Showing 54001 words to 57000 words out of 137542 words

Chapter 19 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

motar ta kaji na fad'a maka tashi kaban waje ".

Tashi yai ya fita ransa a mugu mugun b'ace da wannan hukuncin na Abbah, yana shiga d'akinsa yai cilli da rigarsa ya fad'a gado yana huci da firzar da wata iska me zafi,wai nufin Abbah shine driver na wannan yarinyar wai auran Dolan ma akai mai bai isa ba kuma sai an bishi da dokoki masu zafi haka,gaskiya an takura shi wlh shi wannan yarinyar ta zama masifa a cikin rayuwar shi ,anya bazai nemi hanyar korar yarinyar nan daga gidansu ba ko zai samu ya wataya,saida ya gama kuncinsa da b'acin rai ya shige toilet ya watsa ruwa don yaji sauk'in zafin da ransa Ke masa.
Yana kwance ya kasa bacci yana nazari kan wane Irin k'auna Abbanshi kewa Nahna haka har yake fifita lamuranta akan na kowa,dame ta siye zuciyar mahaifinsa haka,in yai tunanin sai dai kawai yaja mugun tsaki ya juya,a hankali kuma zuciyar shi kuma ta fara mai lissafin Irin k'ok'arin yarinyar wajan yin duk abinda ya umarceta da wanda ma bai umarceta ba,kamar dai yau ko sau d'aya baiyi zaton a wannan safiyar zata iya yimai girki ba kafin ta fita amma daya tashi yana tunanin inda zai sami abinda zaici yana fitowa parlour yaga ta shirya mai komai a table gashi ta gyara ko ina har tana k'ok'arin gyara mai d'akinsa badan yace ta tafi ba amma gashi ma a dawowar da tayi da yamman nan hartai girki ta gyara mai d'aki ta wanke mai toilet, gaskiya in haka ne fa tana k'ok'ari, mutttssss kuma yakuma jan tsaki wani sashin na zuciyarsa na fad'a mai to meye amfaninta daman in batai wad'an nan ayyukanba tunda daman ta saba da wahala tun agidansu.
Haka yaita sak'awa da kuncewa har bacci yai gaba dashi ransa ba dad'i.








Taku ce
Y'ar mutan Ja'oji???j%??]?j
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


??1]??1]??1] ??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? ??


*Allah* *ka* *zab'a* *mana* *shugabanni* *na* *gari* , *Allah* *karka* *barmu* *da* *zab'in* *kanmu* .???a


0(???3(???0(???



Yauma daga sallar asuba ban koma ba na shiga kitchen na fara ayyukana bayan na gyara gidan ko ina na shirya cikin doguwar riga y'ar k'asar Sudan bak'a mai yalwataccen k'asa nai rolling da yalwataccen mayafinta wasu sabbin takalmi da jaka na fiddo cikin kayana orange color kasancewar aikin jikin rigar shima orange ne,dole in kula wajan canja shiga don duk lokacin da mace tai aure idon kowa akanta yake don aga yanda kamannin ta zasu canja da yanayin sutturarta,musamman y'an makaranta(duk da ba yabon kaiba y'an department d'in Arabic sa ido bai damesu ba abinda Ke gaban su kawai sukeyi)

Nazo k'ofar d'akin nasa naji motsin alamar ya tashi don haka na tsaya nai knocking,ya bada izinin shiga,da sallama na shiga ya amsa fuska d'aure tamau cikin sanyin muryata na gaisheshi bai d'ago ba ya amsa,nace "Em daman zan gyara d'akin ne".
Tashi yai ya shige toilet daman dagashi sai towel d'in wanka, tsaf na gyara d'akin nasa turare sannan na wuce nai break, ina mik'ewa yana fitowa cikin shiri 'kauda kai yai gefe yana fad'in" In kin shirya wuce mu tafi".
Cikin D'an dibirbircewa nace "Tom bari in d'auko jakata"
bai tanka ba ya juya ya fice nima da hanzari na shiga na d'auko jakan na fito tare da kulle k'ofar, harya tada motar na bud'e na shiga, cikin fishi naga yaja motar da gudun gaske ya fice nidai kaina naga takardar dake hannuna ina karantawa, kafin me sai ganinmu nai a gate d'in school d'in don bala'in gudun da yake yi har ciki ya shiga dani yaja burki da k'arfi ya tsaya,cikin mutuwar jiki nace "Na gode" na bud'e mirfin motar zan fita yai magana da izzarshi "Ke k'arfe nawa zaki tashi" 4:00 insha Allah "
Waya ya mikomin "sa number d'in ki anan" karb'a nai nasa mai ina mik'a mai zan fita ya k'ara tsaida ni "tsaya" naja na k'ara zama, kira naji cikin wayana ina d'aukowa yace "kiyi saving in kin tashi ki kirani da ita".

1k ya mik'omin rannan nashi kamar yaji sak'on mutuwa, nidai kaina na kawar ina cewa " ka barshi akwai kud'i a hannuna ".
" wannan ba damuwata bace in zaki amsa ki amsa karki b'ata min lokaci ".
Karb'a nai ina godiya na fice a raina ina mamakin bak'in hali Irin nashi mutum koda yaushe k'unci kuma a haka y'ar uwarsa Ke fad'in dad'in zama gareshi ,ina wannan tunanin na k'arasa Hall d'in da zamuyi lecture a ciki.

B'angaren sa kuwa cikin bacin rai ya koma gida lokacin ya duba agogo ko takwas har sa'ilin batayi ba aka tasheshi a bacci sabida wannan yarinyar tsaki yaja ya wuce dining ya cika cikinsa sannan ya koma d'aki yama rasa abinyi ga bacci Sam ya bar idon nashi daya d'an k'ara matsewa,gashi ba wajan zuwa gareshi ba duk abin dai ba dad'i,haka dai ya d'au wayansa ya shiga net don rage kad'aici.

Ni kuwa lecture ta nai a nutse saida muka shiga period d'in k'arshe ne ya rage saura minti goma mu fito na kirashi nace mun tashi don bansan Sai mun fito in tsaya jiran sa.
Ai kuwa ko bayan fitowarmu saida nai kusan wata minti goman sannan ya kirani yace min yana gate,Allah yasa daman kusa da gate d'in mukai lecture din don haka ba b'ata lokaci na k'arasa da sallama na bud'e na shiga ciki ciki ya amsa nace mai " Barka da yamma ".

" yawwa " kawai yace ya tada motar.



************
Haka rayuwar mu taci gaba da gudana kadaran kadahan ranakun da nake zuwa school hud'u don bama lecture Friday duka rana kun nan shi yake kaini ya dawo dani,sannan weak end da yamma mu fita ya koya min mota duka wannan lokacin ba abinda ya canja daga zamanmu yanda muke dai haka muke Sai dai ni bana wasa wajan yin duk abinda nasan hakkinsa ne dake kaina,sai dai b'angaren Abbah yana k'ok'ari matuk'a wajan son faranta raina don haka nima duk sanda nake da lokaci banje school ba ina zama in shirya mai abinda nasan yana sonci kamar su danbu,dashishin alkama,zob'o,kwad'an zogale kona rama duk ire iren abinciccikanmu na gargajiya don haka kullum cikin kyautatamin shima yakeyi.

A haka muka kai wata guda cif da auranmu,lokacin UK ya fara damun Abbah da maganar tafiyar sa don a cewarsa duka abokansu da aka zab'e su tare zasuyi course d'in wai Duk sun fara don haka Abbah badan yaso ba yace yaje ya fara shiri sati biyu masu zuwa sai Ya tafi,Ba haka yaso Abbaan yace ba,yaso ace kwana biyu kawai ya bashi amma har sati biyu, haka ya hak'ura yabi umarnin Abban,

Ranar da Dare Abbah ya Kira ni a waya inzo yana kirana, ba b'ata lokaci naje anan yake shaida min miji na zai koma indai nan da sati biyu kamar yanda na shaida da tafiyar don haka ya k'ara ban baki yana nunamin mahimmancin Abinda zaije yi badan hakanba yace bazai barshi ya koma d'in ba, Nikam mirmishi kawai nai nace "Ai ba komai Abbah, Allah ya kaimu lokacin kamar yaune zai dawo fatanmu Allah ya bada sa'a ".

Sosai Abbah yaji dad'in maganar tawa yaita samin albarka.

Bayan na dawo part d'in mu naketa tunanin tafiyar tashi araina daga baya na watsar naci gaba da abinda Ke gabana .

A cikin kwana kin na k'ara azama wajan kyautata masa kuma ina k'ok'arin kyautata alak'a tsakanina dashi, duk da shima na lura a kwanakin ya d'an rage had'e giran da yakeyi in yana zaune zai d'an sassauta fuskanshi ko in sweety ta shigo muna hira yakan d'an jefa baki kad'an inma abin dariya mukai zai d'an murmusa, amma fa har lokacin bai min zancen tafiyar ba haka Nima ban nuna mai na sani ba.

Ya rage saura kwana biyar tafiyan ranar lahadi Abbah yace ya kaini gida shima ya gaisa da yaya na yai musu sallama, ai kuwa ina zaune bayan na gama duk ayyukana nazo ina karyawa ya shigo yana kallona ya kalli agogo sannan ya k'ara dubana yace " Ke ki gama duk abinda kike nan da 15 minutes zakije gidanku Ku gaisa,sannan zan musu sallama kin san 5 day's ya rage in koma India ".

A nutse na dubeshi ido da ido ina kurban copy d'in dake hannu na na gyad'a Kai tare da fad'in" Tom" kawai, Juyawa yai ya shige d'akinsa, ni kuwa yana shiga na daka tsallen murna na kwashe kayan danai amfani dasu zuwa kitchen na wankesu, nan da nan sannan na k'ara kintsawa don dama a shirye nake kayan jikina kawai na canja don daga doguwar riga zuwa wani lafiyayyan less dinkin riga da zani na d'aura d'an kwali na d'as nasa mayafi da jaka da takalmi duka kalan adon less d'in, bansa turare ba sanin haramcin hakan sai dai humra me dad'in k'amshi dana shafa, lokacin dana fito parlourn sha biyu dai dai na tsaya k'ofar d'aki??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n nasa ina knocking daga ciki naji yace "ki jirani ina zuwa"

Ina zaune kan kujera kusan minti uku sannan ya fito cikin shigarshi ta gado wato k'ananan kaya kallo d'aya nai mai na kauda ido ina fad'a cikin raina "wai mutumin da zaije gidan surukai ne yai wannan shigar shi koda yaushe bashi da shiga sai wannan, amma insha Allah a sannu saina canja salon wannan shigar tashi don a duniya ni ina son inga namiji da manyan kaya da Babbar riga hakan na birgeni . . . . ."
"In kin gama kallon ko tunanin ki wuce muje " maganar shi ta dawo dani cikin salona na basarwa na kauda ido tare da mik'ewa nai nai gaba ya biyoni a baya yana kulle k'ofar ".

A compound d'in muka had'u da sweety nace mata gida zani tazo muje tana dariya tace "um um sai wani zuwan in zakije zamu tare".
Marairaice murya nai nace " Haba don Allah kizo muje"
Rad'a tai min a kunne tana dariya "Ke wake bin miji da mata unguwa inje in katse muku hanzari in hanaku soyewa a mota "
Dukan kafad'anta nai tare da hararanta na wuce na barta tanata min dariya.

Muna tafe cikin motan zama irin na kurame saida ya gaji ne ma ya kunna wak'a yana bi tare da kad'a Kai, ni kuwa kaina na jingina jikin mirfin motan idona a lumshe ina jin wani nishad'i da ban san kona mene ba, a haka danja ta tsaidamu na bud'e idona naga me tallan chocolate yana mik'owa ko zamu siya,kallonsa nai ina marairaice mirya nace "pls zan sai Abu".
Gyad'a min kai kurim yai, na sauke glass d'in ina cewa yaron ka bani kwali biyu yana k'ok'arin mik'owa yace " K'ara mata kwali biyar da sauri na kalleshi nace "bafa wani Abu zanyi dashi ba yara zan kaiwa, kwali biyar yai yawa 12 peaces ne a kwali d'aya".
Kafad'a ya d'age yana fad'in in tai musu yawa Ke kyasha daga haka ya mik'awa yaron kud'i yana karb'ar ledan da yake mik'omin kan cinyata yaja motan don lokacin har an bada hannu.

Motan na tsayawa k'ofar gidanmu naji farin ciki ya lullub'eni na bud'e mirfin cikin zumid'i na zan fice yace " Ke in kin shiga kice zan shigo mu gaisa".

Ina bud'e gate d'in naci karo da yaya na yana goge motarsa kasancewar weak end baya fita,da sauri na k'arasa gabansa cikin farin ciki ina cewa "yaya"
Shima cikin farin cikin yace "Nahna Oyo yoooo" duka dariya mukasa na zube k'asa ina gaisheshi ya amsa cikin fara'a yana tambaya ta ya gida yame gidan "Ai yaya tare ma muke dashi yana waje ".
" OK to shiga gamu nan shigo wa dashi ".

Da sauri na k'arasa ciki da sallama ina kwalawa su Ashra kira ai kuwa da gudu suka fito suna rungumeni nan Aunty ma ta fito da murnarta tana min sannu da zuwa, bayan mun gaisa naji sallamar yaya sun shigo,Sai sannan nake ce mata "Aunty tare fa muke dashi gasu nan shigowa da yaya". Da sauri ta tai d'aki don d'auko hijabin ta,
K'arasowa sukai parlourn ni kuwa inata faman wasa dasu Ashraf d'ina suna ban labari,anan Aunty ta fito tana mai sannu da zuwa bayan ta zauna suka gaisa cikin girmama juna ta mik'e tana fad'in " Bari a kawo ma ruwa ".

Mik'ewa shima yai yana " a'a wlh ki barshi tafiya ma zanyi".

Yaya yace "A haba Daddy ka zauna mana kasha ko D'an ruwan ne daga zuwa sai tafiya".
Mirmishi yai yana mik'ewa Ashraf kud'i yace" ba komai yaya wani lokacin inna dawo na sha".
Yaya yacewa Aunty " Tafiyar tashi ce fa ta taso wannan satin zai wuce ".

" Au Daddy tafiyar ce tazo,To Allah ya kiyaye hanya ya bada sa'a ".
Amsawa yake da "amin amin " ya fita yaya yabi bayan sa.
Bayan sun fita muka d'an fara hira da Aunty sai ga yayan ya shigo yana cewa "jeki zai wuce "
Mik'ewa nai cikin jin kunya na fita, a bakin mota na sameshi yace " In anyi sallar magriba a zanzo in d'auke ki "
"To Allah ya kiyaye saika dawo".
Juyawa yai ya shiga motan na shiga cikin gida.

Yinin ranar muna tare da Aunty tanata k'ara koyar dani dabarun zaman aure da yanda ake kula da miji .

Bayan sallar la'asar na tafi gidan yaya Haroon muka rungume juna da Aunty Amrah wadda naga cikinta harya d'an fito, itama dai k'ara min darasi take kan dai rayuwar sai gab da magriba na koma gida na koma gida, ina salla naci abinci banfi minti biyar da gamawa ba ya kirani a waya in fito yazo,anan ma saida yaya ya fita suka k'ara yin sallama yana mai fatan alkairi muka wuce.








Taku ce
Y'ar mutan ja'oji ???j%??]?j
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

??1]??1]??1] ??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? ??



0(???3(???1(???



A hanya muka tsaya yai take away, sannan muka wuce gida, muna shiga ana sallar isha'i don haka kai tsaye toilet na wuce nai wanka sannan na d'auro alwala nai salla,ina kan sallayan ya lek'o d'akin karo na farko kenan daya tab'a zuwa " In kin idar ki Samar min abinda zanci don wannan abincin dana siya yai yaji da yawa"

Kafin ya k'arasa ma na mike ina nade abin sallar na saka riga y'ar k'arama iya gwiwata na fice " a zaune na hangoshi a k'aramin parlourn yana kallon ball,don haka da azama na shige kitchen d'in na fara k'ok'arin dafa mai ko jelof Na taliya ne.

Cikin 30 minutes na dafa mishi taliyan tasha kifi sai k'amshi take,lokacin danake zuba mai kuwa har yawunsa ya tsinke don shi akwai son dad'i, ina zaune gefenshi harya gama na tashi na had'a kayan ina cemai "saida safe " d'agowa yai ya kalleni tsaf sannan yace "OK"

Ni kuwa ina shiga d'aki handouts na d'auko nai karatuna Sama Sama don ina jin bacci, nan da nan kuwa bacci ya d'auke ni.

Yauma kamar kullum da asuba na tashi nai duk abinda zanyi na had'a break fast sannan nai wanka,ina shiga d'akinsa naga ya shiga wanka kafin ya fito na gama gyaran d'akin bayan ya fito na gaisheshi ya amsa na wuce toilet d'in na wanke.

A dining na sameshi muka karya,amma yau sai naga baici abincin da yawa ba, haka ma muna tafiya a mota naga sai d'an yatsina yake kamar bai jin dad'i, munje zai saukeni naga ya d'an matse cikin sa yana rufe ido ,tsayawa nai ina kallon sa yana bud'e ido muka had'a ido a sanyaye nace " baka da lafiya ne"
Girgiza min Kai yai alamar a'a nai Jim sannan na fice ina cemai "na gode "


Tunda muka fito a lecture nake kiransa ganin ban ganshi inda ya saba jirana ba in yazo, kusan kira biyar sannan ya d'aga wani iri naji muryansa " ki d'an jira na turo driver yazo ya daukeki".
Bayan ya kashe wayan saiga driver ya duk jikina a mace na shiga motan ina tunanin baida lfy daman naga alama tun safe amma yace ba komai .

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login