kanki ki daina kula samari.
Kodai shid'in kina sonsane?
Kai subhanallahi mutum se tambaya kamar dan jarida? Ta fada da murya kasa2.
Me kikace? " um- um cewa nayi ni me xanyi dashi.
Jinjina kai yayi sannan yace " shiga ciki" Ai kamar jira take ta balle murfin mota ta fita da sauri har tana had'awa da gudu gudu.
Binta yayi da kallo yana murmushi, Mariya case yace a hankali.


A kwana a tashi ba wuya, su Mariya an gama ss2 har an shiga ss3.

A wannan karonne kuma babnta yaxo, dama dai yasaba xuwa tunkan Mariya ta dawo gidan.


Wannan xuwan Na mariyane Dan ya sanar da Abba cewar ' yan uwansa sunce xasuxo Neman auren Mariya wajensa Dan sunce kara da zasu masa kenan su nemi aurenta gurinsa.


Abba beji dadin hakan ba dan baiso Mariya ta koma can in so shine samuma danshi d'aya ya aureta.


A take nan ya Yanke shawara a xuciyarshi kuma ya sanar dashi Mariya sun daidaita da d'aya daga cikin 'ya'yansa.
Shima babanta yayi farinciki dajin haka Dan baiso yi mata auren doleba.


Bayan tafiyarsa ya samu mami da xancen, snn ya tambaeta dawa ya dace a hadata.
Bud'an bakinta tace SADIQ. Shi kuma Abba yace SALIM shi yafi cancanta.
" ka manta Salim yana da wacce xai aura"?
" kayya ni auren yarinyarnan ya fita kaina , Ubanta ya nuna baida dattako"
" To amma Ai Salim bece ya fasa ba"
" ke dai muyi adduar
Allah ya tabbatar da alheri."amin"


ASALINSU.......




In dedication to Halima Auwal.


08161594233 for cmmt.




FASAHA WRITERS🖊🖊
hi nagode sosai Allah yakaremu da duk wani shaidanin mutum ko aljani harshi shaidan dim kowa yace ameen sannan Allah yqkara hada kawunanmu namma kowa yace ameen bayan addua daakayi akasoma cin abinci mai martaba yace waini hajiya ina yarkine naga duk wannan bidirin bangantaba murmushi hajiya tayi tace aitana islamiya amma yanzu nasan tana hanyar dawowa tsaki fairooz yaja yanda bazaajiba baffa abu yayi carafa yace ai yarki tanada hankali nafeesa wallahi yarinyar akwai shiga rai_




_kwarai kuwa kafadi gaskiya inji hajiya zainab mata ga baffa alhaji yarinyar akwaita da kamun kai amarya nafisa tayi tsurut tace ai baffa wallahi yaya yarima yayi dacen mata duk wurin aka kwashe da dariya vanda fairooz wanda yaji kamar yashakuresu duka a gurin ummy kuwa shigowarta kenam wanka tafada duk tagaji tana fitowaa wando kayan bacci tasaka riga tadauko wasu littafanta tana dubawa anan bacci yadauketa mumce tazo kiranta tazo suci abinci taga hartayi bacci haka takoma tagaya masu fairooz yace wai samun guri bacci tun yanzu lallai yarinyar nam taji dadinta damma rainin wayo kowa yaje tarbata banda ita metadauki kantane harsai anje ankirata zaki gane shayi ruwane mai martabane yatabashi yace mekake tunabi kowa yanacin abinci banda kai majid yace ai baffa tunanin gimbiyarsa yajeyi yaji yana yabonta dariya mai martaba yayi yace banda abinka ai matarkace bawanda zai hanaka ganinta wani mugun kallon yakewa majid dayake bakin gilashine bawanda yagane saishi wanda akeyi dominshi wani tukukin bakinciki takeji amma lallai majid dan iskane dariya nasir keyi ciki ciki yace majid kajawa kanka bakaganin yanda gogan yake kallonka tuntsirewa sukayi da dariya baffa abu yace anyakuwa qalau kuke kara tuntsirewa sukayi da dariya cikin mugunjin haushinsu fairooz yace kyalesu baffa inaga vasuda hankaline haka akaci abincin aka kare fairooz daya matsu yabar gurin_




*26*


_baffa alhj yayi gyaran murya yace waikai yarima haka zakayita zama bazaka kare gidankaba kutare kaida matarka miye amfanin haka ehhh dagajin maganar kasan in serious yafada sosa keya fairooz yayi kowa yazubamashi ido yace aidama baffa sonake saitakare secondary dinta tunda nima yanzu inason zankoma Egypt ne zankaro karatuna zaiyi daidai da karewarta itama amma duk abinda kukace shi zaayi kamar da gaske yana magana yana wani sunne kai baffa abu yace toai shikenam mudama kai muke jira mujita bakinka wannan aiba matsala bane kadaiyi kokari kakare gidanka kafin lokacin kaga kanadawo sai akaimaka amaryarka duk sukayi dariya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login