Showing 27001 words to 30000 words out of 137542 words

Chapter 10 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

murna zata fita waje, ni dariya ma ta bani nace
"kwana uku kawai da kawoki shine kike son fita".

" hhhhmmm Nahna ji nake kamar nai wata a gidan nan".

Bayan munyi sallar isha'i yaya ya shigo muka fito, a k'afa yace muje ma motsa k'afa yai parking motarsa,muna tafe muna d'an hira har muka k'araso gida, a k'ofar gida muka had'u da yaya ya dawo daga masallaci cikin fara'a yace "a'a amarya harda ke akai rakiyar, to sannu da zuwa".

A cikin gidama Aunty Hafsa da fara'arta ta tari amarya suka gaisa cikin girmama juna ta gaida yaya ma tanata jin kunya wai ita ga wan miji.

Nanma hira akaitayi basu bar gidanba sai tara da rabi.



Bayan mako biyu ne aka sasanta da gomnati da ASSU dan haka aka janye strike,nan muka fara shirin komawa school on Monday.


Tunda muka koma school karatunmu ya k'ara d'aukan zafi,na k'ara maida hankali sosai ga karatuna.


Lokacin da yaya Usman ya gama cin angwancinsa zai koma bakin aiki yazo ya samu yaya na yana Neman alfarmar inje gidansa in rink'a kwana da Amrah don tace tsoro takeji bazata iya kwana ita kad'aiba, nan yaya ya amince,yace ai ba damuwa.

Ranar daya koma bayan sallar magriba na d'auki kayana da zanyi amfani dashi da safe in zani school da kayan baccina,na wuce gidan yaya usman.


A yanda na sameta kamar Mara ladies tana kwance kan kujera,na k'arasa da Sauri ina fad'in " Aunty Amrah bakida lafiya ne?".

Lumshe ido tai tana fad'in "lafiyata qlau Nahna kawai ina kewan habeebina ne".

Y'ar dariya nai nace " kai Aunty nah daga tafiyarsa yau har kin fara kewansa?".


D'an zaro ido tai tace "hhhhmmm khadijah kinsan kuwa me ake nufi da aure? bazaki gane girman so da k'aunba sai kinyi aure,wlh yau ji nake kamar inyi me Nahna nai kuka nai kuka harna gaji,ji nake kamar yai wata guda da tafiya don tsananin kewansa na yini gudan nan".


Cikin mamaki nake kallonta don sai nake ganin kamar Wannan son da Takewa Yaya usman yayi yawa,ban tunanin zan iya son namiji haka a rayuwata,kai ina bazan iyaba gaskiya.


A hankali na dafata cikin sigar rarrashi ganin k'walla ta fara kwanciya a Idonta " kiyi hak'uri Aunty na insha Allah kamar yaune zakiga ya dawo tunda yace sati biyu zaiyi ya dawo,kuma kinga yacema transfer yake nema zuwa kano insha Allah nan kusa zai samu ya dawo gida gaba d'aya aita shan k'auna".

Mirmishi tai tace "na gode Khadijah, amma nasan yau da k'yar zan iya bacci wlh".

Nidai a zahiri rarrashinta naitayi amma a zuciyata ina mamakin mata irin wad'annan masu zazzafan so ga maza.


Da lokacin kwanciya yai tace mu kwanta a bedroom d'inta nace " a'a bari dai in kwanta a Wannan d'akin tunda shima da gado".

"Meyasa bazaki kwanta anaba ?".

Girgiza kai nai ina fad'in " gadon da mijinki yake kwanciya bai dace in kwanta akaiba,bama niba kowa ma bai dace ya kwanta kan gadon da kuke kwanciyaba".

Jin jina kai tayi tace "To muje can d'in mu kwanta,daman bama kwanciya Wannan d'akin".


Mun kwanta muna d'an hira tanata ban labarin Lokacin tana school da rayuwar boarding school d'insu, nikam sai dariya nake ina jin jina rayuwa irinta boarding school, wayanta tai ringing da sauri naga ta tashi zaune tana dafe k'irji tace " wayyo my hubby".

Mirmishi nai kawai nai addu'a na shafa tare da juya baya na lumshe idona ina son bacci ya d'aukeni don jin yanda take magana da yaya kamar wata y'ar Baby.

Amrah irin matan nan ne masu soyayya matuk'a in tana tare da yaya sai tai ta baka kunya don idonta rufewa yake taita mai soyayya.

A hankali naji ta dafoni tana fad'in "Khadijah ga yayanki zakuyi magana".

K'arb'a nai nai sallama muka gaisa nake tambayarshi sun sauna lafiya,ya amsa da eh can yace " Autan Baffah ki kula da Auntynki kinji kirink'a bata hak'uri kinga dik ta tayar da hankalinta kinji".

"To yaya ba damuwa zan rink'a kula da ita sosai insha Allah karka damu".


Bayan ta karb'i wayan taci gaba da shagwab'anta tana sakar mai wasu zafafan kalamai,nikam duk jinai kunya ta rufeni nai tsit ban k'ara ko motsiba.


Da safe tana bacci na tashi na shirya abin breakfast naci na shirya zuwa school, saida zan fita na tasheta " Aunty ki tashi ki rufe gidan ni zan wuce school ".

Da sauri ta tashi tana fad'in " Khadijah bikiyi breakfast ba zaki tafi,wlh bacci ne ya d'aukeni da nauyi,bari in d'ora miki ko ruwan tea ne kisha".

Mirmishi nai nace "Ai na shirya komai ma har naci nasa miki naki a cooler".


" Ayya sannu da k'ok'ari Nahna na gode ".


Har k'ofar gida ta rakoni ta rufe gidan.

Da yamma dana taso na wuce gida, sai dare na k'ara komawa gidan Yaya Usman.


Ya zama kullum haka nake da magriba in tafi gidan yaya Usman da safe in wuce school in na tashi kuma in wuce gida,har tsawon sati uku Yaya dawo ya kwana Biyar ya k'ara komawa,


*****************
Haka rayuwa taci gaba da garawa komai yana wucewa, kwanaki sunja sosai Wanda ya rage kwana uku UK ya dawo daga karatunsa, tunda labarin nan ya ziyarceni naji hankalina ya tashi matuk'a na rasa inda zan tsoma raina,sabida nasan lokacin aurena yazo kenan da Babban mak'iyina.


Kowa dake tare dani ya lura da canjin dana shiga duk walwalata ta kau,don haka Aunty Hafsah ta Sani a gaba da nasiha da maganganu masu dad'i taita ban shawara kan in k'ara dagewa da addu'a, anan na d'anji nutsuwa tazomin.


Ana jibi zai dawo Sweaty tazo gidanmu ganin irin yanda yanayina ya canja yasa ta fara min magana cikin sanyi " Nahna Duk kin canja damuwa ta bayyana tare dake kuma nasan don dawowar Broth ne,amma don Allah ina Neman alfarmarki daki kwantar da hankalinki waje guda kamar yanda kikai a baya,ni inaji a jikina tarayyarki da Broth d'ina alkairi ne garemu gaba d'aya,don Allah karkiyi abinda za'a gane hankalinki bai tare da yayana har ai k'ok'arin fasa auran nan naku,kinji my sweet Nahna".


Matse k'wallar idona nai nace "sweety bana fatan a samu matsala ta b'angarena domin zanzama y'ar halak ga Yaya na, kawai dai ina tunanin irin rayuwar da zanyi tare da d'an uwanki ne bisa dolan da za'ai mishi akaina,nasan bazan tsinci komai cikin auransa ba sai tsana da tsangwama".

" a'a ki daina fad'in haka My Nahna insha Allah zakiyi alfahari da auran Broth d'ina zaki sameshi me adalci a gareki kiyi hak'uri ki kwantar da hankalinki kiyita addu'a kinji".

Share idona nai nace "To ba komai insha Allah zan kwantar da hankalina ki tayani da addu'a Allah ya daidaita tsakaninmu".


Haka dai taita k'ara kwantar min da hankali,har wajan magriba ta tafi.

Da dare ina kwance d'aki a gidan Yaya Usman ba bacci nakeba kawai tunani nakeyi, Aunty Amrah na toilet tana wanka,bayan ta gama duk abinda zatai ta rufo Wancan d'akin ta kashe duk kayan wuta ta shigo d'akin da sallama,a hankali na amsa mata tazo ta zauna bakin gadon tare dafani tace " Khadijah wai don Allah make faruwa dake ne? Kullum damuwarki k'aruea take Amma inna tambayeki sai kice Norma ne,Khadijah yanzu bankai matsayin da zan San damuwarki ba kenan,koda ban kasance matar yayanki ba ni yanzu na d'aukeki matsayin k'awata kuma y'ar uwa ta, bazan b'oye miki damuwata ba,don haka Khadijah ki fad'amin meke damunki in na shawara ne in baki shawara in na addu'a ne in tayaki da addu'a ".

Tashi nai na zauna ina share hawayena nace " Aunty Amrah aure za'amin da mijin daya tsaneni bai ko son kallona, akan lefin da bansan nai mai ba haka nan tun fara ganina dashi ya kafawa rayuwata ido ya tsangwameni gashi yanzu aure zai shiga tsakaninmu".

"Nahna kina nufin auran dole za'ai miki? Duk gatanki duk yanda yayyanki suke sonki suke ji dake?".

" a'a Aunty Amrah ni a b'angarena ba auran dole za'aiminba,shine dai za'a mai dole a gidansu don mahaifinsa ne ke son had'amu.. ."

Nan dai na kwashe komai na fad'a mata tun farkon had'uwarmu a school har alak'ar dake tsakanin mahaifinsa da yaya usman da k'awancan dake tsakanina da k'anwarsa, da k'ullin da mahaifinsa yake son k'ullawa a tsakaninmu.

Jim tayi zuwa can tace "Nahna gaskiya dole ki shiga damuwa amma Wannan matsala ce mai saurin warwarewa indai zaki bada had'in kai wlh a sannu Zai soki so ma irin na mutuwa,amma sai kinyi hak'uri kin sawa ranki cewa bautar Allah zakiyi a cikin gidan auranki, Nahna shi namiji agun mace ba komai bane matuk'ar ta iya zama dashi tasan yanda zatayi mu'amala dashi tasan lagonsa da hanyoyin kyautata masa wlh a sannu zai zama a tafin hannunta,sai yanda tai dashi, Khadijah ki kwantar da hankalinki ki k'ara addu'a tunda har da bakinki kince kinyi ta istahara kuma duk sanda kikai kina jin yana Jin tsanarsa ta ragu a ranki to kinga gashi har yakai yanzu kinajin zaki iya zama dashi kuma bakya k'yamarsa kamar da kinga ai addu'a tai tasiri kenan,don haka yanzu ma bacci bai kama kiba tashi zakiyi kiyi alwala kiyita kai kukanki ga Allah, nima bari inyi alwala in tayaki rok'on uban gijinmu".

A zahiri maganganun Aunty Amrah sunmin dad'i don haka na tashi muka d'auro Al'wala mukai sallah raka'a hud'u mukaita addu'a har bacci ya fara fizgar Aunty Amrah taje ta kwanta,ni kuwa saida dare ya raba naje na kwanta inajin zuciyata wasai,( tunasarwa garemu y'an uwa aduk sanda matsala ko damuwa tai mana yawa to Addu'a kad'ai itace mafita)


" da asuba ma wasai na tashi nai sallah ban koma ba na d'auko k'ur'ani naita karatu bayan nayi azkar ban kwanta ba sai wajan shida da rabi kasancewar ranar bamu da Lecture sai k'arfe goma.


****************
Ranar Laraba k'arfe hud'u na yamma UK ya sauka a filin jirgin malam Aminu kano inda ya sami tarar Abbansa da K'annansa,cike da murna suka tareshi kowa na nuna farin cikin sa na ganin sa, nan suka d'unguma zuwa gida, nanma ya tarar an shirya gidan Ka flowers masu tsananin kyau anyi decorations tin daga bakin gate har zuwa cikin harabar gidan, zahirin farin cikin sa bai b'oyuwa don ganin yanda aka k'awata gidansu don tararshi kamar wani ango.

Kai tsaye Sweaty tai mai iso zuwa d'akinsa da aka k'awata maishi nanma da flowers ga kamshin turare air freshener tako Ina, ruwan wankama sweety ce ta had'amai yaje yai wanka,tsawon awa guda ya d'auka yana kimtsawa kafin ya fito harabar gidan inda duka family d'in gidan suka had'u suna jiransa, yana fitowa suka shiga gabatar mai da kayan abinci Abubuwan motsa baki kala kala harma ya rasa me zaici aciki sai dai ya cakuli Wannan ya fincini wancan, yanaci sunata mai hira kowa na nuna kulawansa akansa,har akai sallar magriba suka wuce masque shida Dad.

Ranar dai har k'arfe sha d'ayan dare Daddy (UK) yana tsakiyan danginsa suna hira yana basu lbrn karatunsa.

Da safe k'arfe bakwai saiga kiran waya daga sweaty ina gani naji gabana ya fad'i cikin kasala na d'aga wayan, "Hello Aunty nah kin tashi koni na tasheki?".

" hhhhmmm Sweaty na tashi tun d'azu harma nai shirin school ".

" OK kin tashi lfy ya gida?".

"Lfy qlau yasu Abbah da Aunty murjah?".

" kowa lafiya qlau yake amma biki tambayi Broth d'ina ba kuma dai kinsan ya dawo".

Jim nai inajin fad'uwar gaba nace " hhhhmmm ni ban San ya dawo ba tunda biki fad'aminba".

"OK ya dawo to tun jiyama nata kiranki wayanki a kashe in sanar dake ".

" hhhmm To ya dawo lfy?".

"Um lafiya qlau ya dawo yaushe zakizo mai sannu da zuwa?".

" hmm bari zamuyi maganar yanzu zan wuce school ne".
Nai saurin yanke zancan don ban San me zance mataba

"OK to a dawo lafiya Aunty Nah".

Muna kashe wayan na sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da d'aukan jakata naiwa Aunty Amrah sallama.



******
Bayan kwana biyu da dawowar UK da dare yana zaune parlour shida Sweety sunata hira tana nuna mai hotuna a wayanta,a hankali yazo kan folder d'in hotunansu na bikinsu yaya usman a sakkwato,yana kalla a hankali yace " sweety a ina kukai wannan pictures d'in ?".

"Lab Broth a sakkwato ne fa".

" meya kaiki sakkwato ke kuma?".

"Broth bikin yayan friend d'ina nefa mukaje".

" yanzu Abbah ya barki tafiya biki har sakkwato,don sangarta".

"A'a broth akwai alak'a sosai tsakaninmu da ita,kuma yayanta da take gunsa mutumin Dad ne suna harkar kasuwanci sosai".

" um hmm" kad'ai ya fad'a yaci gaba da kallon pictures d'in,

Yazo kan pic d'in amarya Zainab da angonta a gun dinner ya saki mirmishi yana fad'in " wannan ne angon ya wani dankama hula kamar bawa, ni ran aurena ma k'ananan kaya zansa, nasan zagi kawai zansha gun jama'a nikuma maganar kowa baya damuna ".

Cikin zumud'i sweaty tace " oh my Broth don Allah ka kusa yin aure? Ai k'ara kasa hankali wlh kayi,na matsu naga auranka".

Kallon ta yai dalala cike da mamaki yace " sabida me kuka matsu nayi aure, nawa nake da za'a matsu inyi aure 30 years kawai shine za'a sa idona akan inyi aure, haka fa Dad ya matsamin tun kafin in dawo kullum sai yamin maganar aure aure Ku kamar wasu y'an k'yauye kawai ayi aure ayi aure shine burinku lalle kuwa zaku dad'e Baku ga auran ba ".

Rik'o hannunsa tai cikin sigar rarrashi take cewa" cool down my Broth mana meye na d'aukan zafi haka daga maganar aure,shine nan tunda baka so anbar maganar daga yau".

Komawa yai ya jin Gina da kujerar yana fesar da iska me zafi,

" Sisy kinaji ko wato ban San in matse rayuwa inyi aure tun yanzu daga aure kuma shikenan sai a fara haihuwa a gidanka shikenan kuma an shiga wani zance na daban, Haba ina impossible ace guy kamar ni a fara kirana baba kuma Abba Haba baxai yuyu ba,gaskiya ba yanzu ba zuwa nan dai da 5 years haka".

Kallon sa k'ir sweety keyi can tace " yanzu Broth duk tarin baby's d'in da nake gani tare dakai daman duk ba sonsu kakeyiba?".

" hhhhmmm gaskiya ke yarinya ce kawai don kina ganina da emmmata kuma duk saisu zama ina sonsu? Lalle da sauranki, To duk yaran da kike gani girls friends d'ina ne kawai,guda d'aya ce kawai cikin su Fadlah y'ar k'asar nan ce da muka had'u da ita a can take nacemin sai munyi aure,to itama bawai auran nata zanyiba amma duk dai tsarinta yaimin don ta had'u babbar girl ce ko ina tayi gata educated gata so beautiful, gata gentle babyn tayi kawai don ba aure zanyiba da ita zan aura".

Dammm gaban sweaty ya buga don tasan za'a sha wahla matuk'a kafin a daidaita dashi akan Khadijah, jitai duk zaman ta gun ya isheta don haka ta mik'e tsam tana fad'in "broth bari in kwanta na gaji".

" OK good night " kawai yace bai d'ago ya kalleta ba.

Tana shiga d'aki ta fad'a gado zuciyanta fal tunani.

Shikuwa Nan ya zauna yana tunanin me yasa akeso yai aurene,to yama gano dabara daman so yake ya juya inda ya fito don shi bai tunanin zuwa yanzu zai iya zama a Nigeria zaman waje yafi komai dad'i a gunsa kayi rayyuwarka bamai sama ido, don haka bari gari ya waye ma yajewa Abbansu da wannan maganar.


B??0soB???

Readers mu masoyanku ne tunda munayi don ku, amma Ku duk yanda kuka rik'emu babu damuwa,Masoya da mak'iya duk muna alfahari daku???i
B??0soB???



Taku ce
Y'ar mutan j'aoji.???j%??]?j
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??

%?8[Kq?? %?'[? 8[Kq?lKq?lKq?lKq?lKq?lKq?lKq??


?? ]?? ]?? ]?? ]?? ]?? ]?? ]
JINJINA GAREKI MY NASMAT INA TAYAKI MURNAN KAMMALA NOVEL D'INKI (Y'AR GWAGWARMAYA) HAK'IK'A MUN ILIMANTU MUN FAD'AKANTU KANA MUN NISHAD'ANTU DASHI,ALLAH YA K'ARA BASIRA SIS NASMAT
UP
UP
UP
ZAMANAWA KUNAYI MUNA JIN DAD'I ???b
?? ]?? ]?? ]?? ]?? ]?? ]?? ]?? ]

0(???1(???8(???


Da sanyin safiya Daddy(UK) ya tadda mahaifinsa a turakarsa zaune yana kallon labarai a BBC, waje ya samu ya zauna cikin girmamawa ya gaisheshi,cike da fara'a ya amsa mai yana k'ara tambayarshi ya sauran gajiya,ya amsa da babu tare da k'ara tank'washe k'afa ya fara magana cikin nutsuwa da lankwasa kai " Abbah daman wata magana na k'ara zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login