Showing 102001 words to 105000 words out of 137542 words

Chapter 35 - YAN ARABIC Book Complete By Layuza Kabir.doc

na fito zuwa part d'in masu aikin, sumun su nai har sunyi wanka sun k'ara gyara part d'in nasu batun abunci daman da kitchen d'insu a ciki ansa musu duk kayan girki zasu rink'a yin nasu da masu aikin maza, cikin sauri suka shiga gaida ni na samu waje na zauna muka gaisa, nan nace karima da Binta suzo muje su tayani aiki su bar Baba ta huta ita.




Munata aikin abinci amma hankali na bai tare dasu ko sweety data shigo ta amsa ragamar aikin tanata min tsiya da tsokana nako kasa amsa mata sai dai yak'e nake,ji nake kamar zuciyata zata faso k'irjina ta fito don fargaba, a haka wajan sallar azahar aka gama komai aka shirya su a wasu k'ayatattun warmas masu d'aukan ido,tsaf muka shirya dining table d'in duk girmansa saida muka cikashi da kala kalan abinci da kayan mak'ulashe, k'arfe hud'u zai shigo gida don haka bayan mun gama komai sun k'ara gyaramin gidan suka koma part d'in su.


Wanka nai nazo na zauna bakin gado gabana na k'ara tsananta fad'awa jikina harya fara rawa, ambaton Allah nai tayi sannan nutsuwa ta saukar min, cikin rashin kuzari na kimtsa tsaf cikin wata doguwar riga y'ar k'asar dubai pink color ce an mata adon stone silver, kyau iya kyau rigan nadashi, jikina na wanke tsaf da turare masu d'aukan hankali, bansa d'an kwali akaina ba gashi na da yasha gyara na k'ara tajewa na shafeshi damai sannan na sake shi ya zuba baya, na d'auko plate d'in takalmi kalan kayan nasa a kafata don ban yawo ko cikin d'akina ne ba takalmi sabida sanyin tile's, kasancewar cikin sanyi nake yin komai yasa na d'au lokaci don Dana duba agogo ya muna min uku da kwata, na tabbata zuwa 30 minutes zai iya shigowa gida, don su sweety ita da Abba dasu yaran tuni suka k'arasa Airport don tararsa,


Parlour na dawo na zauna ina tunani kala kala cikin raina, can naji tsayuwar motoci a harabar gidan da sauri naje jikin window d'in da zai sadani da kallon duk abunda ke wakana a k'asan harabar, shine ya fito daga motar sanye da k'ananun kaya jikinsa kalan brown Wanda suka amsheshi sosai k'afansa sanye da brown takalmi sau ciki,haka ma fatan agogon hannunsa take brown, kallo d'aya zaka mai ko daga nesa ne ka tabbatar da tsantsar kyawun da yayi hakama fatar jikinsa tai frees alamun ana hutawa. Gaisawa yake da ma'aikatan da suka taso suna gaida shi,yayin dasu Abba da duk y'an rakiyar tashi sukai mai sallama suka juya zuwa gida Abba yace abarshi ya huta zuwa jimawa sa k'ara gaisawa.


Yanda yake taka k'afafunsa yana tunkaro cikin gidan haka k'arin bugun zuciyata ke tsananta, gumi ya gama lullib'e ilahirin jikina,k'afafuna da hannayena wani bala'in karkarwa suke, na jingina kaina jikin window d'in ina ambaton Allah da neman d'aukinsa.


A babban parlourn k'asa ya dakatar da ma'aikatan da suka biyo shi da jakunkunansa, tsayawa yai yana k'arewa parlourn kallo fuskar sa d'auke da mirmishi kallo yake yaga ta inda zan bayyana jin shiru yasashi sakin wani k'ayataccan mirmishi ina k'iyasto dad'in da zai kwasa yanzu ba anjima ba,juyawa yai ya rufe k'ofan parlourn ya fara taka k'afafunsa zuwa matakal da zata sa dashi da saman benan, cikin wani cool voice yake fad'in "my pretty! my angle! my heart! my sweetness! My heartbeat fito mana in ganki idanuwa da ruhina duka sun matsu su ganki don Allah yi sauri ki fito ina marmarin jinki a cikin k'irjina, zo inji d'uminki, fad'a yake yana lallek'a d'akunan harya k'araso d'akin da nake ganina tsaye na juya baya yasa shi k'arasowa da sassarfa yana fad'in" badai fishi kuma ake dani ba don na dad'e ban hayo saman ba, wata wawuyar runguma yamin ta bayan yana kwantar da fuskar sa akan wuyana tare da sakin wata nauyayyar ajiyar zuciya, matseni ya k'arayi a jikinsa yana jin wani nishad'i na saukar mai, a hankali ya juyo dani idonsa a lumshe yana k'ok'arin sanyani cikin k'irjinsa jin abu ya tokare shi yasa bud'e idonsa yana kai kallon sa ga cikina, k'ara bud'e idonsa yai sosai don yaji kamar gizo abunda ya gani idonsa kemai d'an janye ni baya yai yana kai hannunsa kan cikin ya danna jin tauri yasa shi d'agowa da sauri yana kallona Wanda zuwa lokacin har hawaye ya gama jik'a fuskata jikina kuwa kamar mazari haka yake rawa idonsa ya zuba sosai cikin nawa yana son tunano meyema wannan a jikina, don shi duk tunanin sa ya tsaya,tsawon lokaci muna tsaye a haka,a hankali kuma ya zame jikinsa a jikina ya zauna bakin gadon dafe da kansa, ni kuwa banma sami sukunin zaman ba ina dai tsaye jikina nata mazari kamar nayi sata an kamani, can sama da mintina goma ya d'ago da idonsa da suka kad'a ya saukesu a kaina, cikin k'arfin hali ya fizgo maganar dake son fitowa daga bakinsa, "Khadeejah meye wannan a jikin ki"?.

Sunkuyar da kaina k'asa nai don banda amsar bashi,muryarsa naji tsakiyar kaina yana k'ara tambaya ta Karo na biyu, nanma ba amsa shiru nai,wata razananniyar tsawa naji ya sakar min karo na uku yana tambaya ta meye wannan a jikina, jinai cikina ya murd'a abunda ke cikina ya dunk'ule ya tare waje guda sanadiyar haka naji fitsari ya fara bin k'afafuna, cikin sark'ak'k'iyar murya na fara fad'in" Kayi hak'uri don Allah ka yafemin wlh ban san ya zaka d'au lamarin ba shiyasa ban sanar dakai ba tun tuni".

Hannu ya d'aga min yana mik'ewa tsaye cikin tsananin b'acin rai yace "ba wannan na tambayeki ba ca nai ki fad'a min meye wannan a jikin ki".

Cikin tsananin kuka nace " Ciki ne".

"Ciki ? wa yai miki shi".

Cikin firgici na d'ago idona a kansa ina kallon sa, kafin daga bisani naji zuciyata ta soye kukan ma ya d'auke k'af nace " Me kake nufi ne umar me kake nufi? Kana tambaya ta wayamin ciki akwai Wanda zaimin ciki ne bayan kai,to kai kamin shi cikinka ne dana taho dashi daga India Wanda na same shi satin da zan baro India, inka so ka yarda".

Zuba min ido yai cikin tsananin b'acin rai yana gyad'a kai yace" naji naji amma meye dalilin da kika b'oyemin tun sanda kika san da zamansa a jikin ki,Khadeejah tun yaushe nake fad'a miki ban shirya fara tara y'ay'a ba sau nawa na sanar dake haihuwa bata cikin tsarina a shekara uku ma nan gaba, na sanar dake ban so ban so, ban shirya tsufa yanzu ba,banso ban marmari,amma don ha'inci irin naki sai kika b'oyemin tun sanda za'a iya zubar dashi,yanzu a lissafe nasan yafi wata takwas yanzu duk dabarata nasan sai kin haife wannan cikin, tom kinyi kuskure na farko a cikin rayuwar ki ,saida kika bari na aminta dake sannan zaki haince ni,to kije ki haifeshi ki raini abunki".



Daga haka yasa kai ya fice yabar d'akin.







Taku ce
Y'ar mutan ja'oji???jA???
??1]??1]??1]??1]??1]??1]
??-\??-\??-\??-\??-\??-\
*'YAN* *ARABIC*
??-\??-\??-\??-\??-\??-\
??1]??1]??1]??1]??1]??1]

*NA*
*LAYUZA* *KABIR* *ADAM*

_DEDICATED_ _TO_ _ALL_
_ARABIC_ / _ISLAMIC_ _STUDENTS_
??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd??Nd


???a???_%??]IqkpHq??Fq?p? ?]Iq??
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
??Qd
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_



0(???4(???9(???


Da kyar yakai kansa d'akin dake daura da nata dafe da kansa ya fad'a bisa faffad'an gadon yana runtse ido tare da furzar da iska me zafi,cije lips d'in sa yai yana fad'in "why why? Khadeejah zaki min haka,me yasa zaki yaudareni,me yasa zaki b'oyemin? Kin san yanda na dawo da k'ishin ruwan ki kuwa,kinsa yanda zuciyata kemin rad'ad'i kuwa,na tara buk'ata ta watanni takwas ina zumud'i da marmarin k'arasowa gareki ki biya min buk'ata ta amma gashi daga dawo wata naci karo da bak'in ciki da b'acin rai, naci karo da abunda ya canja tunani, kin yaudare ni Khadeejah, kin kutso min abunda ban tsarashi a tsarin rayuwata ba a kusa,zan janye miki in barki da cikin in zai baki farin ciki da kwanciyar hankali tunda shi kika zab'a akaina".

Surutai yai tayi marasa tushe yana bubbuga kai jikin katifa,wanda b'acin rai ya saukar mai da wani mahaukacin ciwon kai, kwanciya yai lif bisa gadon bai san takamaimai ma halin dayake ciki ba tsawon lokaci yana a haka.


Bin bayansa nai da kallo harya bar d'akin na saki wani kuka me cin rai, nadama da dana sanin auran sa nake a wannan rana,na gama kyautata zaton d'abi'unsa sun dai daita ashe da sauran rina a kaba, dukda dai nasa ni kuma na tabbata daman hakan zai faru amma bansan wannan maganganu zasu fito daga bakin sa ba, ba komai kamar yanda ya fad'a inje in kula da cikina tunda shi na zab'a to zanci gaba da kula da shi har Allah ya rabamu lafiya kuma Allah ya rayamin abunda zan haifa.
Tashi nai na d'auro Alwala don kaiwa Allah kukana da neman sassauci yanda zuciyata ke rad'ad'i da k'unci.

Har sallar magriba ina zaune kan prayer mat inaiwa Allah tasbihi da zikiri,ina kai kukana gareshi da neman d'aukin sa cikin wannan cakwakiya data taso min.




Bayan sallar isha'i na fito zuwa parlourn k'asa cin karo nai da dukkan kayan Abincin dana jera ba'a tab'a komai ba,hakan ya tabbatar min baici komai ba kenan,tunani nake a raina,tabbas nasan mijina bai wasa da cikin sa kuma duk yanda akai yanzu yana cikin yunwa,yanzu kenan haka zan barshi ya kwana da yunwa ga abincikan dana b'ata lokaci wajan had'a su, zasu zama asara kenan fa, kasancewar zuciyata tai sanyi yasa na taka a hankali na koma saman, k'ofar d'akin sa na nufa knocking na farayi a hankali kusan sau biyar na k'wank'wansa ba'a tanka ba ci gaba da knocking d'in nai har na fidda ran za'a amsa min sai kuma naji yace"waye " cikin wata dashashshiyar murya me cike da tsantsar b'acin rai.

Tausasa lafazi nai a sannu nace " Nice,daman zan fad'a ma abinci na dining fa".

Had'e rai ya k'ara yi sosai ciki ciki yace " bana buk'ata kije kawai" .


Wani k'ululun bak'in ciki ne ya tasomin yake k'ok'arin mamaye d'an sassaucin dana samu, cikin mutuwar jiki na juya zuwa d'akina ina ambatan sunan Allah. Sabida ni akoda yaushe sunan Allah bai gushe min ko cikin tsanani ko sauk'i, koda na koma d'akina kwanciya nai ina share hawayen dake ziraromin.tabbas nasan zan fuskanci haka daga UK don haka dole in koyi dauriya in sawa raina har ranar da Allah zai kawomin mafita kan lamarin.




**********
Juyi kawai yake kan gadon cike da tarin damuwa, zuciya a kuntace rai ba dad'i, ga wata yunwa na sakutar cikinsa ji yake kamar yaci babu,ya daure ya daure amma fa abun ya faskara ganin zai halaka donshi mutum ne bame wasa da cikin saba yasa ya mik'e ya fito k'ofar d'akin ta ya kalla yana sakin tsaki, a sannu ya sauko zuwa k'asa kai tsaye ya haye kujeran dake dining d'in bubbud'e warmers d'in ya farayi k'amshi ya cika hancin sa,nan da nan yaji wata kahaukaciyar yunwa ta k'ara taso mai.da sauri yai serving d'in kansa ya fara cin abincin ba kad'an bafa yaci iya ci tare da shan drinks d'in masu d'an karan dad'i,mik'ewa yana mik'a tare da fad'in 'Alhamdulillah ".


**********
Haka na kwana ba ishashshan bacci don haka ina sallar asuba na koma bacci me nauyin gaske ya d'auke ni Wanda bansan adadin lokacin dana d'auka yinsa ba. Kawai cikin kaina naji hayaniya anamin ihu aka, da ambaton Allah na tashi ina gani dishi dishi ,tsaye na ganshi rik'e da k'ofan d'akin yanata wani uban muzurai" ke malama dake nake ina abincin break d'ina kika kwanta bacci har k'arfe tara".


Da sauri na kalli agogo saina fara k'ok'arin sakkowa a gadon ina daddafawa tare da rik'e mara irin dai na masu tsohon ciki. Wani wawan tsaki naji yaja tare da sakin k'ofan d'akin ya juya,jiki a sanyaye na k'arasa sauka zuwa toilet nai fitsari ko wanka ban tsaya yiba na wanke fuskata na fito,sauka nai zuwa kitchen d'in k'asa na fara k'ok'arin had'a me saukakken abun karin kumallon, doya da k'wai na soya tare da daga ruwan tea daya sha kayan k'anshi, sai sauran parfesun jiya na d'umamashi, zuwa nai na kwashe duka kayan dining table d'in anan naga uban abincin daya d'iba,girgiza kai kawai nai na kwashe kayan tas nakai kitchen sannan na gyarashi na jera mai girkin.
K'ararrawar d'akin masu aiki na danna,bayan Lami ta shigo nace tayi wanke wanke ta gyara kitchen d'in, sannan na koma d'akina.


Wanka nai na tsara kwalliya bame tsauri ba sannan na shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi don yanzu babu kayan da nake jin dadin su kamar dogayan riguna, turare na feshi jikina dashi sannan na fito zuwa d'akin nasa inata knocking ba'a amsa ba nai tunanin kulawa ne bazai ba dana lek'a k'asa ta tsakiyan k'arfinan da akaiwa corridor d'in ado dashi saina hangoshi yanata uban kwasar girki.
d'akin na shiga na fara gyara mai dukda dai komai k'arfin hali nakeyi,sabida yanayin jikin nawa,na wanke mai toilet tas tunda daman ba wani datti bane ,sannan nasa mai freshener na d'akin ya d'au k'amshi, ina k'ok'arin fita ya turo k'ofar ya shigo,matsawa gefe nai na bashi hanya,baiko kalleni ba ya wuce risinawa nai kamar yanda na saba na gaisheshi ciki ciki ya amsa min ya wuce bakin gadon ya zauna yana saka safa da takalma, jinai zuciyata ta karye hawaye ya kunshe min,a sannu na k'arasa gabanshi na tsugunna tare da rik'o k'afafunsa cikin shashshekan kuka nake fad'in "Ka yafe min mijina ka yafewa laifina,insha Allah bazan sakema laifi makamancin wannan ba,wannan d'in ma bansani ba rabo ne ya ratsa bansan na samu wannan cikin ba".

D'aga min hannu yai cikin razanarwa " karki raina min hankali mana ,don kin maidani gara zakice tsautsayi ne, in rabo ne me yasa da kikaga cikin ta bayyana biki sanar min ba tunda wuri insa a zubdashi,ai na fad'a miki ban son haihuwa yanzu ban shirya zama baba ba yanzu,d'an yaro dani anmin aure cikin shekarun k'uriciya na hak'ura na amsa kuma ma sai ciki sai haihuwa, shi kenan mutum ya zama tsoho, wlh impossible, badai dani ba".

Yana kaiwa nan ya janye k'afar sa yabar d'akin.

Niko nace( oh??9? me hali baya fasa halinsa,anata murna UK ya shiryu ya gyara d'abi'unsa ashe da sauran rina a kaba)

Bin bayan sa nai da kallo ina share hawaye na,cikin zuciya ta nake rok'on Allah ya dafamin ya kawo min agajin sa cikin lamarin nan.


Yana fita kai tsaye gidan su ya shiga don jiya yana cikin damuwa Sam bai samu damar komawa sun k'ara gaisawa dasu ba.

Yanda Abba yai tunanin ganin sa cikin tsananin farin ciki ba haka ya ganshi ba,don fuskar nan tashi d'aure tamau yai sallama cikin parlourn Abban ya shiga, binsa yai da ido yana mirmishi yace "Babana ka samu fitowa ".

Zama yai sosai gaban Abban yana d'an kalato fara'a ya risna ya gaida shi,cikin farin ciki yake amsa mai tare da tambayar sa ya hanya ya gajiya kuma.

Cikin d'an yak'e yace " Abba gajiya ta gudu sai abunda ba'a rasa ba".

"To masha Allah, ina fatan dai komai lfy ko".

" eh Abba,ina Aunty murjah ?".

" Taje kawo min abinci ,amma kuma Daddy ya naga fuskar ka kamar da matsala".

D'an shafo gashin sa yai yana d'an tsakin gefan baki yace "A'a Abba ba komai kawai kaina kemin ciwo tunda na tashi a bacci amma na sami magani ma a gidan nasha".

"To Allah ya sauwak'e gajiya ce kawai kuma daka sani ka kwanta ka huta sosai zuwa azahar sai ka fito".


Zaiyi magana Aunty murjah ta shigo d'auke da kayan Abinci fuskar ta kuwa cike da fara'a tace" A'a mutanan k'asar Hindu har ka fito ".

Cikin mirmishin yak'e yake gaisheta bayan ta sauke kayan abincin, zama tai tana amsa mai da tambayar sa ya gajiyan hanya,sannan ta had'awa Abba abincin suna d'an hira kad'an kad'an .

" Daddy matso muci Abincin mana".


Girgiza kai yai yana fad'in "Wlh Abba a k'oshe nake sosai yanzu na gama break fast".

Dariya Aunty murjah tai " Haba Abba kaima dai tsokana kakeyi yaushe zaici abincin mu ,bayan kasan y'ata ta cika mai ciki da kayan dad'i ".

Dariya sukai ita da Abba amma shi kam d'an mirmishi yai yana shafa kansa.


Jimawa kad'an Aunty murjah ta tashi ta basu waje don su D'an tattauna, Abba nacin Abinci suna hira yana mai tambayoyi kan karatun nasu da company nin da suka bud'e.


Yaso cinye maganar cikin nan Amma abun bazai cinyu ba,don haka ya k'ara gyara zama yace " Abba kasan sama Khadeejah nada ciki".


Fara'ar Abba ce ta yalwata yace "Eh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login