Showing 57001 words to 60000 words out of 110493 words

Chapter 20 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2290

min ranan.

Yace photon da kika gani har yanzu yana nan koya bata nace yana wajena na boye a yanzu haka su Abbu basu San photon yana gurina ba a yanzu.

Kuma kin tabbatar da mahaifiyar ki tana Raye na gyada masa kai nace tana raye tana turo da kudi ana muna sayayya da komai ko wanan gidan da muke zaune Abbu yace itace ta saya muna shi don mu zauna.

Komai ban boye masa ba na fada mai game dani lokacin ya koma ya zauna saman kujeransa sai faman dan juyawa yake yana saurarena.

Da kuka na karasa ina kaico da rayuwata da irin gori da zagin da nake fuskanta a yanzu gun mutane.

Bayana naji ya dan bubuga a hankali yana fadin kuka bashine abinyi ba gareki yanzu nasan you deserve it amma lokacin kuka ya wuce agareki yanzu.

Cool down GF kina jina yanzu ba lokacin kuka bane akan wanan lokacine da zaki gina kanki ki zamo wani abu a rayuwanki da zaikai har an manta da past dinki.

Hakan kuma ba zai samu gareki ba ayanzu sai kinba kanki taimako ke da kanki zaki samu biyan bukatanki.

Kaina dake duke nake kokarin dagowa don in fahinci me kalamansa yake nufi da saini da kaina na taimaki kaina as how ta yaya me hakan ke nufi.

Yana tsaye a inda yake har dago baiko motsa ba kusa dani muna gab da gab da juna dashi a zatona zancen banza zaji daga bakinsa yasa na dan kura masa ido cikin mamaki.

Shima kallon ido da ido yake min bai kawar da nasa idon yace yes sai kin taimaki kanki kafin burin ki ya cika zaki kau da kowa da komai a yanzu a rayuwanki including me da zancen su Abbu kiyi facing din studies dinki kawai a rayuwanki.

Idan kinyi hakan non taimakawa rayuwanki dana duk wanda yake kaunarki da alheri ajiyan zuciya na sauke lokaci guda.

Saboda nasan tundaga level one har yanzu da nake zancen shiga uku shine ya biya min kaf don ko naje biya zasu ce dani ai anbiya har an bada resist akan biyan.

Muryan shi da yake fadin kin min alkawarin hakan a yanzu yasa na dawo ga dan dogon tunanen dana shiga cikin dan lokaci na kalloshi ya kura min idonsa a kaina.

Samun kaina nayi da daga masa kai alaman eeh a lokaci guda yace good idan kiyi hakan kin taimakawa kanki.

Ya juya zai koma wajen zamansa yana fadin kasan nan na bukatan mata a wanan fannin na karatunki musanman matan arewan nan namu.

Karatun ki shi zai kaiki ga matakin da ido ko keya ba zai iya fuskantanki da wani challenges din rayuwa ba zaki gane me nake nufi dake a nan gaba.

Motar da Auwal ke kai ki school dashi nasa a canza maki iyakar Auwal dake satin nan kece zaki dinga driving da kanki baki da matsala akan karatun ki matukar zaki daure kiyi kamar yadda na bukace ki dayi a yanzu.

Abbu dinki kafin na bar kasan nan za,a fadada masa shagonsa ki dauki wanan abin a matsayin tukwici ga zaman mu dake yadda kona tafi ba zaki shiga wani damuwa ba akaina.

Yanzu kan kuka sosai nayi a lokacin wanda ba zance ga dalilin yinsa ba kuka na halarcinsa gareni ko na rabuwa dashi ?

Dams haka yayan mask kudi Duke ashe koshi wanan rayuwansa take daban dana saura ashe dama nike haukana kamar yadda bai taba nuna min soyayyaba ko da wasa haka abin yake har cikin zuciyarsa ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/22, 9:49 AM] Zainab Idris Makawa Writer: https://www.facebook.com/groups/293543855250655/permalink/1171299937475038/[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc

LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

2️⃣8️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftP

Kaina kife saman tabel din ina mai fitar da sautin kukana sosai banjo yai magana ba kuma ban fasa kukan da nakeyi din ba .

Muryan shi naji yana fadin ga Auwal nan waje yana jiranki zaikai ki gida akwai aikin da zamuyi yanzu .

Kaina dago a hankali da zumar in kalleshi don jinshi bai damu da irin damuwar dani nayi ba ko nake ciki na rabuwan daya zo min a bazata cikin rashin sani.

A daidai lokacin da na sakakankace dashi ina mafalkan dabana gaskiya ba a kansa Ashe shi nasa shirin daban ne a kaina shima share hawayen yakeyi a lokacin a daidai lokacin salman ya turo kofa ya shigo.

Tsaye yayi turus yana kallon mu daya bayan daya kafin ya iya bude baki yace tasan komai ke nan naji ya bashi amsa da ta sani kira Auwal ya tafi da ita yanzun nan don Allah.

Ya juya da Saudi don ya kira Auwal din baifi second ba saigasu yakecewa Auwal din kaita gida zamuyi magana daga baya GF ya fada da dan sauri yana harhada kayansa tare da soka wani bindiga da nagani a hannunsa kamar a mafalki.

Hakan yasa na mike cikin tsoro da sauri na danja kujera don inji dadin fita kafin kuma in tsaya na kara juyowa na dan sake kallonshi ina jin wani abu na sukan zuciyana lokaci guda.

Anyi sa,a shima din niyake kallo cikin wani yanayi mai ban tausayi da sauri na karasa wajensa kamar zan rugumeshi sai kuma na kasa na zube kasa a gabansa ina kuka.

Dan tsuki salman yaja ya fita daga office din Auwal ya bishi a baya lokacin naji ya kamoni yana fadin tashi a kaiki gida muna gab da fara aikin mu kada ya rutsa dake zan zo gidan ku insha Allah jin hakan yasa na mike ya kamoni har zuwa dan waje yana kiran Auwal yazo da sauri muka fice wajen baiko kara bi ta kaina ba kuma.

Ba kuka yakamata kiyi ba yanzu addua ya dace kiwa yallabai don shi yafi bukata a yanzu Allah ya fitar da su wanan takon a cikin sauki inkin duba duk school din nan a zageye yake da jamian tsaro yau tun karfe hudun yamma.

Hakan yasa na dago kai ina bin ko ina da kallo yake fadin akwai wani malami bamaguje dake amfani da sunan musa yana yaudaran yara akanshine su yallabai sukazo aiki kasan nan.

Shi din kuma ya kware wajen safara tare da tura su fita masa da kwayoyi waje bayan ya kwadai masu maku dan kudi a ransu.

A wanan school din na tambaya cikin mamaki yace kwarai kuwa yana sajewa da mutanen kirki yana barna ba tare da an sani ba shiya kawo yallabai kasan ga aiki kuma yau insha Allahu dubusa ya cika.

Sadin a ganosa kuma shine wata yarinya Madina da ya tura aka kama ashe tana da halaka da wani babba a cikin kasan nan nanne asirinsa ya fara tonuwa.

Ba fahintan zancen nakeyi ba dakyau a lokacin don haka ban damu da na san komai ba a yanzu don abinda yazo min kamar a mafalki bashiri ba tsamanin hakan.

Yana ajeni a kofan gidamu ganin mota na tsayawa na fito da sauri zuwa cikin gidan banko tsaya nayi mai sallama ba yadda muka saba shima din yana cikin damuwa kamata don haka bai damu ba yaja mota da karfi yabar wajen.

Anyi arangama kafin a kamashi wannan musa din Wanda ainihim sunansa Moses ne ya juya zuwa musa sai ki rantse shi din musulmi ne saboda ya iya bata sau dinshi ga mutane.

A bazata suka dira mashi daidai lokacin da yake kokarin fita da yara hudu da aka gama shiryasu biyu yan mata biyu maza saiga Jami,an tsaro sun shigo masu a bazata data shi har yaran aka kamasu aka taxi dasu dama shi mai laifine nemansa ake a can turai ya dawo nan ya fake da sunan aiki yana cutan diyan jama,a a fakaice saidai a nemi yarinya ko yaro a rasa daga karshe kuma a rufe babin su.

Yanzu Allah ya tona mashi asiri kan wata madina days tura aka kamata da kwayoyi da zata kai masa can shine tace shiya bata sai basu fitar da zancen ba don suna son kamashi.

Asamau ce kusan abokiyar sirina yanzu a gidan ko yanzu ma da nashigo ita ta kula da yadda nake a birkice ta sameni daki.

Mummy lafiya ta fada tana tsaye a kaina ta zuba min ido ina kife saman gado ina darzan kuka da ni kadai nasan abinda nake ji a zuciyana lokacin.

Ganin kukan da nakeyi ta juya ta rufo kofa data bari a bude ta dawo gareni zaune takai bakin gado ta sake maimaita tambayanta a kaina.

Da kyat na dago ina fadin Asmau Man Bashir ya tafi ashe yaudarata yayi Asmau dama ba soyayya yake dani ba bada saune kawai nasu na yansanda yayi amfani dani.

Mummy ban gane me like fadi ba fa hakan yasa na dago ina fadin Man Bashir nace dake ya tafi ya koma inda ya fito Asmau ashe shi dan sandan leken asirine aiki ya kawoshi nan dama kuma ya gama ya tafi.

Kinsan yan sokoto koba kaso sai sun baka dariya don hakan ya faru dani da Asmau a lokacin saboda cewa tayi.

Har da uwatai da ubanai duk sunka bar kasan mummy kallonta na tsaya yi kafin in girgiza mata kai nace a,a Asmau shi kadai ya tafi.

Ban yarda ba walls keji na hwada maki ban yarda ya tafi ke nan ba baki kara ganinshi saidai in wani abu yaka nuhi.

Amma tunda uwatai da ubanai duo suna garin nan dolena ya dawo watarana indai yace ya rabu daketa daga yanzu na yarda da hakan .

Abinda ta fada yasa na juyo ina kallonta tace to haka dai zikau yaka hwadin ya rabu dake babu komai ni walle ban yarda ba ko yanzu wani plan ne ya koma shirya maki irin nasu wayayyu.

Mummy kema kiyi tunane mana wagga zance ba gaskiya bata akwai dai akwai abinda yasa yace haka.

Asmau bada wasa ya fada ba dama na dade ina zargin hakan a raina don ba wani abin soyayya da yake nunawa a kaina zalla mutunci ce kawai a tsakanin mu wanda bansan dalilishi ba .

Alma nafi daukan hakan da rabonane ya tsaga aljihunshi yasa muke tare dashi har haka amma zancen soyayya sam babushi Asmau.

Yanzu dai koma meye ai shiya sani in nine me mummy nuna zanyi nima haka take garan in gyagiji in kilance inyi clean sosai fiye da yanzu in mayar da hankali ga karatun da yace tunda shi at burine gareki.

Aji komai mummy kiyi facing din karatun naki don gaskiyana ba a San abinda gone zaiyi ba ga bawa ai kega ya baki shawaran kwarai.

Shiru nayi ina nazarin zancenta don Asmau da tayi book akwai kaifin basira a tare da ita taxi uwar da yarta samira hangen nesa in tana magana zakice wata tsohuwace ke magana.

Kamar wasa sai gashi zancen Asmau yana tasiri a zuciyana don ko wasa wasa na dauki zancen nake nuna ba abinda ya faru saidai na zuciya na kasan zuciya ta yana cina.

Washegari koda muka isa school ko ina labarin abinda ya farune a jiya akeyi gum nayi da bakina bansan komai ba kowa da irin labarin da yake bayarwa sai gashi an kafa notice an rufe school din don bincike da akeyi sai idan an kiramu mu dawo.

Hakan yasa kowa ya kama gabasa ga Auwal ya riga daya tafi taxi na tara na dawo gida na samu Abbu zai fita nake masa bayani yace Allah ya kyauta .

Hakan yasa dole muka koma gida da zama nakan fito na hadawa su Asmau zobonta ko samira wanda Allah yasawa albarka a yanzu da sunyi da sun sayar saboda yadda muke hadashi da kauri ga kuma fridge lafiyayyun masu aiki sun samu da ansaka sai sanyi.

Wani lokaci nakan tsaya inyi girkin rana kona yamma da za,aci a gida abu dayane shine banyi aikin talliyan da anty keyi don ya zama aikin karfi .

Bayan hakan kuma ina jin yadda takanta fada da diyanta kan aikin yasa bansa kaina a cikinsa ba gashi yanzu wanan sana,an yasa ko yaushe tana gida zaune ta daina yawan fita din da takeyi na yawon talla.

Da mun gama yan aiyukan mu da safe muna gida zaune su suna da yawan son kallo ko yaushe don lokacin ana barin wutan Napa sosai ba a daukewa don haka ko yaushe TV yana aiki a gidan.

Hakan sai ya dan rage min damuwa da naso shiga na rashin Man Bashir ayanzu don ni banji komai a kansas ba ban kuma ji wani labarin Auwal bama.

Sai hakan yaso ya dameni da farko amma yadda muke a yanzu ya rage min damuwan don ko yaushe cikin hayaniya suke su.

Farida ta shigo min wani safiya da zancen bukin gidan Rabakaya daya taso duk family guda ake dash don haka muma bukin ya shafemu saidai bansa kaina ba sosai.

Saboda yan gidan su basu da kunya komai sunawa mutaneshi a gadarancene da isa suna nuna su wasune a waje kai ba bakin komai kake ba idan suna waje.

Wanan yasa ban gwamatsesu ba sosai amma dai ana dan mutunci idan an hadu bukine na za a fitar za a kuma kawo masu ma,ana yar gidan zatayi aure hakama dan gidan shima zai auto mata a kawo masu sarakuwa.

Zancen anko tazo min dashi don sati mai zuwane bukin gashi mu bamuyi anko din ba don hakane tazo gidan mu je mu karbo namu.

Naso naki zuwa sai akai rashin dace Ammah tana wajen lokacin don haka tai cikin rigar arzikina da fada dole na shirya muka tafi.

Saida ta shiga gida ta kira yan uwata mu biyar da Asmau data biyoni muka zagaya zuwa gidan gidan da bazance ga shekarun dana diba ban shigeshi ba sai gashi yau dalili yasa zan shiga.

Tun a kofa muka fara cin karo da wata yarsu dake gida tana zawarci muka tsaya muna gaisawa da ita tace wai Aeesha ce haka ?

Nice anty na fada na sake gaida ita din muka shiga daga ciki farida ce a gaba tayi part din yan matan da suka cika daki dam ana hayaniya.

Muna shiga kuma kallo ya dawo garemu aka fara gaisawa zaune nakai saman wani dan Stoll da wasu kaya ke sama nacewa Asmau tazo ta zauna na dan gusa mata muka zauna a tare.

Yanzu anty Fati idan ba munzo ba ba za a aika muna da anko din ba farida ta fada wace aka kira da fati din race to farida ankon kala ukkune bansan wanda kukeso ba ciki.

Hakan yasa ta juyo gareni tana fadin wait wani zamuyi Aeesha nace wani event zamu tafi a ciki ?

An kwaso anko din ba laifi gaskiya dana dinner saina kamu sai sai kuma na ranan yini yadda akai muna bayani yarinyar dake bayani din tana wani kaudi take fadin idan duka zakuyi yakama sha biyu ko wani mutum guda lokacin kaya suna da sauki sosai zeey don da yanzune zaikai almost to fourty thousands gaskiya .

Yanzu dai a bamu muje dashi muyi shawara sai a dawo da sauran amaryan ta fada kamar jira wace ta kawo kayan keyi naji tace a,a anty gaskiya ba bashi ba zan bayar ba kizo ki tafi gidan mijinki ki barni da yawon hanya karban bashi karshe azo a fadama maganan banza.

Farida ta barshi don Allah na fada ina mikewa tsaye don yadda take kokarin bamu kunya a gaban kawayensu zakice bata san inda muka fito ba.

Sai naji amaryan tace kamar ya abarshi Aeesha a barshi mana aiba dole bane sai kunyi dama maryam da take mai saurin zuciya har takai kofa tana fadin kuzo muje don Allah.

Amaryan tace haba maryam kema kinsan halin saratu ai da zancen banza idan basuyi ba suwaye zasuyi su yan gida da kike wanan magana haka ?

Nan dai amaryan tayi cikinta tare da sauran yan dakin suka nuna mata rashin kyautawanta kafin amaryan ta juyo tana fadin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login