Showing 39001 words to 42000 words out of 137542 words

Chapter 14 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

k'orafin Duk an wahalar da ita,dariya Amrah tayi tace "kuma daga yau har ranar da za'a kaiki gidan Umar ana miki wannan gyaran jikin, me gyaran jikin ce ta fito,ta bud'e jakarta ta fiddo wasu kullin ledoji ta bud'esu tana kallon Nahna tace " wannan ki rink'a sha da madara wannan kisha da Zuma wannan kiyi turaren tsugunno,cikin rashin fahimta tace "na meye wannan din kuma?"

Dariya Aunty Amrah tayi tacewa me gyaran jikin " Barta zan mata bayani a d'aki naga kamar kunya takeji".

Mirmishi kawai Nahna tayi ta mik'e tsaye tana fad'in "bari in wuce gida maman biyu".

" he lalle ma Nahna bakinki ya bud'e,kema kwana nawa ne zaki zama maman biyun ".

Da sauri Nahna ta rufe ido tana Neman mayafinta ta gudu,ruk'o hannunta tai tace "zauna zamuyi magana kafin ki wuce"

Wuce wa tai ta raka me gyaran jiki k'ofar gida sannan ta dawo, ta zauna tana fuskantar Nahna sosai ta fara " Nahna sweety tazo da magana zakuyi amma Baku sami zama ba taban sak'o ki shirya in Allah ya kaimu gobe Umar zaizo Ku gaisa, sannan yace a shirya events sabida abokansa zasu zo,don haka mun tsara nida sweety, kamar yanda kika ce ran Alhamis kinaso ayi lecture da kamu to hakan za'ayi,amma batun walima da zakiyi bayan d'aurin aure da yamma ta tashi dinner za'ayi da dare,asabar ayi culture show da yamma ayi lunch dangin amarya Dana ango duka waje d'aya sai Lahadi ayi mother's day akai amarya,bayan an kaiki kuma zaku fita friend night sabida abokansa da zasu zo,ina fatan baza ki bamu kunya ba Nahna don in kika Bijire zai fara ganin kin fara mai gaddama tin kafin kuyi aure,ki nuna mai Ke me biyayya ce bisa umarninsa".

Nahna jitai kamar zata kurma ihu,abikinta duk za'ayi wannan bidi'oin,wlh ita an gama da ita,me ake da auran me bud'e d'd'en ido wanda boko tai mai tsiro, amma kasancewar bamai bijirewa na samanta bace yasa bata tanka ba ta tashi tace "Babu komai Aunty Amrah bari inje gida kafin akira magriba".

A gida ma dai maganar d'aya ce nan Aunty Hafsah taci gaba da bata baki,akan ta tausasa zuciyar ta ayi komai a gama, nan ma bata tanka ba sai gyad'a Kai da tayi alamar amincewa.


*******
Washe gari ma dame gyaran jikin tazo Aunty Amrah ta kirata a waya tazo, na yau kam anfi dirzarta, har ta gaji da k'orafi, tai shiru turaruka kuwa kala kala aka rink'a turara mata na tsugunno dana jiki, da yamma yauma aka gama,nan taji tanata jin jiri Aunty Amrah ta kawo mata milk me sanyi tasha,nan ta kwanta kan kujera tana hutawa, Aunty Amrah kuwa na kitchen tanata aikinta.



******
Sweety da UK motarsu ta tsaya k'ofar gidansu Nahna, wani mugun kallo UK yake bin gidan dashi yana ayyanawa aransa duka gidan baifi kaso d'aya cikin goma na gidansu ba, dukda tsarin ginin gidan yayi kyau amma yayi k'ank'anta abunda yaketa rayawa a ransa kenan,har sweety data shiga gidan kiran Nahna ta dawo ta bud'e k'ofar motar ta shiga tana fad'in " broth bata nan tana gidan d'aya wanta nan k'asa ne ba nisa mu k'arasa can d'in".

Tsaki yaja kawai ya juya kan motar yana bin hanyar data nuna mai,suna tsayawa k'ofar gidan yaya usman ya k'ara kallon gidan ya saki wani tsaki duk gidajan kamar na sadaka wasu kananu dasu wai yar wannan zuri'ar akeso ya aura muttsss nan ya kuma sakin wani dogon tsakin,ita dai sweety bata tanka mai ba ta fice a motar.

Bayan ta shiga sun gaisa da Aunty Amrah suka gaisa da Nahna tace "Aunty nah muna tare fa da Broth a waje, dummmmmm taji gabanta ya fad'i amma saita karanto sunan Allah cikin ranta, Amrah tace " sweety ai munyi zaton sai dare zaizo"

"Hhhmmm ai Broth baya fita da dare Duk yawonsa iya rana ne zuwa yamma".

Ita dai Nahna na zaune bata tanka ba, saida Aunty Amrah taje ta bud'e sitting room ta dawo tace " Sweety kice ya shigo ciki"

Yin duniya sweety tayi yak'i shigowa yace ba zama yazoyi ba,kawai tace ta fito karta b'ata mai lokaci don baiga wajan zama ba a wannan d'an gidan, rasa yanda zatayi tayi kawai saita juya cikin gidan tana fad'in " Kinga yanzu yanzu aka kirashi a waya yayi bak'o a gida kuma daga nesa yake,shine yace tunda yazo kawai ta fito su gaisa ya dawo wani lokacin".

Aunty Amrah tace "ayya,ba damuwa ai Nahna ki fita Ku gaisa to".

Mik'ewa tai a sanyaye tasa hijabinta ta fice, koda ta fita k'ofar gida ta hango motarsa fake a gefe dukda ba sanin motar taiba amma tasan shine tunda motar kad'ai ta gani a layin, tsaye tayi bata k'arasa ba,amma datai wani tunani saita k'arasa gaban motar b'angaran driver ta tsaya, saida ta d'au tsawon lokaci sannan ya zuge glass d'in motar yana Mata wani kallo na rainin hankali, gefe ta kauda kanta tana fad'in " ina yini"

Taki yaja yana kauda kai gefe yace "bashi nazo jiba kuma karki yi farin ciki kiyi zaton ko zance nazo,Sam har abada bazan tab'a zuwa zance gun y'ar Arabic ba,har abada,wato don la'in ba maita da k'aunar da kokemin kin kasa jurewa shine da kika daina ganina a school saida kika bibiyi gidanmu kika zo kika cinye kurwar Abbana da maitarki,harya tura minke wai in aureki,to wlh ki sani zaki gamu da uk'uba ta da kanki zaki bar gidana wlh,ki shirya zaman rashin y'anci don kin jamin an ruguzamin tsarin rayuwata,an tauyeni wlh saikin d'and'ana kud'arki,waima in rasa wa zan aura sai y'ar Arabic, jibi wani tafkeken hijabi da kika saka waike ustaziyya, ni wlh an gama dani,kuma ina so ki karkad'e kunnuwanki da kyau ki jini, domin in kika kuskure koda da wasa kika watsani cikin friends d'ina wlh kin k'arawa kanki bala'i,Kinga dai yanda aka shirya bikin nasan wai ina son bikinba sai don in fita kunyar abokaina,don haka in akazo gaban jama'a kika nuna wa duniya Ke gidahuma ce wlh zaki shiga hannuna, don haka ki bud'e kunne kiji ki k'ara ji friends d'ina zasu zo daga k'asashe daban daban in kika nuna gaban su Ke y'ar Arabic ce ustaziyya hhhhmmmm".

Wani takaicine ya mamaye zuciyar Nahna amma saita rink'a kiran "innalillahi wa inna ilaihi ra'jiun" cikin ranta nan nutsuwa ta sauka a zuciyar ta,takalleshi karo na farko ta kauda kanta tana wani mirmishi na gefen baki tace "duka naji zancen ka,inka gama zan wuce ciki".

Baice mata komai ba ya zuge glass d'in sa yana bawa motar key,
Ganin haka tai wucewarta gida, tana shiga sweety tai musu sallama ta fita,Sam bata bari Aunty Amrah ta fahimci wani b'acin rai tare da itaba, bayan kusan 10 minutes itama ta wuce gida,tana danne duk b'acin ranta.




Taku ce
Y'ar mutan ja'oji???j%??]?j
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??-\ *Y'AN ARABIC* ??-\


NA

LAYUZA KABIR ADAM

DEDECATED TO ALL
ARABIC /ISLAMIC STUDENTS
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd

???a???_%??]IqkpHq?Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI WRITERS ASSOCIOTION*

??Qd
%?'[? ?Z?? ?W??? d??W??? t?k ????uc?t??, M?kti???t?? ?l?? ???lt??W?t?i?l ?kuW? W????????W??UB?? '[? ??



0(???2(???4(???



Saura kwana hud'u a fara biki y'an sakkwato suka fara zuwa mota biyu, washe garin zuwansu akaje akayi Jere(kafi),tunda suka dawo kowa tofa albarka cin bakin sa yake kan tsaruwar gidan Duk da gidan a cikin gidan su yake,kamar yanda mahaifinsa ya fad'a sai ya dawo daga India zamu tare a gidanmu, an k'ara tsara part d'in sosai gashi kayan sun amshi gun,duk zancen da suke ina jinsu araina ina addu'ar Allah yasa in riski farin ciki a cikin gidan ba wai had'uwar gidan ba.


Shirye shirye fa sun kankama don yau laraba gobe Alhamis za'ayi kamu da lecture, yau tun safe bamu zauna ba,k'awayena da y'an uwana duk muna tare gidan me k'unshi wanda muka fita tun bakwai na safe amma har ya zuwa yanzu k'arfe biyar ba'a gamawa mutum uku cikin mu ba wai duk da hakan ma masu kunshin su uku ne a gidan, duk y'an uwana wanda suke sa'annina da k'awayena ban bar kowa ba,sabida ina jin yanda ake k'orafi duk sanda biki ya taso cikin k'awaye ko y'an uwa in amarya ta x
Zab'e wasu ta bar wasu cikin duk hidimarta shi yasa na d'auki aniyar yin iya bakin k'ok'ari na wajan ganin ban b'atawa kowa ba,


Waya ta dake kan cinyata ta d'auki ringing na kalla fuskana d'auke da mirmishi na d'aga wayan" Hello Amarya kin dawo gida ne?"

"Um um sweety wlh har yanzu muna can".

" kai Ku nawa ne haka?"

"Hhhmmm mun kai mu ashirinfa ko ma munfi,amma da yawa an gama don kusan mutum goma sun koma gida saimu sha d'aya yanzu anan".

" ok Kinga muma yanzu muka dawo daka gun k'unshin Kinga duk y'an uwanmu na katsina sunzo, yanzu kan maganar kayan da za'a bada gift ne gobe gun lecture, yanzu masu aikin suka kirani sun gama komai shine nace ina za'a kai a ajiye miki tunda bakya gida".

Shiru nai can nace " Gaskiya gidanmu ba wajan ajiyar kaya Sweety don cike yake da mutane,kuma gidan yaya usman ma cike yake,ina ganin kawai ki ajiye a gidanku sweety goben sai ku wuce dasu gun".

"OK to ba damuwa Aunty nah,ya maganar gyaran kan goben fa da wuri zamuje kar mu shiga lokacin kamu".

" hhhmmm zamu b'ata fa in kina cemin Aunty kawai kicemin Nahna na yafimin dad'i".

" ni dai bazan ceba,ki dai shirya da wuri goben".

Mirmishi nai kawai na kashe wayan.



Bamu muka tafi gidaba sai bayan sallar magriba, a gajiye muke matuk'a ga yunwa damuka tara tun Karin safe sai lemo da biscuit kawai da mukasha, gidan namu babu masakar tsinke don jama'a ana tai mana sannu na sami gefen kujera na zauna ina fad'in "Wash Allah".

Gwaggo na dake zaune kan kujerar tace " sannu Khadijah tun safe sai yanzu dole Ku gaji ai".

D'an mirmishi nai nakai dubana fa Aunty Amrah data shigo parlourn d'auke da abinci tana ajiyewa mutanan d'akin a gaban su, nace "maman biyu bamu key d'in gidanki mu tafi yanzu don Duk a gajiye muke wlh".

D'auko min key d'in tayi tana rad'amin Abu a kunne ".

Girgiza kai na fara ina fad'in " wlh ba ruwa na nifa na fice daga parlourn da sauri ina dariya".

Babbar kula aka cika mana da abinci duka wanda zamu kwana dasu gidan yaya usman suka taso muka wuce.


Kusan raba dare mukai hira da y'an uwana da Aminiyata Hafsah wadda ta had'o kayanta ta dawo gidanmu har agama biki,


Da safe bayan munci abinci mun gyara gidan me gyaran jikin nan sarkin naci tazo wai tunda yau jiya ba'ayiba yau ba inda zanje sai anyi,badan naso ba na zauna aka fara min,
Wayata aka kawo min da take ta k'ara nasan sweety ce koda ban gani ba,ina d'agawa tace "Amarya gamu k'ofar gidan yaya usman ".

" Ku shigo mana".

Bayan sun gaggaisa da jama'a ta lek'o da kanta d'akin da ake min gyaran tana d'an mirmishi tace "y'ar Sudan a gyaramin ita da kyau yanda d'an uwana zai gigice inya ganta".

Hararanta nayi ina mirmishi nace " jirani 10 minutes za'a gama"


Bayan kusan minti a shirin na fito inata zuba k'amshin turaren da ake turaramin jiki wanda ya gama kama fata ta, duban y'an matan nayi ina fad'in " dawa dawa ne basuyi gyaran Kai ba?".

Da yawansu ko wacce da gyaran kanta tazo k'alilanne zasuyi

"To kunsan yanda za'ayi munyi magana da maman Amira me saloon ta cikin layinmu zan kawo mata costumers kuma kunga ni sweety taje ta biya kud'i a sabon gari tayi bucking, don haka Kar maman Amira taga rashin kyautawarmu taga mun gujeta don haka Ku kuje gunta tai muku in na dawo zan bata kud'in ita Hafsah sai muje da ita can karna barta nan cikinku bata san kowa ba zata takura koya kuka gani".

" eh hakan yayi saikun dawo ".

Bayan mun shiga shiga mota Sweety na driving sai Ramla cousin sister d'inta na zaune gefenta nida Hafsah muna zaune baya, ta cikin madubi ta kalleni tana mirmishi tace " Amarya gaskiya kina birgeni wlh yanda kike ji da family naki,komai baki son b'ata musu rai family dinku sunada zumunci matuk'a wlh".

Y'ar dariya nai ina fad'in " kinga kuwa tun jiya su Aziza suke tambayarki kina ina yanzu kuma da kika zo suna can gidan mu buku had'u ba sai zuwa jimawa ".

Dariya tai sosai tace " kai Aziza y'ar is ce wlh harna tuno bidirinmu a sakkwato in muna chart inna tuna mata ces din gidan lalle muyita dariya,inaji da Aziza Duk cikin y'an matan family d'inku nafi ji da ita don Kuna matuk'ar kama wlh dukda kamanninku duk d'aya ne amma kamarku da Aziza ta b'aci shiyasa nakeji da ita".

Hira mukaci gaba dayi har muka k'arasa cikin kasuwar sabon gari, gefen shagon saloon d'in mukai parking bayan ta rufe ko ina na motar muka shige shagon, mutum biyu ne ciki me shagon da yarinyar ta ba b'ata lokaci aka fara min yarinyar kuma ta fara yiwa Ramla.


Kasancewar su k'wararru a harkar gyaran kai yasa ba'a d'au wani lokaci ba aka kammala mana dukanmu muka taho gida.


K'arfe uku aka fara tafiya wajan kamu da lecture wanda za'ayi a sani Abacha an shirya gun sosai son lecturer d'inmu ce zatayi lecture d'in akan zaman aure yanda nake son malamar yasa muka saba da ita sosai babba ce a hukumar hisbah, ina jin lecture's d'inta a gidan radio don haka na k'udurta a raina ita zata min lecture d'in aure na.
Sosai nayi kyau cikin wata rantsattsiyar lifaya y'ar asalin na nad'ata ta zauna das a jikina fuskata d'auke da k'ayatacciyar kwalliya ta amare,kasancewar malama zarah bata son b'ata lokaci a duk lamuranta yasa ta gargad'emu da kada mu b'ata lokaci gun zuwa ai kuwa k'arfe hud'u hole d'in ya cika damk'am da jama'a, hud'u da y'an mintuna ta iso wajan ita da malama khadijah me tafsiri,
Kamu aka fara yi, wanda yake bisa ala'da dangina suka min kamu da turare me k'amshi daga nan fa Mlm Zarah ta fara suburbud'a lecture akan abunda ya taramu a gun, Allah yaiwa Mlm Zarah kaifin harshe da iya jan ra'ayin wanda takewa magana don ya maida hankali ya saurareta da kyau hakan yasa dukkan hole d'in baka jin maganar kowa sai girgiza kai kawai da akeyi (wa'azi ya fara ratsa mata,???i)

Tofa zance fa Mlm Zarah take saki kasancewar Duk hole d'in ba namiji duk mata ne yasa ta k'ara k'aimi wajan sanar da mata sirrikan rik'e miji gam a tafin hannu, wani abin ma inta fad'a kunya saita rufeni Allah yasa naja lifaya ta na rufe fuskata, tofa nan ta fara kwararo batu kan azabar da Allah ya tanadarwa matan da suke muzguna ran mazajensu,zo kuga jikin mata yayi qlau Duk jiki ya mutu, tana fad'in girman aure da matsayinsa cikin musulunci da yanda ya dace mace ta girmama mijinta, ban k'ara karaya ba saida naji ta waiwayo kan batun biyayya kan macen data auri mijin da bata so, dole ne ayiwa miji biyayya koda kuwa ba'a sonshi, haba Duk sai jikina ya k'ara mutuwa,
Lecture na awa d'aya da rabi tayi tai dagargaza sannan Mlm Khadijah me tafsiri ta tashi ita kuma,ta fara bada wasu sirrika da kissosi nan fa tafi da kabbara suka b'arke a gun, har Irin tafiyar daya dace mace tayi a gaban mijinta saida ta nuna haba wa nanfa na k'ara tsumuwa inaji araina anya duk zan iya wannan abubuwan da suke fad'i kuwa.
Minti talatin Mlm Khadijah me tafsiri tayi, sukai sallama tare da addu'a suka rufe taro, kayan rabo kuwa daman kowa an bashi nashi tun mutum zai shigo ake dank'a mai jakarsa a hannunsa ya shigo hole d'in da ita maganin mutum yace bai samu ba.

Su kuwa malaman gift na alfarma aka shirya musu sosai farantai manya aka shishshirya musu kayan snacks dasu naman kaji aciki lemo da ruwa ma katan biyu biyu aka sa musu tare dasa musu kud'i dubun ashirin matsayin su zuba mai a mota wanda Ummu sulaim ce yayar sweety ta basu kud'in aka rakasu har mota anata musu godiya tare da amsar number wayoyinsu kowa na cewa zata gayyacesu lecture.



Haka ma tunda muka dawo gida labarin wannan lecture ake musamman y'an matan da iya shege zasu tuno wani abun su kwashe da dariya suna fad'in " Nahna da fatan dai lecture d'in nan ta shiga kanki kije ki girgiza Umar".

Mirmishi kawai nake ban tankawa ko waccen suba na wuce toilet na gasa jikina da ruwa me zafi sannan na d'auro alwala nazo nai sallar magriba na maida isha'i don har an fara kiraye kirayen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login