Showing 12001 words to 15000 words out of 110493 words

Chapter 5 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2276

yayin da har na kai ga hasa wuta ita kuma tana zaune kamar an shukata cikin tunane sai muryanane ya dawo da ita da nake fadin.

Ammah akwai sauran gari ko nake tambayarta don tun lokacin nan da sukai tafiya ya kasance gari bai katse muna a gidan har sai mun tsaya jiran Abbu ya dawo daga kasuwa don muna dan ragewa a yanzu din sai hakan yake muna amfani wani lokacin kafin ya kawo din munyi amfani da dan wanda ke nan kuma ya ishemu a gida.

Saida ta dan dauki lokaci kamar ba zatayi magana ba kafin naji ta sauke ajiyan zuciya da dan karfi tana fadin wanan shimkafan da maman Aimana ta aiko dashi nake son a dan sulala da wake mu dan canza abincin yau tunda Allah ya kawomunashi.

Dakin na nufa don nasan inda kayan suke wake na dauko don in gyara can daga gefe daya na koma na fara gyaran waken nima dai zuwa lokacin a cunkushe zuciyana yake.

Don tun sanda nasan da zancen mahaifiyana nake faman dakon bakin cikin daya yafi na baya a zuciyana sanin koni waye a yanzu yafi tayar min da hankalina.

Don zuciyana tana min wasi wasin akoda yaushe akan koni yar halakce kamar yadda nana din ta fadawa yan uwanta saidai ni zuciyana yafi karkata da cewa ni din ba yar sunna bace gaskiya.

Duk da hankalina a lokacin ba zai iya hango min gaskiyar zancen da Abbu ya fada min sai nafi hasashen Abbu din ya saya min zancen nasane don in yarda dasu din.

Wai baki sauri Aeesha ki daga kanki ki dubi gabas tab yake da dari daya hadu yana shirin game gari kin zauna kina tunane haka .

Hakan yasa na mayar da hankalina ga abinda nakeyi a lokacin bani kadai ba har ita Ammah ina kule da jikinta a mace yake har lokacin nasan kuma sanadin rigar nan dana fito dashi daga wajena nayasar a wajene yasata shiga wanan tunanen haka.

A raina nace lalai Ammah da nana din nan da Abbu yace itace mahaifiyata akwai wani abu mai karfi a tsakaninsu don yadda Ammah din take shiga cikin damuwa haka.

Zuciyanace ta bata amsa da fadin gaki kuwa baidai wuce matsalanki Aeesha don rikon dan da baka san asalinsa ba yanada wahala.

A take naji idanuwana sun ciko da ruwa a lokaci guda tausayin kanmune ya mamaye zuciyana a wajen don nasan nikan a yanzu mara gatace duk da kokarin gatan da Abbu da Ammah ke nuna min sai wanan lokacin nake jin hakan bai wadatar dani ba a gaskiya.

Ba malam bahaushe ba ko wani kabila nason ace yau ga asalinsa nikan a yanzu nagama sanin banda wani asali ko gata a duniyan nan kuma.

Tunda ba wanda yau zan nuna ace dan uwan mahaifinane mace kona miji ina wanan tunanen ni dakaina naba kaina amsa da fadin No wander yan uwan Abbu suke min abu issa issa idan nashiga cikin su.

Daga yara kuma har manya haka zasuyi ta hattarana kamar ba yan uwana ba har yakai idan munje wani taro nasu na daina nisa da Ammah duk inda take anan zaka sameni .

Sai ya kasance yanzuma dana girma bani sha,awan bin Ammah zuwa sha,aninsu saidai taje ita kadai ta dawo na dauki shekaru a yanzu ban zuwa sha,anin su.

Kauye kuma da take zuwa tun ina saka rai har na fahinci bata son zuwa danine kauye sai nafi daukan zancenta a lokacin da tace dani don mayu sunyi yawa a garin nasu yasa bata son zuwa dani wanan yasa na debe rai a lokacin.

Amma yanzu da naji tarihina a wajen Abbu na gane kuma na fahinci abinda yasa Ammah din take min hakan don haka ya zamo wajibi in debe raina a dukka bangarensu biyun ga baki daya.

Ba kuma don komai saboda in tsirar da mutuncina gare don daga yara har manya duk sun san asalina nake gani akan me zan matsawa kaina yanzu shigarsu bayan nasan asalina a yanzu cikin al,umma.

Asalin Abbu dan cikin kanone dama nomane ya mayar da iyayyensu kauyen su Ammah har suka zama yan gari amma kowa nasu yana a cikin kano har kuma wasu daga cikin yan uwansa mata sunyi aure a kauye don can mahaifinsu ya maida rayuwansa a lokacin.

Ko a bakinsu zasu iya jin tarihina a lokacin sai a yanzu da wayau yazo min kuma nasan asalin nawa wanan tunanen yake zo min a raina don haka a yanzu gaba daya saina share wanan gabaki daya a raina.

Ina fada maki hakane mai karatu don jin da nayi da Abbu ya dawo yana fadawa Ammah zancen bukin wani dan uwasa da zai ma dansa aure.

Gashi kuma idan ana bukin a can Ammah take kwanaki kusan biyu ko ukku saboda tazaran dake akwai a tsakanin mu don Abbu bai yarda ya sai gida ako kusa da unguwarsu ba a lokacin.

Can yaje nesa sosai dasu yasai wanan gidan da muke ciki don rikona da ya dawo wajensu yayo kaura a kauye zuwa nan kano don rayuwana ya inganta ba tsamgwama .

Saidai duk da hakan ba a tsira ba don anyo gudun garane aka fada zago saboda kallo daya zakiyi min dani da iyayyen nawa babu wani kamanceceni da nayi dasu don haka ba sai an tsaya bata bakin fadin su din ba iyayyena bane na asali.

Don haka tunda wanan zance yazo kunnena na yankewa kaina shawaran ba zanbi Ammah zuwa bukin nan duk yadda ta taya min zuwa saboda yadda a yanzu na tsani shiga cikin mutane saboda haka nake daukan kaina kamar wata muji a gaban mutane idan na shiga waje.

Daga inda nake jin Ammah na yanka fadan rashin fada masu bukin da wuri da ba,ayi ba don gashi jibinr ita ko wani shirin kirki bata dashi a yanzu don haka an mata girshi a bukin.

Dariya yaso kamani nake fadi a raina su Ammah ho wanan wajen ko kinje da shirinki na gaske wa zaisan ma kinzo mutanen da suka goge suka waye idonsu na a bude.

Karshema su ke zama yan aiki don angansu na kauye a wajen duk da gaskiya kira da tsarin su Ammah ba abin kushewa a cikinsa don mutanene tsayayyu ga diri da ake bukata a wajen mace Allah ya hore masu.

Irin wanan kamar itama nana din nan tana da wanan halittan nasu a yadda naga zubinta a cikin hoton don ba inda ta rago Ammah din wajen kama saima ince kamar ta fisu cikar halitta ko don ita ta wayene fiye dasu yasa hakan oho bandai san komai a game da rayuwanta ba har lokacin.

Aiko ban kai ga karshen tunane ba naji bayan Abbu ya fita Ammah din tana kwala min kira hakan yasa na amsa kamar a tsorace na fito lokaci guda daga dakin.

Ashema har Abbu ya fita ban farga ita kadai na samu a zaune a tsakar gida take fadin abinci fa nace yanzu zanci Ammah.

Na juya zuwa inda abincin yake na dan debo kadan gefenta na dawo in zauna ina shirin zaman naji tana fadin kinji min mutanen Aeesha ?

Don rainin wayau da an mayar damu tallaka wai sai yau din nan ake sanar da malam zancen bukin dan gidan Alh sale don kawai sun raina mutane inbashi ba iyayye uwa daya uba daya ace sai yau din nan malam zaiji wanan zancen don Allah ?

Mafarin in ba ajeba suce an ki zuwa ni yanzu na rasa data ina zan fara ma tunda nasan zuwa dole tunda banji yace dani komai ba.

Shirun da taji nayine tana magana yasa ta dago ta dan dubeni tana fadin bakiji mena fada bane wai ina magana kinyi shiru haka ?

Idonta data sauke ga abincin nawa yasa kuma ta canza akalan zancen bukin da fadin wai meke damunkine yanzu Aeesha ?

Ina kule dake fa a yan kwanakin nan da kamar akwai abindake damun zuciyarki ace wai wanan dan abincin kamarki zataci kamar za abawa jariri dan watanni haka ?

Dan murmushi nayi ina fadin amma malamin mu yace yawan cin tuwo haka da yawa yana sa mutum kiba lokaci guda ni kuma banson kiba wallahi na wayance da fadin hakan gareta.

Dakuwa tayi min tana fadin kaiya yaro dai yarone wanan bokon na karanto maku karya a rayuwa kiba kan idan kin gada ai sai kinyi dama kin sani ki daina wahal da kanki don mu zurian mu bamu da gadon kiba can din nan bandai sani ba ko can cikin zurian ubanki idan su sun gaji kiba wata kila.

Ai a Nasarawa banga mai kiba ba cikinsu suma duk da ba zubinsu na kwaso ba ban sani ba ko dangin mahaifin nawa can akwai mai kiba dai .?

Wani kallo Ammah din tayi min lokaci guda kuma na fuske kamar ban san abinda na fada ba a lokacin sai cin abincin nakeyi a hankali a lokacin cikin daure fuska.

Yayin da Ammah din ta danyi dan shiru na dan lokaci tare da zuba min ido kamar tana tunane sai kuma naji ta nisa tana fadin.

Kai anya Aeesha sai kuma naji tayi shiru fasa fadin abinda tayi niyar fada a lokacin don dan tunanen da tayi a wajen a zuciyarta.

Takai wani lokaci kafin naji ta sauke nauyayyen a jiyar zuciya tana fadin Allah ya kyauta ta tashi ta daga zuwa daki ta barni a wajen har na karasa cin abinci ina gab da tashi ta fito tana fadin.

Ni mutanen nan su dagula min lissa na rasama ko dame zan fara a yanzu ni gani ba sabon dinki ba ko takalma kirki bandashi a gidan nan balle sabon zani duk yan tufafin nawa sun sani dashi a baya tun wancan bukin na kwanaki.

Ammah meyasa kike son matsama kanki kan wanan zancene wai kiyi amfani da abindake gareki mana irin wanan wajen wasan ma ka saka balle yasama ido mutanen da duk yadda ka iya dasu ganinka suke dan kauye .

Sai naji Amma din ta katseni da fadin aini bani nake jiwa ba Aeesha a yanzu kece tunda kinkai munzalin budurwa a yanzu dole ki dan bukaci abin da zai dan sauya ai bari malam ya dawo.

Inji ya za ayi da wanan zancen ance da wuri wuri ake fara shiri ba sai tafiya yazo ba inji manya da sauri na dan kallota ina fadin ba inda zani Ammah a gida zan zauna .

Kafin in rufe baki naji tace dani akan me wai nifa yanzu na rasa ganr inda kika dosa Aeesha cikin kwana biyun nan komai sai ki dinga jan kanki a baya.

Bukin dan hjy karime din ne zakice baki zuwa matar da idan ta ganki take rasa inda zata sakaki tana fadin ke yartane yanzu kice wai baki zuwa sha,aninta wanan ma wasa kikeyi don ko malam ba zaiji dadin hakan ba ai ace bukin dan dan uwansa zakice kr ba zakije ba Aeesha ?

Baki na turo gaba ina bata rai nace Ammah ni wanan irin abinda suke min a cikinsu bana so sai a dinga nuna mutum haka kuma duk inda kabi idon mutane yana kanka wananne bana so wallahi .

Yo me ruwanki dasu din kedai kiyi sha,aninki kawai kibar mutane don ba,a iya masu makin in bata amsa ko in tsaya saurarenta don ma ta gane ban son zuwa din ai yasa na mike din na barta a wajen.

Ina ji can dare da Abbu ya shigo Ammah din ta kara tayar da zancen bukin kuma tundai inajinsu har barci ya daukeni a haka sai washe garine na tashi naga Ammah din tayi kumshi ashe a cikin daren don fara rage hanyar tafiyan dake gabanta duk a cikin garine bukin amma ai kwana zatayi a can har biyu ko ukku.

Na fito da shirina tsab na school tana zaune tana saka taki a kafanta ta dago ta kalleni tana fadin aina zata yau zaki huta ki danyi gyaran jiki kije gun maman Aimana kiyi sammakon bin layin kitso ?

Shiru nayi nan ma banyi maganan ba hakan ya dan harzukata tana fadin amma kinji mena fada kon kyale kinyi shiru ni wanan takama da izzan naki ya fara isata wallahi.

Yarinya a magana sai faman miskilanci kike zubawa kamar bakijina don wullakanci jin hakan yasa na juyi ina fadin nifa sai asabar zan tafi kitso inna kada inyi yanzu ya walwale min a kai kinsan kitso baya kwana biyu a kaina bai tashi ba.

Ikon Allah ana gabas kina yamma yar nan ko kin manta da zancen bukine wai yau da gobene kadai muke da lokci a gidan nan.

Ammah nace fa ban zuwa kuje sai kun dawo amma ni ba zanje ba gaskiya don,,,,,,, dakuwa data miko min tana fadin karbi naki ni kike mussu dani haka Aeesha ?

Muryan Abbune dake fitowa a daki yake fadin haba wai meke faruwa hakane tsakaninki da yarkine tace bata zuwa ki barta mana tunda bata ra,ayin hakan.

Koke ai don zuwan naki ya zamo kamar dolene da bakije ba don ba lokacin hakan amma hjyce nasan yadda kuke da ita yasa zan barki badon shiba babu mai zuwa a gidan nan gabaki daya tunda bamuji a cikin lokaci.

Amma dai malam za ace hjy tana bukin danta yadda muke ace yarinyar nan tace va zata taka ba duk yadda muke naji Abbu din yace Ammamatan ina gargadin ki da ki kyale yarinyar nan don Allah tunda tace ba zataje ba ki barta.

Ya juyo gareni yana fadin jeki ke ki shirya kada ki makara don lokaci na kurewa maki ya juya ya shiga dakin kuma tsaye tayi cikin mamaki tana bin bayansa da kallo a cikin mamakin kafin ta maido kallonta gareni tana fadin kiji dashi.

Wanan yar ga baki daya kin sauya min a yan kwanakin nan na rasa inda kika dosa Aeesha yarinya da izza da jinkai kamar wata yar basarke haka ?

Nikan a gurguje na shirya da saurina na shiga daki na dauko jakkata banko tsaya karya ba kodana fito na samu Abbu a tsaye kofan dakin yana dakon fitowa ya miko min dari na na karyawa na rusunna har kasa da hannu bibiyu ina karba tare da godiya .

Na juya na fita na barsu nasan a bayana zasuyi zance a yadda na barsu din don kowa dai ransa ya baci a lokacin kan zance .

Inda niko iyakar gaskiyana ke nan na fada masu ba zanje ba don in ban manta ba zuwa na karshe sha,aninsu da kukana na dawo gidan kan abinda akai min lokacin.

Muna fada irin na yara na dan duki abokiyar wasan tawa tasa kuka ranan yan gidan su Abbu suka taso min kamar zasu cinyeni danya Amma sai hakkkuri take basu suko inda suke shiga ba nan suke fita ba a lokacin .

Wanan yasa banji marmarin komawa ba sha,aninsu lokacin ban ma san asalina bake balle yanzu din dana sani cewa ni din ba yar kowa bace ashe.

ZAINAB IDRIS MAKAWA[7/31, 10:10 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND

MAMAN BIBO KAYAN MATA

08068871330 KOKO ROAD SOKOTO

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

0️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Ammah naji tana gani haka ta tafi wanan sha,anin ta barni duk da bata so hakan ba amma ba yadda ta iya tunda na kafe akan ba zanje ba yasa Abbu yayi mata fada sosai akan matsa min din da tayi a lokacin.

Taso zuwa dani din ne tayi kwanakin da take sonyi acan din sai naki zuwa dole yanzu in angama ta juyo don hankalinta ba zai kwanta ba a can din ni ina gida.

Gashi a can din kuma yara da manya suna tambayanta ina Aeesha maman Aeesha saita labe da cewa bata zo dani bane don ana makaranta don hakane ta barni gida.

Sai kuma bata samu kan ita uwar bukin ba a wanan karon don uwar bukin kowa yana complain din fuskanta a daure yake lokacin sha,anin yasa an gama buki washe gari karfe biyu sai ga Ammah din ta shigo gida dawowana ke nan daga school ina zaune ni kadai a tsakar gida nayi tagumi ina faman tunanen duniya ta shigo.

Na mike da fara,ara ina taron ta itama fuska a sake da murnan ganina ta rugumeni yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login