Showing 75001 words to 78000 words out of 110493 words
Chapter 26 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx
yajawa yaya kunne yazo yana mata barazana da bindiga zai halbeta.
Suka kwashe da dariya sosai husna tace wallahi ta tsorata kowa saida ta fadawa amma gwaggo kura ta kara turata kan yarta ta kara tunzura kan zancen.
Kinji wata mara son mutane ni wallahi badon umma ba sai in shekara ina zuwa garin nan banje gidanta ba.
Kura ai bata rage hjy da komai ba saima kari data samu wanan da namiji ta fito da anga sarauta a wajen ta da mutan garin nan sun shiga uku da ita wallahi.
Sai Allah ya ragewa aya zaki da mijin nata ya mutu duk da mutane sun camfata ita da danta tundai yan uwan mijin cewa sune suka kashe mijin don suci dukiyarsa kinga aiko abin baiyi ba.
Nasan ba zatai hakan ba hali daine idan yayi daidai sai akama zarginka dashi yanzu haka hjy Nasare na zuwa goma gidan nan Kura bata shigo ba.
Ai ba halinsu daya ba dama anty ummi ta fada mummy Nasare da zakaje ta rikeka bata son ka wuce amma mummy kura kamar batason kazo idan ta ganka saima ta tsiro zuwa unguwa tana ita fita zatayi fa.
Sai bayan azahar suka bar gidan tsofin don zasu koma gida su dan huta kafin shirin dinner da za a fitayi karfe hudu zuwa dare duk da dinner din har biyu za ayi da wanda yan uwa zasu taru da kuma wanda za ayi bayan magariba ango da kawayen amarya kawai yanzu na karfe hudun suke son halarta su.
Gasu husna da sai sun koma gida sun dauko tufafin da zasu saka don basu sanda zancen bukin ba sai anan sukeji yass suka tafi gidan nasu baki daya.
Saida ta gama photo da uban harsu maryam sun gusa suma yace ta kirani nazo na karbi wayana da yake faman juyawa a hannun nasa na dan lokacin .
Hannuna da yarinyar tajan yasa dole na bita zuwa lokacin ya fito da kafafuwansa duk daga cikin mota ina isowa yake fadin wanan wayarkice ?
Na amsa da ehh ke yar gidan Ammah kice kin zamo babban yarinya a yanzu wanan wayan aisai ministoci ko yayansu rikonsa.
Ya miko min wayan saidai garin amsa saida hannunsa ya taba nawa hakan yasa na fisga da sauri daga hannunsa easy kada ki yarda wayan ya fadi.
Amirah in barki wurin daddy ko ta gyada min kai alaman eeh hakan yasa na juya da sauri zan bar wajen yake fadin naga kamar a tsorace kike ?
Hakan yasa na dan juyo ina fadin muna saurins zamu tafi wani waje da wa yancan dama ni suke jira yace is Ok ya fada nikan na juya na bar wajen .
Ina isa gunsu maryam matarsa na lekowa kofan gidan daga dan nesa ta hangomu zamu gidansu maryam ta karaso inda yake tsaye tana fadin .
Tou tana wajeka ashe har zan bi yan matan can da suka dauke ta ai yace dukkansu kannenane eeh mummy ta fada min shiyasa aina bari suka fito da ita.
Kanon nan naku ina tsoronshi in yaro ya bace ta ina zan fara nemanta gara dai tana kusa dani yafi ta fada tana jingine jikinta da motarsa.
Kaga Amira din nan son yawo gareta haka ta lakewa mai kama da half cas din can har mummy na ganin laifina itama ai kanwatace ba gudu zatayi da ita ba ato nasanine ?
Ta fada a cikin hausanta daya surka da yare take masa zancen ga yarinyar na fada mata sunyi photo da daddy amma bata kula mata ba alokacin.
Irin matan nan ne na yare masu bala,in kishin tsiya akan mijinta zata iya komai kan kishi don gaban kowa bata iya boye hakan dake ranta.
Maryam ce ke fadin hakan akanta bayan ta juya ta ganta a tsaye tare dashi tsuki naja ina fadin waya damu da mijinta fata muke Allah bamu namu mazan ba muje wa mijin wata ba.
Suka kwashe da dariya sai gashi da yamma zamu tafi wajen dinner umma na fada min matar yayan ku zata biku Aeesha kinsan bata da sakewa nake son hadata daku don Allah.
A gaban umma washewa nayi nace aiba komai amma muna komawa gefe daya sai dariya suka soma min dariya nan na soma fadin yanzu sai yaya ke nan wa zamu sauke a motan ke nan.
Suka koma gardama tsakaninsu dole farida ta hakkura zatabi motan da zai dauki yan mata ita matar yaya habib din zata zauna gaba su kuma su matsa baya su hudu suka juya yiwa maryam kuma dariya wai hjy gaba sai a dawo baya yanzu.
Mun fito zamu gida mu shiryane muka hade da yaya sulaiman bawan Allah ya rame ya fada yayi duhu ashe ba kallon dare kawai nayi mai a ranan ba harda na tsoro kasa wucewa nayi na nufishi muka jera tare nake tambayanshi meya sameshi haka duk ya sauya ga baki daya.
Yake fadin Abba ma tambayan da ya gama yi min ke nan ai haka umma keso idan ta rasani ai kowa ya huta ko ?
Haba yaya sulaiman ka taba ganin uwar dake son mutuwar danta yace gani kuwa Aeesha umma tasani kece farin ciki amma ta zabi rabani dake da karfi da yaji yanzu.
Wai ki duba har sakawa tayi a duba matani idan an gamu tare a fada mata da safen nan farida ke fada min hakan dana fito nace kai haba yaya kamar wani yaro yace Allah Aeesha nima haka nace wa Farida ai.
To yanzu ya zakayi gashi kowa ya gan mu tare a yanzu yace su fada mana zan fada mata gaskiya idan har tayi min magana.
Dama ashe plan suka shirya saida naje can kaduna din sai ga wata kalmasasa wai huraira wa itace ashe za a hadani da ita .
Dariya ya ban sosai don banga abin fushi ko bacin rai kan abinda nasan ba mai yuyuwa bane a yanzu don ni kaina a yanzu ba fa,ari ba sulaiman yayi min kadan inyi zancen aure dashi kuma don haka na maida abin wasa in samu in lalabashi mu rabu lafiya da kowa.
Da alaman kuma yaji dadin kulashin da nakeyi saida muka kai kofan gidan mune muka tsaya nan ma wani sabon hira mukasa yana fadin .
Aeesha nifa a yanzu na fara shakku a kanki abinda nake ji kanki yanzu da nazo naga zahiri sai nake ganin a yanzu kinfi karfina Aeesha ?
Haba yaya sulaiman ka taba ganin inda mace tafi karfin namiji ai saidai namiji yafi karfin mace maganan gaskiya .
Lalai Aeesha kin sauya kwarai yanzu don har da bakin ki ya bude a yanzu da a bayane ba zaki tsaya kina zance haka a gabana ba.
Lah yanzu kuma laifine don na nuna fadin cikin a gabanka kaima kasan nafi kowa farin ciki da zuwan ka garin nan koba komai dai munyi tozali da juna ai.
Murmushi yayi ya bude baki zaiyi magana Asmau ta rigashi da fadin mummy don Allah ki tai zuwa mu shirya kar muzo mu makara irin na ranan nan kuma ke tsaya nan kina dumi haka ?
Asmau ina zuwa yanzu zan shigo na bata amsa a lokacin abinda ya fada ya kashe min jiki don cewa jeki Aeesha kada in bata maki lokaci a banza ko yan gidan ku yanzu sun san keba sa,an yina bace kinji zancen yarinyar nan ai ?
Me zaisa ka damu da ita tunda ba wurinta kazo ba koma meye wallahi ban ganin laifin kowa saina umma ina nan cikin rufin asirina ta rabamu da karfi da yaji dake.
Nasan da ina garin nan dole zuwa yanzu gwaunatina ya gama kafuwa ga kowa kanki amma yanzu kam sai yayi shiru nace bari har anjima zamu karasa da haka muka rabu da juna dashi.
Ashe bayan ya bar wajena ya koma gida umma din ta tsuresa a daki tana masa fada farida tana kuryan daki tafito tana fadin haba umma ?
Wace Aeesha kuma a yanzu don Allah kawai kawaici irin natane takewa yaya sulaiman a yanzu don Allah ki bar zancen nan tun wani ma bai ji ba kin rabasu ta barshi yanzu kuma har zumuncin tsakaninsu kike son rabawa don Allah ?
Saboda haka kwanaki Aisha ta dauke kafanta gidan nan sai daga baya muka samu ta dawo ko yadda muke da ita aiko boye wani abu umma Aeesha ba yar iska bace yadda kuke dauka tunda ko saurayi bata da uwarta dai ke turo mata da kudi tana abubuwan da kuke gani gareta ko Abbu ya fadi hakan ranan yace ko gidan da suke ciki na uwar Aishace .
To nidai yaji abinda na fada mai banson wana zancen don yarinyar nan ba kayansa bace aje can gasu gada ba nan ba.
Umma ke nan wai baki san waye Aeesha bace ko tace wacece ita banda shegiya mara uba da asali shine shi zai kakabo min wahala ya bata min zuria.
Umma wata rana zaki tuna da munyi magana nan dake irin ta yau nasan Aisha da farko tana son yaya sulaiman amma banda yanzu.
Da dai yafi uwar ta fada ta fice daga dakin tabi uwar da kallon mamaki har ta fita ta sauke ajiyan zuciya taci gaba da shirinta.
Kudi na zube akai min dinki nagani na fada mai kyau suma nasu ba laifi don ya karbi jikin kowa munso makara karfe hudu da rabi muka karaso wurin bukin.
Saidai babu halin shiga sai kana da pass na shiga wai ashe matar yaya habib bata da pass din da zata shiga nan muka tsaya gardaman yaya za ayi ?
Kai tsaye samira tace ba sai ta koma gida ba nace haba dai yaya za ayi hakan kuma ke asmau ki bata naki dole dai daga baya su bude get sai ki shigo.
Tace amma dai mummy kedai ya kamata ki bada naki tunda koba kati dole su barki ki shiga ke amma nikan waka kallona wanga waje
Nawa na mika mata akan idan amarya tazo sai in bita a baya mu shiga tare Aimana dasu samira da Asmau sukace bari su shiga don su samu waje muka tsaya da maryam a waje cikin mota.
Muna jin kade kade na tashi sai shiga mutane keyi suna wuce mu muna zaune kamar ba abinda ya faru damu muna kuma kallon rikici a tsakanin masu tsaron da mutanen wajen.
Isowan anty ummi da tawaganta su khairat da sauran mutanenta ganina yasa khairat din tsayawa suma sauran suka tsaya muka gaisa take tambaya meyasa bamu shiga ba nace zamu shigo yanzu ai muna jiran watace.
Haba dai tashi mu shiga don Allah idan tazo ta sameki ciki ta riko hannuna nace bari na rufe mota har ta tsaya muka rufe muka nufo gurin tare dasu donsu su anty ummi sun danyi gaba muna zuwa yace kati ta hararesa tace kama kanka kaji.
Nan muna tare da yallabiyan garin nan dungurungun idan kaja kajika a prison ba ruwana yace aisai ki fada min harda dan sarawanshi na ban girma a haka muka samu shiga din.
Naso zamewa amma ta rike min hannu dole muje table dinsu dani da maryam din muka nufi can tun kan mu karaso anty ummi din tace wasu yan mata su daga su bamu waje ta nuna masu wani kujera.
Mai waka yayi gaskiya kudi shine duniya mata kuma sune jin dadin kudin don ko kana ganin shigar kowa a wurin kasan anzo buki na kece raini.
Gwala gwalai suna nuna kansu da fashion kowa ta kure adaka ba mazanba ba matan ba amma haka Khairat ta dan rankafo ta rada min a kunne da wallahi kinyi kyau matuka Aeesha .
Na dan murmusa kawai don't kunya da nake ji koba a fada ba kasan anty ummi din matar wanine a wajen don yadda ake haba haba da ita a wajen mutane na zuwa suna gaisawa.
Hankalina yana kan wayata naji khairat na fadin ita kuma wacan yar girman kan gaiyawa wajen nan jin hakan yasa na dago kai na kallo inda take kallon.
Wanan hindatun ce ta Man Bash da wasu suka shigo cikin taron ina kawar da kai naga ummin tayi tsuki itama ta kawar da kanta gefe daya saga kallonsu.
Da alama yadda suka shigo taron sandan sandam dasu bamu ko mayafine ya bata haushi ga dinkin ya matse su sosai ya fitar masu da sharp din jikinsu har shafin part dinsu kana gani a ciki don't matsewa.
A,a anty Ummi ashe kunzo garin ta fada ta dago tana fadin hindu mama ya kuna lafiya ya su mama wallahi mun shigo har muna batun fito jibi in Allah ya kaimu zan koma saboda school din yara.
Khairat yaya a,a ashe gaba dayan ku kunzo harda su husna sai idonta ya sauka a kaina take fara,anta ya gushe lokaci guda har ta kasa boye hakan.
Tace bari tazo ta juya ta samu abokan tafiyanta husna taja tsuki tana magana kasa kasa da yar uwarta na kara mayar da hankalina kan wayata din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/27, 10:34 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Faridace tazo ta kiramu muje za a shigo da amarya hakan yasa muka barsu don zama a nan dama a tsarge nake duk na dago kai zan samu data daga cikinsu ta kura min idanu tana kallona sai hakan yasa na tsargu da kallon da suke min.
Munje din an shigo da amarya harkace dai ta karya ta aron al,ada da akeyi a yanzu don ba,a san bahaushe da hakan ba..
Anyi buki anci ansha anyi raye raye su Asmau su samira Aimana balle farida kirjin buki sun cashe sunyi rawa sosai nida maryam ce bamuyi wani rawa ba tun bayan shigowa da amarya muka samu waje muka zauna.
Anyi budan kai inda anty ummice a matsayin uwargida don itace matar farko a gidan kuma sarakuwa itace ta sayi bakin amaryam da kudi masu tsada saida kowa yayi ihu.
Sannan wasu a cikin dangi sukai ta saye suma abin gwaunin ban sha,awa dai anyi photuna harma da wa yanda ban sani ba haka zasuzo suce ayi photo.
Su khairat dasu husna muyi sosai dasu kafin na nemo matar yaya da dai muna tare tashi yin hoton yake dan rabamu sai ta dan sake dani muna hira jefi jefi tana tambaya wasu abin.
Don haka na nemota don ganin har anyi isha,i a lokacin abinda akace karfe shida da rabi za a tashi nida ita sai asmau da maryam muka samu fitowa wajen mun bar sauran yan uwa a ciki.
Ina tafe rike Amira da tayi barci wani soja yasha gabana yana fadin good day madam don Allah oga yace inyi magana dake yana nuna min motan ogan daya aikoshi wurina.
Gaba dayan mu muka tsaya a wajen cikin duban direction din daya nuna din kafin nace you de crazy iam married woman murmushi yayi dan aiken kafin ya juya zuwa hausa yace saida muka tambaya don kada mu saba doka hjy a cikin dan murmushi.
Gashi a can amma kaga sauri mukeyi a yanzu na fada ina masa wani kallo ayi hakkuri please ko minti biyune zuwanki zai tamaki rayuwana rashin zuwan ki kuma akasin hakan he son Allah please.
Na fahinci me zamcenshi ke nufi kai tsaye yadda a take yai min magiya da fada min gaskiya a takaice na Dan juya kafin na sauke ajiyan zuciya nace .
Shida ke son ganina aishi zaizo nan ga motana a can na fada ina kokarin wucewa naji yace sorry hjy babbanne fa son Allah ki daure.
Hakan baisa na tsaya ba na nufi mota don yarinyar tayi min nauyi a hannu uwar ta zauna na mika mata ita su maryam suka bude baya suka shiga.
Hjy gashi can a jikin wancan motan ya sake fada hakan