Showing 114001 words to 117000 words out of 137542 words

Chapter 39 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

ya kwankwasa k'ofa naje ya mik'o min little zai wuce masallaci, Goggo na mik'awa ita na tada salla,ita kuma ta had'a ruwan wanka ta mata.



Wajan k'arfe shida su yaya sukazo shida yaya usman ne, nida Goggo muka shiga bayan motar UK yanata d'aga mana hannu ya koma, ganin yanda naga jikin su yaya amace lis yasa ni k'ara firgita, cikin share hawaye nace " yaya wai meya sami umman ne".


"Cikin sanyin murya yaya usman ya amsa min " wlh ciwon ciki ne ,wai harya tab'a Mata hanji yauma za'a mata aiki".

"Ya Allah ya bata lfy yasa ayi a sa'a" Goggo ta amsa da "Ameen".



*******
Lokacin da muka shiga sakkwato kai tsaye asibitin muka nufa.yanda muka tatar da y'an uwan mu cirko cirko yasa jikin mu k'ara mutuwa, da sauri na k'arasa ina tambayar su jikin nata sukace an shiga da ita aikin tun tuni,zaman awa guda mukai kafin aka fito da ita,duk kanta mukayo amma aka dakatar damu da cewa ko d'akin kar Wanda ya shiga don tana buk'atar hutu.

Har dare muna zaune muna zaman jiran farfad'owar umma amma shiru,sai cikin dare ta farka amma kuma ba cikin hankalin ta ba,k'arshe ma sai ta fara suma hankali tace muka kira doctor yazo kanta, allurai yai mata nan bacci ya k'ara d'aukan ta, mukam duk hankalin mu a tashe har gari ya waye.


Tsawon yinin ranar nan haka mukayishi cike da tashin hankali don jikin umma fa ba sauk'i saina Allah, kuka nayi shi harna gaji,kawai tunani nake in umma ta rasu shike nan banda uwa banda uba,sai gatan y'an uwa.
wajan yamma Allah ya taimaka jikin yai sauk'i harta fara dawowa hankalin ta,cikin yanayin tsananin rashin lfy ta mik'omin hannu na k'arasa jikin gadon ina share hawaye nace "sannu umma,Allah ga baki lfy ".

Can k'asan bakinta tace " Ameen Auta, ina miki wasiyya da yiwa y'an uwanki biyayya, musamman Haroon ki kula dashi da rayuwar sa,baki da sama dashi duk duniya, sannan kibi mijinki, kibishi iya iyawarki,sannan ki kula da tarbiyar abunda kika haifa kinji ".

Gyad'a kai kawai nake ina share hawayan daya keta gudu a idona. Haka sauran y'an uwan mu ke zuwa bakin gadon suna mata sannu duk da ka taketa amsa musu don maganar ta rik'e ,daga haka kuma sai bacci ya k'ara d'aukan ta, duk sai muka d'an sami nutsuwa, har mukaje mukayi sallar magriba da aketa kira.


Gab da sallar isha'i ta k'ara farkawa da shak'uwa me k'arfi tanayi k'irjin ta har sama sama yakeyi duk likitocin nan suna kanta, sun koramu waje, bayan mintinan da basu wace sha biyar ba rai yai halin sa,Aunty salma dake jingine jikin window d'in taga sunja zani sun rufe mata jiki har fuska bayan duk sun cire injinan dake aiki ajikinta,wata k'ara data saki ya samu ankara da gudu mukai jikin window Wanda dai dai nan likitocin suka fito suna bamu hak'uri.





*Taku ce*
*Y'ar mutan ja'oji*???j
??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\
*'YAN* *ARABIC*
??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??1]??1]??1]??1]??1]??1]

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd


???a???_%??]IqkpHq??Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
??Qd
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_




0(???5(???3(???



Jina da ganina ne ya d'auke na wasu mintina zuwa can ya dawo min tare da hargitsi da firgici,ganin duk wata halitta data jib'anci ahalin mu zubar hawaye take,nan take na k'ara tabbatar da mahaifiyar mu ta rasu kenan.kuka Wanda ya amsa sunan kuka shine ya kawomin ziyara, na kifa kaina jikin bango ina kuka me cike da ban tausayi da maraici, wato rashin iyaye babu babba ba yaro ba mace ba namiji duk wanda aka tab'a sai ya koka. Ganin yanda muka cika asibitin da koke koken mu yasa aka hanzarta bamu gawar zuwa gida, daga nan aka shiga sanar da y'an uwa jana'izar da safe in Allah ya kaimu.

Nikam ban ma cikin nutsuwar da zan sanar da wani don duka a firgici nake ,ina zaune gaban gawar addu'o'i naketa mata idona na zubda hawaye,Allah sarki Mama abokiyar zama ta gari maman su yaya Haroon ta fice hayyacin ta don suma ma tai da taji labarin rasuwar,sabida shakuwar dake tsakanin su ta wuce misaltuwa busiyi zaman kishi da juna ba tun farkon zaman su har tsufan su.



Haka muka kwana tsam a zaune muna ta yi mata addu'a da karatun Qur'ani,tare da rok'a mata gafarar ubangiji.


*******
Tashin hankalin rashi be k'ara gigita wanda yai rashi irin idan an d'aga gawa za'a fita da ita,duk dakiya da k'arfin imanin mutum in aka d'aga gawa sai ya girgiza, k'arfe bakwai dai dai aka d'aga gawar umma cikin makara zuwa k'ofar gida,don sallatar ta,gidan ya hargitse da koke koken jama'a yayin da nikam idona ya kafe k'am ba hawaye don zuciya ta ta wani bushe idona ya k'afe sai wani k'una da nakeji kamar ana suya cikin k'irji na yanda nake a jingine jikin bango ina bin kowa da kallo duk da fahimtar komai nake ba amma kunnuwa na naga k'ofar gida inda nake jiyo saurin muryar liman yanata kabbara, a haka kuma hayaniyar tashin ababan hawa ya karad'e tabbacin an idar za'a tafi kaita makwancin ta.runtse idanuwa na nai ina taune lips d'ina tare da dafe kai cikin raina nake wa Allah tasbihi don neman sassauci a wannan yanayin da k'unci yai wa zuciya k'awanya.




Misalin k'arfe tara ina kwance kan gadon umma na kuka nake mara sauti me cike da k'una, a bayana naji muryar sweety da Aunty murjah suna gaisawa da mutanan d'akin tare dayi musu gaisuwa,juyowa nai da kumburarrun idanuwa na na bud'e su da k'yar a Kansu.
K'arasowa sweety tai bakin gadon tana dafani tace "Sannu Aunty nah,sannu Allah ya jikan umma ya gafar ta Mata zunuban ta".

Mik'ewa nai da k'yar na zauna idona na zubda hawaye , gaisawa mukai da Aunty tana k'ara min gaisuwa, sweety ma tamin gaisuwa tare da zama kusa dani,a hankali tace " tare muke dasu Aunty Amrah harda Abba da broth,tun daren yaya Haroon ya sanar da Abba mun nemi tickets wanda zamu sami jana'izar amma bamu samu ba,saina yanzu ".

Jijjiga kai nai ina share hawaye nace " Wlh ni nama manta ban sanar da kowa ba,wayar tawa ma ban san inda take ba".

"Eh ai munata kira ba'a d'aga ba".


Su Aunty Hafsa ne suka shigo d'akin itada Aunty Amrah idanuwan su taf da hawaye suka zauna muka gaisa tare da yiwa juna gaisuwa.

Wajan k'arfe goma Abba da UK suka shigo gidan don yin gaisuwa wa mata,da k'yar na mik'e na fita zuwa parlourn mama inda suke mata gaisuwa, k'arasawa nai na tsugunna ina gaida Abba " cikin tausayawa yake amsamin tare da min gaisuwa, shi kuwa UK idanuwan sa akaina ya kasa furta min ko kala sai kallon tausayi da yake bina dashi kawai, ni kuwa kaina yana k'asa banma san me yake ba,mik'ewa Abba yai shima yabi bayan sa suka koma k'ofar gida.


*****
Bayan sallar la'asar Abba ya aiko inzo,a bakin gate na same shi dasu yaya haroon a tsaye k'asawa nai ina k'ok'arin taugunnawa yace "A'a yashi tashi Khadeejah, daman sallama zan miki zamu wuce don jirgi zamu k'ara bi kuma biyar zai tashi,amma nida murja ne zamu wuce Rukayya da Daddy na suna nan zuwa jibi sai su taho, kiyi hak'uri kinji Khadeejah ki rage kukan haka addu'a take buk'ata yanzu,ita tata tai kyau tunda ta rasu ta sanadiyar ciwon ciki kinga tayi shahada,fatan mu Allah ya karb'i shahadar ta".

D'aga kai kawai nakeyi kamar k'adangaruwa don ba baki da nayi niyar yin magana kuka ke k'wace min.

Bayan munyi sallama yace in turo Aunty murjah su wuce.

Dana isa na sanar da ita taje taiwa mama da y'an uwa na sallama, sweety ta rakata gun Abba a k'ofar gida yaya usman ne zai kaisu airport a motan shi.



Da dare ina zaune ina baiwa little nono Goggo ta shigo tana mik'omin waya ta wadda kota kanta banbi ba,k'arb'a nai ina duba tarin miss call d'in dake kanta ban tsaya duba kona su waye ba na ajiye ta gefena,ina dafe kaina da yake tsananin min ciwo kamar zai tsage, wayar sweety tai ringing kasancewar tana salla kuma wayan sai ruri take tana k'ara min ciwon kan yasa na jawo wayar ba tare dana duba me kiran ba nai picking call d'in ina sata a kunne nace"Tana salla ne".

"Khadeejah".

Naji ya furta a taushashe, shiru nai karo na biyu ya k'ara maimaita suna na anan na amsa da " na'am ".

Yace " Khadeejah kiyi hak'uri kinji,bamu samu keb'ewa nai miki gaisuwa ba, Allah taji kan umma yai mata rahma,Allah ta karb'i shahadar ta".

A can k'asan bakina na amsa da "ameen".

Shiru duk mukai nad'an lokaci daga bisani yace " Ina little? ".

" gata tana bacci".

"Ok ki shafa min kanta,sai da safe".

" ummmhmmm".
Kawai nace na kashe wayan,don yau d'in nan magana masifar wahla take min. Lalle rashin iyaye masifa ne,wato yanzu sai nakejin har rasuwar Baffa tana dawo min sabuwa fill, duk da ban girma a cikin gidan mu tsakiyar iyaye naba hakan bai hana shakuwa me k'arfi a tsakani na dasu ba. Shiyasa yanzu nakejin ko sauran y'an uwana da suke gari d'aya gida d'aya dasu basu kaini jin mutuwar ba.Tabbas ina son mahaifana so na hak'ik'a kamar yanda zuciyoyin su suka ginu suma da k'aunata.tsakanin d'a da mahaifi sai Allah kawai.


******
Washe gari ma haka akaci gaba da amsar gaisuwa har dare, sai wajan k'arfe tara hankali na yakai ga neman little don tunda akai rasuwar tana gun Goggo sai tai kuka take kawo min ita in bata nono, tunda tasan bana cikin nutsuwa ta nima me rarrashi na nake nema.

D'an kalle kalle nai kozan hango ta hannun wani amma ban ganta ba,gashi kuma na hango Goggo a tsakar gida tana salla, komawa nai na kwanta don bazan iya tambayarta wani tana inaba koda qlau ne balle ina cikin wannan halin.



********
UK ne tsaye cikin d'akin da akai mai masauki yana ta jijjiga little dake ta d'an kuka tana son yin bacci, tunda yai sallar isha'i ya kira sweety ta kawo mai ita yake ta fama,don tunda yazo bai ganta ba ko sau d'aya.

Yaya haroon ne ya shigo yana ajiye mai flask d'in abincin daya shigo mai dashi,ya d'an lek'a fuskar little yana fad'in "Ta hanaka zama ko,aima naga ta rufe ido ko bacci zatai?".

Mirmishi yai yana fad'in" eh daman in zatai bacci sai tai rigima,yanzuma baccin zatai".

Gyad'a kai yaya yai yana fita daga d'akin, a ransa yake sak'a tun jiyan fa dasu UK suka zo baiga sun had'u ko sau d'aya da Nahna ba,gaskiya ya kamata su had'u ai. Wayar sa ya ciro cikin Aljihu yana lalubo number can ya sa a kunnan sa yana fad'in "ki sameni d'akin Sadeeq yanzu".
Daga haka ya kashe wayan.


Ni kuwa jin kiran da yayan kemin yasa na mike a hankali na jawo hijab d'ina dake gefe na nasa tare da fita, a tsaye bakin d'akin na sameshi,ina zuwa kusa dashi na fara hawaye,rik'o hannu yai yana fad'in" muyi hak'uri mu duka Nahna, lokacin umma yayi dole bazata k'ara ko second guda ba,addu'ar mu take nema a halin yanzu kinji ki tsagaita da kukan nan haka kinji ".

D'aga kai nai alamar gamsuwa .can ya cika hannun nawa yana fad'in " ki shiga d'akin umar na ciki ki amso Babyn don kuka take ".

Gyad'a kai nai kawai tare da nufar d'akin, sallama d'auke a baki na, a bazatta yajiyo muryar tawa don haka cikin taraddadi ya amsa,na bud'e na shiga tare da jingina jikina jikin k'ofar.
Zuba min ido yai can ya numfasa tare da kwantar da little a gefan gadon ya taso zuwa gareni, sosai ya matso jikina har muna gogar juna,zubawa fuskata ido yai wadda ta fad'a fiyau yana sauke numfashi akan ta,ni kuwa idanuwa na a lumshe suke sai hawayen dake fita cikin su suna bin kunci na.
A hankali yasa harshen sa yana lashe min hawayen tare da rik'o hannuna guda cikin nasa yana murzawa alaman rarrashi, duk yanda yake sid'an hawayen bai sa sun tsaya ba illama k'ara yawa da suke, zuciya tace naji tanata wani bugawa da sauri sauri wanda har jikina shima ya fara rawa,k'ara Matsoni yai sosai ya rungume ni a jikin sa yana k'ara lasan fuskata, sannan a hankali yasa bakin sa cikin kunne na yana fadin " sorry my wife ki bar kukan haka kini,sorry plsss and plsss". Ya k'ara tsantsameni a jikin sa yana hura min iska a kunne da saman fuskata. ni kam na kasa hanashi abunda yake wanda ban san dalilin hanawan ba,a hankali nutsuwa ta ziyarceni hawayen idon nawa ya tsaya, shi kuwa zuwa lokacin harya fara manta lallashi na yakeyi ma. kwankwasa k'ofan da akai yasa ya sakeni da sauri ya koma bakin gadon ya zauna yana min nuni da ido wai in bud'e, ban musa ba na bud'e k'ofar,yaro na gani dan yaya Babba yake tambaya wai yaya Sadeeq na ciki ana neman sa,ban iya amsa mai da baki ba sai kai dana girgiza mai kawai ya juya ya tafi,na rufo k'ofan tare da juyowa ina kallon gefe nace "kawo ta mu koma daman yaya haroon ne yace inzo in karb'eta tana kuka".

Bai cemin uffan ba sai zuba min ido da yai cike da tsantsar tausayi na.
Ganin tsaiwar tai yawa yasa na k'ara magana Karo na biyu cike da k'osawa
" ka kawota muje mu kwanta dare yayi fa".

D'auko ta yai ya nifoni yana zuwa ya k'ara had'e ni da jikinsa murya a sanyaye yace "Tunda nazo bamu samu had'uwa ba,Ya hak'uri".

" Alhamdulillah ".
Na fad'a ina mik'a hannu na zan amsheta,bai hanani ba ya sakar min ita yana fad'in" sai da safe,insha Allah gobe in anyi addu'ar sadakar uku zamu wuce".

"To Allah ta kaimu da rai da lfy".

Amsawa yai da " ameen" yana bud'e min k'ofar na fice.



Da baya da baya ya koma ya kwanta akan gadon yana dafe kansa tare da lumshe idanuwa,tunano tsawon lokacin daya d'auka rabon sa daya rungume ta haka yake yi, tun randa ta baro India yanzu wata goma sha d'aya kenan an tunkari shekara, gaskiya ba k'ara min dakewa yake ba da jurewa,tunma kafin ta haihu suna cikin rikicin nan take tsaka da buk'atar ta amma wannan turtsetsan cikin bazaima bari ya kusan ceta ba,gashi ba jituwa ko kad'an a lokacin, yanzu kuma tunda ta haihu ba fuskaba magana ma sai da niya take amsa mai,kwana biyu nema ta d'an fara sassaura mai akai rasuwar nan, kuma koba haka ba yana tsoron daga fara ganin y'ar fuska ya fito da zalamar sa tace ma don haka yake binta da bata hak'uri, shiyasa zaici gaba da daurewa da cijewa da shan k'wayoyin kwantar da sha'awa,har Allah ya k'ara sassauta zuciyar ta ta sake su dawo normal.


Ni kuwa tunda na koma ciki naiwa Little shirin bacci na kwanta ina lallab'ata tai bacci a haka nima baccin yai gaba dani.




******
Washe gari sadak'ar uku su Aunty ummu sulaim suka zo ita da mijin ta, suma by air suke, don haka ana sallar azahar sukace zasu koma ,tare dasu sweety da uk , duk sun shigo sunwa kowa sallama, na fito yi musu rakiya bakin gate nan na sami mijin ummu sulaim da UK tsaye,muka k'arasa mijin sulaim ya k'ara min gaisuwa tare da min sallama, yaya Haroon zai kaisu airport, duk sun shiga motar sai shi dake tsaye jikin murfin motar hannun sa rik'e da little yana kallo na, matsowa kusa dani yai sosai yana mik'o min ita,sannan a hankali yake min magana" ki k'ara hakuri akan wanda nasan ki dashi,kiyi tayi musu addu'a Allah ya gafar ta musu, ki rage damuwa a ranki kinji?".

Gyad'a kai nai idona na cikowa da k'walla,juyawa nai bayan na karb'i yarinyar nan na d'aga musu hannu na wuce cikin cikin gida.


******
Tsawon kwanaki bakwai muna karb'ar gaisuwa, zuwa lokacin zuciyoyin mu duk sun rage rad'ad'i, a cikin wannan kwanakin tun bayan tafiyar su UK kullum sai yayi min waya safe da dare yana k'ara ban hak'uri da kwantar min da hankali, duk da ba wata doguwar hira muke ba amma hakan yana min dad'i tunda ya nuna kulawar sa gare ni.

Washe garin bakwai d'in kuma muka d'auko hanyar gida dasu yaya da matan su.
Tunda muka fito a gidan kuka na ta dawo sabo shi kenan yanzu duk sanda nazo sakkwato bazan k'ara ganin umma na ba???i.

A mota dai bamai rarrashi na don suma duk dakewa kawai suke,amma duk zuciyoyin su babu dad'i.



La'asar likis muka shigo gari,kai tsaye ni suka fara saukewa sannan suka wuce gida.

Tunda na shiga gidan duk ma'aikatan suka yo kaina suna min barka da zuwa tare da d'aukar akwatin kayana.

A gajiye nake likis don haka a daddafe na zauna a parlour muka gaisa dasu sukai min gaisuwa na tashi na hau sama na barwa su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login