Showing 42001 words to 45000 words out of 137542 words

Chapter 15 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

sallar ishan, yau ban tayasu hiran da suke ba don a gajiye sosai nake don haka gado na haye na lumshe ido bacci nasan d'aukata,amma kafin minti biyu wayata ta fara ringing kamar bazan bud'e idon ba haka na daure na bud'e ina kallon kan wayar bak'uwar number ce banyi tunanin komai ba na danna tare da sata a kunne na sanyin muryata ya had'u da baccin da nakeji ya k'arasa muryar yin sanyi matuk'a, sallama nayi tare da saurarawa don jin waye, shuru naji anyi na y'an dak'ik'u sannan naji anyi magana cikin gadara da isa " ki fito k'ofar gida ina jiranki kuma karki b'ata min lokaci".

UK ne na fad'a cikin raina don har abada muryarsa bazata tab'a b'acemin ba to me zan masa me ya kawo shi guna yanzu kuma?

Banda amsar bawa kaina don haka na mik'e jiki ba k'arfi nasa zumbulelen hijabi kan kayan baccin dake jikina,tambaya ta suka farayi ina zani ban kalli ko waccen su ba nace " ina zuwa kirana ake a waje yanzu zan dawo ". Nasa kai nai waje . . .




Taku ce
y'ar mutan Ja'oji ???j%??]?j

??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??


ALLAH KAI MANA MAGANIN ABINDA YAKE DAMUN MU ALLAH KA SHIGA CIKIN LAMARINMU???a



0(???2(???6(???



Jin Hannun Hafsah a kafad'ata yasa na juya ina dubanta,mirmishi tai min tana fad'in "Angon yazo ko? Kinga ya dace mu wuce yanzu gashi har 8 ta wuce ".

Jin abinda Hafsah tace yasa me kwalliyar yin dariya tana fad'in " Amarya Bari mu kwarara miki turare dukda naji sirrin humrah tare dake gaskiya daga ji me gyaran jikinki tayi amfani da zafafan turaruka wajen gyara ki".

Hafsah ce ta tanka mata ni kuwa ban iya cewa komai ba har zuwa sanda ta d'auko kwalbar turare ta fara min feshi kamar ance ta k'arar dashi a jikina, net ta d'auko me taken one million Stone shima ta feshi shi da turaren sannan ta yafa min akaina wanda hakan ya bawa fuskata damar d'an sakayawa shima net d'in babbane sosai ya zuba ta baya,ta gaba kuma fuskata da k'irjina kawai ya rufe,

A hankali nake takawa kasancewar takalmin yamin tsini da yawa,gefena Hafsah d'aya gefen me kwalliyar ce ta rik'emin hannuna,tun kafin mu k'aroso bakin motar abokinsa dake driving ya dannan pin nan take mirfin motar ya bud'e, fitowa Angon yayi cike da fara'a d'auke da fuskanshi hannayensa biyu yasa ya ruk'o hannayena yana lek'a fuskana ya d'ago yana mirmishi me kwalliyar tace " Angon kasha k'amshi ga amaryarka nan nai Mata bridal makeup don k'ara fito maka da ita".

Alamar jinjina yai mata tare dasa hannunsa a aljihu ya ciro kud'i yana mik'a mata yace "ga tukwicinka nan don wannan kwalliyar ta cancanci tukwici bayan an biya kud'in ta ".

Dariya tai tana mai godiya ta juya ta koma, shi kuma yana rik'e da hannayena ya sakani cikin motar, Hafsah gaba ta zauna bayan ya rufe motar Hafsah ta juyo a hankali tana fad'in " Ango barka da dare ya taro"?.

Cikin d'an sakin fuska ya amsa mata,kafin ta kuma magana Abokin Angon yace cikin tsokana "wato Sabida ni ba ango bane shine baza'a gaisheni ba ko k'awar Amarya".

D'an mirmishi tayi tana fad'in" Ah Afuwan ba haka bane kaima zamu gaisa mana,ya taro ya fama da jama'a".

Nan ya amsa cikin tsokana ya juyo gareni yana fad'in " Amarya ansha k'amshi ya taro".

Kaina a k'asa gabana nata fad'uwa, ina k'ok'arin amsa mai Yai caraf ya amshe " Kai dalla rik'e gaisuwarka bama buk'ata, wayon kaji daddad'ar muryar mata ta ne to na amsa Mata".

Dariya Abdushshakur yai yana tada motar ya cilla ta kan titi cikin gwanancewa,

K'amshin turarena daya cika motar taf ya shak'a tare da lumshe ido kasancewar sa me matuk'ar son k'amshi, yana bud'e ido suka had'a ido da Abdushshakur ta madubi ya kashe mai ido yana fad'in yadai my friend ko har ka. . . ." da sauri ya rufe baki yana dariya,

Hararansa yai yana cewa "wlh ka lalace dasa iso friend ban sanka da haka ba fa".

K'ara matsowa kusa dani yai sosai jikinmu na gugar juna yake yima Abdushshakur gwalo tare da fad'in ka daina kallon mu fa Malam". Bakinsa yasa dai dai kunnena yana magana cikin rad'a" Ke karfa kiyi wani tunani cikin ranki game ne kawai zamu buga kuma wlh kika bari aka miki game over zamu had'u,k'ara kiyi iya yinki ki fiddani kunya kinji na fad'a miki ".

"Hhhhmmmm daman nasan za'a rina ni nasa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n ba saduda yayi ba kafiya kuma irinta UK amma ba komai Allah yana tare dani ai".

Music me dad'i Abdushshakur ya kunna cikin motar tare da k'aro Sanyin A.C nan motar ta wani shika da nishad'i,tunda muka shiga banyi k'ok'arin d'ago fuskata ba yanda take a lullub'e haka na saddata k'asa har muka isa MEENA EVENT CENTER nan motar mu tai parking a compound d'in gun duk sauran abokansa suna waje don jiran isowarmu, motar sweety ma tana wajan tana ganin isowaemu ta shiga ciki domin fito da sauran y'an matan da zasu shigar da Amarya da ango,
Duka y'an matan anko ne a jikin su yayin da mazan suke da shiga mabanbanciya, muna zaune cikin mota sweety ta shirya gun ko wace mace da namiji kusa da ita,yayin da gaba aka jera plower's baby's guda shida,
Ana mana izinin fitowa ya danna pin Motar ta bud'e shi ya fara fita sannan ya kamo hannu na ya fito dani muka tako a nutse hannuwanmu suna sak'e cikin na juna, muka shiga tsakiya gabanmu y'an yara bayanmu emmata da samari muna k'arasawa kusa da hall d'in aka saki kid'an police Band cikin taushi dasa jiki ya motsa, nan fa y'an yaran suka fara takawa cikin rausaya Kai haka ma emmatan da samarin , muna shiga ciki fa waje ya rud'e da ihun zuwan amarya da ango, a tsakiyan fili muka fara tsayawa nan aka shiga mana b'arin kud'i waje ya rude da rawa da lik'i, min dad'e tsaye m.c ya buk'aci kowa ya koma ya zauna a mazauninsa abar Amarya da Ango kad'ai a tsakiyan filin,
Nan kowa ya koma mazauninsa muka rage mu kad'ai tsakiyan filin ai kuwa ziciyata taci gaba da bugawa da sauri sauri ganin yanda ya k'ara matsowa kusa dani sosai, m.c ne ya buk'aci Ango daya bud'e fuskar amarya,ai kuwa cikin wani salo yasa hannuwansa biyu ya d'age net d'in dake rufe da fuskata k'asa sosai na k'ara yi da kaina ya d'ago da fuskana fuskanshi d'auke da mirmishi ahankali na lumshe idanuwa,nan wani annuri da asirtaccen kyau ya k'ara bayyana tare dani, yarrrrr yaji a jikinsa yana tunanin anya wannan y'ar Arabic ce kuwa,sosai ya zuba min ido don tabbatarwa a zahiri dai yana hango kamannina a fuskana amma wannan tsananin kyanfa daman haka wannan yarinyar take da kyau kodai makeup d'in nan ce tasa tai wannan tsananin kyan. . .

Ihu da tafin daya cika wajan ne ya dawo dashi tunanin daya shiga ai kuwa yaji wata bala'in kunya ta kamashi amma duniyanci Irin nasa da nuna shi wayayyene yasa kawai ya bud'e babbar rigarsa ya sakani a ciki tare da hugging d'ina yana dariya, nan duk friends d'insa na gida Dana k'etare sukayo kanmu da sabon lik'i suna b'arin manyan kud'i don nuna kara ga abokin nasu, ganin yanda mazan suka kewaye mu naji wani sabon fargaba da ta k'ara lullub'eni ai kuwa ban san sanda na kifa kaina bisa k'irjinsa ba tare da kewaye hannuwana jikinsa,wani k'ara rungumeni yai yana shafa bayana tare da kashe wa abokansa ido cikin shak'iyanci ai kuwa waje ya k'ara rud'ewa da ihu m.c ya samu abinyi fad'a yake yana k'ara fad'a"gaskiya wad'annan ma'aurata sun dace da juna Allah ya kawo zuri'a ta gari Allah yasa wata Tara masu zuwa muzo shagalin suna". Masu video fa hotuna suka shiga aikinsu na d'auke d'auke.

Mun d'au tsawon lokaci sannan m.c ya bamu damar zuwa mu zauna nan ya ruk'o hannu na muka tafi gun zamanmu muka zauna a high table,anan na k'are mai kallo shima kayansa kalan nawa ne light blue shadda d'inkin babbar riga da y'ar ciki babbar rigar irinta samarin Zamani y'ar k'arama dai dai jikinsa, idonsa sanye da farin glass kamar yanda ala'adarsa take,sai wata hula zanna me tsadar gaske da akewa lak'abi da minister kalan kayan nashi, hannunsa sanye da agogon vansar chairman world, sai k'afarsa sanye da bak'in takalmi south, duk a cikin abunda bai kai minti d'aya ba nai mai wannan kallon.

Nan akaci gaba da gudanar da event d'in cikin aji da nishad'i,zuwa d'an lokaci aka fara raba abinci ganin duk hankalin jama'a ya bar Kansu yasa ya sunkoyo sosai yana min magana cikin kune "Hhhhmmmm yarinya taga faffad'an k'irji shine harda wani lafewa a ciki to k'walelanki wannan k'irjin na matar zab'in raina ce ba matar tushe ba ".

Ganin masu Neman abinyi sun fara d'aukanmu a hoto yasa ya janye jikinsa yana wani mirmishi, Wanda nima mirmishin ne d'auke a fuskata wanda ban san name ne ba.

Sai misalin k'arfe sha d'aya aka tashi, yanzuma motar Abdushshakur muka hau Hafsah a gaba kamar yanda muka zo,
Bayan sun ajiye mu k'ofar gida ina shirin fita a motar ya rik'o hannuna yana magana k'asa k'asa " yau kin fidda kanki kunya sai kuma Sunday shima kiyi k'ok'ari kinji ko".

Ganin Abdushshakur na kallonmu yasa na gyd'a mai cike da gajiya wanda zakai tunanin shagwab'a ce.


Koda na shiga cikin gida tsokana ta akai tayi wai mun kasa hak'ura zuwa jibi gaban jama'a muke rungume juna, mirmishi kawai nakeyi ba tare dana tankawa kowa ba.

Washe gari asabar akai culture day tun k'arfe biyu ake gudanar da wasannin gargajiya da al'adu a filin wasa na Ahmad Musa sannan zuwa k'arfe hud'u aka wuce lunch sai bayan sallar magriba aka dawo.

Yau lahadi kuma akeyin Mothers day yau kam mu ba fita zamuyi ba a gida muke yinin mu inda muka yini masu kid'an k'warya suna cashewa, tunda naga anyi sallar la'asar fa jikina ya fara mutuwa naji zuciyata ta narke duk y'ar walwalar dake tare dani ta kau na koma jugum,

Ina jin kiran sweety a waya kuwa tana fad'awa Aziza ta fad'a a cikin gida ana sallar magriba fa za'azo d'aukan amarya nan jikina ya k'ara sanyi hawaye suka fara bin kuncina duk k'awayena ma sai jikin su ya mutu da sauran y'an matan, kayan takaici da rawar kai Irin na abokan UK wai tun kafin akira magriba suka fara zuwa d'aukan amarya ance sunzo da wuri wai sai ca sukai eh duk nuk'u nuk'u da fad'an da za'a yiwa amarya ayi mata kafin suyi salla su fito don ana idar da sallah zasu d'au amarya.
Nan fa na rikice da kuka wiwi na k'udundune cikin d'akin Aunty Hafsah ina matsanancin kuka me shiga rai, Iyayena suna zaune tare dani suna k'ara min nasiha kan hak'uri hak'uri dai nikam kuka kawai nake Aunty Hafsah ta shigo d'akin tana fad'in "Nahna tashi kiyi wanka kiyi salla Kinga an fara kiranvsallar".
Mik'ewa nai cikin jan hanci na shiga toilet wanda daman an gama had'amin ruwan wankan,ina wankan ina kuka saida naji ana min magana in fito haka na hak'ura na fito tare da d'auro alwala, ina sallar ma ina kuka haka naita addu'a a sujjadata ta k'arshe ina rok'on Allah yasa min albarka a cikin rayuwar aurena,
Ban wani sa komai ba humra kawai na goga a jikina nasa kaya aka fito dani ina fitowa Yaya Haroon na shigowa ya koro yara da suke bin motocin da suka d'auki y'an kai amaryar, fad'awa nai jikinsa ina kuka ya rungumoni yana bubbuga bayana shima duk zuciyarsa ta karye, cikin sanyin jiki yace " Kiyi shuru Autah kinji ki daina kuka haka Allah yai miki albarka Allah ya baki zuri'a me albarka Allah yasa farin ciki cikin rayuwar ki ".

Muryarsa ce ta fara rawa don haka yai shuru tare da jawoni zuwa waje da kansa ya sakani cikin motar yana shirin juyawa na ruk'o hannunsa ina fad'in " Yaya na ka yafemin ja yafemin don Allah ".
Janye hannunsa yai cikin nawa yana shafa kaina tare da d'an mirmishin yak'e ya juya da sauri jin idonsa ya ciko da k'walla".

Duk wanda ke wajan saida ransa ya sosu haka umma maman su yaya Haroon ta shigo ta zauna gefena yayin da k'anwar mama ba na ta zauna d'aya b'angaren Hafsa Aminiyata kuma ta shiga gaban motar aka cilla damu,shike nan na bar gidanmu wayyo Allah na.

Muna sauka a mota na shak'i k'amshin iskar gidansu sweety naji wani fad'uwar gaba,yanzu shikenan nan ne fa gidanmu, cikin kunnena Umma tace " maza yita addu'a kinji Khadijah Ke malama ce yi addu'a ki shiga da bisimillah kinji".

Cikin raina naita addu'oi ina neman tsari da dukkan fitinar da take gidan tare da neman Alkairan gidan tare dani, bisa al'ada cikin gidan aka shigar dani wajan iyayensa, parlourn cike yake da manyan mata masu aji da izza kallo d'aya zaka musu kasan ko wanne yana ji da kansa a nera, bayan gaisuwa ga juna umna ta fara mik'a amanata garesu " To Y'an uwa ga Nahna Khadijah nan mun kawo muku ita ta zama y'ar ku,Khadijah dai duk wanda yasanta yarinya ce bame fitina bace ko cikin y'an uwanta halayyarta daban take,amma yanayin rayuwa koda zaku ga wani abin k'i daga gareta Ku mata fad'a Ku nusar da ita tunda yarinya ce k'arama, mun baku Khadijah bisa amana kamar yanda muke kyautata zaton zata sami Duk wani kula daga gareku kamar tana tare damu".

Wata mata ce cikin isa da nuna ita wata ce ta fara magana" OK duk munji baya nanki kuma muna fatan Allah ya bamu ikon rik'onta ,amma dai Ku cigaba da yiimata fad'a don kun san rayuwar ta data Daddy ba d'aya bane ,maybe zai iya yin wani Abu taga kamar yai mata ba dai daiba so dole tayi hak'uri dashi tunda tsarin rayuwar sa duk cikin manya yayi ta,to Allah ya tsara madai itace matar sa amma mun so k'warya tabi k'warya. .
Da sauri wata matar ta katseta da fad'in "Haba Aunty iyami wannan ba girmanki bane meya kawo kad'an nan maganganun haba bai dace ba wlh,gaskiya biki kyauta ba ai yanzu Duk mun zama d'aya tsakaninmu dasu Khadijah tunda aure ya shiga tsakani".
Kafin itama ta k'arasa abinda zata ce Aunty murjah ta fito tana fad'in " Ku shigo da ita Abbansu yace a k'araso mai da ita su gaisa".
Son jin gulma dame za'a fad'a yasa Aunty iyami mik'ewa ita da wata magulmarciyar irinta suka bi bayanmu zuwa b'angaran Abbah wanda zuwa lokacin Duk raina ya gama b'aci matuk'a da maganar Aunty iyami ta k'arshe don haka na rik'e sunanta tsam cikin raina don nasan zaman da zanyi da ita.

A gun Abbah kuwa tarb'a muka samu sosai don da fara'arsa ya taremu yana cewa kowa ya zauna akan kujera ganin su umma na zama a k'asa,nikam a k'asan na zauna ina k'ara duk'un k'une kaina, "zo matso kusa dani Khadijah karki zauna a can "

A hankali na tashi na k'arasa gabansa na zube ina gaisheshi cikin muryar kuka,dafa kaina yayi yana cewa "Yi shuru bar kunan haka y'ata y'ar albarka ban son ganin hawayenki".

Gaisawa sukai dasu Umma yanata tambayarsu ya taro ya hidima , su kuwa cikin jin dadin irin karbar daya musu suke amsawa, nan ya shiga musu godiya sosai ya k'aramin nasiha sosai " Khadijah kiyi hak'uri da dabiun Daddy kinji Nasan Ke yarinya ce kamilalliya me ilimi don haka naita addu'a ina kwadayin Allah yasa ki zama abokiyar zamansa don nasan zanyi alfaharin auranki da Daddy,dukkan y'an matan dake rubibin sonsa nasan suk shirme ne ba wacce take sonsa domin Allah, amma ke kuwa nasan zaki zauna dashi cikin ta ilimi zaki rink'a nusar dashi abubuwa da yawa kiyi hak'uri kinji Khadijah ".

Wani bak'in ciki ne ya turnuk'e su Aunty iyami da jin kalamansa don sun san gugar zana yake musu suda y'ay'ansu da suke kwad'ayin auran UK,

Mun jima zaune Abbah nata Nasiha daga bisani ya zaro key d'in mota ya mik'awa Aunty Murjah yace " murjah ga kyautar y'arki nan dana tanadar mata duk randa aka kawo ta gidan sabida zuwa school ".

Cikin fara'a Aunty murjah tace to Abbansu Khadijah ta gode kuma muma mun tayata godiya Allah ya k'ara bud'i".

Su Umma ma Godiya sukaita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login