Showing 3001 words to 6000 words out of 110493 words

Chapter 2 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2270

amma ba zan taba barin ta sani ba insha Allah kome ko zaka fada min.

Hannu ya kai ya kara dago photon ya kurawa hoton idona dan lokaci kafin ya sauke ajiyan zuciya ya kalleta duk da akwai duhu a lokacin hakan bai hana yaga yadda ta kafesa da idanunta ba .

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/21, 10:28 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

0️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Mayar da kai yayi sauke daga kallonta kafin yace kinyi gaskiya Nana hakika wanan kece tare da mahaifanki na asali da suka haifeki suka kuma yi sanadin zuwanki duniya.

Wanan da kike gani itace mahaifiyarki data haifeki sunanta Nana Asiya amma ana kiranta da nana a inkiya dashi mutane sukafi saninta dashi.

Nana kanwace ga Ammah uwarsu daya ubansu daya gaskiyace keba yar jinsin bakake bane tunda mahaifinki gashi balarabe kina gani.

Asalin faruwan hakan kuma ya samo asali da bayar da mahaifiyarki da mahaifanta sukayi riko ga wata hjy yar uwarsu daga karshe ta dauketa zuwa saudiya.

Da sunan neman kudi a can bayan ta kwadaitawa iyayyensu irin makudan kudin da zata samo masu acan din idan ta dawo daga can .

Mutanen kauye basu yarda ba harda ita mahaifiyar su ammah din amma da yake dangin ubane ita hjy ba yadda ita mahaifiyar tasu zatayi.

Inda yarda da ita kuma gata yar uwa yasa mahaifansu maza suka dauki nanan suka kara danka mata ta tafi da ita kasa mai tsarki na tsawon shekaru.

Ba a sake jin duriyansu ba sai labarai kala kala ke zuwa game dasu inda kowa ke fadan labari daban daban akan shirunsu a can din .

Sai bayan shekaru masu yawa don har kowa ya fitar da rai ga sake ganin su saiga Nana ta dawo muna da goyonki kwatsam da rana tsaka.

Wanan babban tashin hankalin ya dagawa mutane hankali tare kawo muna rudani da tashin hankali sosai a lokacin yan uwa da abokan arziki hankalinsu ya tashi ainun da gani haka .

Nan tsegumi ya fara tashi haka kuma wa yanda sukai Sanadin abata nana ta tafi da ita a lokacin daga baya duk suka jaye hannunsu suka koma gulma da nune ga iyayyensu.

An tutse nana aka tayi bayanin yadda ta samu ya amma ta kasa bayani ssboda kukan da take aiki yi hakan yasa mahaifinsu ya kwanta ciwo jinya mai tsanani yayi a lokacin duk sanadiyan hakan daya faru.

A gidan mu kawai nanake samu kwanciyan hankali a duk fadin kauyen nan zatazo ta wuni taci tasha sai daren kwana zata koma gida.

Haka kuma washe gari zata dawo nan tunda safe haka tayi ta faman yi a lokacin don yadda mutane har gungu sukeyi do zuwa ganin yar balarabiyan da tazo da ita a goye wace ta zamo abun kallo a wajen mu.

Wanan dai in gajarece maki ciwon mahaifinsu ya kara tsananta sosai har yakai yayi ajalinsa ganin haka yan uwa suka kara hattaranta akan sanadintane mahaifinsu ya mutu don bakin cikin abun kunya dataja masa a gari.

Suka kori nana daga gidan ta dawo nan gidan mu da zama a wajen mu ta zauna inda Ammah ke faman dawai niya da ita da yarta sannu a hankali tafara sakewa tana rage damuwa har yar uwarta Ammah ta samu jin labarin abinda ya faru zuwansu saudiya da taki ta fadawa kowa da farko.

A yadda tace da suka je can sana,a take sosai kashe rika suna samun kudi amma kudin ba nata bane na hjy ce.

Don har hjy ta gina gida anan kano da iri kudin da take turowa a nan gida Nageria kuma ashe ita hjy din takan shigo nageria tayi abinda zatayi ta koma ba tare data je kauyensu ba.

Ana cikin haka da girma ya soma ita nana hankali ya fara zuwa mata ta nemi da ta koma gida amma hjyn ta hana don takarrdun da komai nata na wajen hjyn .

Dama kuma haka sukeyi da anje can ance sai su karbe takardun tafiyan ka sai kagama masu bauta ka gama wahala zasu fito maka dashi a lokacin kaima zaka fara neman kudi ka.

Suna hakane har Allah ya hada ita nana din da wani balaraben mutum shi wanan da kike gani a jikin photon dai da shakuwa yai shakuwa a tsakanun su har ya nemi auren ita nana a wajen mutanen su nacan.

Wanda ba tunanen komai hjy din da sauran shuga banin su suka taru suka aurawa nana wanan mutumin acan suka sha bukinsu batare da kowa na ita nana ya sani ba ana gida.

Yadda ta fada muna zama sukayi na so da kauna dashi na fi sabi lilah har Allah ya kawo masu rabonki aka samu cikinki a lokacin.

Wanan mijin nata tace yayi murna sosai da samun karuwankidon ya gwada mata gata iya gata kamar yadda Allah ya umurta a nunawa iyali.

Har Allah ya sauketa lafiya suka radawa yarinya sunan nana Aeesha ma,ana Aishatu a nan dai wajen mu.

Ya kula dasu yadda ya dace sosai ko bayan haihuwanki din kwatsan suna nan ta fara ganin canji a gurinsa na wasu dabiun da bata sanshi dasu ba daga baya ya fara nuna hattara da tsana daga ita har yar nata.

Abinda nana bata sani ba shine ashe auren contragi yayi da ita nawani dan lokaci dama sai kuma aka samu akasin hakan rabo ya shiga tsakani a lokacin.

Shi aiki ya kawoshi saudiya yayi wanan aurene don kaucewa zina kamar yadda sukeyi acan din wanan yasama ya zabi bakar fata yayi auren hakan da ita.

A nasa shirin idan zai koma gida kasansu saiya sallami ita nana din sai kuma rabonki tsakaninsu ya shiga ciki wanan ne ya daga masa hankali a lokacin.

Har ya fara nunawa nana da yarta wanan halin gashi kuma kasansu sun fara matsa masa lamba ya dawo gida hakana son har ya kara lokaci a can.

Kwatsam nana ta wayi gari bashi sai takarda da kudi masu yawa daya barmata wanan ya dagawa nana hankali sosai a lokacin.

Mutanen su nacan ta fara nema ta sanar masu da abindake faruwa kinsan halin mutane sunga wurin cin kudi sai suka fara karban kudi a hannun nana da sunan suna taimaka mata a lokacin a gano inda Abduljalil ya shiga.

Dadewa dasu yasa nana din ta farga da abinda suke mata kudinsu kawai sukeci suna mata karya bayan haka ba wani taimakon da suke mata a lokacin sai karairayi na yau daban nagobe daban.

Don haka ta daure bakin aljihunta ta tsuke wanan ya kawo sukai mata sheri ganin ga dukiyan da miji ya bar mata ya gudu ya koma kasansu sai sukai shawaran yi mata cune ga askar dinsu nacen.

Don idan ta baro can din su koma su mallake komai nata wace tayi shekaru mai yawa a cikinsu tasan hakan zai iya faruwa don hakane ko yaushe tana tafiya da dukiyanta a jikin ta da komai a cikin jikinta tace.

Kwatsam kuwa rana daya sai gashi Askar din sun sallama mata akan suna tuhumarta ta hauro kasan ta kazamin hanya tazo nan tana aikata alfasha a kasansu.

Wanan abin yayi sanadin da suka hada da ita da wasu da aka kama suka ingizo keyansu zuwa nan Najeriya shine ta nufo gida a lokacin kwatsam muka ganta.

Kinji Nana duk abinda mutane ke fada a kanki cewa ke shegiyace baki da uba ba gaskiya bane kedin har halak ce kamar ko wani da a duniya illa akasin da aka samu naki kaddaran yazo a haka.

Ya dago yana kallona zuwa lokacin hawaye ya gama bata min fuska don kuka nakeyi shafe shafe ya shiga lalashina a cikin tashin hankali yana fadin.

Na dauka shekarun ki yakai na rugumar kaddara a yanzu yasa na yarda na fada maki asalinki da muke boye maki a yau ai nana da nasan ba zaki iya jure hakan ba da banyi gangancin baki wanan labarin ba a yanzu.

Wanan kukan da kikeyi zai iya jawo hankalin makwabata su yi zaton ko wani mugun abin nayi maki gashi ni kadaine dagani saike a gidan nan yanzu.

Jin hakan yasa ta tsagaita kukanta don gaskiya Abbun ya fada balle tumba ta aiko kan tazo gidan nasu kamar yadda uwarta Ammah ta fada.

Tace anan zata kwana bata zuwa can din tuno hakan yasa ta mike zuwa dakin kwanta ta kwanta shima Abbu din bai kara cewa da ita komai ba a lokacin don zuciyarsa da ba dadi.

Saboda tuno da abubuwan da suka faru a baya game da yarinyar yasan dole sai hakan ya faru dasu don tun suna boye mata dole wata rana zaizo da zasu fada mata gaskiya akan zancen ta.

Haka kowan su ya kwanta da bacin rai ga Aeesha ba zancen barci a ranan haka ta kwana tana tunane akan mahaifanta dataji labarunsu a yanzu wanda abin ya tsaya mata a zuciya sosai.

Sai tambayan kanta takeyi da meyasa ya rudi mahaifiyar ta har ta yarda da hakan yasan ba auren fissabillah yayi mata ba a lokacin.

Da irin zancen nan ta kwana a zuciyanta idan tace tayi barci a wanan ranan karya ta fada yadda taga rana haka taga dare a wajenta dukko da dun,bin gajiyan dake jikinta ta nemeshi ta rasa a rana.

Hakan yasa washegari ta tashi da wuri jin Abbu ya fita zuwa massalaci itama ta tashi tayi sallah bayan ta idarne ta fito ta hasa wuta don yin dumamen da zasu karya dashi.

Koda ya dawo har kunu takai ga dama masu da dan guntun gumban da Ammah ta rage har ya saura zuwa wani lokaci Abbu ya dawo daga masallacin da tasbaha a hannunsa yana ja.

Shimfida ta shiga ta dauko masa tayi mai a wajen da yake zama tare da dauko abun karyawan ta jera masa yadda Ammah dinta ke masa a kullun idan zai karya.

Albarka da fatan alherin daya saba jero mata ya dinga saka mata duk da yasan a ranan hankalinta ba a kwance yake ba alama ya nuna tana cikin damuwa sosai a lokacin.

Ta juya zata shiga dakinta taji muryanshi yana fadin nana zonan yaki yana nuna mata gefenshi da alaman tazo ta zauna zaiyi magana da ita lokacin.

Kamar itama yasan da sauran zancen da take son tambayanshi a lokacin kasan zuciyanta ta dawo ta dan tsuguna a gefenshi don ta kasa zaman daidai yadda ta sabayi dashi a lokacin.

Kafin yakai ga furta mata wani zance yaji ta jefo masa tambaya tana fadin Abbu dama nace yanzu ina ita wanan Nana din take da kace itace mahaifiyata ?

Ya dan murmusa a fuskanshi yana kada kai tare da kai loman tuwon da ya yanko a bakinsa yace Nana nan insha Allahu muna sa ran hakan saida tana can kasa mai tsarki don can ta koma.

Duk da dai bada yardan mu tayi hakan ba don data kawo shawaran komawa can din daga baya bamu yarda mata da hakan ba sai ta shamace mu ta sulale ta koma ba tare da sanin bu don ba zata iya rayuwan nan ba don acan ta taso tayi rayuwanta da komai.

Hankali ya so ya tashi bayan batanta saida na zaunar da ita Ammah nan na bata magana don tafiyanta ya nuna tabar muna amananki a hannun mu nida Ammah din don wayiyar gari mukayi muka nemeta muka rasa a lokacin.

Sai ke kadai a dankin kwanan kwace da yar takardan da wasu tarkace cikin leda data bari a gefen ki na daukeki Ammah ta bude ledan kudine a cikinsa masu yawa sai sarkan gwal guda biyu a cikin wani leda daure.

Ganin batarta zai iya jawo magana tun kan mutane su farga da hakan yasa nayi shawara da ita Ammah washegari nazo nan cikin kano na saya muna wanan gidan nan a wanan unguwar a cikin kudin.

Nakoma can kauye ba wanda yasanda hakan saiji sukayi kawai munce munbar gari zuwa nan cikin kano da kowa nawa wanan yasa kikaga ko dayan mu zaije gida bamu yarda muje dake har yau din nan don gujewa abinda zuwan naki zai haifar a kauyen mu din.

Gudu tayi ta barni ke nan a wajen ku itama na fada ina kallon fuskan Abbu din da alokacin shima ransa a bace yake da tuno da abubuwan da suka faru a baya.

Cikin murmushin yake yace dani ba zance gudun tayi ba kuma zan iya cewa hakan don hankalinta nacan kan nema maki inda zataji labarin mahaifinki daya tafi ya barku da kuma makomar dukiyanku data baro a can a lokacin.

Wanan nake zargin ya mayar da ita wacan kasan a lokacin don mun taba samun labarinta wurin wani mutumin garin mu inda har tabada sako garemu yace taji dadin ganinsa kuma shima din yace bai ganta a mugun kama ba lokacin.

Kinga ke nan duk inda nana take tana cikin koshin lafiya haka kuma muna a ranta musanman ma ke din nan da a yanzu tasan kin girma kin kai munzalin hakan a girma.

Ba abinda muke kullum sai adduan Allah ya karkato muna hankalinta zuwa gida ta dawo cikin yan uwa kamar kowa wanan shine fatan mu a yanzu.

Ki godewa Allah nana da kika taso a cikin mutuncin daba duk ya zata samu hakan duk da muke ba mu muka haifeki ba Allah ya dora muna kaunarki a zukatan mu fiye da yayan da muka haifama a ciki mu a yanzu.

Don ke din kin kasance ammace a wurin mu idan munyi maki rikon daba daidai ba ranan gobe kiyama Allah zai tambaye mu wanan a bainan jama,a.

Na sani Abbu banda kamar ku a fadin duniyan nan koda kuwa yau uwata da ubana zasuce zasu dawo gareni basu kaiku girma da daukaka ba a idanuna.

Masha Allah tunda har kin san wanan to ina son ki cire duk wata damuwa dake kasan zuciyarki game da iyayyenki a yanzu haka kuma ki daina kwankwanto koke wacece daga wanan ranan .

Don kema ya ce kamar kowa da aka samu ta hanyar halak banson in kara ganin ki a cikin damuwa wanan kaddarankice da Allah ya zano maki tun farko.

Abbu yayi min magana da zasu kwantar min da hankali da wanda zaisa kada inga laifin mahaifana da suka haifoni kuma suka kasa rikona a hannunsu don saba lamba.

Da haka Abbu ya fita zuwa kasuwa bayan ya ban dari yace insai taliyan hausa in sulala da rana inci komawa nayi daki naci gaba da tunanen duniya don har yanzu zuciyana ya kasa gaskanta labarin da Abbu ya ban game dani din ashe mutane sunyi gaakiya da suke dangantani da larabawa tabbas ni din yar balaraben asaline ashe .

Jinin sune a jikina kamaninsune na kwaso nake ruwa dasu jinin su shiyafi karfi a jikina bisa ga na mahaifiyata wanan tunanen na wuni yi ni kadai a gida da haka har barci ya daukeni ban sani don idona dake da rankon barcin jiya da banyi ba.

Koda ta falka karfe ukun rana ya gwauta a gagauce ta debo tuwa a randa ta shiga bayi ta watsa ruwa tafito tayi alwala zuwa sallah bayan ta idar wanan hoton dake gefenta ta kara jawowa ta zubawa matar jikin photon ido na dan lokaci tana nazarinta.

Tabbas ko a cikin hoton rayuwa ya nuna tana cikin jin dadi da walwala a lokaci saboda yanayin da suka dauki photon ya nuna gidane hadade ko a dacan baya don akwai abubuwan more rayuwa a gidan da photon ya nuna.

A fili take fadin don me zaki gudu ki barni cikin bakin ciki da takaici bayan kune sanadin zuwana duniya a haka ina kika shiga kika watsar dani haka kamar marainiya ?

Idonta ta mayar kan wanan balaraben tun daga rawaninsa daya dan daura ga kai har zuwa fuskansa dake nuna tsawon dogon hancinsa zuwa dan gashin bakinsa kafinta mayar da idonta kan farar jallabiyan jikinsa tana runtse idanuwanta.

Cikin jin kuna da wani irin tsanarsa a zuciyanta ba zan yafe maka ba ta furta a fili kayi sanadin zuwana duniya ta hanyar yaudara kuma ka wofintar dani a cikin duniya duk da kasan da ina raye a doron kasa.

Hakana dinga sakin maganganu ni kadai a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login