Showing 6001 words to 9000 words out of 137542 words

Chapter 3 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

ciro wasu dogayan riguna y'an ubansu guda biyar sannan takalma k'afa uku da jakunkunan su sai wasu jakun kunan irin wanda d'alibi yake buk'ata masu kyau ya tura mata gabanta yana fad'in
"To gashi amma Allah yasa rigunanma suyi miki dai-dai don naga kin k'ara tsayi"

Tsananin Murna bayyane kan fuskarta take d'aga kayan tana fad'in "masha Allah broth?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? amma ka burgeni na gode Allah ya k'ara muku bud'i da wadata ya yalwata arzik'inku"

Da mirmishi kan fuskarsu suke amsawa da Ameen don a kullum burinsu bai wuce ganin farin cikin autar tasu ba ko don amanar da Baffansu ya bar musu.

Da sassafe yaya Nura yai shirin d'aukar hanyar sakkoto bayan ya cika wa Nahnah jakanta da kud'i yace don tana buk'atar kud'i a irin wannan lokacin.


A haka Nahnah taci gaba da tafiyar da karatun ta cike da nutsuwa sai abu guda da yake cin ranta yake dagula mata lissafi shine UK ya matsantawa rayuwanta da yawa duk inda ta shiga sai ya bita kuma daya ganta ba maganar arzikin da zai furta mata sai masu ciwo arai.

Yau ma kamar kullum ta shigo cikin skul d'in sanye da doguwar riga yellow an mata aiki sa stones red color masu d'aukan ido don haka tai amfani da red d'in mayafi wajen yin rolling d'in kanta k'afanta sanye da takalmi red da jaka red, kallo d'aya zakai mata ka Tabbatar da ainihin kyan da tayi masha Allah.

Tafiya take cike da nutsuwa da kamun kai irin na d'aliban da addini ya ratsa su.

hon d'in motan dake bayanta ne ya isheta don haka ta juya don ganin waye yake son rikita mata kwanya haka,
Caraf idonta ya fad'a cikin na UK yana mata wannan banzan kallon nashi me cike da izza da jin kai, a hankali tai k'asa da idonta tare da Kau da kai gefe tana jin wani b'acin rai aranta.

Tsawon tafiyar da tai daga bakin gate d'in zuwa inda zatai lecture UK bai fasa bin bayanta ba tare da sakar mata hon d'in motar Wanda hakan yai sanadiyar jan hankalin dukkan wanda ke bin hanyar kanta.

Sanin halinsa da d'aukacin d'aliban sukai yasa hakan bai zama bak'on abu agunsu ba, sun sanshi d'alibi ne mai d'aukar magana da maida mace ba abakin komai ba,kai tsaye sun san tsokananta yake yana son watsa ta.

Jiki babu k'wari ta k'arasa hole d'in tana shiga ta zauna zuciyanta na bugawa don b'acin rai, ko sallama batai wa d'aliban dake zaune gefanta ba wanda wannan ba d'abi arta bace kai bama d'abiar duk wani d'alibin Arabic bane.

Tun shigowarta suka fahimci akwai damuwa tare da ita amma ba Wanda ya tanka mata kasancewar Malam ya fara darasi.


Babu abinda ta tsinta cikin lecture d'in har malamin ya fita, ahankali taji Hafsah ta dafa kafad'anta tana fad'in
"Khadeejah ya akayi ne na ganki so silent?"

Sharrrr hawaye ya fara bin kumatunta don dama kad'an take jira tai kuka,

"Subhanallah Khadeejah meke faruwa haka ko baki da lfy ne?"

Kuka sosai take kamar wadda akaiwa mutuwa, abinda ya tayar da hankalin Hafsah matuk'a ta shiga rik'e hannunta tana jijjigata, abinda yaja duka hankalin matan dake ajin suka shiga Tambayar lafiya meya faru.

Ganin mutane sun cika kanta yasa tai k'ok'arin tsaida kukanta ta share hawayen,
Nasiha suka rink'a mata akan kome ke damunta ta barwa Allah ta daina kuka haka, gyad'a Kai kawai tai ba tare da ta furta komai ba.

Kusan 5 minutes suna zaune gun ita da Hafsah ta sauke ajiyan zuciya tare da furta" Hafsah me na tsarewa wannan mutumin yake takura rayuwata me namishi?"

Kallon ta Hafsah tai cikin rashin fahimta tace "Waye ne Khadeejah?"

"Mutumin nan daya takura min a skul d'innan,_ yau tun daga bakin gate yake bina da horn har bakin hole d'in nan, Hafsah biki ga yanda mutane ke kallona ba kamar nayi lefi. . ."

Ta k'arashe maganar tana matse k'wallan da ya k'ara taruwa a idonta.

Shiru na d'an lokaci ya shiga tsakaninsu daga bisani Hafsah tace " kiyi hak'uri Khadeejah ki cire wannan mutumin aranki, duk abinda zai miki karki sa damuwansa cikin zuciyarki,irinsu suna da yawa marasa mutunci kinga maybe ma shi yanzu ya manta ya miki hakan ke ya barki da damuwa."

"Hafsah biki San yanda na tsani kallo ba, duk yanda muke da mutum ban so ya fiye kallo na amma yau mutumin nan yaja min tarin idanuwan jama'a akaina kamar nayi lefi."

Ruk'o hannunta Hafsah tai tana fad'in " Tashi mu tafi kiyi hak'uri ki bar batun nan kinji."




**********************
Kwanaki da yawa sun shud'e yayin da karatun su Nahnah yai nisa sun fara shirin fara exam na first semester N.C.E one, ta maida hankalinta sosai kan karatun ta don ita bamai wasa bace kan harkar karatun ta.


Damuwanta d'aya ne UK a kullum k'ara matsawa rayuwarta yake ba sassauci duk wani motsin Hafsah akan idonsa yake, abin haushin kuma ba wai fa yana sonta bane a'a kawai kullum burinsa ya ganta ya musgunawa rayuwarta da bak'ak'en kalamai wai yana fad'in tunda ya nuna da farko yana ra'ayinta ta watsa mai k'asa a ido ta watsashi to shima sai ya rama da babban wulak'anci agareta.

Yau zasu fara da exam d'in Education 111 Wanda za'a shiga k'arfe goma.

Tun k'arfe Tara saura kwata tazo skul d'in kai tsaye (N????2??NN) library ta wuce don taci gaba da duba hand out nata.

30 minutes ta samu cikin ???2??NN d'in ta fito zuwa inda zasuyi exam d'in don ta sami waje me kyau,

Ta kusa daf da lecture Theater d'in taji ana bin bayanta kamar za'a taka mata takalmi da sauri ta tsaya cak ba tare data wai waya ba don jikinta ya bata ko waye, ilai kuwa muryanshi ya daki dodon kunnanta " ke villager girl yau kuma saurin me kikeyi haka, ho har college d"in ta fara bugarki naga an daina yangar da yauk'in"

Tsit bata bashi amsa ba yaci gaba " ke ko muguwar gidahuma ce a haka dai gashi jiki ya karb'i gayu amma cikin kan sai duhun jahilci taf, sai anyi batu kuce wai Ku y'an ARABIC ustazai, me ake da macan Arabic medium babu komai a tare da ita sai duhun kai da rashin wayewa, duk gayu da iya kwalliya irin na macan Arabic inka latsata ba wayewa, banza tsami kawai ware ki bawa mutane waje."


A kasalance ta d'aga k'afarta ta tafi zuciyanta kamar zata fito idonta duk ya kawo ruwa.

Wannan shine abinda kullum ke faruwa inta had'u da UK Wanda ita har mamaki abin ke bata na yanda baya fashin rana wajen bibiyarta.

Haka ta k'arasa cikin ajin jiki a mace, ganin Hafsah tana mata mirmishi yasa ta saki ranta ta k'arasa kusanta ta zauna suka gaisa.



Tsawon satittika suka d'auka suna exams d'in wanda Nahnah taketa zumud'in su gama ta had'a kayanta zuwa Gida sakkoto birnin shehu.

Kwanasu d'aya tak da gamawa ta shilla sai gida cike da d'okin ganin iyaye da y'an uwa.

Tunda ta dira a sakkoto Dangi suka baibayeta kowa murna yake yana fad'in " Nahnah an girma an zama emmata"
Ita dai mirmishi kawai takeyi aranta tana fad'in babu abinda ya kai mahaifa dad'in in kana mahaifarka sai kaji kamar kafi kowa.

Bata sami kanta ba sai dare tai wanka tai sallah bayan taci abinci ta haye gadon ummanta cike da nishad'i.

Hira sosai sukai da ummanta har wajan sha biyu kana sukai bacci.


Zuwanta sakkoto ziyara take sosai daga gidan wannan zuwa na wancan gidan yayyinta mata da maza da duk dangin mahaifanta.

Kasancewar hutun nasu duka na sati uku ne yasa kwanta goma sha takwas ta d'auko hanyar kano tare da kaya nik'i nik'i Wanda yayyanta suka harhad'a mata da y'an uwa.


Bayan sallar magriba ta iso gidan cike da gajiya, gaisawa kawai sukai da Aunty Hafsah ta ajiye jakanta ta fad'a toilet tai wanka ta d'auro alwala, bayan ta idar da sallar tai addu'oi ta fito parlour inda ta samu Yaya Haroon ya dawo nan ta zauna suka gaisa cike da murna yana tambayarta ya ta barosu ta amsa " da duk lafiyansu qlau"


Nan ta zauna sukaci abincin dare suka shiga hira har zuwa wani lokacin sannan kowa yai niyar kwanciya.




************************
Rayuwa ta lula yayin da karatu yai nisa gasu Nahnah, yanzu suna satin k'arshe na cinye second semester d'insu , Wanda tun dawo warsu hutu bata k'ara ganin UK ba, hakan ya haifar mata da kwamciyar hankali don babu me shigar mata rayuwa yanzu.


Bayan kwana biyu, tana zaune ita da Hafsah da ummy usman suna d'an hira sama sama tare da duba littafan dake hannunsu suna nazari aciki,
Shewan samari taji a gabansu suna ihu tare da tafa hannunwa d'aya cikinsu na fad'in "kai gaskiya nayi missing skul d'innan tun ranar final exam ban ko bi ta hanyarta ba"

"To gidan ubanka ce skul d'in da in ka gama saika ci gaba da zuwa"
Wani ya fad'i yana yamutsa fuska,

"Kai dole ya shigo mana tunda ya bar babyn sa acikinta duk da ma dai suna had'uwa a wajen shan eh . . .. "

Dariya suka d'auka duka suna tafawa.

"Kai Kai kai UK kaga waccen lady d'in kamar Bak'auyiyarka nan Y'ar Arabic."

A tare duka sika d'aga kai suna kallon inda yake nuna musu daga bisani suka shek'e da dariya suna fad'i " villager villager girl"

Yar taji gaban ta ya fad'i tai saurin yin k'asa da idonta.

A hankali ya tako zuwa gabanta yana tafa hannu tare da fad'in " Gidahuma daman kina nan ni harna manta dake ma, ana nan dai da duhun kan irin naku na y'an Arabic ko? Jibi banza meye to na sunkuyar da kai kamar bak'auyiyar amarya? Dalla d'ago kiji me zance miki."

Daga gefansa wani yace "anya UK ba son yarinyar nan kake ba inba haka ba meye na shiga rayuwarta haka?"

Da sauri UK ya dafe kai yana fad'in " AA ka cuceni ka gama dani ka wulak'anta ni ka tozarta ni wallahi Allah ya isa tsakani na da kai, kama rasa da wa zaka had'ani saida wannan Y'ar Arabic d'in me tarin duhun kai da k'auyanci, wadda ko Kalmar Love bata iya furtawa ba balle tayi shi, wlh da inyi love da Y'ar Arabic k'ara in mutu banyi aure ba, meta sani da zata min meta iya mutttsssss, AA kasan dai ni mijin wayayyiyar mace me aji ne wadda zan shiga da ita ko ina ta fiddani kunya."

Dariya sosai sauran abokan keyi na yanda ya daddage yake masifa har idonsa ya canja da b'acin rai.


Tsaki yaja ya bar gun sauran suka bishi.


"Khadeejah don Allah me kikaiwa wannan mutumin haka, Tun tuni nake ce miki mukai k'ararsa ga hukumar makaranta kika ce abarshi zai daina gashi nan yanzu ya bar skull d'inma bai fasa shigowa yimiki hauka ba."

D'agowa tai tana mirmishin yak'e Wanda yafi kuka ciwo ,
" Hafsah nifa ban jin haushinsa yanzu nasan jahilci da rashin sanin addini ke damunsa, yaje yayi duniya ce wata rana zai daina."

Ummy tace "ni kin san abinda yafi b'ata min rai dashi da yake cewa me macan Arabic ta sani a harkar love me zata iyayi, Allah ina rok'on ka daka had'a shi da y'ar Arabic a gidan auransa naga yanda za'ayi."

"Don Allah muyi abinda ke gabanmu mu bar wannan zancan haka."










Taku ce y'ar mutan ja'oji ???j%??]?j
??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *YAN* *ARABIC* ??-\


*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*




DEDICATED TO ALL
ARABIC/ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd


??Gc *ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??

%?8[Kq?? %?'[? ?Zaku iya samun littafan mu a Facebook%?'[? ?? ???a???_
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


??ad %?'[? ?Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu%?'[? ?? ???a???_
Zamaniwriterassociation@gmail.com




0(???0(???6(???



Tsawon wata goma Nahnah bata k'ara ganin UK ba Wanda hakan ya tabbatar mata da ya kammala skul d'in gaba d'aya,kuma tasan a wannan lokaci yana hidimar k'asa tunda shi a b'angaran degree yake, hakan ya k'ara kwantar da hanlalinta harta manta shi cikin rayuwarta.

A lokacin suna N.c.e 2 ne shima sunyi nisa don har sun fara shirin zuwa Teaching practice (T.P) da sunyi exam d'in second semester d'in zasu tafi Wanda zasu cinye tsawon semester guda baza su dawo ba sai wata second semester N.C.E 3.


**************
Alhj Usman katsina shahararran D'an kasuwa me wasa da y'ay'an nera, mutum me karamci da girmama talaka bashi da girman kai ko kad'an yana da tsananin kyauta da son mutane, yana da gaskiya matuk'a a harkar kasuwancin sa, matsalansa d'aya ce masifar son ya'ya' baya son abinda zai sami d'ansa ko kad'an duk yanda kuke dashi to matuk'ar ka shiga harkar ya'ya'n sa to zaku raba gari abinda d'ansa ke so shi yake so ba tare daya kula da munin abun ba.

Wannan son ya samo asali ne daga rasuwar matar sa uwar ya'ya'nsa Wanda ta rasu tun yaran suna k'anana su uku a haihuwar autar ta rasu awa d'aya da haihuwar,
Tausayi da k'aunar ya'ya'n ta taka rawar gani wajen sangarta su.
Yakai tsawon shekara bakwai bayan rasuwar baiyi aure ba ya tara ma'aikata sama da goma agidan suke kula da yaran nashi cikin kulawa da aminci, yayin da shi kuma yake cika musu lalitarsu da kud'i don ya gamsu da kulawar da sukewa y'ay'an nashi.


Umar shine Babba Wanda yaci sunan kakansa suna kiransa da Daddy, sai ummu sulaim , sannan Ruk'ayya auta wadda taci sunan mamanta me rasuwa, suna ce mata sweety Wanda Abbanta yake kiranta har sunan ya bita.


Iya nacin da akewa Alhj. Usman akan yayi aure bai yi ba saida Sweety ta shekara bakwai sannan Allah ya had'ashi da Aunty Murjanatu wadda ta tab'a yin aure shekarta d'aya ta fito ya ganta ya aura kan sharad'in kulawa da y'ay'ansa cikin amana da aminci.

Zuwa yanzu tana da y'ay'a biyu a gidan duk maza zaid da haris.

Umar wato 'Daddy' a yanzu yana can kwara state yana N.Y.N.C.E d'insa Wanda ya rage mai wata d'aya ya gama, kuma anan gidansu Abban sa ya gama yimai shirinsa tsaf don tafiya k'asar India yin wani course na shekara biyu akan fannin karatunsa.

Ummu sulaim kuwa an Mata aure bada dad'ewa ba har yanzu tana kan karatunta a bayero.

Sai sweety itama yanzu tana shekararta ta biyu a northwest.


Yaya haroon abokin kasuwancin Alhj Usman ne yana karb'ar shinkafa a gunsu ya raba a wajan aikinsu da sauran store store, Jinin su ya had'u matuk'a Alhj yana son yaya Haroon sabida ya kula da amanarsa, wani sa'in har gida yake kiransa su tattauna a maimakon office d'insa.


Rashin lafiya ne ya kama Alhj Usman sakamakon yana da ciwon sugar har aka kwantar dashi a asibiti, kwanansa d'aya a asibitin yaya haroon yace Aunty Hafsah da Nahnah su shirya ya kaisu su dubashi.

Bayan sunyi sallar magriba ya d'aukesu suka tafi,
Kasancewarsa babban mutum yasa Asibitin cika da jama'a masu dubiya, a haka dai suka ratsa cikin d'akin,
Alh Usman yana hango Yaya Haroon ya fara mik'a hannunsa yana kirmishi irin na mara lafiya, a hankali yaya ya k'ara yasa Hannunshi cikin nasa suka gaisa yana tambayarshi ya k'arfin jikin, cikin jin ciwo ya amsa, nan su Aunty Hafsah da Nahna ma suka gaidashi suka mai ya me jiki sannan Duk suka gaida da mutanan d'akin.

Tun shigarsu d'akin Nahnah ta kula da Sweety dake gefan gadon tana share hawaye, tausayinta ya kamata tasan me take ji tasan k'aunar mahaifi, tasan tsoron Sweety kar mahaifinsu ya rasu, tana wannan tunanin wayanta tai k'ara alamar ana kiranta, fita tai daga d'akin don ta samin damar d'agawa,


Tana nan tsaye tana wayan taga fitowar sweety daga d'akin taje can nesa ta zauna tare da kifa kanta tana kuka sosai.

Bayan ta katse wayan ta zubawa sweety ido tana cike da tausayi, samun kanta tai da k'arasawa wajanta,a hankali takai hannunta ta dafa bayanta tare da mata sallama, da sauri ta d'ago kanta tana share idonta, tsugunnawa tai tana magana k'asa k'asa " kiyi hak'uri ki bar mai kuka, addu'anki yake buk'ata,asannu Allah zai bashi lafiya kinji."

Gyad'a kai sweety tai tana goge idonta tace"na gode"

"Ba komai naga ne tunda muka shiga d'akin kike kuka zaki karyar mai da zuciya, ki tamai addu'a,kinga ai jikin nashi ma da sauk'i tunda ance jiya baima San Wanda ke kansa ba."

Gyad'a kai kawai take don nuna gamsuwa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login