Showing 15001 words to 18000 words out of 137542 words

Chapter 6 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

INA GODIYA DA K'WARIN GWIWARKU GARENI Y'AN GROUP D'IN Y'AN ARABIC ,KARKU DAMU ZAKURINKA JINA AKA-AKAI INSHA ALLAH.






0(???1(???0(???



A yanda Sweety taga Nahna ta tareta ba wani damuwa akan fuskanta, cikin fara'a da murna kamar yanda ta saba kullum,bayan sun gaisa da Aunty Hafsa suka shige d'akin ta.

"Nahna manya, kin tafi da fishi kuma kin kashe wayanki don karma in kira ko".

"Hhhhmmm ban kashe waya don keba, kawai ina son in huta 2 day's shine na ajiyeta".

Kallonta tai sosai tana d'an mirmishi tace "To nidai zuwa nai in k'ara bada hak'uri don Allah, ban San maganata zata b'ata ranki ba".

"Karki damu ya wuce, daman ni batun soyayya ne kawai banso".


" hhhhhmmm Nikam sai nake ganin kamar da matsala akan wannan ra'ayin naki, don kuwa farin cikin rayuwa baya cika saida soyayya".


Cikin basar da zancen tace " kin tsareni da surutu ko ya jiki ban k'ara miki ba, ina fatan dai kin warke sosai".


"Tunda kika ga na fito ai na warke".

Cikin tsokana Nahna tace " a'a kefa k'afar yawo ce ko biki warke ba in ya motsa miki sai kin fito".


Dukan wasa ta kaimata tana cewa "ji sharri nice k'afar yawon, wlh in ba skl ba da nan gidan da gidan Aunty sulaim sai inyi wata nawa banje ko inaba, ko friends d'ina suke zuwa gidanmu in sun matsu, sun gama k'orafinsu kaina sun gaji, ke d'inma don ta dabance yasa kullum nake zuwa gidanku tunda ko ba komai za'a k'aramin karatu".


"Tom na gode emmata da zuwa gidanmu da akeyi".

Dariya sukai , sannan suka shiga wani hiran.


B'angare guda na raina kuwa na riga da na gama tsara rayuwata dangane da mu'amalata da sweety da ma gidansu gaba d'aya, dole zan rage alak'ar dake tsakaninmu, zan janye musu sosai kuwa, sabida naji tana fad'in shekara biyu zaiyi a can k'asar kuma yanzu yayi shekara d'aya da watanni, don haka kafin ya dawo mun raba. hanya ma dasu tunda dama sweety ke shigemin ita ta dage ta k'ulla k'awance dani tun ina yakicewa har muka shak'u, sabida haka zan sake sabon taku, don nasan duk randa UK ya dawo ya ganni a gidansu to Allah kad'ai yasan kuma tozarcin da zaimin, don haka kafin akai ga jallin ma k'ara inyi gefe.


Itakuwa b'angaran sweety tana kan bakarta na son had'a wannan soyayya, tunda dai Nahna ta nuna mata bawai d'an uwan nata ne bata soba a'a soyayyarce duka bata miradin farawa a yanzu, to zatabi duk hanyar da zatabi ta rink'a tausar Nahnan a hankali har ta janye ra'ayinta daga nan saita dawo mata da zancen d'an uwan nata.


*********
Kwatsam Yaya yaji kiran Alh usman yana shaida mai ya shirya wannan shekaran yana cikin way'anda ya biyawa aikin hajji,

Wayyo Allah ina yaya zayyi don murna, ba shiri sai gashi yayo gida ya taremu da wannan abin farin cikin, nan muma muka rink'a murna dasa albarka, nan muka shiga sanar da y'an uwanmu na sakkoto suma sukaita murna dasa albarka. Har gida mukaje mukaiwa Abban sweety godiya na wannan alheri dayaimana.


Shirye-shirye duk sun gama kankama na tafiyan yaya don muna sa ran ko wace rana za'a iya kiransu.

Duk wani guziri dame gida ke barwa gidansa in zaiyi tafiya irin wannan ta aikin hajji Abban sweety shi ya mana mai makon yaya, kama daga kan kayan abinci kayan masarufi har zuwa kan kud'in da zai bar mana Wanda zamu rik'e hannunmu, duk iya yanda yaya yai wajan nuna mai ya barshi yana da isassun kud'in da zai barmana komai amma Alh,usman d'in ya nuna ba komai ai duk cikin neman lada yake.


Yaya bai son me zai k'ara ajiye mana ba don komai ya wadacemu don haka kawai ya bar mana ATM CARD d'insa duk sanda wani abu ya taso mu ciri kud'i cikin account d'insa.



Bayan kwana biyu su yaya suka tashi zuwa k'asa me tsarki, ya barmu da tarin kewarsa.
Wanda tafiyar sunkai su ashirin k'ark'ashin jagoranci Abban sweety kama daga y'an uwansa na matarsa da ma'aikatansa da kuma shi, wanda duk shekara dama shi ba fashi, iyalan gidansa kuwa babu Wanda bai tab'a zuwa ba don sweety ma tacemin sai biyu taje aikin hajji ummara ma sau biyu.


Tun tafiyar yaya sai gidan yai mana fayau don yaya mutum ne mai sauke hak'k'in iyalinsa, koda yaushe in yana gida zai kasance tare damu ana hira da wasa da dariya, wata rana yajani mu had'ewa Aunty Hafsa kai muyita tsokanarta,wata rana kuma ni da ita muke had'e mai kai mu tsokaneshi iya son ranmu, yaya yaci abinci kwano d'aya damu ya nemu shawararmu kan al'amuransa na office dana kasuwa, ba Aunty Hafsa da take matarsa ba harni da nake k'anwarsa nayi kewarsa matuk'a hakama yaransa su Asharaf kullum cikin maganar Daddynsu suke, ahaka har muka saba da kewarsa.


Ana saura kwana uku sallah aka kawo mana sanmu na layya daga gidansu sweety don harshi abbansu ya d'auki nauyi kawo mana,amma duk da haka yaya ya siya mana k'aton rago mai makon sa da rago da yake yankawa.




Ranar sallah bayan mun dawo idi mahaucin dake mana fid'a yazo ya yanka mana sanmu da rago muka rabashi gida uku muka shigar da kaso d'aya gida, sannan kaso d'aya muka rarraba kyauta zuwa gidan abokan yaya da dangin Aunty Hafsa, kaso d'aya mukai sadaka ga marasa k'arfi kamar yanda addini ya tanadar.





Duk yanda sweety take son inje gidansu nak'i, tsakanina da ita sai waya wayarma wani sa'in kashewa nake don karta dameni, in tazo gidanmu kuma zai amshe da fara'a kamar da, wani lokacin kuma in tace zata zo sai ince bana gidan duk don dai janyewa daga gareta.




Bayan sati d'aya da sallah su yaya suka dawo gida Nigeria, mukai murna kamar me da dawowarsa,kamar yanda shima yai farin ciki da ganinmu cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali.


kwana uku da dawowar yaya ba tare daya huta gajiya ba muka shirya muka d'au hanyar garinmu sakkoto sabida yawon kiran da suke mai da masu cewa zasu zo mai sannu da zuwa, ganin zai wahalar da yan uwansa ciki harda iyayensa mata yasa yaga k'ara shi yaje musu,don yasan zumunci irin na family d'insu kowa k'ok'ari zaiyi yaga yazo, don haka k'ara shi yaje su ganshi.


Mota guda aka d'aukar mana daga tasha sabida yaya bazai iya dogon tuk'i ba sabida akwai gajiya tare dashi, ta d'ebemu da kayanmu da tarin tsarabar da yaya yaiwa dangi, don saida ma yaje kasuwar haji camp ya k'aro kaya da tarin yawa don tsarabar saudiya bazata ishi arabawa danginmu ba don yawonsu.




Mun isa sakkoto yamma lis cike da gajiyan mota, y'an uwa da abokan arzik'i aka taremu cikin farin ciki da murnar ganinmu, bayan mun gama gaggaisawa da kowa muka nufi b'angaran umma na inda nanne masaukinmu da Aunty Hafsa shi kuma yaya ya nufi b'angaran samarin gidan don yai wanka ya huta, muma wankan mukai sannan mukai sallah aka kawo mana abinci da fura mukayi k'at.


Bayan sallar isha'i yaya ya shigo parlour ya samemu d'an zama yai cike da gajiya yana cewa "Umma zuwa zanyi in kwanta don jikina ba k'wari wlh".

Cikin nuna kulawa ummana tace " Ayya sannu Haruna ai kayi k'ok'ari daga dawowa ka d'auko hanya haka, Mu munata shirin zuwa maka barka".


" ai umma in nace zan barku Ku taho wahalar zatai yawa,amma yanzu da nazo duk saimu gaisa da kowa, in mukai sati guda sai mu koma kinga hakan yafi ai".


"Haka ne kam sannu kaji, tashi kaje ka kwanta ka huta, Allah ya tashemu lafiya".

Mik'ewa yai yana mana sallama ya fita zuwa sashin mahaifiyarshi umma Babba itama yai mata sallama sannan ya wuce shashinsu.




Washe gari da safe bayan mun karya kumallo munyi wanka . yaya ya fito da tsarabarsu ya warewa iyayenmu mata nasu sannan y'an uwanshi maza da mata sannan ya ware na sauran family duk Wanda yazo sai abashi abinda ya samu.


Ranar gidan yini akai bak'i na zuwa yiwa yaya sannu da zuwa har dare.


Tsawon kwanakin da mukai babu inda mukaje ,sai mu da ake zuwarwa, haka har muka cinye sati guda mukayo kano.






Taku ce
Y'ar mutan Ja'oji???j%??]?j
??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *YA'N* *ARABIC*??-\


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*
%???

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd



??Gc *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd .
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??

%?8[Kq?? %?'[? ?Zaku iya samun littafan mu a Facebook%?'[? ?? ???a???_
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


??ad %?'[? ?Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu%?'[? ?? ???a???_
Zamaniwriterassociation@gmail.com






0(???1(???1(???





Tun bayan dawowar yaya Haroon daga saudiya sai alak'arsu ta k'ara k'arfi da Alh.Usman domin Alh, ya bud'awa yaya sosai a harkar kasuwancinsu, a da kaya yaya ke ansa agunsa ya ringa rabawa ma'aikatan wajan aikinsu, in anyi salary su bada,Yanzu kam abin yafi gaban nan domin yanzu ya bashi damar sa han nunshi sosai harkarn kasuwancinsa, duk wasu kaya in sun shigo mai sai ya bawa yaya jagorancin rarrabasu zuwa store store, don haka ya zama yaya shima yanzu baya samun zama, daya tashi gurun aiki zai shiga sabgogin kasuwancinsa, don haka yanzu sai bayan sallar isha yake shigowa, wata rana ma sai wajan goma, sosai muka k'ara samun ci gaba aharkar rayuwa, har mota yaya ya siya sabuwa ya aje mana tsohuwar tashi a gida tare da driver duk inda zamu ya kaimu.



Ban garan karatu na kullum k'arewa yake don shirye shiryen final exam muke nan da sati biyu.

A b'angaran Sweety kuwa duk yanda nake k'ok'ari wajan yakice ta ita tak'i barin hakan, kullum tana gidanmu ni kuwa na daina zuwa nasu, tayi Iya k'orafinta harta gaji ta bari.


************
_BAYAN_ _WATA_ _GUDA_

Yaya zaune tare da Alh, usman a katafaran parlourn sa na ganawa da bak'i, gyaran murya yai ya fara magana,

" Haroon dalilin nemanka na yau ya banbanta Dana kullum, domin yau magana ce me tarin mahimmanci zamuyi da Kai, wadda bata shafi kasuwanci ba, ina fatan samun nasara".

Sosai yaya haroon ya maida dukkan hankalinsa ga Alh, Usman don jin abinda yake fad'i.

" haroon kan maganar k'anwarka Khadeejah ne, hak'ik'a tun ranar dana fara ganin khadeejah na tabbatar da ingancinta nasan lalle yarinya ce daban da y'an matan wannan zamanin, nutsuwarta, kamun kanta tare da tarbiyarta duka abin birgewane ga kowane mutum dayasan kansa, tun a lokacin na fara wani tunanin game da ita, na fara sha'awar kasancewarta surukata, haroon don Allah alfarma nake nema a gareka ka taimaka ka bani Khadeejah na had'ata aure da Daddy".

Dammmmm yaya yaji gabansa ya fad'i, don bai san mema zaicewa Alh, usman ba, don haka yai shiru kamar me tunani.

Muryan Alh,usman ce ta ratsa kunnuwansa yana fad'in " Haroon taimako na zakayi alfarma nake nema gareka nasan khadeejah tafi k'arfin auran miji irin Daddy don khadeejah matar kamilallun maza ce amma ka taimka kayi wani abu akai".

Cikin sark'ewar murya Yaya yace " To Alh, zanyi shawara da ita Nanan don a sani na dai nasan Nahna bata kula ko wane saurayi don haka bata soyayya, to Amma wani abu guda akwai alk'awari dana d'aukarwa Mahaifina tun sanda ya bani kyautar Nahnah kan cewa bazan mata dole ba a cikin rayuwarta, don haka Alh,yanzu zanjewa khadeejah da maganar nan a matsayin shawara ba dole ba, zanji ta bakinta abinda tace zanzo maka dashi".

Shiru Alh, yayi zuwa can yaja ajiyar zuciya tare da fad'in " Shikenan Haroon ina sauraranka,Amma don Allah kayimin k'ok'ari kaji".

"Insha Allah zanyi k'ok'ari"
Jiki ba k'wari yaya yai mai sallama ya fito.

Tafiya yake a mota amma duka nutsuwarsa bata tare dashi tunani ne barkatai cikin ransa, yama rasa ta ina zai fara don a zahiri bai son abinda zaiwa Nahna dole a cikinsa, Tun had'uwarsa da Alh, usman baifi sau biyu ya tab'a ganin Daddy ba, amma ganin da yai mai ya tabbatar irin sangartattun y'ay'an masu kud'innan ne, hak'ik'a baya son abinda zaisa Nahna cikin matsala ko kad'an don amanar Mahaifinsa ce,
A haka ya k'arasa gida jiki ba k'wari ko kad'an.

Tun shiganshi gidan Aunty Hafsah ta lura da yanayinsa don haka suna shiga d'aki ta dafa kafad'ansa tana fad'in "Abban Ashraf meke faruwa na ganka haka"?

D'an mirmishi ya k'ak'alo yana Shafa gefan kumatunta yace " me kika gani Hafsa?"

" naga rashin nutsuwa da walwala a tare da kai ?"

"Karki damu zamuyi magana anjima yanzu had'amin ruwan wanka tukun?"

Cikin tsarguwa tace "Allah yasa naji alkairi wlh har gabana ya fara bugawa"

"Karki damu bari zuwa anjima d'in".



Ina k'ule kan gadona inata zuba karatu don exam d'inmu tayi nisa yanzu kullum ina kan karatu ko zaman parlour banayi Iya kacina cin abinci nake komawa d'aki, sallah kad'ai ce take shiga tsakanina da littafina, yau kam dake ina hutun sallah ko kad'an ban motsaba, ina jin shigowar yaya amma ban fita ba sai yaje sallar magriba ya dawo zanje masa sannu da zuwa.


Jin shigowarsa shida su Asharaf daga sallah yasa na fito parlourn,
" yaya sannu da zuwa ya aiki"?
"Yawwa sannu Nahnah ya gida ya karatu"?

"Alhmdll karatu yazo k'arshe ai yaya".

"Masha Allah , in angama kuma sai a koma degree ko sai kin huta"?

"A'a yaya k'ara in wuce kai tsaye don wannan tsyawa hutun shi kenan sai abu ya shiririce".

"To Allah ya taimaka Nahna autar Baffah".
Ya k'arashe da D'an mirmishi.

Dariya itama tayi kawai tana tuno Baffanta cikin ranta.

Bayan sunci abinci akai sallar isha nan kowa ya tashi don himmar sallah,

Koda Yaya ya dawo daga masallaci yau bai zauna hira ba a parlourn d'akinsa ya wuce kai tsaye inda Aunty Hafsah ta bishi, ganin ba kowa a parlourn yasa su Ashraf shigowa d'akin suna fad'in Aunty zamu kwanta,

"nace da wuri haka me yasa yau bazakuyi kallo ba "?

"Abba ya shiga d'akinsa momy ma ta kwanta"

"OK to bari a kashe kayan kallon"?

Fita tai taje ta kulle duka k'ofofin gidan ta kashe kayan kallo sannan tazo ta shirya su Asharf d'in suka kwanta kan gadonsu.

Tunda ta koma gadonta ta kwanta take tunani aranta, duk yanda akai yau akwai damuwa tare da Yaya ta lura duka d'an wasan da yakeyi k'arfin hali yake, ko dake jiki da jini k'ila baya jin dadi ne.

Watsar da tunanin tai ta shiga karatunta.



A d'aki kuwa Yaya yake shaidawa Aunty Hafsah duk yanda sukai da Abban sweety, itama shiru tai tana tunani zuwa can tace" Da farko dai ina son karka tunkari Nahna da wannan maganar har zuwa ta kammala exam's d'inta don yanzu babu buk'atar a kawomata rud'ani cikin zuciya, sannan shawara ta gaba inka samu Nahna kan batun nan ka bita da rarrashi, sabida inka bata umarni tabi kai tsaye zata ga rashin adalcinka gareta, shima Abban sweetyn ka bishi a sannu karka nuna mai kai tsaye had'in bai ranka domin zaiga rashin kyautarwa gareshi tunda shi yana iya iyinsa wajan ganin ya kyautata maka, sannan babban muhimmun abu shine muyita addu'a Muna neman alkairin Allah cikin lamarin".

Cike da gamsuwa da maganar Aunty Hafsah yaya ya gyad'a kai yace " Naji dad'in shawararrki Hafsah Allah ya shige mana gaba".

Amsawa tai da ameen zuciyarta cike da sak'e sak'e.


******************
Tsawon sati guda yaya bai Sanar da Nahna halin da ake ciki ba, ya bari sai ranar datai last exam d'inta zai zauna da ita.


Ranar Laraba itace ranar da zasu gama exam, duk sinyi shirye shiryen graduation d'insu,
Ranar suna fitowa a final paper d'insu kowa ka gani bakinsa bai rufuwa wasu na fad'in Alhamdullillah, wasu ko Allahu Akhbar kawai suke fad'i, sab'anin wasu da zakaga suna fitowa zasu hau ihu Mara dalili, Wanda (Y'AN ARABIC) suka sha banban da sauran.


Kai tsaye Open theater suka wuce inda zasu gabatar da '?NGN?N???iV' wato programs na larabci tare da masrihiyya, wajan ya cika yayi mak'il da alumna inda zakaga duka ( y'an Arabic) mata sanye da ankonso na Atamfa sai mazan sanye da shadda iri d'aya gwanin sha'awa da birgewa,

Nahna sanye da kayan sarakuna an mata ado da alkyabba da takalmi irin na sarakai, kasancewarta matar sarki cikin drama d'in, fadawane keta bin bayanta suna mata kirari irin yanda akewa sarakai, a hankali take takowa yayin da masu video da masu d'aukan pictures sukai Ca a kanta, cikin kunnanta taji muryan Ashraf da Khaleel suna fad'in
" Aunty Nahna Aunty Nahan"

D'ago idanuwanta tai ta dubi sashin da suke tare da sakar musu mirmishi,


Tana zuwa ta fara gabatar da kanta cikin harshe mad'aukaki (Arabic) bayan tai sallama ta mik'a gaisuwa ga prover's ga dikkan malamai tare da dukkan Wanda yake wajan,sannan kai tsaye ta shiga gabatar da shirin, inda hankalin dukkan Wanda yake wajan ya dawo kanta.


Yanda take sarrafa harshen larabci tamkar harshenta shine abinda ya burge kowa gashi sin d'in da aka d'orata a kai ya dace da ita,
Bayan gama drama d'in aka shiga muhawar tsakanin maza da mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login