Showing 126001 words to 129000 words out of 137542 words

Chapter 43 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

gidan ya sarara kowa ya tafi,y'an aiki duk sun gyara ko ina,
Aunty murjah ma tana b'angaran Abba yasa muka k'ara baje kaya ni da sweety tana ganin kayan, nikam inata tsokanar ta ita dai duk jikin ta a mace yake,sallamar UK parlour d'in yasa muka kalli k'ofan a tare, muna had'a ido ya sakar min harara y'ar dariya nai ina mik'ewa gareshi tare da mai sannu da zuwa,"A'a ni kam ba ruwana dake yau gaba d'aya kin manta dani ina ta kiran wayar ki ma bikiyi picking ba".

Marairaicewa nai ina fadin "hubby nah wake mantawa da zuciyar sa,dukkan abunda nakeyi ruhina na tare da kai gangar jikin ce kawai anan ".

Lakuce min hanci yai yana fad'in" um dad'in baki dai da wayo za'a min kawai".

Kad'a ido nai tare da rik'o hannun sa nace "zoka zauna ka kalli kaya kafin in had'ama abunda zaka ci".

Nan na barshi tare da sweety na wuce kitchen da azama na fara shirya mai plate daman na riga na ajiye mai abincin daran da naiwa Abba, tuwon semo da miyar d'anyan kub'ewa da taji tantakwashi.

Center table na jawo mai gaban sa na shirya mai abincin akai,bayan ya fara ci na shiga d'ad'd'aga mai kayan yana kalla,jinjina kai kawai yake yana yabawa tare da addu'ar fatan zaman lafiya ga ango da amarya.



Sai wajan sha d'aya muka zagayo gidan mu,kai tsaye toilet muka wuce mukai wanka tare da alwalan kwanciya don neman kariya daga shed'anin mutum da aljan.

Muna kwance hira muke tab'awa kad'an kad'an yana matsa min jikina dake min ciwo sabida gajiyan yau,cikin tsokana yace" wato ko ki tambayeni ma yau ina na tsaya sai taran dare kika ganni".

Cikin rashin damuwa da batun nace"Ai nasan don kasan muna hidimar mutane ne baka shigo da wuri ba,don koda ka dawo ma a hidimce zaka ganni,lokacin daka shigo ma ban dad'e da gamawa Abba abinci ba".

"Hhhmmmm yarinya shi yasa nima nai tafiya ta tad'i don nasan in na shigo ma gidan da wuri bakya nan".

Da sauri na tashi daga jikin sa cikin fargaba nace " me kace?".

Cikin dakewa da basarwa yace"Naje gun k'anwar ki ne tace ma in gaida ki sosai".

Jinai wani mashi ya soki zuciya ta da k'arfi,amma cikin y'an seconds nai tunanin wace ce ni,mace me aji nake,don haka na d'an murmusa tare da fad'in "hhhhhmmm ina amswa sosai nima ina gaishe ta sosai".

Kaina na maida jikin sa na kwantar, zuciyata na wani irin bugu.

Mamaki ne ya kamashi ganin yanda na dake duk da yasan tsananin kishin da nake dashi,a zahiri yaga firgici tare dani amma kuma sai furucina ya nuna ban damu ba, cikin son k'ara jan zancan yace" biki tambayeni wace ba kuma ya sunan ta sannan a ina take ba".

K'ok'ari nai na fizgo kalmomi daga bakina nace" hhhmmmm ai wannan duk ba hurumina bane,in ma kuma ina da hurimi dasu nasan in lokaci yai zanji ai".

Daga yanda nake furta maganar yasan nazo wuya kawai b'oyewa nake k'ok'arin yi. Amma kuma sai yaji ba dad'i da ban nuna zafin kishi kansa ba,

D'ago ni yai zaune shima ya zauna tare da fad'in "Da wasa nake miki my life karki d'auka da gaske fa".

Kallon k'yar namai tare da fad'in" Ko da gaske kake ba abun damuwa bane ko b'oye b'oye, na dad'e ina fad'a maka ban marmarin rayuwa da kishiya a rayuwa ta,amma in har akwai zama da kishiya cikin rayuwar aure na to zan zauna da ita tsakani da Allah kuma in amsa kaddara ta hannu biyu, kuma ai zuwa yanzu daman ya dace ka fara neman aure ko don samun Baby kaga sai damuwar ka ta tafi akan son haihu. . .".

Da sauri ya rufe min baki yana jawoni jikin sa sosai, tsawon minti guda sannan yace " Wlh Allah da wasa nake miki Khadeejah, kin sani nasha fad'a miki ban ra'ayin tara mata matsayin nawa,sam sam banda wannan ra'ayin balle har kike cewa wai kodan in sami Baby, kina nufin har anzo matakin da zan miki kishiya don biki k'ara haihuwa ba? to kima cire wannan daga ranki wlh duk abunda nake nema nadaga yaya fata na su zamo daga gareki, kodan samar musu da kyakykyawar rayuwa me cike da nutsuwa da tarbiya, ni da wasa nake mu bar wannan maganar ma don Allah ".

Yana gama fad'a ya koma ya kwanta tare dani a jikin sa, nidai lumshe ido kawai nai zuciyata ba dad'i duk da kalaman da yai yanzu sun Dan samun nutsuwa da kwanciyar hankali amma sai nake jin zuciyata cikin kishi sosai".


A haka bacci yai gaba damu,Wanda bamu farka ba sai asuba, bayan mun idar da salla munyi azkar wanda shi ya ke karantawa da fassaran hausa don bai haddace su duka ba,shiyasa na bashi littafin yake amfani dashi.

Tsawon 30 minutes muka shafa na jiyo ina gaisheshi kamar kullum ya amsa min cike da kulawa sannan ya k'ara k'asa da murya sosai yace" my life kiyi hak'uri da maganar da nai miki jiya Allah wasa ne kawai nake miki".


Mirmishi bayyane kan fuskata nace "lah nifa har nama manta da wannan issue karka damu nasan raha ne kawai ka ke yi".

Shafa kaina yai cikin nutsuwa yace" masha Allah, Allah yai miki albarka mata ta".

Cikin jin dad'in Addu'arsa na amsa"ameen ameen my zaujee,Allah ya kare min kai daga dukkan abun k'i ya faranta rayuwar ka duniya da lahira".





********************
Abun fa yazo, don yau ne Alhamis za'a saka Sweety a lalle, tun safe ban gida duk da gidan nawa cike yake taf da k'awaye da y'an uwan su,duka d'akunan k'asa da parlour sun baje suna bidirin su, shigowa ta daga wajan saloon kenan na zauna tsakiyar su muke gaisawa da d'an hira,wasu da yawan su na san su,wasu kam yau na fara ganin su,dukkannin su y'an mata ne sai mutum biyu da na gani da yara hannun su,da kuma wata shukra ita bazawara ce, raha sosai muke dasu ana hira, na kira lami nace su kasance a part d'in sabida kula da hidiman bak'i da gyara waje, cike da girmamawa ta amsa da fad'in "To uwar d'akina an gama insha Allah".

Daga bayana naji an saki wani siririn tsaki,juyawa nai idona ya fad'a kan Zee yarinyar Aunty uwani,wanda tun shigowa ta ma ban kula da ita a wajan ba,d'auke kai nai daga gareta ina cewa Lami " shi kenan jeki".

Ta mik'e ta tafi,nima tashi nai ina ce musu barin
in d'an watsa ruwa.



******Tunda na shiga d'aki nake tunanin wannan karon zan koyawa zee hankali,sabida duk sanda muka had'u wajan wani taro nasu ko a kano ko a katsina sai taita min tsaki tana hararana ta gefan ido, tun ban gane me nai mata ba,har na fara fuskantar tsakanin ta da UK don da ta ganshi zata fara wani rausaya da rangwad'a tai ta shige mai,babu Wanda ya sanar dani da kaina na fahimci hakan,don haka nasa a raina zan daina koda kulata bare ta rink'a min kallon banza.





************k'arfe biyar aka fara gudanar da kamu a wani babban fili na Abba dake cikin layin namu can k'asa.

An shirya wajan da kayan al'adar hausawa komai yayi gwanin birgewa, yayin da aka d'auko makad'an k'warya na gidan sarki suke cashewa.
shigata nai cikin wani sari riga da siket da mayafin sa, har da sark'a da D'an kunne kalan sa don akwati guda UK yai min na kayan fitar biki kamar yanda yai wa kansa ma,kuma duk yawanci kayan namu kalansu d'aya ne, nai kyau badan san kai ba sai dan sanin cewar nayi kyau d'in. duk in da na ratsa za'a ce kai kinyi kyau, mirmishi kawai nake nace "na gode".

Ina lura da Zee da hararar da take wurga min tunda na shigo wajan,kallon arziki bata isheni ba,don haka sabgar gabana kawai nake yi.kasancewar wajan ba maza sai yara kawai yasa muka cashe abun mu,amarya ta fito na balle bandir d'in kud'i inata mata lik'i itama bud'e pos d'in ta tai ta fiddo kud'i ta shiga maida min martani,ganin haka yasa Aunty ummu sulaim itama tazo tanata mana lik'i ai kuwa sai akai rubdugu cikin filin ana mana watsin kud'i, masa kid'an kwarya fa sun ga abun nema sai suka sake dagewa da sakin sabon kid'a.
Zee ji tai kamar zata mutu don takaici,haushi taje ji in taga family d'in su na nan nan dani kowa sona yake wanda na tabbatar kyautatawar da nake musu ce tasa suke k'ara k'aunata,ita kam takaicinta yanda nake ba y'ar boko ba ba wata me bud'ad'd'an ido ba amma na iya zama da mutane da siye zuk'atan su,(bata san ba anan take ba,iya zama da mutane baiwa ce,kuma hankali da nutsuwa ke sa ka fahimci kowa ka iya zama dashi gwargwadon halin sa)

Tai nisa cikin tunani hassada da kyashi taji an dafa bayan ta,juyowa tai taga waye wata cousin sis d'in ta ce wadda halin su yazo kusan iri d'aya, tace"sis ya kike zaune anan duk son ki da rawa ga jama'a nata cashewa ?".

Yatsina fuska tai cikin takaici tace "A'a filin ba irin namu bane,naga kucakai sun cika wajan".

Dariya Khairy tai yace" Hhhhhhhh nasan kuma da wa kike,wlh karki sa damuwar wannan yarinyar ta hanaki walwala wajan bikin da kika ci burin rak'ashewa".

D'an tsaki tai tace "ke ni wlh fa ko son kallon ta bana yi sam yarinyar nan bata min ba,ai Broz ya tafka asara wlh duk ajinsa ya k'are ga wannan yarinyar".

Rashin abun yi yasa suka ita gulmar su,nikam inata rak'ashewata da walwala banma San suna yi ba.

Sai magriba aka tashi daga kamun.



***********duka gidan nawa muka rankayo da su,ni dai bayan na tabbatar nasa su lami sun ajiye musu duk abun buk'ata sama na haye don yin salla.


Wanka na fara yi sannan na d'auro alwala bayan nai sallar na d'an shafa creem tare da perfumes d'ina, riga da sket English wear nasa wanda suka zauna jikina d'as na sanya hula kan kitson da aka yarfa min tamkar na barebari,don tabarakallah gashi a kaina kam ba'a magana, ganin har lokacin UK bai shigo ba yasa na k'ara sakkowa k'asa, nan na same su sun baje a parlour suna cin abunci wasu na hira,wasu na danna waya,tsallakawa nai kusa da Ikee na zauna ina tsokanar ta" manya gatan wasa ke baki cin abincin ne?".

Y'ar dariya tai da fad'in "Auntyn mu wlh banjin yunwa ne kawai a gajiye nake jina".

" Ayya sannu,to ko ruwa za'a had'a miki me d'an d'umi kiyi wanka,maybe gajiyar zaman mota ne".

Lumshe ido tai tace "Eh yanzu zan yi wankan in kwanta,waya nake son in gama".

Dariya nai da fad'in" hhhhhmmm ashe soyewa ake yi nazo na zauna,bari in canja waje to".

Dariya duk akasa,nan muka shiga hira da labarin yanda kamun yau ya kasance.

Da gudu gudu Sweety ta shigo parlourn tana fad'in "Aunty na Aunty na".

Cikin kulawa nace " ya akai Amarya?".

"Zo sirri ne abun taso mu matsa kar way'annan yaran su jimu".

Dariya wasu suka sa yayin da wata cousin sis d'in tace" Eh lalle yarinya nuna mana zakiyi kin girma za'a miki aure shi yasa kike kiran mu yara".

Gwalo tai mata da fad'in "Eh d'in fa ba yaran bane ku,amma banda Shukrah da Aysha da Ummy su sun girma amma duk ku d'in nan yara ne".

Ni kaina dariya nai ina mik'ewa don jin sirrin me zamu yi, caraff cikin kunnena naji yo wani lafiyayyan tsaki Wanda babu tantama nasan daga bakin wa yake don haka ko juyawa banyi ba sai Sweety ce tace " Wai ke Zee meke damun ki yau duk na ganki a wani cunkushe ?".

Harara ta watsa mata da fad'in "ba case d'in Ki bane wannan".

Tab'e baki Sweety tai ta rik'o hannu na muka haye sama.

Cikin damuwa ta kalleni bayan mun zauna tace " Aunty nah Allah wannan abun da kika bani nasha yana bani matsala fa".

Cikin dariya nace "Matsalan me ?".
Marairaicewa tai da fad'in" Ni gaskiya bazan k'ara shan komai ba Allah, kinji yanda nake jik'ewa kamar me period, gashi sai injini in feelings ko yaushe, har ji nake kamar ana tsankwalina wlh".


Dariya nai sosai nace "To ai shine gyaran mana Sweety, ko yaushe an fi son mace a jita da danshin ni'ima ba abushe k'amas ba,kin ga kayan nan tun daga gun Sis Nasmat y'ar mutan ark'illa sokkoto nasa aka aikoshi,don ko yaushe ina jin yanda y'an group ke zuzuta kyan kayanta,koni danai amfani dasu na tabbatar da ingancin su, don haka karki damu kiyi ta amfani dasu,Allah zaki zama sarauniyar mata a zuciyar Angonki,domin gyara shine mace,ke Sister in low ce dana bud'e miki zancan kin gane".
Na k'arashe maganar da dariya, turo baki tai da fad'in" A'a ni kam basai an bud'e min ba,Wanda ma ake min bita kullum sun isheni,kin kaini group d'in matan aure ma kullum sai lecture suke kin suna karar min da ruwan kai na".

Tare mukasa dariya dai dai lokacin UK ya shigo yana fad'in "Gulma dai ta kusa k'arewa daga ran lahadi, kullum sai Ku k'ule d'aki kuyi ta gulma".

Dariya mukai ita da Sweety ta mik'e tai downstairs,k'arasowa yai ya zauna kusa dani yana matsa cinyata yace" kun bar bak'in Ku a k'asa kunzo kunata gulma,wai me kike fad'a mata ne kullum yanzu na ganku tare kuskus kukeyi".

Kashe mai ido nai nace "Abun sirri ne tsakanin mu oga".

Matse min hannu yai har nai y'ar k'ara yace" Akwai wani sirrin da za'ai da wani bayan wanda akeyi dani,ni dai Allah yasa ba bata labarin ihun da nake cikin dare ake ba,don Ku mata in za'ai wa yarinya aure sai kuyi ta fad'a mata sirrin ku wai don itama ta rink'a yin haka a gidan mijinta".
Serious na koma ina kallon shi nace "kana tunanin ina cikin mata masu bayyanar da sirrin Auransu? Duk duniya babu wani mutum da zan iya shearing sirrinka dashi duk kuwa yanda muke dashi,rashin ilimi kesa mace bayyanar da sirrin kwanciyar auranta ga wata, ban ce ma mata in sun had'u basa wannan hiran ba amma gaskiya yawanci bita ne mu keyi tare da k'ara wayarwar da junan mu kai kan rayuwar aure da matsalolin cikinta".

Numfashi ya saukr yana fad'in" Yawwa hakan ai yafi, amma ka gama shagali cikin dare da safe a bawa k'awa labari ai an tsiraita ka".

Dariya nai kawai ina kauda zancan ta hanyar fad'in "In had'a maka abunci?".

" A'a bari nai wanka tukun".

D'aki muka wuce don na had'a mai ruwan wankan.




______________Washe gari jumma'a da yamma akai fulani show da dare akai dinner, Ranar asabar kuma akai yini wanda shima a gida akai filin Abba, da dare muna zaune tare da amare UK ya shigo parlourn daga bakin kofa ya tsaya yana kira na,yaron Aysha ne a hannu na,ina zuwa ya amsheshi tare da fad'in "Ki kawo min jakan ban dana baki ajiya me ita yazo".

Nace " OK " tare da juyawa zuwa sama.

Gefen kujerar da ba kowa ya samu ya zauna yana wa yaron wasa yace "Aysha Naeem sa'an little ne ko?".

Amsa mai Aysha tai da fad'in" Eh little ma ta bashi sati biyu".

Gyad'a kai yai da fad'in "Da tana raye da tuni itama fa taba tafiya,yanzu shekara guda da wata uku kenan da rasuwar ta".

Sakkowata ne ya dakatar dashi ya k'arb'i jakan tare da mikomi yaron ya fita.

Ban san hiran da sukai ba ni dai bayan na zauna dai naji zee ta kalli Ikee tana tab'e baki da fad'in" Wato sis in baki labari wata ce a group chart d'in mu tai aure tsawon lokaci bata haihuwa ba,bayan wasu shekaru ta haihu sai d'an nata ya rasu kuma gashi mijin nata yanzu bala'in son haihuwa yake, kuma ita ta zama juya don haka mijin harya fara tunanin k'arin aure amma dalilin an shanye shi ya kasa furtawa,wai shine take neman shawara ya zatai,don tasan duk randa aikin da ta ke yi a kansa ya karye tana cikin tasku".

Dariya Ikee tai tace "yo shi aikin asiri duk yanda ta kai ga sabun tashi wata rana zai karye k'ara ma ta barshi yai auran sa tun da wuri ".

Dariya Zee tai tare da mik'a mata hannu suka tafa tace" ai kuwa bari in bata shawarar nan taki".
Kamar gaske ta kunna waya ta shiga dannawa kamar tana typing wani abu.

Ni dai ko yarinya ce nasan dani Zee take,amma ko a fuska ban nuna na fuskanci zancen ta ba,sai Aysha tai k'ok'arin sa musu baki a zanjan nasu da fad'in "To banda abunku ai haihuwa Allah ne ke bada ita,kuma wlh yanzu ma ba kowane namiji ke son haihuwa a kufe a kufe ba".

Tanka musu da Aysha tai ya basu damar jan zancan sukaita yada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login