Showing 66001 words to 69000 words out of 137542 words

Chapter 23 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

shiga d'aki donyin sallan,

Yau kam nayi baccin farin cikin wanda Har naso makara,haka na yini ranar ba wata damuwa Har mamakin kaina nake yanda zuciyata take k'ara fad'awa tarkon k'aunar wanda banko son kallonsa ada mutum na farko daya takura rayuwata kuma na tsani d'abi'unsa amma gashi k'addarar aure ta gifta tsakanin mu har gashi na fad'a k'aunarsa ikon Allah kenan wanda yafi gaban komai.




Bayan kwana biyu ya k'ara kirana da dare muka gaisa nan ma dai ba wata doguwar hira mukai ba yai min sallama,
Tun daga ranar ya zama duk kwana biyu zai kirani mu gaisa ya tambayeni koda wata matsala nace mai babu, duk yanda Allah ya jarrabeni da masifar k'aunar sa ban bada kaina don koshi ban nuna mai na matuk'ar damuwa da rashinsa balle wanda Ke kusa dani mutum bazai gane inda na nufa ba,kuma hakan bai sani na fasa addu'a da rok'on Allah alkairi cikin rayuwar auranmu ba.



A b'angaren UK kuwa fadlah ta sakoshi gaba da nata makaman yak'in kullum da salon da take zuwar mai, kasancewar har ita aka d'iba cikin masu k'ara yin course d'in kuma gidajan da aka kama musu dukka jere suke cikin wani katafaran estate akayi sa'a kuma gidan sa da nata suna jere da juna don haka ko yaushe tana biye dashi cikin school ko a gida, Fadlah nada girman da bai iya wulak'antata don tana cikin matan dayasa aransa inda zai aure a kusa ita zai aura,amma gashi yanzuma da akai mai auran k'addara ta kasa hak'ura dashi kullum fad'a mai take ita ta amince zata zauna dashi a matsayin matar sa ta biyu, ya nuna mata ta hak'ura da batun aure kawai suci gaba da zumunci da mutunci don shi yanzu inma yai mata alk'awarin aure yai k'arya damanshi tsarin rayuwar sa mace d'aya ce zai aura donshi d'an boko ne to amma tunda gashi anmai auran dole to ya k'arb'i k'addararsa bai jin zai zama cikin maza masu tara iyali wannan wanda Basu wayeba, ganin kullum batada aiki sai mai naci damai kuka yasa ya rarrasheta yace ta bari dai yaga yanda gaba zatai amma yanzu suyi abunda ya kaisu kawai randa suka dawo gida Nigeria sa nemi mafita,amma a ranshi yasan bawai auran ta zaiyi ba gaskiya.




Kwanaki suna ta tafiya har yai wata guda da tafiya kuma a sannan muka fara exam wanda ta d'auke mu wata guda itama duka hutun sati biyu muka samu don haka ma wannan hutun bai cikin wanda zanwa mijina ziyara sai hutun mu na gaba da zamuyi tsawon sati shida a gida shine Abba yace muna yi zan tafi India .



Mun koma school nan naci gaba da karatuna cikin kwanciyar hankali sai dai yanzu abunda ya fara damuna sai UK yai sati guda bai kirani a waya ba, kuma inma ya kira Sama Sama zamu gaisa ya kashe tun ina daurewa har abun ya fara damuna matuk'a . . .




Man+sge man+sge





Taku ce
y'ar mutan ja'oji???j%??]?j
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

??1]??1]??1] ??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? ??



0(???3(???5(???


Sosai nasa abun a raina har hakan ta fara bayana kowa ya fara gane halin da nake ciki,yin duniya sweety tayi in fad'a mata matsala ta amma sai dai inyi mirmishi ince ba komai tasan zurfin cikina amma duk da haka ta alak'anta hakan ne ga rayuwar aurena,taso gane matsala ne tsakanina da mijina amma batai shishshiga ba taja bakinta tai tsit, ko a school haka abokan karatuna zasuyita tambayata ko banda lfy amma amsar dai d'aya ce ba komai, a haka wata rana Aunty ummy tace min zata kawomin ziyara kasancewar yanzu muna huld'a da ita sosai fiye da da don yanzu duk inda zaka ganmu da Hafsa Aminiya zaka ganmu da Aunty ummy kasancewar tanada matuk'ar k'ok'ari yasa tamu tazo d'aya don muna k'aruwa da juna matuk'a asalinta babanta balaraben chadi ne mamanta kuma fulanin nijar ne don haka kana kallonta zaka gane ba bahashiya bace amma zama cikin hausawa da auran miji bahaushe yasa ta rikid'e a magana da mu'mala tunda tace min zata kawomin ziyara naketa murna don zama da ita akwai k'aruwa sosai ko a harkar karatu ko a harkar yau da gobe, ran asabar ne zuwan nata don haka ina tashi nai ayyukana tsaf nai wanka na gama komai kasancewar sweety ranar bata nan ana bikin k'awarta tun sassafe ta fita, wajan sha d'aya na kira wayanta nace "Aunty ummy shiru baki zo ba"
Dariya tai tace ina shirya oga ne tare zamu fito ya saukeni amma nan da 30 minutes insha Allah ina gidanki"
Sallama nai mata ina cewa saita k'araso.

Tashi nai na shiga kitchen ina tunanin in fara rage aiki kafin tazo don haka na d'ora tuwo don nasan masoyinta a duniya tuwon shinkafa miyar d'anyan kub'ewa kuma ta fad'a min shi zan mata, inata aikina wajan awa guda har na gama tuwon na kwashe zan d'ora miya naji knocking da sauri na k'arasa ina fad'in " sai yanzu Maman boy gaskiya kin makara " na fad'a tare da bud'e k'ofan dariya tai bayan ta shigo tace bazaki ganeba Kedai Khadeejah, tsayawa nai kallonta ganinta ita kad'ai nace 'ina Farha da my boy na ganki Ke kad'ai"

Sai da ta zauna kan d'aya daga kujerun parlourn sannan tace "Abban su ya wuce dasu gun mamanshi wai tace kwana biyu basuje mata week end ba"

"Haba amma shine harda yarona za'a tafi inata murna yau yarona za'a kawo min ziyara"

"Ke bar wannan yaron naki rigimamme ai nan da 4 days zan yayeshi don bazanyi Ramadan dashi ba tunda daman ba shan nono yake sosai ba "

Wuce wa kitchen nai ina cewa"a'a yarona bai kai yaye ba sai dai in kuma k'ani aka samo mai"

Ruwa da lemo na kawo mata sannan na zauna muka gaisa sosai bayan ta d'an sha ruwan tace "Wane k'ani kuma ai nida wata haihuwa sai nan da shekara uku ko hud'u insha Allah kafin nan boy ya shiga school banda wata matsala amma ai konikan danai tsakanin Farha da boy ta b'aci don haka yanzu nake Neman tsari da konika"

Dariya nai kawai ina mamakin yanda take gudun haihuwa kusa kusa,
Hira muke sosai na saki jiki daga hiran karatu yanayin duniya har muka gangaro kan rayuwar aure, to an tab'o inda kemin k'aik'ayi duk da ban cikin mata masu rashin sirri amma wani abun dole kesa kai magana, tana lura da yanayin da nake kwana biyu wanda shine sanadin zuwan ta ma tunda tayi tayi a school taji damuwata nak'i,yanzu kuwa cikin hikima ta sako zancen yanda zan fad'i mata komai kafin ma ta tambaya, labarin mijinta ta fara bani "wato Khadeejah rayuwar aure sai hak'uri mazan yanzu sun girmi karatun me karatu, shiyasa zan iya kashe ko nawa ne kan namiji zan iya sadaukar da dukkan lokaci na ga namiji matuk'ar hakan zai zaunar dani daram cikin ransa, wato Khadeejah akwai wani lokaci da Abban boy ya tafi canada rimi rimi fa muka rabu tunda ya tafi kullum zamuyi waya muyi chart amma daga baya Duk saina ga canji ya fara bayyana inna kirashi sai ya gama hidimar sa zai nemeni kuma inya kira ba wani k'wakk'waran uzuri tsawon lokaci muke a haka na d'au fishi dashi na daina nemansa nima duk sanda ya kira ma sai naso zan d'aga wayan,ban Sani ba ashe dama na bashi tayin abunda yaso,wata yarinya ce take d'auke mai hankali a can tai kanai kanai cikin rayuwarsa janyewar da nai dashi nai fishi sai ta bashi damar sakewa da ita, sai daga baya nai tunani naiwa kaina fad'a nai na shiga nemansa ba dare ba rana na mak'ale masa koda yaushe naita kiransa a waya in yana aiki ya bani uzuri daga na kintaci ya tashi aiki zan ta kiransa saimu raba dare a waya koda yaushe bashi da lokacin kowa sai nawa duk sauran lokacin shi daba na aiki ba to nawa ne wani sa'in ma ko wanka zai yi sai ince yasamin video call zan rink'a tayashi wankan, a dole yarin yar nan ta fita cikin rayuwar sa don kota zo gunsa muna waya zaice ta tafi zai nemeta in da safe kuma aiki bazai bashi damar neman ta, a haka na shawo kan matsala ta cikin sauk'i,Kinga danaci gaba da d'aukan fishi shikenan na barwa wata banzar mijina tun suna soyayya ta iya baki da baki harta koma ta jiki da jiki shikenan ni an cuceni ko".

Jin jina kai nai ina nazarin kalaman Aunty ummy wanda kai tsaye zuciyata ta ban amsa da cewa lalle Irin halin da UK yake ciki kenan a India ba makawa nan da nan hawaye ya kuncewa idona, ni ban tab'a d'an d'ana zumarshi ba wata banza na can tana k'wak'ubemin miji, lafad'a ta Aunty ummy ta dafo tana fad'in "Khadeejah meya faru kuma naga kina kuka?"

Cikin sheshshek'an kuka nace "Maman boy kusan fa cikin wannan halin nake ciki yanzu Umar bai kirana a waya sai yai sama da sati bai neman ba kuma yana kira bama wata magana daga gaisuwa zai kashe,ina jin tsoron ko dai nima wata mace ki janye mai hankali "

Girgiza kai tayi "a'a Kar kiyi wannan zaton Khadeejah ko nima ban zargi mijina ba sai da na sami k'wakk'waran hujja daga abokin aikinsa, don haka karki fara zargin sa ba kyau kin Sani maybe shi ko aiki ne yasha kansa,ko wani dalili kuma mafa ni ina ganin kamar da sakacinki Khadeejah Ke kike bari ya kashe wayan maybe shiru kawai kikeyi bayan kun gaisa bakya fad'a mishi Irin halin da kike ciki na Ke wansa da buk'atar sa kk?"

D'an zaro ido nai nace" Aunty ummy yanzu sai nace mai ina buk'atar sa koma?"

Wani kallo naga tabini dashi na rashin fahimta sannan ta rik'o hannuna tana fad'in " Khadeejah kina son kicemin baki buk'atar mijinki baki muradin ganinshi kusa dake bakya marmarin sake had'a shin fid'a dashi akoda yaushe? "

Jim nai araina ina tunanin kodai ma in sanarwa Aunty ummy asalin yanda zaman mu da Uk yake ko in shaida mata ma bamu tab'a had'a makwanci ba maybe in samu mafita gareta,kai na sake girgizawa cikin raina nace bana cikin mata masu fad'in sirrin auransu wannan haramun ne matuk'a duk halin da zan shiga bazan tab'a fad'awa wani wannan sirrin ba,

Girgiza kafad'a tai cikin yanayin bani kwarin gwiwa tace "Khadeejah ki tashi tsaye ki damk'i zuciyar mijinki da gangar jikinsa karki bari kawaici da Kunya Susa miki waigi tsakaninki da farin cikin ki lalle ne in har kina son samun mijinki a tafin hannunki sai kin zama karuwa y'ar bariki me zafafan kalamai da zafafan aiki amma na soyayya sannan zaki cimma burinki, ina baki shawara Khadeejah yanda mijinki yai doguwar rayuwa cikin masu bud'ad'd'an ido to ganinki za'a rink'a yi a kulle biki san komai ba musamman keda kike *Y'AR* *ARABIC* da yawa mutane wani kallo sukewa macen da take y'ar Arabic me ilimin addini gani suke bata iya soyayya ba bata iya komai ba kunya da kawaici kamun kai da nutsuwar mu mu Y'AN ARABIC ita kesa ake mana wani kallo na daban,abunda ba'a Sani ba mu fitsara ce ba fidda tsiya bamu iya ba amma a bed munfi duk wata da take jin kanta wayayyiya fanni soyayya mu d'in na daban ne domin mu soyayya mukeyi me y'anci Irin wanda musulunci ya koyar kuma take tafiya da kowane Irin Zamani, Khadeejah mufa d'alibai ne masu karantar Islamic tome za'a layance mana duk mutumin fa da yake karanta rayuwar gidan manzan Allah (s.w.a) babu wata rayuwa da zata bashi matsala kota dameshi, ya karanta yaji yanda ake zama da miji yanda ma ake zama dako wane irin mutum, duk duniya fa babu wani mutum daya kai manzan Allah iya soyayya da rayuwar aure shi yasan yanda ake kula mace a ririta ta tayima abunda bata san tana yinba, shi yasan yanda ake faranta ran juna kuma shi yake koyar da matansa yanda zasu kula dashi suyi Abunda ransa zai fari,agidan manzan Allah aka saukar da duk wata soyayya shauk'i da nishad'i to mu kuma d'aliban Arabic meye bamu karanta ciki ba meye bamu Sani ba,daman anfanin ka nemi Sani kan rayuwar manzan Allah ai don kayi koyi da ita ne to mukam mun koya mun san komai kuma mun gode Allah don haka Khadeejah kiyi amfani da 'sak'afa islamiyya' (wayewa ta musulunci" da 'sak'asa ilmiyya' (wayewa ta ilimi) ki daidai ta rayuwar ki da mijinki rayuwar zata fimiki dad'i, don wlh Allah duk rayuwar da babu namiji cikin ta rayuwa ce Mara dad'i mara armashi Khadeejah ki mori rayuwar ki kiji dad'i kuma ki sami aljannarki".

Sosai maganganun Aunty ummy suka shige ni kuma sukai tasiri a jikina da zuciyata lokaci guda naji wani Irin k'warin gwiwa ta saukar min, godiya nai mata sosai sannan muka shiga kitchen mukai miya a tare muka had'a kunun aya bayan munyi sallar azahar mukaci abincin nan mukaci gaba da hiran mu wanda nake k'aruwa da ita matuk'ar k'aruwa har bayan sallar la'asar sannan Abban boy yazo ya d'auketa nai mata rakiya gate da kayan shafa na mata cikin leda inata k'ara mata godiya.

Bayan na idar da sallar magriba ina zaune kan abun sallar tunanin duka maganganun mu na d'azu da Aunty Ummy nake tabbas saina cire duk wata kunya dake tare dani da kawaici na nemawa kaina y'an ci don haka daga yau insha Allah zan fara dukkan wani k'alubale na shirya karb'ar sa, ina nan zaune har akai isha'i na tashi anyi tare da shafa'i da wutiri nai addu'oina naje na watsa ruwa a lokacin ne sweety ta shigo a gajiye tik'is itama wankan tai ko abinci bata nema ba tanayin salla ta kwanta, parlour na dawo na kwanta kan kujera sannan na fara lalubar number d'in sa a hankali na danna kira harta katse ba'a d'aga ba ban karaya ba na sake kira shima tana gab da tsinkewa ya d'aga duummmm naji gabana ya fad'i amma saina kira sunan Allah wanda shi zai bani k'warin gwiwa, "Assalamu Alaika " na fad'a cikin wata murya
" wslm , ya kk ya Guda"
" lfy qlau muke kaifa"

"Nima lfy ta qlau"
"Masha Allah, ya karatu"

"Gashi munata yi"

"Tom Allah y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a taimaka "

"Ameen"

Shiru ya ratsa na d'an sa'anni na rasa me zance,amma dana tuna meke gabana saina k'ara k'asa da muryata sosai kamar me rad'a nace" Saura ne wata nawa ka dawo "

Wani iri yaji tambayar wadda har taso bashi dariya amma sai ya basar yace "wata na nawa ne da tafiya yanzu "

Jim nai ina tunani can nace "um yanzu watan ka fa hud'u yanzu "
"OK Kinga basai na fad'a ba saiki k'irga ki gani saura wata nawa yanzu tunda dai wata goma sha biyar zamuyi"

Shagwab'e murya nai kamar zanyi kuka nace " nidai Allah watannin nan basa sauri nifa duk na matsu ma muyi hutu in kawo ma ziyara "

Tofa ya fad'a a ransa me yarinyar nan Ke nufi ne, d'an mirmishi yai yace " kina son zuwa inda nake ne?"

Kamar y'ar k'aramar yarinya nace "um ina son ganinka fa kullum sai naita tunaninka inji kamar ma inzo in ganka"
Wani bak'on yanayi yaji ya ziyarce shi, don salon yanda maganar Ke ratsashi har ya fara shiga cikin jikinsa, jin danai yai shiru yasa nace " mijinaaaaaaa"

Wawwwww ya furta cikin ransa yau kuma shi ake kira wannan sunan,
Ni kuwa rasa sunan da zan fad'a mai ne yasa na kirashi da wannan sunan don dai ba girma ba ladabi in kirashi da sunanshi na gaskiya Umar,kuma bazan iya cemai UK ba wannan sunan abokai ne, broth kuwa sunan da y'an uwansa Ke cemai ne,Sai Daddy shi kuma sunan da Abban sa da sauran dangi Ke fad'a mai ne ni kuwa nafi son in kirashi da sunan da wani bai tab'a fad'a mai ba,ai kuwa da gaske sunan ya bigeshi ,amma basarwa Irin tasa yasa ya basar d'in yana fad'in "um ina jinki "

"Baka kewanmu ne kai "
" hhhmmm inayi mana me kika gani "
"A'a naji baka cewa ma kana son zuwa ka ganmu ne"

"Inna fad'a ma baza tai amfani ba tunda nasan ba zuwan zanyi ba ko,nida gida sai nayi wata goma "

"Hhhmmm haka ne tom ni zan kawo ma ziyara nanda wata uku insha Allah, wannan karon semester d'in mu wata uku ce yanzu munci wata d'aya da komawa nanda wata biyu zamu fara exam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login