Showing 66001 words to 69000 words out of 110493 words
Chapter 23 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx
Koda mukaje gida shiru mukayi mun samu Ammah ta dawo take fadin ance kuna gidan ban ganku ba kuma nace Mina dakin umma da Anty Fati .
Karban aikin abincin nayi kafin lokacin fitan my zuwa wajen bukin ranan yayi nikan ina gamawa daki na shiga kwanciya nayi sai barci sai zuwan su faridane suka tayar dani na falka lokacin Aimana ta dawo ashe wai gida taje ta dauko abu acewarta.
Cacakata sukayi wai nasan zamu fita kuma na kwanta ina barci haka farida na kalla cikin karfin hali da muryata dake nuna barci yaci idona har lokacin nace ba.
Wai kece kawar amarya dai halan in naga wanan bukin duk kin shanye zakinsa farida to Aesha ko bani bace kawar amarya kanwar amarya nake ko saida anty fati fa ta kara turowa a fada muna kada mu makara karfe hudune.
Nina na rasa dalilin da yasa ta kula damu haka cikin sha,aninta maryam ta fada tana zama gefen gado sai Aimana tace.
Kema ai kin sani mana tunda taga yan mata haka shar kun waye da kauyawane wallahi ko kallonku ba zasuyi ba kawai kun zamo hasken bukintane ku.
Nan na barsu suna zancen su wanka nashiga nayi na fito na zauna zaman shiri suma dai hira sukeyi a wajen
Wani dogon rigan lace mai kyau na jawo na dora saman gado kafin na juya na fita kodana dawo na samu dan kwalinsa a hannun Aimana tana fadin.
Amma dai wanan lacce ba garin nan aka sayesa ba na dan kallota nace nan kuwa a Dan kwarai muka saya.
Ta sake juya lace din kafin ta aje dan kwalin maryam ke fadin wanan tellan naki Aeesha badai dinki ba kan shi yayi wanan halan nace shi ke min dinki ai yanzu.
Wait ina kika zakulo tellan don Allah tellan manyane fa garin nan yadda naji kai tsaye nace da it's khairat ta hadani dashi.
Khairat wacece hakana nace yar gidan shehi ce ita tana UG four yanzu school din mu wanan dake karanta Education bata faye shiga mutane ba sosai data matsa saida ta gano tace what wanan ai yayan manyane Aeesha.
Sister din su Man cefa na fada tace wai ina man don Allah tun jiya nake son in tambayekishi ai nace man ya koma America da zama Aimana cikin wani yanayi na ban tausayi.
Tace ke ki bari don Allah nace wallahi da yanzu bakiji ya kirani ba ko kiga Auwal gidan nan da sako cabdi jam ashe karya ta kare maki ke nan Aeesha ?
Jin abinda ta fada yasa na dago da sauri na kalleta tayi saurin fadin eh mana ai gaskiya na fada ina zaki samu irinsa yanzu don Allah ?
Mutum kamar baisan zafin kudi ba yadda ya dinga maki basin kudi kamar wanda ake bugasu a gidansu ba jin zafi ko takaici ?
Lokaci daya ya sauya rayuwanki fa Aeesha ki dubeki ki dubi gidan Ku a yanzu don Allah INA zaki sake samun wanda baisan zafin kudin ba irinsa haka yanzu ?
To ai ba cewa tayi dake sun rabuba cewa tayi ya koma America da zama yanzu ko maryam ta fada ta sake fadin me hakan me nufi ya tafi basu kai ga matsaya ba ya tafi ke nan.
Amma Aimana kina zance kamar wata mai bakin ciko ko hassada kin sani ko zai dawo ko kuma Allah ya bata wani wanda yafishi ma Aeesha fa bamu bane macece da kowa zaiso ta a duk inda ta shiga maryam ta sake fadan hakan.
Wai ke Aeesha shike nan kin fita zancen yayana ko cewa sulaimam lokacin na juyo na kalleta nace farida aini banki yaya Suleiman ba kema kinsan inda matsalan mu yake ai.
Yau ko zaizo nace shima aiya san ban kisa ba matsalan mu dashi ummace tunda tace ni banda asali na fada kai tsaye ga yar nata don tasan na sani.
In Allah yayi ai ba wanda ya isa ya hana hakan saidai gaskiya koshi a yanzu ya ganki yasan kinfi karfinshi shida ko taya baida keko harda motar kanki a yanzu ni wallahi naso insan man din nan amma kuma ya tafi.
Man Dan ka,idace maryam ko a school ba kowa ke ganinsa ba Iran kin ganshi ya fito yin lectures dinsa ne yana gamawa ya koma ciki.
Na shirya tsab na dauko gyale da takalma da jakka na kara fesa turare muka fito bayan na rufo kofa mukaiwa su Ammah said mun dawo.
Hakana suke matsawa su hudu a bayan motar nida maryam muna gaba muka nufi event center inda za ayi wasan a haraban wajen .
Wurin ya cika dam da mutane na samu wuri dan nisa kadan na faka motar a gefe daya daga inda muke muna hango cikin taron muna ganin abindake wakana a filin.
Farida ta matsa sai mufita muje mu samu waje a cikin taron muma ina duban yadda zamu tsara wajen haka zuwa bangaren mu zauna.
Dole dai haka muka shigo wajen cikin jama,a muka ratso kaina a kasa ga mc din ya canza kida slow music na tashi ya kuma mayar da hankalin mutane a kan mu yana irin shakiyancinsu na mc a lokacin.
Wurin zama muka kama faridace ta samo wajen muka zauna gaskiya ba laifi don zamanin nan kwaliya yana gyara mace ko wacece iya kudinka iya shagalinka don kowa ya kure adakansa a wajen wajene na yan mata da samari amma duk da haka wasu matan aure sun tafi wajen da yawansu ma.
Kaina na duke ina karanta sako a wayana naji an rugumeni ta baya dago kai nayi mukai arba da kharat din da muka gama hiranta dazun.
Cikin mamaki da baiya jin dadin ganinta nake fadin antu Kharat ashe kunzo bukin kuma ?
Tace ehh family din mijin antyn mune angon tare mukazo dasu ta nuna min ta inda suke zaune tace amaryan takuce ko ?
Eh family din mu daya da ita yar wanan Abbuce ita unguwa daya kuma muke dasu kice kune da amaryan ashe ?
Dan dariya nayi ina mikewa na gyara saitina kafin nace muje in gaisa da anty din ta riko min hannu tana fadin har da yaya Salman yana wajen nan ai.
Gabana naji ya fadi ambato min sunan salman da tayi sai naji kamar naga Man Bashir ne a yau din duk da bankai ga ganin salman din bama a lokacin.
Amma a fili cewa nayi da ita ashe zamu hadu ke nan dashi lalai dai kam amma kuna waya da yaya magaji kuwa ?
Sunan data kirashi dashi din ya daure min kai don ban taba jin wani ya kirasa da sunan ba gabana sai ita a ran taci gaba da fadin ance numbers din da akansashi dash yanzu basu amfani.
Lokacin na gane watake nufi gashi kuma mun karaso wajen table din da yayan nata suke zaune naji tace anty ummi ga Aeesha ku gaisa.
Ta juyo don kallon mu matar tayi bala,in kama da sir salman sosai tana sauke fara,a a fuskanta tace au kece Aeesha din Man Bashir wai kin dai bar kura tsakanin Magaji da mai babban daki.
Zo ga waje ki zauna ta fada tana nuna min waje daga gefenta da sauri nace no thanks anty tare da yan uwana muke nazo in gaida kene dama.
OK nagode ta kara fada saina kalli kharat din nace anty kharat bari koma wajensu kada suga na barsu zaune tace tsaya ai muna photo tare da Anty for remembering kinsan ba nan take zaune ba tana Ghana da mijinta dan kasuwane shi.
Au dama ba kasan nan suke ba ashe na fada muka sata tsakiya mukai photo ai kafin na bar wajen munyi photo da wajen mutane biyar saiga Farida tazo tana fadin.
Aeesha don Allah zo mu tafi kada ayi badamu ba taja hannuna na dan waigo ina masu sai an jima wai ina zamu na tambaya tace gun angon nai za a karban kudi gasucan ta nuns min su daga nisa zuwa lokacin su maryam na tsaye daga baya kadan.
Wai nifa kinsan ba irin abin nan na iya ba farida da kunje kawai zaifi idan kun dawo ku sameni tace don Allah muje dai ayi a gaban mu gasu maryam can suna jiran mu.
Dole muka karasa daga dan baya kadan muka tsaya muna jin yadda suke ciniki kamar wani kayan sayarwa suka kasa gajiya nayi da dan tsayin naja tsuki tare da dan juyawa ina fadin nifa na gaji zan koma wajen Asmau idan kun gama ku sameni naji sunce yyauwa ga wa yanda muke jira sun karaso motar yazo gaban mu ya tsaya.
Na ciki suka fifito cikin wata farar mota sai sheki takeyi tana walkiya kamar kura haka na zamo a cikinsu don har ga Allah ban taba wani amarci ba sai wanan karon.
Bakin saratu kake ji yana tashi tana fadin ai wanan halin tsiyane ku bamu kudin amarci abu ya gagara sai yawo kukewa mutane da hankali.
Jin hakan cikin rashin da a yasa nace umm,umm haba ina jan tsoki na juya naji wata kawar Fati na fadin Aeesha karaso don Allah wai kece zaki fadi ko nawa za a banu.
Three hundreds thousand's zasu bayar saboda amaryam mai tsadace na juyo ina fadin hakan garesu sai naji sun saka ihu lokaci guda.
Kamar zanyi magana sai kuma na dake ban kara magana ba na juya kawai ina jin angwanan sun kwashe da ihu wai na cika kudi suna ganina nice mai hankali a cikin mu ashe nafi saura barna.
Shi suka bukata shi zamu basu wani so gentle ya fada ya nufi mota ya cirosu Cash yace amma ni zan karba na juyo nace kaba anty saudat dai.
Kece dai zan ba tunda ke kikaiwa amarya kudi suko sai fadi suke don Allah Aeesha jeki karba mugani hakan yasa na taka nazo na mika hannu saiko ya miko min ba musu wurin aka sa ihu lokaci guda matan da mazan.
Saratu don bata da kunya harda guda da shewa cikin watse na juya na barsu nan suna hira dasu muna zaune kawai saiga su saratun da wata da nake yawan ganinsu koda yaushe wai in basu kudin.
Zakice badani take magana ba ganin yadda nayi banza da ita sai kawai ta fara zagina tana fadin kada ki kawowa mutane rainin wayau wallahi me kike nufi da ba zaki bada kudin ba cikin daga murya.
Kudin me mummy na fada masu a gurguje aiko kamar zata tafi ila ya jawota ta dawo tana fadin dole dai ki bayar dasu tunda ba bukin gidan ku bane ai.
Ke ta gidanku nah bari yayan kwarai suyi magana don Allah ba irin ku yuyuyu ba ta dauka zata iya nan Asmau ta wanketa kwal a cikin mutane kai wa yan nan yara sun iya cin mutunci wallahi.
Da kyat na samu na izzasu zuwa wajen mota suka shiga Allah yasa an rage sosai a lokacin don yamma tayi maryam da Aimana suka biyo mu suka shiga muka bar farida da bamu samu gani ba tare dasu.
A karshe akanta fadan ya koma ashe don tace wai na lake kudi ina son in zame wani abu daga ciki ita kuma farida tace haram wallahi badai Aeesha ba kan.
Abamu kudi donta zakice zata rike aikuma wai donme farida zata fadi hakan suka kuma kwasa sukaiwa juna kwal a wajen.
Ba gidan mu na tsaya da mota ba kofan gidan Rabakaya na faka mota ashe ango da wasu abokansa suna nan sunbar wajen taron tare da amaryansu.
Nayi sa,a kawarta din nan saudat suna tare na kirata zan danka mata kudin tace haba Aeesha kamar abin gudu rikesu wajen ki har mu natsu.
Akan kudin ga akai bala,i tace dawa nan suka fada mata abinda ke faruwa tace shege wai gara da baki bata ba da yau ta cucemu wallahi saratu fa bala,i ce don Allah ku aje har anjima.
Gyale na cire na saba a kafada cikin gajiya ganin mun dawo kofan gida ba mutane da yawa lokacin na nufi mota na bude na zauna.
Wayata na ciro ina duba hankalina bai ga surutunsu saijin mutum nayi a gefena yana fadin surutu yayi yawa a can ko hakan yasa na dago kai wanan ne daya miko min kudin yazo inda nake kafin ya jingina jikinsa a motana yana fadin.
Da alama ku yan uwane da fati ko nace eeh ina kokarin saka takalman dana da cire kafa daya a kafata na gyara na fito daga motan.
Aida kin zauna zamu tafine anjima dai zamu dawo zance da dare gun amaryam mu zamu hadu nace ba tabbas don gidan mu ba aikai wanan lokacin a waje balle dare .
Zancen ya bashi dariya kafin yace babban yarinya kamarki haka za a tsayawa fada kada ki sani dariya don Allah yanzu a gajiye nake nima anjima dai zan dawo insha Allahu.
Nadago da zumar zance ba wasa nake ba kada ka dawo fa idona ya sauka kan yaya sulaiman gefenshi kuma yaya habib ne da yarsa yana alwala .
Saidai muna hada ido ya sako min wani harara dana kasa fassara kona meye a lokacin ko halin nasa na muguntane ya motsa oho ?
Kafin na dago har maishi ma ya juya ya fara tafiya saratu ta karaso muka shiga mota nayi ribas zuwa gida a can ta fita ta bude min get na shiga da motar .
Tsayawa mukayi kus kus ina bata labarin abinda ya faru sai cewa tayi me zakiyi dasu don Allah shidai wanan ai karsanane yana da mata zai hanaki hirane ?
Shi kuma Suleiman wallahi kada kima tsaya kulasa tunda uwarsa bata kaunarki mummy ki rabu dashi kawai don Allah.
Asmau bai mun komai bafa kuma muna waya dashi gaskiya da nasan ya iso garin nan bama zuwa kofan gidan nan yau.
A,ato mummy kina son wahal da kanki kuma rabu da uwar mijin data fara nuna maka tsana da danta tun a waje wallahi garama wace ta boye sai kaje ta fitar da halin ai.
Ke mummy nifa ban maki fatan kowansu a yanzu wallahi suma sunsan kinfi karfin su a yanzu wallahi.
Waiku baku shigowa gida kun tsaya kamar masu tsunami muryan Ammahce data leko take fadin hakan garemu sai asmau tace kai Ammah magana mukai da uwata wanan yar iskan yarinyar keson ta raina muna wayau.
Nan ta shiga koro mata fadansu da saratu naji dadi da amsan da Ammah ta bayar a lokacin nace mungama zuwa bukin tunda wanan yarinyar dai ta nuna bata kaunanku cikin sha,aninsu.
Wanan halin tsiya har ina zata saka min yarinya a gaba cikin mutane da zancen banza tunkan a fara bukin nan yarinyar nan take tsokanar Aeesha ina taushewa kaza na son data koda take takasa.
Don ba fin Aeesha tayi asali ba nata kaddaran ke nan yazo mata haka ku shige kuyi sallah lokaci na wucewa ta fada a karshe muna alwala su samira da Aimana suka shigo nan suka fada muna fadan da akayi da farida bayan tahowar mu.
Daga daki Ammah ta fito tana fadin kun gama zuwa wanan bukin dama da dai da duniya yaran nan na hjy Aginatu basu gaji arziki basu dan dama dan namijin nata yana da dama shi.
Buta na mikawa Aimana na mike zuwa daki don inyi sallah tare da cire tufafin jikina har lokacin ina tsinkayo fadan Ammah har lokacin.
Bayan isha,i muna falo ana ba anty safiya hiran abinda ya faru yaro ya shigo yana fadin wai sulaiman na kiran Aeesha.
Tsit falon yayi na dan lokaci guda Asmau tace kace tayi barci nace kai ce masa ina tafe kaji lalai kam ya Suleiman nefa Aimana ta fada.
Suka hau fada wai wallahi kar inje kawai in fita batunsa kiran me zai min kuma bayan uwarsa ta rabumu.
Na dai mike na shiga daki na fito a tsaye na sameshi ya jingina jikinshi da bango tare da harde kafa kamar yana tunane a lokacin yana ganina ya saki ajiya zuciya tare da fadin.
Ran gimbiya ya dade ashe zaki fito na dauka ai ba zaki fito ba idan yace maki da kafa nazo ban iya bakar magana ba da nayi masa amma sai na wayence da murmushi ina fadin.
Aeesha da ka bari daice wanan ba wata Aeesha bace aka canza idan ma zolayata zakayi ni har yanzu ina nan yadda nake ban canza ba saidai kai kila mutanen kaduna sun sauya ka.
Ke kinga alaman sauyawa a wajena Aeesha har yanzu ina nan a Suleiman dina da kika sanni