Showing 15001 words to 18000 words out of 110493 words

Chapter 6 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2279

nayi mata na dauki kayan ta nasa daki kafin in firo in karbo mata ruwa na kawo mata tasha.

Tun a nan ta fara bani labarin kan bukin tana fada min abubuwan da suka faru inda ta dora da fadin ai gara da bakije bama Aeesha .

Saina koma ban ganin laifinki kuma na matsa makin da nayi sai muje tare don muma da mukaje din munyi dana sanin zuwan tunda damu da babu mu a wajen uwarsu daya.

Ke bari yar nan hjy ta ban mamaki wallahi matuka don banyi zaton hakan a wajenta ba sai lokacin na bude baki nace Ammah kuma ke nan balle ni da duk da sun saba ganina amma haka zasu samin baki da ido suna tambaya a kaina wanan yasa ban son shiga mutane yanzu wallahi.

Budan bakin Ammah din tace aiko sai ki zama kofin rijiya don ko mutane haka su a ko ina da saka ido kan abinda bai shafesu ba yanzu.

An daiyi bidiri kan gaskiya an kumaci an sha gaskiya tubarkallah wallahi don buki yayi kyau amarya kuma sun iso tun jiya daga yola.

Shima Allah mai tangaram ance nan da wata ukkune bukin yayansa anma so a hada da wanan gidan iyayyen ita wanan yarinyar suka matsa ayi don su sun shirya sukace.

Na dago ina fadin gidan su anty mami ke nan tace aisu mami din nake jin za aiwa auren ko kuma dai bada ita ba amma dai cikinsune su ukkun .

Allah sarki sun karasa karatun nasu ke nan nidai suna birgeni wallahi don babu ruwansu da daukan kai faran faran dasu ko wani lokaci.

Amma ita wanan da akace yar matarsa na yanzun ce itakan saboda itace ma banson shiga gidan su wallahi.

Keko ai dole tunda uwata ke mulki a gidan su uwarsu ta rasu tun suna kanana shine ya auro hjy Binta din itama ta dinga haihuwa kamar tururuwa masa.

Dariya zancen ya bani har yasa na dan murmusa ina fadin kamar tururuwa kuma tace ehh mana kin san mu mata ai wani lokaci kan kishi kishi ma harda wanda bai duniya in aka hadu da marasa tsoron Allah sai kiga anyisa ai.

Mun kai wani lokaci a wajen zaune muna hira saida akai sallah la,asar ne muka shiga daki bayan mun fito ne ina shirin islamiya tacigaba da min hiran.

Don nice dai abokiyan hiran Ammah din a gidan don Abbu ba zama yakeyi ba ko yaushe kasuwarshi yake zuwa yaci sai yamma yake dawowa gida ko yadawo din kuma yana waje gun abokan hiransa suna rage dare a wajen.

Ankai wasu yan kwanaki aikin ke nan bada wanan labarin bukin a bakin Ammah din duk da tace an masu wullakanci hjy ta nuna kamar bata sansu ba wanan karon amma kuma tana yaba kyau bukin.

Jerabawan mu na karshe yazo haka muka zanashi cikin yardan Allah muka koma kuma zaman gida zaman jira jin sakamakon daga Allah don jerabawa dai irin wanan dacene sai wanda Allah yabawa sa,an cinyeta yake hayewa.

Duk wanan zaman dakon kuma da mikeyi ban taba jin Abbu yayi min maganan makarantana ba da yaimin alkawarin karasawa gaba a lokacin.

Niko zamcen yana a kasan raina don gaskiya ina sha,awar karatu nikan a rayuwanta duk da nasan iyayyena basu da halin hakan don karatu na masu karfine.

Ga zaman gidan dana sawa kaina a yanzu ya fara isata nima banda wajen zuwa sai dan aiken daba,a rasa ba da nakan jewa Ammah a makwabta shine kadai zance yana sani fita.

Gashi kamar kada ace na kare karatun nan wani irin girma yazo min a lokacin halittana na asali ya kara baiyana a fili sosai har yasa idan zan fita a yanzu na tsiro saka nikaf a fuskana don bat da kamana saboda ido akaina yake ko wani lokaci nake gani.

Ranan na dawo daga islamiya wajen hadda na samu Abbu a gida nayi mamaki kwarai haka kuma a yadda na sameshi yana dauke tabarma da buta da kofin ruwa yasa nagane yayi bako a lokacin.

Don gaskiya ba lokacin dawowanshi bane a lokaci haka kuma dana shiga gidan na samu yanayin Ammah acikin damuwa zan ma iya fadin har kuka tayi a lokacin haka kuma gata saye da hijjabi a jikinta yasa gabana kara faduwa.

Saidai banyi magana ba bayan gaisheta daki na nashiga na aje jakata na dan jima ban fito daga dakin ba sai can naji Abbu ya shigo daga baya sun shiga daki suna zance kus kus kus a tsakaninsu.

Duk da kasa kunnen da nayi don in fahunci kome ke faruwa ban gane komai ba cikin zancesu hakan yasa nima na koma sukuku a ranan.

Ban taba kawo zancen Nana ba araina lokacin yo ina zan kawota ma kusa matarda ba wanda yasan ina ta shiga ko a saudiyan zanyi zaton daga wurinta hakan ya fito.

Wai asheko itace tayowa su Abbu sakon kudi masu yawa a lokacin kuma mai sakon yazo da albishir din cewa tana nan lafiya a wani gari tana aure har ta haifi yara biyu a lokacin shi shedan hakane don sun jima dasu a cikin masallaci a madina a nan suka hadu dashi har ta yaba da hankalinshi mutumin ta yarda ta bashi sako zuwa wajen iyayyen nawa na yanzu.

Wanan yasaka Ammah kuka a lokacin don jin labarin yar uwarta da kuma tarin sakon data bashi yazo muna dashi abin mamaki kuma shine.

Ita tana da labarinsu su daine basu da nata a yanzu amma har inda suka koma ta sani don itace tayowa mutumin ma kwatancen gidan namu yazo.

A yadda mutumin ke fadi ita nana din a yanzu tayi karfi a can itama don tana business dinta tana samun kudi sosai yadda ta bashi labari har ya bukaci ya ganeni akace dashi ina islamiya.

Bayan fitan Abbu gidan kawai ina bakin murhu ina hasa wuta naji Ammah ta saki wani irin kuka daya tayar min da hankali lokaci guda har bansan sanda na fada dakin ba a razane cikin tashin hankali.

Wurin Ammah din dake durkushe ta zubawa wasu kaya idanu na nufa ina tambayanta a gigice da Ammah waya mutu meya faru anyi wani abune ?

Duk lokaci daya nake wanan babatun cikin tashin hankali a gareta kafin idona yakai ga kayan dake gabanta a take zuciyana yayi wani irin ras ras a wajen .

Hakan yasa nakai durkushe a hankali ina bin kayan da kallo da ido abinda ya fito bakina lokacin shine Nanace ko Ammah ?

Wani irin kallo Ammah din ta watso min a lokacin sai kawai na mike na fice daga dakin lokaci guda cikin karfin hali na nufi wajen aikin dana soma naci gaba ba tare dana sake waigen dakin Ammah din ba kuma.

Fitowanta cikin mamaki yayi daidai da shigowan Abbu gidan dauke da kayan cefanen daya sawo muna na dago da idanuna da sukai ja ina masa sannu ya amsa da fadin dama nasan haka Nana ina sauri da Allah Allah karkiyi talge kafin na karaso.

Kayan da Ammah ta karba a hannunsa nabi da kallo da dan buhun daya nuna abincine a cikinsa daya aje gefe daya sai kuma na kawar da idona da sauri akan kayan na juya zuwa aikina ina jin Ammah na fadin malam zo nan ya bita zuwa daki.

Abbu bai karasa shiga dakin ba Ammah din ke fadin yau naji abin mamaki a bakin yarinyar nan da sauri ya juya ya kalleni yaga ina gyaran wuta ya juyo gareta yana fadin meya faru kuma ?

Tayi ajiyan zuciya mai nauyi ta sake kafin tace sunan uwarta naji ta ambato min a bakin ta kamar a mafalki fa malam da cewa Nana ko ?

Dan murmushi yayi kafin yace kin dauka duk tsayin nan bata san komai bane ta sani tasan komai game da uwarta don har hotonta ta gani a dakin nan ai ranan.

Kirji ta dafe tana fadin na shiga uku malam garin yaya haka ya faru yace ban san ya akayi ba amma ta gani ta kuma san komai zaune takai saman dan gadonsu na katako lokaci guda tana dafe kai.

Wai meye hakan data sani tayi wanin abin asshane a gareki ki natsu kibi yarinyar nan a yadda ta bimu ban son tashin tashin da zai kawo bacin rai a yanzu kuma.

Hakan bai sa Ammah shiru ba sai bayan sallah insha,i Abbu ya dawo daga sallah ya fita ta zauna a inda muke zama nan tasa min kira daga daki na amsa na fito zuwa gareta.

Tana zaune a cikin damuwa har lokacin nafito ina fadin gani Ammah ta dago tana fadin barci zakiyi bakici abinci bane Aeesha ?

Na koshi na fada a razane ta dago kai tana sauke min wani kallo tare da fadin me kikaci kika koshi dashi ba komai na fada ciki ciki a wani irin yanayi na damuwa.

Waime ke damun rayuwankine haka kika sakawa kanki wanan damuwa haka to ki jini da kyau wallahi Allahma shedanane Aeesha dani da bawan Allah nan don bamu rageki da komai ba a rayuwan ki .

Yau abinda bawan Allah nan ke dauka a kanki kodashi ya haifeki ya tsaya a nan amma kin bi kin damu kanki kin tsiro da wasu halaiya na daban a yanzu akan abinda bashi bane gareki.

Yau dai nasan duk abinda wani zai fada maki a duniyan nan mukace dake ga gaskiya dole ki yarda da hakan a kanki don shine gaskiyan gareki.

Don ba zamu fada maki abinda zai dawo ya cutawa rayuwanki ba daga baya muma ya cutar damu don muke tare dake ako wani lokaci.

Kuka na dan farayi naji ta sake min tsaya tana fadin ba kuka na zaunar dake nan ki mun ba kiranki nayi inji waya fada maki wani labari a game damu ko ke ?

Kaina girgiza mata a lokaci alaman ba komai a rayuwana saidai ina mai jin wani iri kasan zuciyana kamar in kashe kaina don bakin ciki.

Nake ji a lokacin abinda yasani dagowa shine muryan Ammah din dake fadin duk da kin kasa tambayana labarin da kikewa bakin cikin kike wanan rama to ni nan nasan kin sani.

Saidai ina kwankwanton a inda kikaji wanan labarin shine ya daure min kai a yanzu ba wani abuba so nike insan me aka fada maki game da mahaifiyar ki ?

Da alaman tsoro a fuskana na dago ina kallonta sai kuma na dukar da kai ina tunane tsokin takaici naji taja tana fadin.

Ga kayan can da taba wani bawan Allah tare da kudade masu yawa ya kawo maki har damu don haka sai ki tashi ki duba idan zaki iya don naga kin sakawa zuciyar ki abinda bashi ba a yanzu.

Kaina girgiza nace ko tsinke bana so Ammah abawa wanda duk ya dace nagode ai bankai karshe ba naji saukan hannun Ammah a fuskana saida naje tangal tangal daga zaunen da nake don zafi.

Fada ta fara tana fadin ni zaki kawowa diban albarka Aeesha sakaiyar da zaki min ke nan a yanzu ace na hinjiraki ban maki rikon gaskiya na tsakani da Allah ba.

Idan Nana da mahaifinki sun maki laifi da farko idan kin kula yanzu ita Nana kokarin take ta burgeki ai taga ta wanke maki zuciyar ki.

Ina laifinta ga hakan tunda duk wani abu donko take turoshi a garemu saboda rayuwanki ya inganta ai kada ki dauke mu bamu san abinda mukeyi ba mana.

Ko duniya Nana ta mallaka a yanzu wanan bai tsone min ido ko in kalla balle raina ya biya da ace aikin banza takeyi a can mutumin nan saida ya rantse muna kamar yadda itama ta rantse masa da aure ta daura a can din bayan ta koma saudiyan.

Don haka ki shiga taitaoyin ki dani kafin ranki ya baci kada ki dauko min wani surfa banza ki dagwala min lissafi dashi yanzu kuma.

Sautin kukanane ya karu a lokacin akan nace ban karban kayan da Nana ta turo muna Ammah ke min wanan fadan da baida tushe haka har duka abinda bata taba min a rayuwana ba tunda na tashi.

Gyaran muryan Abbu alaman zai shigo gidan a lokacin yana sanar muna hakan baisa na rage sautin kukan da nakeyi ba wiwi ina jan majina ta hanci don zuciya daya kawo min.

Tundaga kofan gida yake fadin wai yayane meke faruwa hakane wai daga Ammah har ni ba wanda yai masa magana a lokacin.

Sai ya cigaba da fadin tambaya fa nakeyi anyi shiru meya kawo haka kuma yanzu Ammamatan ya juya kanta ya kureta da ido yana son jin amsa .

Haba malam kamar Aeesha zata zauna tana gardama dani yau don wani ya rutsata ya fada mata maganan daba shiba ta dauka tana kokarin rainawa mutane wayau.

Juyawa yayi gareni saida ya kare min kallo a cikin tausayi yace haba Ammah kibi yarinyar nan sannu mana don Allah yau ko me tayi tayisane akan kurciya da dacin rai.

Don ko an tabata dole tayi hakan ina hakkurin ki ya shiga da zaki biyewa yarinya kuna saida hali a cikin shiya muryan kukanta har waje na tsinkayoshi.

Ai dole in biye mata malam da wani yarinyar nan ke son inji a yanzu da nata iya shegen da takeyi yanzu ko da wanda muke fama dashi kan rashin yar uwarmu.

Duk yadda take ji mumafa muna jinsa a yanzu aiko inga dubaiya ban cancaci hakan a gareta ba a yanzu me muka rage yarinyat nan dashi don Allah malam a yanzu ?

Umm,ummm Ammamatan ki duba lamarin nan ki auna shekaru ba daya bafa yau ace kaine hakan ya rutsa dakai ko babban kanka ke ya zakaji abin don Allah.

Shi yaro a sannu ake fahintar dashi ya gane bada garaje ba irin hakan ya juyo gareni yana fadin ke nana rufe min bakin ki a yanzu idan kina son muyi magana a tsanake dake ko kuma in fasa hakan inyi fushi nima in baki baya in fita a zanceb in barki da Ammamata din kuyi tayi.

Jin abinda Abbu din ya fada yasa na sassauta kukan nawa sannu a hankali yana ganin hakan ya juya ya fice daga gidan ban jima ba na mike na shige daki na barta a wajen cikin bina da kallo.

Ya dan jima bai shigo ba sai can naji shigowansa yana rufe gida kafin kuma naji muryansa a kofana yana kwala ma sunana kira da ke nana fito ki karba nan .

Jin hakan yasa na fito daga dakin ya bini da kallo kafin yace ungu jeki randa ki debi ruwa ki daureye fuska da baki kizo ki zauna kici.

Na koshi na fada a sanyayye wani tsawa ya buga min da yasa na nufi sashen randan ruwab namu da sauri ina diban ruwan .

Zama yayi saman shimfidan da yayi a tsakat gida kodana dawo gefensa ya nuna min yana fadin zauna nan a kusa dani .

Ba mussu nakai zaune kamar yadda yace din ya miko min leda da tun kan in bude nasan meye a cikin ledan don kamshin dake fita a cikin takardan ga kuma nutrients milk mai sanyi har guda biyu.

Bayan na karbane ya fara kwalawa Ammah kira itama ta fito ya mika mata ledan yana fadin karbi bude muna nan ya mika mata itama zama tayi cikin damuwa tana bude ledan daya miko mata din a lokacin.

Dan juyowa yayi yana sauke min kallo tare da fadin bissimillah mana Nana nakine wanan gani nayi yau rayukanku sun baci bakuci abinci ba zaku kwana da yunwa daga karshe hakan ya zamo maku matsala.

Maza ki bude ki somaci kikuma saurari abinda zan fada a yanzu ina son kowa ya bani kunnuwansa ya saurari abinda zan fada a yanzu wurin nan.

Don zancene da zanyi a matsayina na uba kuma maigida a gidansa don haka kai tsaye umurni zanba ko wani ku a nan ko kuma doka a gidana don haka ina son kowan ku ya ban hankalinsa yanzu ya saurareni.

Ke Nana dake zan fara don haka ina son ki saurara kiji abinda zan fada a yanzu a kanki don a yanzu kece wace kika saura da wanan zance kuma idan kinyi hakan ba laifi bane don kinyi a wajen kowa.

Ko ita uwarki gata zaune bacin raine da damuwa ya saka tayi maki wanan boren a yanzu amma ba don taso hakan a gareki ba.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/1, 9:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND

MAMAN BIBO KAYAN MATA

08068871330 KOKO ROAD SOKOTO

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

0️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login