Showing 18001 words to 21000 words out of 110493 words

Chapter 7 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2306

KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Nana na dauka ilimin ki da wayaun ki tare da tarbiyan ki zai saki natsuwa ki fahinci gabar da muke son dora rayuwan ki a yanzu ?

Sai gashi kuma na hango ba hakaba a wajen ki don nayi zaton yadda ake zuzuta ilimin da kwazo a yanzu zaisa ki hango matakin da muke shirin doraki.

Idan kinyi tunane da babu dan dana taba bari yai zurfin ilimi a gidan nan kamar yadda ke muka barki a yanzu kina samun ilimi shin azaton ki yanzu nayi hakan ne saboda ban haifeki ba ko me ?

Da sauri na dago kai ina kallonsa cikin hawaye ina girgirza kaina a gareshi da nufin ba hakan bane yace kamar hakane Nana a ganina.

Bari kiji dalili a yanzu na hango ilimin nan shine tsanin takawa a duniya shine matakalan cinma burin rayuwa ga dan adam yanzu.

Inkai manomine sai da ilimin nan na zamani yake bunkasa haka in kai malamine saida ilimi kake samun cigaba a rayuwa ke komai yanzu da zakayi hatta kasuwanci yau ya koma idan baka da ilimi hakan bai bunkasa yadda ya kamata ga bawa.

Hakan yasa nayi amfani da wanan daman na ke kokarin ganin mun inganta rayuwanki don gabarki ki samu makoma mai kyau a cikin rayuwa.

Alhamdullahi kuma donke din yarinyace mai natsuwa yare da tarbiya yasa muke maki hangen hakan a kanki a yanzu don ba zanso mu tauyeki ba mu durkusheki nan gaba ba zaki fahinci mun maki rikon tsakani da Allah ba.

Amma da ilimin nan na zamani zaki fahinci komai a rayuwa a yadda muke fata haka kuma keda kanki zaki warware ma rayuwanki dana iyayyen ki hukunci in muna da rai da lafiya.

Idona na runtse cikin dacin rai daga inda nake zaune ina maijin yadda zuciyana yake tafarfasa lokaci guda don ambatosu da yayi a zancensa.

Ya dora da fadin to don hakane nake son in baki dama daman da ban taba ba wani yaro ba a gidan nan don ki samu ilimi mai inganci da zaki taka kafarki dashi har hakan ya zamo maki bangon dafawa a rayuwan don akwai rai akwai mutuwa ga bawa in mune yau ba mune gobe ba a duniyan nan.

Amma fa duk wanan dole saina saka daga wanan arzikin da ita mahaifiyarki take turo muna hakan zai yuyu don ke shedace banda halin wanan hasashen da nake maki a yanzu.

Don haka zancen ace kince ba zakiyi amfani da dukiyar da mahaifiyarki ta turo ba baiko taso a garemu ba yanzu wajen ki nana.

Don koda rantsuwa nayi a wajen ban kaffara ta turo munane don inganta rayuwanki a gaba don ba Ammamatan bane kadai ta bari ai nan najeriya suna da yawa meyasa bata turawa sauran yan uwa kudina idan sun mata yawa ne kike gani.

Don haka banso ki zalunci kanki da kanki nana in ma wani abu kike tunane a yadda nasan Nana Asma,u sai naga ya girgiza kai ya kare da fadin nana tafi wayau da dabara a duk wajen nan.

Don tasan inda ta fito tasan darajan iyayyenta dana yan uwa ba zata bari wani abin asha ya shigo rayuwanta ba a can wanan yasa ina cikin wa yanda suka yarda da abindata fada dari bisa dari da wanan kaddaran rabonki ya gittamata a lokacin.

Nasan ko waye nana a lokacin don a wajen mu ta fara zama kafin a kulla karbanta daga hannun mu abawa hajiya Naito rikon da ya zamo sanadin komai a yanzu daga baya kuma kowa ya dare ya koma gefe yana gulman hakan.

Ki godewa Allah Nana kina cikin gatanki da rufin asiri akwai dubunki da hakan ya rutsa dasu nana basu san kowa nasu ba a duniya sunan nan suna walagigi da tangaririya a cikin duniya.

Ke ko uwarki tayi maki gata bata barki ba sai da ta tabbatar da ta barki a hannun yar uwarta daba zaki taba kukan tanshita a kusa dake ba.

Don haka in dai har na isa dake ina kuma da kima a idanunki daga yau din nan na kawar da zancen Nana As,mau a gareki har zuwa dawowanta haka kuma duk abinda ta turo da sunan naki ki dauka kiyi amfani dashi Aeesha.

Ke kuma Ammamatan daga yau din nan bason a kara tayar da zancen nan don Allah har hakan yaba wani daman shigowa ya dauki sirin da muke faman dannewa shekara da shekuru a zukatan mu.

Akwai sarka guda biyu da nana ta bari a lokacin suna wajen mu har yanzu mun masu boyon da ba mahalunki da zaisan dashi a gidan nan bayan mu.

Don haka zan fito dashi a yanzu akai kasuwa a auna a tabbatar da kudinsa albashin in yaso idan sayarwa zamuyi sai a sayar a fara shirin karatunki da kudin ni nawa shawaran ke nan a yanzu .

Sai naji Ammah ta nisa a hankali tana fadin to amma malam sai naga zancen karatun nan nidai gaskiya bai kwanta min kawai a sayar ta fito da miji anyi mata aure kawai shiyafi a daina wanan zance ko zata samu natsuwa itama.

Dan murmushi Abbu ya sauke tare da fadin kaiya ana baki kina roko amma na fahinci kina ganin wanan shawaran nawa baiyi ba akan yarki ke nan ko ?

Yata kuma yau malam to Allah ya baka hakkuri in abin har yakai can amma ni bada wata manufa ai na fadi hakan ba don kace inda mai magana yayine yasa na tofa nima.

Kayi hakkuri bana rainawa tsarinka bane a yanzu gaskiya don nasan kafimu tunane ai dagani har ita kawai dai ina ganin auren kamar shine mafita a yanzu.

Ammah ina son karatu don Allah na fada cikin sanyin murya don jikina ya gama mutuwa a lokacin da zantukan Abbu din dayakeyi akaina don a kainane zance ita Ammah nata mai saukine ai.

Nice dai bawan Allah keson ingatawa rayuwana a wanan zaman kuma iya abinda ya rage ke nan suyi min a yanzu din har incinwa burukana na duniya a yanzu.

Yadda yace hakan ya faru don washegari da safe yai kirana da kansa ya mika min tulin kayan da nake gani kamar wani shara a lokacin a hannuna ya kuma kara min nasiha akan rayuwa.

Don gaskiya Abbu ya fada ba wanda ya isa ya kaucewa kaddaransa sai in Allah yaso hakan ga bawa haka kuma ko wace kaddara tana da wata manufa ga bawa Allah kadai ya barwa kansa sanin dalilin hakan.

Yadda nakai kayan daki na watsa ban dago na sake waiyayansu ba duk da zuciyata tayi laushi a lokacin amma nake ganin kayan wani mugun abu a gabana.

Don haka zan iya cewa ban bude ko leda daya na duba inga yaya kayan suke bama balle insan kallarsu kayane kuma masu yawa da zasukai kala goma ko fiye da hakan ajiye.

Saidai kamshinsu daya ciki min dakin don kamshi sukeyi irin na turaren yan nahiyar can ta larabawa hakan ya fara sa kaina yana dan sarawa a lokacin.

A hankali har na kai kwance ban fadawa kowa banjin dadin jikina ba a gidan sai Abbune da zai fita yake kwala min kiran da nazo nagani .

Wanan yasa na taso a dunkule cikin hijjab din islamiyata ina dan kaduwa na nufoshi a hankali ya fara walwale min sarkankokin a gabana inda nake tsugune yana fadin.

Kinga wanan biyun tun barin nana kasan nan data tafi ta barmu dake suke boye a hannuna wanan kuma sune ta aiko daga bayan nan.

Saidai gun Alh sani zani dasu don akwai shagon sarkoki a kusa da shagonsa su auna su fada muna nauyi su in yaso sai mu in dawo asan abinyi dasu din kamar yadda na fada a jiya.

Kai kawai na dukar tunda nayiwa sarkokin kallo guda ban sake dago kai na kallesu ba kuma saida na amsa masa dakai kawai hakan yasa ya dago don ya kalleni anan ya fahinci yanayin da nake ciki lokacin.

Da sauri yake furta subbahanallahi meke damun ki haka nanata nan hankalin Ammah dake kokarin kauda kayansu gefe daya ya dawo gareni.

Tasowa tayi tana tamba jikina ta juya wurin Abbu tana fadin jikin gaba daya ya gashe kamar garwashin wuta kina ciwo Aeesh ba zaki fada kika kokarin halaka kanki haka ba gaira ba dalili saboda mugun abunda kikasawa zuciyar ki.

Hannu Abbu ya daga mata ya mike da sauri yana fadin tashi muje chemist haka na daure naje chemist din tare dashi akai min allurori masu karfi na maleria tare da magani muka dawo gida lokacin idona ya gaba rufewa sai barci ya daukeni.

Duk suna zaune sun tsureni da idanuwansu ganin na samu barci mai nauyi yasa Abbu fitowa daga dakin yanawa Ammah hannu da alaman ta biyushi.

Batayi sanya ba ta mike ta biyoshi din zuwa wajen cikin tausa murya ya soma magana da fadin Ammamatan meyasa baki amfani da hankalinki ?

Wani kallo ta watso masa yace kwarai ko so kike yarinyar nan ta bijere muna a yadda muka santa a baya ?

Yanzun ne tafi bukatanki yanzunne kema zaki nuna mata kauna da kulawan ki a gareta don ga baki daya a yanzu bakin mu take gani a wanan gabar.

Dole sai kin kara janta a ciki sosai fiyema da da can baya ki nuna mata itama yace kamar kowa tunda tana damu a duniya koba nana a kusa balle mahaifinta damuma ba mu sanshi ba.

Wanan abin naki zai kara saka yarinyar a wani mugun yanayi da ba zamuso ba ki kwatanta a gareki yau ke haka ya sama a duniya ya zakiji zuciyar ki a lokacin da kika sanda haka ?.

Nan dai ya lurar da ita halin da nake ciki kuma ta gane gaskiya Abbu ke fada hakan yada dana falko naga sauyi sosai a gun Ammah din duk da bada wani manufa take min hakan duk cikin tsawatawan su na manya ne a lokacin.

A hankali na yaye hijjab din dana rufu dashi har kai ina kai dubana ga Ammah din dake zaune a gefena tana yankan kubewa.

Sannu tayi min tana fadin sannu Aeesha kin falka ya jikin naki na dan juya dara daran idanuwana kafin in koma lumshesu ina fadin da sauki Ammah.

Kokarin mikewa nakeyi zaune naga ta tashi da sauri tana kamani tare da fadin ina zaki da kyat na bude baki ina fadin bayi a takaice.

Zaki iya ko in kamaki ta fada cikin kulawa nace cikin karfin hali zan iya Ammah na mike na fita kodana fito na samu ta fito daga dakin ta dauki tsintsiya a hannunta.

Alwala na duka na dauro don duban yanayi da nayi ya nuna min an dade da sallah axahar a lokacin hakan yasa cikin karfin hali na daura alwala.

Nazo nayi sallolina don tun ina alwala aka kira sallah la,asar duk da yau sauri saurine amma dai nasan lokaci tane yayi don basu muke bi sallah ba a gidan sai hudu daidai muke la,asar.

Na dade a zaune ina mika kukana ga sarki Allah wanda yafi kowa sanin dumbin damuwan tattare dani a zuciya wanda ba kowa zai fahinci hakan ba sai wanda kaddaransa yazo daya da nawa din.

Don ace baka da uba kasan hakan da girmaka ba karamin tashin hankali bane a wajen mutum saidai Allah ya kyauta kawai.

A inda nayi sallah nakai kwance a hankali ina bin dan dakin nawa da ba komai na rayuwa a cikinsa sai dan tsohon katifana da akaiwa cikon ragga gefe daya kuma dan tarkacen ghana most go din kayanane a ciki wanda idan ya lalace nakan fadawa Abbu ya sayo min wani in canza a lokacin.

Naso in koma barcin saboda jikin bai sakeni ba amma sai hakan ya gagareni sunayen Allah mai girma na ringa kira don na samu natsuwa a zuciyana a haka barcin ya soma daukana kuma.

Saida naji muryan Ammah a kaina tana fadin haba Aeesha duk da ciwone ki dan tashi zaune barcin yamma baida kyau aiga musulmi.

Hakan yasa na mike na zauna na jingina da bangon dakin nawa ina faman raraban ido tare da tunane kala kala a zuciyana don ji nake na gudu naje saudiyan ayi wadda za ayi acan din nida Nana idan naje.

Amma a take zuciyana ta tambayeni da wani kudi zan tafi din nida banda ko dubun dayan kaina a jikina nake zancen zuwa saudiya a yanzu.

Wasa wasa kwana biyu nayi ina fama da wanan zazzabin na karaf daya kuma nasha allurai gareshi na samu na mike kacar majar daga zazzabin.

Son gaskiya gun iyayyena na samu kulawa sosai har ina mamakin hakan saidai sanin halinsu na kirki yasa banyi wani shakkun hakan da yawa ba.

A dan wanan takin kuma nayi iya bakin kokarina da shawaran da zuciyana ke ban na watsar da zancen Nana da wani mahaifina wanda ma kowa bai sanshi ba a yan uwa.

Ya zama dole gareni in rugumi iyayyena dana taso na sani a matsayin iyayyen haihuwana din don sune dai sanyin idanuwana a duniya.

Don a duniya sun min komai a rayuwana banga abunda zaisa a yanzu in nuna masu wani halin banza ba in tayar masu da hankali alhalin su basu gujeni a yadda nake ba.

Musanman ma Abbu da ban hada komai dashi ba amma ya rikeni riko na fissabillahi in ace ita ammah yar uwatace shiko fa mena hada dashi kuma cikin hakan kuma bai kasa dani ba.

Zance Alhamdullahi a dan takin don yawan addua da kuma kulawan iyayyena yasa na daina wanan tunanen na rugumi kaddara a zuciyana duk da dai ba zan taba manta hakan gareni ba a rayuwa.

Sai hakan yaiwa iyayyen nawa dadi don sun nuna min hakan zaki samemu zaune da Ammah muna hiran mu ta duniya gwanin ban sha,awa duk da ba fita dai nakeyi ba ta gaji ta saka min ido tunda haka na zabawa rayuwana ta barni.

In Abbu yaji tana min fada yakan ce ikon Allah wasu na neman nasu su zauna a gida haka ke Allah ya baki salihar ya kina fada akan fita kuma ?

Ammah din kance malam ace ya mace kullum kumshe a gida ina zata samu manema da zasuso aurenta haka ?

Yakanyi murmushi yace wata rana kyace nace don sai kin kore a gidan nan hakan bai kan gamsar da Ammah din don takan amsa masa da Allah yasa kawai.

Ko jikina ka kalla zaki san hankalina ya kwanta a yanzu don har dan jiki na fara girkawa alaman kwanciyar hankali dai a tare dani din lokacin.

Saidai kullum ina a cikin zullumi da tunanen makoma na haka wani abu dake tsaya min a rai shine wanan kudin da nana take turo ma su Amma din akan meye shi ?

Ita tasani ni dai ban bukatan komai nasu na iyayyena ya wadatar dani a yanzu nakan fada a zuciyana idan nayi wanan tunanen.

Damuwata alokacin jerabawana ya fito yayi kyau in samu zuwa gaba da Abbu yayi min alkawari kullum hiran mu dashi ke nan isan mun zauna.

A wata rana naje islamiya nake jin labarin fitowan jerabawan mu din na dawo gida da murna ina fadawa Ammah itama murnan tayi tare da min fatan alheri.

Haka yasa na kwana ina addun,a da rokon Allah samun nasara akan jerabawan namu don tsoro daya kamani kuma don jerabawa sa,ace akace ba wai iya kokarin kaba.

Banyi sanyi a gwiwa ba washe gari na shirya zuwa duba don an fada min yadda zanyi saukin abin tare da Abbu zamu tafi duba don haka yake da kula akan komai na iyalinshi.

Tun shigan mu school din Abbu ya shedawa kansa yadda na kasa damu suke murnan ganina suna fadin ga anty Shu,wa ga anty social don nina rike wanan mukamin saboda tsabata a lokacin.

Ba wanan ne a gabana ba sai addua nake faman yi a zuciyana tunda muka tunkari office din examiner da yar fa,asab ya tarbemu yana fadin.

Mahaifinki kega nace masa ehh naji yana fadin baba Allah yasa kubar yarku nan taci gaba da karatu don nan gaba insha Allahu akwai alheri idan taci gaba da hakan .

Yakai zaune yana zaro wani dogon takarda a gabanshi yana dubawa tare da fadin saidai muce alhamdullahi baba don bana jerabawa yayi kyau gaskiya munyi alfahari sosai da yaran nan.

Sunana ya dago yana tambaya na fada masa har lokacin jikina yana dan rawa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login