Showing 45001 words to 48000 words out of 137542 words

Chapter 16 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

yi suna jinjina k'aunar da nasan Allah nan kemin tare da karamcinsa gareni".

Haka muka baro gun Abbah zuwa part d'ina muka bar masu bak'in ciki natayin k'us ,

Zuwa minti talatin duk manya y'an kawo amarya sun watse sai y'an mata kawai da za'a fita friends night dasu, sweety ce ta shigo parlourn tana zuwa tazo kusa dani tare da rank'afawa ta lek'o fuskana tana d'an mirmishi tace "Shike nan Aunty nah ta dawo gidanmu ta zama y'ar gidanmu har abada".
Hararanta nai ina kauda kaina gefe,
Matar dake bayan ta ce ta ajiye d'an akwatin kit d'in dake hannunta tana cewa" Ruk'ayya a fara kwalliyar nan yanzu don lokaci na tafiya".

Sweety tace "Aunty nah game kwalliya tazo zata miki Kinga 9 za'a tafi gashi 7:30 yanzu".

D'aki muka shiga na na sake d'auro alwala don nafiso ana gama min na nai sallah kafin mu tafi,araina inata bak'in cikin ace wai sabida boko da wayewa dataiwa mutane yawa daren da aka kawo amarya d'akin ta kuma ace wai a k'ara fita wani fatin na daban,

Yau d'in ma kwalliya sosai akai min bayan an gama kafin nasa kaya nai sallar isha'i don zuwa lokacin an dad'e ma da yin sallar duk y'an Matan ma sun k'ara shiryawa, yau farin gown d'in nasa asalin bride gown na y'an k'asar India itama ta amsheni sosai kaina ba gwaggaro bane yau mayafin rigar aka samin saman kai yayin da akamin gyaran gashi Irin ba y'an India sai wani ribbon da aka samin a gaban gashi kamar Irin na sarauta,yau fuskata a waje take,hannayena duka cike da awarwaraye Irin dai yanda y'an India keyi kallo d'aya zaka min kasan tsaf kwalliyar amaren India akaimin don har wannan d'an abin da suke sawa a goshinsu kamar d'an kunne aka samin,

Ihu parlourn ya d'auka lokacin da na fito daga d'akin kowa fad'i yake har nafi ranar dinner kyau.




Taku ce
Y'ar mutan ja'oji ???j%??]?j
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??


ALLAH KAI MANA MAGANIN ABINDA YAKE DAMUN MU ALLAH KA SHIGA CIKIN LAMARINMU???a



0(???2(???7(???




Ina tsaye duk kunya ma ta baibayeni na rasa me zance musu da shakiyancin da suke tamin, sweety ta shigo cikin shirinta tsaf tana fad'in " yawwa to duk kowa ya fito ya motoci na jiranmu mu wuce".

Fita suka farayi d'aya bayan d'aya ina tsaye ta k'ara so gareni tana rik'e hannuna tace "amarya Kyan da kikai yau ya zarce na kullum,ki jira angonki yanzu da kansa zai shigo Ku tafi".

Ta k'arashe maganar tana mirmishin tsokana, jin takun takalmansa mukai yana shigowa parlourn a tsakiya yaja ya tsaya hard'e da hannayensa a k'irji cikin shigar suite farare k'al har takalman dake k'afansa farare ne haka ma fatan tsadaddan ogogon dake hannunsa, sai gashin kansa bak'ik'irin kwance luf luf kana kallon sa zaka gano tsantsan kyan da yayi, cike da nuna isa yacewa sweety" jeki ku jiramu gamu nan fitowa ".

Tana fita ya k'ara taku biyu zuwa uku yaja ya tsaya yana fad'in "ki kula sosai yauma karkiyi abinda zaki bani kunya kinji ko".

Kai kawai na gyad'a mai ba tare dana d'ago ba, shima kauda kai yai daga kallo na ya juya zuwa k'ofa yana fad'in "zo mu tafi"

A hankali na taka nabi bayan sa har zuwa k'ofar fita daga part d'in sannan ya dakata ya tsaya har ba k'ara so kusa dashi yasa hannunshi ya ruk'o nawa k'am a haka muka k'arasa fita inda muka tarar da motar da zamu tafi a cikin ta sauran motocin kuwa duk sunyi layi daga cikin gate d'in har zuwa waje,da sauri d'aya cikin abokansa ya bud'e mana k'ofar muka shiga sannan yaja muka shiga cikin rukunan moticin ,
Tunda muka shiga bai tanka minba saima d'auko wayansa da yayi yana danne dannansa a ciki, ni kuwa kaina yana k'asa ina wasa da yatsun hannu wana,a haka muka k'arasa gun motocin duk suka tsaya saida aka sanar sa m.c zuwanmu sannan muka fito yasa hannunsa ya rab'oni jikinsa yayin sa sauran abokansa kowanne ya tsaya tare da mace d'aya muka jera a haka har zuwa cikin Hall d'in yayin da wani kid'a me taushi yake tashi haka sukai mana rakiya har zuwa mazaunin mu, bayan y'an matan sun gama cashewa a fili aka basu damar komawa mazauninsu, nan aka cigaba da gudanar da program d'in cikin wayewa irinta rik'akkun y'an boko, dama m.c din ya bawa ango da amarya su fito filin rawa su nuna farin cikin su, a nutse muka sakko filin yayin daya nanuk'eni gefen kafad'arsa,wak'a me tsuma rai aka sakar mana ta turanci me d'auke da dadad'an kalaman soyayya ga kid'inta me taushi, duk yanda m.c d'in ya dage kan na rausaya na kasa shi kuwa gogan rausayarwa sa yake cike da iya wa, ganin ina neman kwafsa mai nak'iyin rawar yasa ya rik'o kuguna da hannayensa biyu yana juyi dani kamar y'ar baby, tafi abokansa Ke masa ganin yanda ya wani basar yana jujjuyani a jikinsa, sosai kunya ta lullub'eni k'asa nai da kaina inajin wani fad'awar gaba, lik'i ne ta ko ina ya b'arke a wajan jinai an farke min rafar kud'i akaina kamar ba'a sonsu,a hankali na d'ago ido don gani wace wannan wadda batayiwa angon sai ni kad'ai shima dai dai lokacin yakai kallonsa gareta yanda naga suk sunyi shock a lokaci guda yasa na k'ara kallonsu sosai a hankali naji yace "tnx fadlah " mirmishi kawai tai ta basar tare da juyawa ta bar wajan, binta yai da kallo yana mamakin yanda tazo wajan don bayyi zato ba ko kad'an wai fadlah zata zo kano bikinsa,ganin kallon da yake mata yasa na juya zan koma mazaunina da sauri ya ruk'oni muka jera zuwa mazaunin namu,bayan anyi ciye ciye akaci gaba da cashiya inda abokansa suke ta rawa suna ihu irin na wayayyun samari y'an boko, gab da za'a tashi aka buk'aci mu fito mu yanka cake, k'awataccen cake ne me d'auke da sunayanmu nida shi, hannuna da nasa ya had'a bayan sun kirga 3 muka yanka nan akaita yi mana tafi m.c yace amarya ta yanka ta bawa angon ta a baki,tab d'in babbar magana kenan nanfa k'irjina ya fara lugude ina jin kamar bazan iyaba,amma dana tuna warning d'insa akaina na kada in kuskura in bashi kunya sai na tattaro nutsuwa na daidaita kaina,a hankali na yanko cake d'in nakai bakinsa ai kuwa caraf ya had'a tare da hannun nawa yasa abakinsa yana tsotsa nan da nan hannun nawa ya fara rawa, saida ya had'iye cake d'in sannan shima aka bashi damar ya yanko ya bani,kai rashin kunya tanaga namiji wai daya yanko cake d'in sai yasa a bakinsa ya rik'e da hak'orinsa sannan ya kamo fuskata zuwa tashi fuskar yana kai bakinsa ga nawa da ido yaimin alama dana bud'e bakina,runtse idona nai ina d'an bud'e bakin nawa turamin cake d'in yai cikin bakina yana hade baku nan namu waje guda, innalillahi kawai nake furtawa cikin raina jikina yana rawa, da k'yar na hadiye cake d'in kwalla tana taruwa a idona ta b'acin ran rashin kunyar da yake tsulawa a gun yana sani jin kamar k'asa ta tsage in shige,
Zuwa lokacin ihu ya gama karad'e Hall d'in gaba d'aya tafi kawai Ke tashi da ihun mutane,su anasu ganin ya gama wayewa k'arshe wannan abin da yakeyi, wanda ni kuwa anawa sashin nake ganin zunzurutun rashin kunya ne da wayewa irinta nasara, abinda yayi da wasa ko don nuna wayewarshi ga abokansa sai ya juye mai ya koma sabon yanayii tare dashi don har ya fara manta inda yake tsaye k'ok'ari yake ya wuce makad'i da rawa Allah ya taimakeni Mus'ab ya gane halin da abokin nasa ya fara shiga don haka yai m.c magana kan ya bawa angon da amarya damar komawa mazauninsu, jiki a sanyaye ya ruk'o hannuna zuwa mazaunin namu,Duk kansa yai mai nauyi, yama rasa tunanin da zaiyi,kawai sai ya lumshe ido, dake hankalin kowa naga filin rawa sai ba'a lura da yanda yanayinsa ya canja ba, a sannu tunanin sa ya fara dawowa wani mugun tsaki yaja tare da furzar da iska tunawa da yayi wai bakinsa ne cikin na wannan y'ar Arabic d'in, har yake neman watsa kansa a gabanta, mutttssssss ya k'ara Jan tsaki tunawa da yayi da matsayinsa da nawa matsayin,ni kuwa zuwa lokacin duk jikina ya K'ara yin sanyi jin tsakin da yaketa ja ,daman gashi dik a takure nake.

Haka aka tashi a taron dukka ni dashi da abinda muke sak'awa cikin zukatanmu, bayan mun fito yacewa abokansa suyi k'ok'ari su maida dukkan y'an matan nan gidajansu, sannan ya amsa key d'in motarsa yace zai ja mu koma ba wanda zai shigar masa mota yanzu,dariya suke ta masa nan wani abokansa ya matso yana rad'a mai gulma kan zuwan fadla da kukan da tayi sanda taga bakinsa cikin nawa, da kyar suka rarrasheta ta tafi, d'age kafad'a yayi yana jan tsaki yace " damuwanta ne wannan ai ban gayyaceta ba" nan motan yayi yana d'agawa sauran hannu muka wuce gida.


Muna zuwa part d'in mu muka wuce ba wanda ya tankawa wani shi yai d'akinsa nima na shiga wanda aka fara kaini cikinsa matsayin nawa, kai tsaye kayan jikina na cire tare da shigewa toilet nai wanka na d'auro alwala nazo naita jero salloli ina rok'on ubangiji ya samin juriya da hak'uri kan Duk yanayin da zan tsinci kaina ciki a zaman aurena, sannan na rok'i Allah ya sanya dukkan alkairai cikin rayuwar auranmu,na dad'e bisa prayer mat ina kaiwa Allah kukana, har tsakiyan dare sannan bacci ya fara fuzgata,banko cire rigar danai sallarba na haye gado da addu'a bakina ba jimawa bacci me nauyi yai gaba dani.

Kiran sallar asuba ya farkar dani da kyar na iya bud'e idona don baccin dake cikin sa,ga tarin gajiyar biki, haka na daure nayo alwala nai salla azkar ma inayi bacci na jana haka nai na koma gado,wanda ban farkaba sai takwas, ina farkawa naji yana bud'e gidan zai fita bud'e labulen window d'in nayi ina kallonshi haryaje parking space ya shiga mota ina tsaye naga ya tada motar ya fice, toilet na shiga na had'a ruwa me zafi na gasa jikina sannan nayo wanka, wasai na jini yanzu duk gajiyan ta bar jikina,banyi wani dogon kwalliya ba powder da lipstick kawai nasa Sai turaran Humra dana jik'a jikina dashi, na d'auko riga da siket na atamfa na saka tare da kama kaina da ribbon na d'aure,ban d'aura d'an kwali ba sai mayafi dana yafa na fito parlor, kewaye gidan na farayi ina kallon yanda tsarin part d'in yake kasancewar nasan ni kad'ai ce a gun baya nan,

parlour biyu duk ansa kujeru, set d'aya orange and copy, set d'aya pink and purple, sai d'akuna biyu suma Duk ansa kaya,a babban parlourn ansa min dank'akemiyar Plasma t.v a gefe guda ansa show glass ta turaren wuta wanda aka cika ta taf da designed na kwalabe aji iya aji sai standard flowers a jere a gefen show glass d'in yayin da akasa wani had'ad'd'an santer table me matuk'ar a tsakiyar jerin kujerun, cen gefe dining area ne wanda aka saka had'ad'd'an dining table me zagaye da kujeru guda shida,daga gefe kuma fridge ne tsaye ash colour, gefen dining area d'in wata show glass ce ta kwance me hawa biyu duk an jera wasu zafafan glasses cups kalan fari tas Dame kalan ruwan garai sai masu flowers duk ajiki, a gefe guda kuma jikin dining area d'in duka k'ofar shiga kitchen ne,wanda yake k'aton gaske me d'auke da d'an madaidaicin stor a ciki,wanda aka cika su taf da kayan abinci, cikin kitchen d'in a kewaye yake da loga sama da k'asa duk anyi min jeren kayan kitchen sai cooker gas me had'e da oven da electronic ajiki, can jikin stor d'in ansa de freezer bud'e ta nayi naga kayan miya da nama acikinta na maida na rufe tare da jingina jikinta ina tunanin meya kamata in shirya na breakfast, Dukda nasan bai zama dole yaci abinda zan girkaba amma dai hak'k'insa ne in dafa mai,wannan tunanin ya bani k'warin gwiwar fara had'a mana breakfast me kafiya, kasancewar akwai dukkan kayan amfani fa na'urorin girki kala kala a gun yasa nan da nan na gama had'a komai na zuba a cikin wasu zafafan Warmer's lafiyayyu, nazo na jerasu jan dining table sannan na koma na gyara kitchen d'in duk abinda nai amfani dashi saida na gyara na goge ya zama kamar ba'ai komai ba a kitchen d'in, turare gidan na k'ara yi da turaren wuta sannan na koma d'aki na k'ara gyara kaina,hijabi na d'auko cikin kayana wanda ya shiga da atamfar jikina,na fito zuwa cikin gidan,a bakin parlour na had'u da sweety da sauran y'an biki da basu tafi ba suna bawa ma'aikatan gidan umarnin inda zasu gyara, tsalle tai ta rungumeni tana fad'in "oyoyo Aunty Nah wlh tun d'azu nake tunanin inje in duboki amma ina tunanin ko buku tashi a bacci ba". D'an hararenta nai ina fad'in "ba wani nan kawai kin manta dani ne cikin gidanku,amma bacci me zamuyi tayi har yanzu around 11" y'ar dariya tai tanamin rad'a a kunne " nasan ko ansha amarci jiya" duka nakai mata ina fad'in "Allah ya shiryeki Ke kam ni ban hanya in wuce". Dariya ta farayi ta ruk'o hannuna " zo in rakaki ciki nasan surukanki kika zo gaidawa" ban kulata ba na fara gaisawa da y'an wajan sannan muka shiga ciki,babu wasu mutane da yawa,y'an uwansu ne na katsina sai tsirarun na nan garin,tsugunnawa nai na fara gaishesu, nan suka shiga ansawa cikin sakin fuska suna tambayata ya bak'unta,kaina a k'asa naji fitowar Aunty Murja daga d'aki tana cewa "a'a amarya kin fito ai na aika muku da abin breakfast akace k'ofar a rufe buku tashi ba". Cikin tsananin kunya nace "Aunty ai nayi mana breakfast d'in ma" haba Khadeejah me yasa kika wahalar da kanki ga gajiyar biki tare dake aida biki yi ba ma kin huta sosai, mirmishi kawai nake kaina a k'asa tace "taso muje ki gaida Abban naku" mik'ewa nai ciki da nutsuwata nabi bayanta zuwa sashin Abban,da sallama muka shiga na tsaya daga bakin parlourn tace " k'araso mana " a zaune muka same shi kan rug yana cin abinci da fara'a kan fuskanshi yace yace "Khadeejah har kin fito" cikin girmamawa sosai na gaisheshi ya amsa yana tambaya ta ya gajiyan taro, d'an mirmishi nai nace "A khan fulfill ah " yace " Murjah Allah yasa dai y'ar taki taci Abinci ko?". "Eh Alh, an aika musu ma k'ofar a rufe basu tashi ba,sai yanzu take cemin ai tayi musu ma ". "Masha Allah, Allah yai muku albarka ya Baku zuri'a d'ayyiba kiyi hak'uri da rayuwar aure kinji Khadijah kisa a ranki jihadi zakiyi aljannarki zaki nema kinji" gyad'a kai kawai nakeyi nan yaci gaba da yimin nasiha sosai , Aunty murjah ce taje ta d'auko key tana mik'o min tace " Khadeejah ga mukullin motarki jiya ban baki ba sabida jama'a Kar ki yar". Karb'a nayi ina fad'in "Na gode Allah ya saka da alkairi Allah ya k'ara girma". Ameen Ameen suketa amsawa, sallamar sace tasa suka kalli k'ofar ni kuwa banko d'ago ba kaina yana ak'asa, nan ya sami waje kusa da Abban ya zauna ko kallon inda nake baiyi ba yace " Abbah barka da safiya, Aunty kin tashi lfy " tare suka amsa da "lafiya qlau ya gajiya " cikin basarwa yace "Normal". Kallon sa sosai Abbah yai yace "d'azu naga fitarka ina kaje da safe haka?" "Ah naje raka friend's d'ina ne airport zasu koma". " ok an gode musu Allah ya saka da alkairi". Inji Abbah mik'ewa yai yana fad'in "Abbah bari in k'arasa in huta " a'a zauna muyi magana ". Komawa yai y zauna badan yaso hakan ba, "Daddy nah ga matarka nan amana ce a gareka Amanar Allah kuma amanata ka rik'e ta da amana ka bata dukkan kulawar data kamata karka sa aranka ni na aura maka ita,ka rink'a ji har cikin zuciyarka cewa kai ka ganta kaji kana so ka aureta,in har kayi hakan ya gama min komai a duniya,kuma zanci gaba da alfahari da kai dukkan wani hak'k'in uba akan d'ansa ka sauke min nawa in har ka kula da Khadeejah, marainiya ce ka zame mata miki ma gurbin miji kuma ka zame mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login