Showing 30001 words to 33000 words out of 137542 words

Chapter 11 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

da ita,amma ina fatan samun had'in kanka kamar yanda ka saba bamu had'in kai a dukkan wasu lamuranmu".
Gaba d'aya Alhj Usman ya tattaro hankalinsa ga d'an nasa yana cewa "OK ina jinka Babana fad'i abinda ke tafe dakai".

" To Abbah daman kan karatuna ne,a school d'inmu sun bamu scholarship mu goma a matsayin way'anda mukafi kowa k'ok'ari a wannan shekarar cikin duk school d'in, kan cewar mu zauna dasu mu k'ara wata goma sha biyar mu k'ara wani course, duka kan business don zasu bud'e company a nan gida Nigeria k'ark'ashin school d'in to suna son mu kasance ma'aikata na farko da zamu fara aiki companyn kuma y"an Nigeria d'in suke so, daga bisani in mun gama course d'in sai ai bikin yayemu sannan mu taho tare dasu a bud'e company mu kasance wakilansu anan Nigeria".
Shiru yai yana tsimayin abinda Abban nasa zaice,
Tsawon lokaci bai magana ba daga bisani ya nisa yana fad'in "Daddy nah naji dukkan batunka kuma nayi matuk'ar murna daka kasance cikin zakarun shekara a school d'inku, wannan babban abin farin ciki ne a garemu baki d'aya, sannan naji dad'in course d'in da zaka k'arayi kan business don karatu ko wane iri ne baya yawa, amma wani hanzari ba gudu ba Daddy nah akwai abu me matuk'ar mahimmanci a gabanka kafin wannan, Wanda shine zai shiga tsakaninka da wannan k'udirin naka".

Da sauri UK ya d'ago ido cikin fargaba yana duban mahaifin nasa bakinsa har rawa yake yana furta " Abbah Abbah meye abinda zai shiga tsaka nina da wannan babban cigaban da zan k'ara samu?".

Cikin rashin damuwa Abban nasa yace " Aure, Aure nake so kayi Daddy nah, auran nan shi kad'aine cikar mutuncinka shine Zaisa ka k'ara nutsuwa kayi cikakken hankali Abbah nah".

A kid'ime yake fad'in " Aure Abbah? Aure fa kake cewa,haba Abbah har nawa nake da aure zai min shigar sauri haka Abbah, wlh Abbah babu aure a tsarina nan kusa,don Allah kamin afuwa ka bar maganar nan ka barni in koma in k'ara samo ci gabana. . . "

Ganin duk yanda ya kid'ime yasa Abban nasa sassauta murya cikin sanyin rai ya fara magana " Daddy nah meya kid'ima ka haka? Maganar auran kawai shine ka tada hankali, haba mana Baba na shin ka manta aure shine cikar mutuncin ko wane d'an Adam ka manta aure sunnar manzon Allah ne, mu ba auran mukai muka haifeku ba? to haka nakeso kaima kayi auran ka haifamin jikoki,ina son ganin iri daga gareka Abbah nah??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????,ina so ace nima yau ga Baba nah ya zama babban mutum, ka kwantar da hankalinki kaji indai don rik'on company ne zan baka guda cikin company nah ka rik'e shi kyauta ma in kana so,nidai burina kayi auran kaji Daddy nah".

Girgiza kai ya shigayi yana had'a hannaye alamar neman agaji yana fad'in "help me my hero help me,kamin rai wlh ban shirya ba ni yaro ne Abbah ban kaiba wlh,ina zan kai mace ni yanzu da k'uriciyata".

Cikin takaici Abban yace " kai d'inne yaro ko ? Shekara talatin harda d'aya kake kiran kanka yaro saiba iya shege, duk y'an matan da kake kulawa daman ba auransu ka shirya ba yaudararsu kawai kakeyi ko, to yau anzo k'arshen shirmanka, don haka kasa aranka Aure ba fashi matuk'ar ina numfashi".

"Wlh Allah Abbah duk y'an matan nan wlh duk friends d'ina ne ni ban tab'a cewa ko waccansu zan aureta ba, kawai su suke haukansu,Abbah ka taimakeni ".

Gyaran murya yai kana ya daidaita zamansa yana cewa " Abbana kwantar da hankalinka ka fahimceni,ni na riga da na zab'a maka matar da zaka aura domin na yaba hankalinta da tunaninta,yarinyar tanada nutsuwa da kamun kai irin matar da kowane namiji ma'abocin hankali yake fatan samu to irinta na sama maka babana, gata na gaba da zanmaka a rayuwa kenan tunda na baka ishashshen ilimi Wanda duk inda ka shiga dashi ka wuce raini,to gashi na zab'a maka mace ta gari abokiyar rufin asirinka,ina Neman had'in kanka Babana akan auran kaji".

Tunda Alhj Usman ya fara Wannan maganar UK ya shiga comma ta d'an lokaci duk sai yaji kansa baya aiki brain d'insa ta tsaya cak,

"Ko baka jinane inata magana kai shiru".
Maganar Abban nasa ya katseshi,

Da sauri ya d'ago idonshi cike da hawayan tashin hankali ya rarrafa ya rik'o k'afafun sa ya fara magana," kaimin rai mahaifina ka taimaki rayuwata ka ceci farin cikina don Allah nine fa Daddynka Abbah nah baka tab'a yimin abinda bana soba baka tab'a yimin dole ba a rayuwa,komai da nakeso shi kakemin amma gashi yau zakamin auran dole, auran dole fa mata akeyiwa Abbah, matan ma marasa gata amma Abbah ni namiji D'an gata za'a yiwa auran dole,kamin rai Abbah na".

Cikin tarin takaici yace "tashi kaje d'akinka Daddy naga kanka ba dad'i naga tunaninka ya tsaya cak, jeka inka samu nutsuwa ka dawo muyi magana amma tabbas ba fashi indai ina Raye da izinin Allahu sai anyi Wannan auran".

Cikin layi da tangad'i ya wuce d'akinsa,kwanciya yai kan fadonsa idanuwansa na nuna mai komai biyu biyu, a haka bai san iya adadin tsawon lokacin daya d'auka ba a kwance anan".


*******
Tsawon kwana biyu gidan ba dad'i don Sam Alhj Usman ya d'aure fuskarshi yak'i barin kowa yazo mai da wata magana akan wannan lamarin,don Aunty murjah tana ta zuwa da zancan amma sai ya d'aure fuska yace tabar mai wajan bai son wata magana data shafi Daddy.

Shikuwa b'angaran UK yana ta fishi ko abinci bai fitowa yaci sai dai Sweety ta kai mai d'aki,duk ya rame yayi fici fici dashi, shi tunaninsa yanda Abbansu yake bala'in son su yasan in yaga ya shiga damuwa zai janye k'udirinsa,amma abin mamaki sai yaga har tsawon kwana takwas Abban bai nemeshi ba,kuma basu had'uba ko sau d'aya don tun daga ranar da akai case d'in bai fito daga d'akinsaba ko salla ma sai dai ya had'ata yayi don dama ba wani damuwa yayi yayita akan lokaci ba balle har yashiga jam'i.


Sweety kuwa duk k'aunar da takewa d'an uwanta bata damu da halin daya shigaba tasan in yayi fishinsa na d'an lokaci zai bari, don kuwa wlh a zahiri da bad'ininta take son wannan auran.

Abbah fa abin ya fara damunsa don rashin ganin d'an nasa yana damunsa,har sama da sati yana k'ulle a d'aki, gashi Aunty murjah tana fad'a mai kullum Daddy fa ramar tashi tayi yawa sai ya nuna mata bai damu ba amma cikin ransa yana jin babu dad'i amma dai dole ya daure a wannan karon ya fiddaa damuwar Daddy daga ransa.


****
Yau ummu sulaim tazo gida tana zuwa taci karo da halin da D'an uwanta yake ciki hankalinta ya tashi matuk'a nan taita kwantar mai da hankali " Haba Broth sai kace mace zaka zauna cikin damuwa haka, kaga yanda duk kamanninka suka canja,don Allah ka kwantar da hankalinka ka gane gatan da Abbah keson yi maka, kasan dai mahaifinmu bazai tab'a cutar damuba, don haka kasa a ranka zakayi mai biyayya sai Allah ya sanyaya zuciyarka".


Cikin kalan tausayi yace "kin San kuwa illar da Abbah yake son yimin, yanzu fa zab'armu akai mu goma za'a k'ara mana wani course akan business sannan a bud'e mana company a nan Nigeria, don Allah duk ba d'aukakarmu bace,amma sabida wannan auran daya k'udura a ransa yace bazan koma ba,wlh tun kafin inga Wannan yarinyar na tsaneta ban ko son ganinta balle ta shiga rayuwata,duka nawa nake da za'a durk'usarmin da rayuwata ".

Ita dai ummu sulaim rarrasinsa tai tayi tana nusar dashi akan yiwa Abbansu biyayya,sannan tace zata zauna har dare in Abbansu ya dawo zata lallameshi ta rok'a mai ya taimaka koda an d'aura auran ya barshi ya koma yayi course d'insa,don dai wata goma sha biyar kamar yaune.





Taku ce
Y'ar mutan ja'oji???j%??]?j
??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??
(Me laya kiyayi me zamani)

A
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


0(???1(???9(???


Lokacin da Abbah ya dawo bayan ya huta yaci abinci, Ummu sulaim tazo suka gaisa bayan sun d'an tab'a hira ta gyara zama cikin nutsuwa ta fara magana "Abbah daman kan maganar Broth ne,yau da nazo na sameshi cikin yanayi Mara dad'i,Wanda hakan Sam baimin dad'i, Nai mai nasiha kuma na nuna mishi mahimmancin biyayyarsa gareka da alherin da zai riska anan gaba da wannan auran,amma Abbah abinda shi broth yafi damunsa da d'aga mai hankali yamin bayanin course d'in da yake son k'arawa da alherin da zai riska a gaba inyai wannan course d'in,shine nace Abbah me zai hana amai alfarma koda auran ne a d'aura sai ya tafi yabarta anan tunda itama Khadijan karatunta takeyi,kamar yaune zaije ya dawo, a taimaka Abbah a duba Wannan maganar ".

Alhj Usman Wanda tun fara maganarta yake naxarinta ya gyaran murya a hankali ya fara magana " Ummu sulaim wato dai inna fahimceki son kai zaki nuna ko? Sabida farin cikin d'an uwanki sai in maida kaina k'aramin mutum idon mutane, mun gama magana yana dawowa za'ayi bikin sai kuma ince musu zai koma amma a d'aura aure subar y'arsu a gida ko? Har tsawon wata ba d'aya ba ba uku ba wata har sha biyar".

"A'a Abbah ba haka nake nufi ba,ina nufin in an d'aura auran saita tare da ta rink'a karatun ta cikin d'akinta tunda yarinyar tanada nutsuwa babu wani kokonta akanta ko".

Girgiza kai yai tare da fad'in " hhhhmmm ummu sulaim ke yanzu in k'anwarkice zaki so akaita gidan miji ta zauna tsawon wannan lokaci ita k'adai a gida kuma daga auran ya tafi ya barta,har yaushe suka zauna suka fahimci juna balle so ya shiga tsakaninsu um?".

Ummu sulaim da duk dabararta ta k'are tai shiru tana nazarin abinda zata k'ara k'ullawa, Aunty Murjah wadda duk ta gama jin hirar tasu tana tsaye tana harhad'a kayan dayaci abinci, ta fita ta dawo sannan ta sami waje ta zauna tana fad'in "Alhj bari dai insa baki a zancen nan dukda dai ka gargad'eni da k'ara shiga zancen, nace Alhj in da zaka sassauta ka sauko da sai ai abinda kowa ransa zai d'anyi sauk'i kuma a sassautawa Daddy,kayi hak'uri a d'aura auran ayi biki da duk abinda akeyi na hidimar aure sai ta tare anan gidan a wancan part d'in da ba kowa,shi kuma sai ya tafi d'in kamar yaune zakaga ya dawo,in tana kusa damu ina ganin bazata shiga damuwa ba tunda ga sweety saisu rink'a kwana tare".

Shiru yai yana jinjina maganar ta, kana daga bisani yace " ke ummu sulaim jeki ki kirashi ".

Ta mik'e cikin jin dad'i ta tafi kiransa, yana kwance rigingine idonshi lumshe,ta shigo tana fad'in " broth broth taso Abbah na kiranka an dai daita".

Da k'yar ya mik'e ya fito zuwa gun Abban,bayan ya zauna Abbah ya dubeshi yaga irin ramar da yai ya fita hayyacinsa,yaji ba dad'i amma sai ya dake yace "Wato Daddy sabida sunnar ma'aiki kake wannan nunk'ufurcin ko,to hakan ma yayi dai dai,yanzu dai Auntynka da y'ar uwarka,sun nema ma alfarma, kan wannan maganar,don haka yanzu za'ayi bikin da komai da komai sai ta tare anan gidan in yaso saika tafi in Allah ya kaimu lokacin dawowar taka yayi sai Ku tare a gidanku"

Cikin in ina ya fara fad'in "Abbah nifa auran ne bana so gaba d''aya ni duka banson maganar auran,don Allah kayi hak'uri ka k'yaleni da batun auran nan wlh ko an d'aura auran nan bazan tab'a son matar ba don tasa an illata ni an lankwashemin rayuwa haka kawai ni . . .

Tassss Tasss kakeji ya d'aukeshi da mari, " don ubanka ko zaka mutu sai an d'aura wannan auran,kuma ma tafiyar na fasa barinka,bazaka ba kuma in dai ina raye da izinin Allah sai anyi auran nan".

Kuka wiy wiy UK yake da idonsa, yana rok'on Abban nasu amma yasa k'afa ya mangareshi, ya wuce cikin d'akinsa.

Aunty murjah da Ummu sulaim Wanda duk suka mik'e tsaye cikin tashin hankali, Sweety ta shigo tana share hawaye ganin yanda d'an uwan nata yake kuka kamar k'aramin yaro, ta rik'oshi tana fad'in "Kayi hak'uri broth ka daina yiwa Abbah gaddama don Allah, taso ka koma d'akinka".

Itada ummu sulaim suka kamashi zuwa d'akinsa,ita kuma Aunty murjah tabi Abbah d'aki donta k'ara rarrashinsa amma tana shiga ya nuna mata k'ofa don bai son ganin kowa tare dashi.

A d'akin UK kuwa kuka yake rizga kamar anmai mutuwa,y'an uwan duk sunyi tsilli tsilli suma sai sharar k'walla suke an rasa me bakin magana, a haka mijin ummu sulaim yazo d'aukanta yai mata waya, ta fito su tafi, badan taso ba ta mik'e tana fad'in " Broth ka kwantar da hankalinka kaji zan k'ara dawowa mu tattauna da Abbah inya huce,sweety ki kawo mai copy yasha yasha paracetamol kada kansa yai ciwo, Daddyn Aslam yazo zamu tafi".

Haka sweety taci gaba da rarrashinsa tana fad'a mai kalaman kwantar da hankali ahaka bacci ya d'aukeshi sannan ta tashi ta for tafi d'akin ta jiki ba k'wari.


*****
Bayan kwana biyu Alhj usman ya sami yaya da zancan sa ranar aure da kai kud'in auran,nan yaya yace zaiyi waya da y'an gidan can sakkwato abinda sukace zai sanar dashi.


****
B'angaran UK kuwa ba sassauci ya k'ara sawa kansa tsangwama, duk yana tunanin Abbah zai gaji ya sauko,ya hak'ura shi duk mamaki ma ya kamashi akan y'ar wani Abbah zai takura d'ansa,wannan wace irin yarinya ce meye had'in iyayenta da Abbansa har ya k'wallafa rai akan aura mai ita,kai duk yanda akai mahaifinta Babban k'usa ne maybe abokin kasuwancin sane kuma yasan tabbas yafi Abbah kud'i da ido a k'asa, don haka kawai yasa a ransa Abbah wani jarin yake son d'aurawa a kansa don haka wlh bazai yarda ba Sam".

******
Yaya haroon yaiwa Babban yayansu waya ya shaida mai za'a zo kawo kud'in auran Nahna dasa rana don haka su shirya ,nan ya amsa da ba komai duk sanda sukazo a shirye suke, da tararsu.

Da dare ya kira Alhj Usman ya shaida mai yanda sukai da yayansa,ba b'ata lokaci yace to zai sanar da Abokinsa da Y'an uwansa guda biyu saisu had'u su uku suje.


Ranar lahadi da safe wakilan Alhj Usman suka d'au hanyar sakkwato bisa jagorancin yaya Usman Wanda direban Alhj Usman usman yajasu.


Tarb'a ta musamman suka samu a gun mutanan sakkwato ina kasa ina ka aje sukai ta musu , bayan sunci Abincin da aka kawo musu sunsha sunyi k'at daga nan suka fara tattaunawa kan mak'asudun zuwansu,cikin girma da mutunta juna akai komai nan suka tsaida Ranar aure wata uku suka bada kud'in aure dana sa rana 100k, haka suka taho cikin farin ciki da nisad'i na tarar da suka samu.




Taku ce
Y'ar mutan ja'oji???j%??]?j9(???
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??
(Me laya kiyayi me zamani)


0(???2(???0(???


Gab da sallar magriba suka shigo gidan don haka Allah alwala kawai sukai suka wuce masallaci tare da Alhj Usman d'in donshi yaya sauka yai tun a hanya ya wuce gidansa.

Bayan sun fito a masallaci suka yada zango a turakar Abban nan da nan aka cikasu da abinci da lemuka,bayan duk sun gama cin abincin yayan Alhj Usman ya fara sanar dashi duk yanda sukai da irin yarar da suka samu a gun surukan nasu,nan abokinsa ya d'ora da fad'in " Ai Alhj Usman kayi dace da surukai masu mutunci da addini, domin kuwa sun mana tarb'a ta k'warai,mun dai daita auran nan da wata uku cif insha Allah ".

Cikin jin dad'in duk maganganunsu ya fara magana " hak'ik'a naji dad'in albishir d'inku, daman nasan tabbas duk inda Nahna Khadijah ta fito babban gida ne,dukda bansan dangintaba bayan yayanta,amma sweety ta sanar dani lokacin da sukaje biki ta shaida min karamcin zuri'arsu Khadijah to gashi yau na k'ara tabbatar da hakan daga bakinku, tabbas na sani komin dad'ewa wata rana Daddy zaiyi alfahari da auran Khadijah ".

Nan sukaita tattaunawa Baffah yace " Usman ina Daddyn yake inmai albishir da samun gidan surukai manyan mutane".

Jinjina kai Abbah yai kana yace "Baffah ai Daddy baya son wannan auran dole nake mai. . ."
Nan ya zayyane musu komai daga farko har k'arshe,

Duk kuma sai jikin su yai sanyi Baffah yace " ka sasauta mai dai Usman kabi a sannu kaita mai nasiha,da kansa zai fahimci alkairin abin,sannan maganar komawa da zaiyi kayi tuni kan maganar dai karkace zaka hanashi kaji ko".

"To Baffah za'ayi yanda kace insha Allah".

" yawwa sannan ka turomin shi gobe ko jibi zan k'aramai nasiha da Jan hankali".

"To ba damuwa zan turo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login