Showing 99001 words to 102000 words out of 110493 words

Chapter 34 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2287

nan ba saidai ingani a wajen wani kila balle a yanzun da nake daliba ?

Yau sai gashi a matsayin nawa wai cigaba nayi da zaro abubuwa duk na,uran ukku wanda zai amfanenine wajen aikina da zanje koyo har Abuja da schoo din mu ta turamu yi.

Sai kuma sabuwar waya dal da hannuna ya dauko karshe wayace ta gaba da wanda nake riko yanzu a hannuna can a cikin kwalin karamin na,uran na tsunci wani envelop a cikinsa da rubutun Man Bash a saman takardan ido na tsura rubutun nashi na dan lokaci ina tuno abubuwa da dama a zuciyana hakan yasa.

Jikina na rawa mika hannu na nake kokarin bude takardan acikin tsoro tare da fargaban abinda zan iya samu rubuce a cikin takardan.

Ina tura hannu don zaro takarda sai na zaro kudi suka zuba daga ciki irin kudin kasashen wajene sabbi a mike cikin takardan da nake zaton wasikace da farko .

Duk da a lokacin bansan darajan wanan kudin ba ina dai ganin su sometimes a photuna ko a film don haka nasan abune mai daraja sosai.

Ina kai ido sai ya sauka ga yar farar takardan dake a nade tsakiyan kudin na dauko na bude nan na fara ganin bayanin komai dake cikin wanan jakar ya tsara min yadda zanyi amfani dashi har kudin dana gani din saida yayi min bayani akansu.

Kudine da zanyi amfani dashi wajen cin abinci zirga zirga da sauran abinda zai saya inyi daraja a gaban kowa koda wajen aiki ba,abamu alwances ba a ma,aikatan ya kasance ni ina da kudi a hannuna haka yai bayani a gajarce.

Bayan na gama karantawa na koma na nikesu yadda na samesu baki a laikum ciki da mamaki fam a zuciyana.

Don haka lokacin haka na koma gado na lafe kwance ina tunane a kan halin Man Bash din.

Zuciyana fam cike da tunanen shi wanan Bash din wani irin mutum ne wai haka da bahagon rayuwa sunan wani littafin makawa.

Monday da safe sako ya shigo min na accepting letter dina da cewa next week coming zamuyi reporting a ma,aikatan don fara training din mu a can din don haka bani da wani dogon lokaci yanzu.

Dole na fara shiri saidai banson barin garin ba tare dana tabbatar da fara karatun yaran antyna ba da yanzu na kwallafawa karatunsu rai kuma ina cikin process din zancen tafiyan yazo min.

Don haka ban bar gari ba saida na tabbatar da yaran anty sun fara karatu samira taje sokoto kwananta biyu ta dawo da takardun su kananun na jefasu primary din da Sama,ila ke zuwa ta gwaunati .

Inda Samira ta samu gurbi a COE amma late addimition muka samu ita kuma Asmau zata yi jerabawan waec ta maimaita shekara mai zuwa inda zata dinga zuwa makaranta daukan darasi.

Bayan na gama dasune na fara shirina na tafiya abuja a gagauce ba wasu kaya mai yawa na dauka ba dan akwatina na tsakiya shina zuba tufafin da zanyi amfani dasu.

Sai kayan amfanina a cikin karamin kuma na loda sauran tarkacen unders dasu mai da sauran abinda zan iya bukata a can din.

Tafiyace wadda ban taba yin irin saba haka zanyi inama nake zuwa nidana tashi a kifin rijiya bansan ko ina ba sai wanan garin kawai.

Mun dade da Abbu da Ammah a daren da zan tafi din suna jamin kunne tare da dorani a hanya kan zama a bakon waje da zanje yi a yanzu.

Kowansu yayi min iya nasihan daya dace inji daga gareshi don Abbu cewa yayi shi yayi niyar kaini da kansa har gidan yaya habib din amma yaya din yace basai yazo ba ai zan iya.

Don hakane tafiyan ya fasu dashi din yanzu ni kadai zan tafi kamar yadda yaya din yace dashi da mun kusa sai in kira waya sai azo a daukeni duk inda nake.

A karshe Abbu ya ciro kudi a aljihunsa ya miko min da sauri na girgiza masa kai ina fadi Abbu ba sai ka ban kudi ba duk abinda zamuyi sun bamu kudi a kansa da suka turo muna jiya a banki.

Ai kaji saukin abin naku ba sai iyayye sun wahala ba dai nikan karatun nan naki yazo min da sauki Nanata duka duka ban kashe wasu kudi daga aljihuna ba akan karatun ki sai nake gani ke mai sa,ace nanata.

A raina nace munyi sa,a dai Abbu Allah ya tsaya muna ya turo muna Man Bash a rayuwan mu mu duka komai yake zo muna a saukake a rayuwa.

Zance rakiyana kamar na barin garine a lokacin saboda gaiyan yan rakiyan dana samu zuwa tasha maryam farida samira da Asmau yar gaban goshina rike da hand bag dina a cikin damuwa.

Don hakane mutane da yawa a unguwar mu suka sanda zanyi tafiya a ranan har gareji mukaje tare dasu munyi sa,a saura mutum biyu motan ta cika.

Ba a dauki lokaci ba sai gata cikon biyu ta iso motan ya cika don duk uban sammakon da mukayi motan farko ta riga data wuceni a ranan.

Saita biyu muka samu a lokacin don haka ba,ama gama saka kayana ba cikon ta bakwai tazo zamu tashi ke nan mubada kudi.

Na mika masu nawa tare da kirga wasu kudin na mikawa maryam ita da farida tace haba dai Aeesha kada kimin hakan nace ba zaki samin albarka ba ke nan ?

Jin hakan ta karba sai kuma su asmau duk da na basu amma bai hana in kara masu ba nashiga mota bayan adduan da Abbu yace inyi tunkan in baro gida na tawakhaltu illa,lah lahaula wula kuwatu illabillah na shafa a fuskana sau uku.

A baya muka zauna mu mata da wata musulma da wata kabila don ta shiganta na gane hakan suna tsaye mota ya tashi naji idona ya ciko da hawaye lokaci guda.

Har na daina ganin su sannu a hankali muke fita garin ta bangaren da ban taba sani ba a cikin kano har zuwa lokacin da muka hau titi da kyau driver ya fara sharara gudu damu a motan.

Inda wasu na waya wasu kuma suna hira irin ta kusa dani ke nan mai bakin surutun tsiya da son a sani.

Irin mu dai sai faman raba ido nakeyi ina bin ko ina da kallo tare da karanta sunan yan kauyukan da muka shigewa a hanya wanda nake jin sunan su.

Ta gefena dake zaune a tsakiya ta dan kalloni tana fadin you seens worried baki so barin yan uwa ba ko haka gida yake ba dadin rabuwa wallahi ?

Murmushi na juya ina danyi kafin na lumshe idona tacigaba da waya da aka sake kiranta a lokacin ina jin damuwa don surutun da takeyi har cikin raina hakan yasa na dan ja tsuki ina gyara zama ta hanyar jingina kaina da gefen glass din mota.

Tana aje wayan ta juyo take fadin akwai sauran zama har yanzu shiyasa nafi son inbi jirgi don yafi min sauki da shiga motan nan sauki .

Sai naji dayan matan ke fada mata ai don yau babu jirgine kuma tana son shiga office da safe itama ta biyo mota.

Ban tashi ba ina dai kwance ina jinsu nayi shiru saida muka kai kaduna driver ya tsaya wai za a duba mashi mota wanan yasa muka fito daga cikin motan .

Ina kallon yadda suke sayayyan abubuwan ci saidau ni komai ban saya ba da sunan ci a wajen a hankali na tura hannuna a cikin jakana na dauko air pies dina na makala ina sauraren sheck albani zariya.

Inda yake bayani akan sallah don kullum ban gajiya da saurarensa shine best malamina a lokacin wa,azin albani.

Hakan yasa nake bin kowa da ido wajen har zuwa lokacin da aka gama duba mai motan cikin abinda baifi minti talatin ba muka kama hanya kuma.

Saidai tun a nan yanayin garin ya sauya sanu a hankali hadari ya hade ko ina bakikirin ba,a dauki lokaci ba kuma ruwa ya sauko mai karfi haka muka iso Abuja ana lema ruwan sama.

Wanan ya tayar min da hankalina gashi ban kira yaya ba kamar yadda yace na kirashi ko matarshi idan na kusa isowa Abujan amma don ganin ruwan saman da akeyi din yasa ban kirasu ba a lokacin.

Ga ruwan sai an dan tsagaita sai kaji ya dawo kuma dole haka na daga waya na kira yaya habib kira biyu bai dauki wayan ba yasa na gwada kiran matarsa basira itama bata samu dagawa ba.

Ya sallam na furta a fili yasa wanan bahaushiyan da muka shigo mota daya dan kallon inda nake tana fadin wanda zai daukekine baki samu ba ko nace wallahi.

Nima gashi ina kiran gida amma sunki su daga call din may be suna can suna barci tunda ban gida.

Shekaran jiya na bar nan Abuja naje buki kano shine na dawo yau wani unguwa zaki ke ta tambayeni nace garki which erea nace erea ten yadda naji a bakin basira din matar yaya habib .

Sai naga ta dan tabe baki tana fadin ni gwarinpa zani ba waje daya zamu ba dana daukeki sai ga wayana yana ringing na daga da sauri yaya habib din ne a layi yake fadin.

Aisha kun kusane nace ina tasha tundazun naga ana ruwane ban kira ba yace kinaji Basira zatazo ta daukeki don ni ina nan nashigo Nasarawa ban kusa da gida yanzu.

Ok to yayi nagode naji ya kashe wayan shi tace kin samesu ko nace eh nagode da kulawan ki sai wajen kamar rabin awa anty Basira din ta iso tana dan waige waige hangota da nayi yasa na fito daga cikin motan har lokacin ana dan yayafi mai karfi .

Kwankwasa mata glass nayi ta juyo tana fadin to har zan juya na dauka ba nan suka saukeki ba ai a nan muka sauka na bata amsa.

Ko ina akwai na Allah wani dan tashan ne ya taimaka min ya kwaso min kayana zuwa bayan motanta muka shiga na fito da dubu biyu na mika mai yana tayi min godiya.

Taja mota muka tafi tana fadin shikan yau babu kamarsa ai yafi driver ma samun riba na daiyi mata murmushi ina fadin mun sameku lafiya ?

Wallahi lafiya kalau Aisha yaya hanya ya kano kuma kai ina su mummy da kowa gida nace suna gaidaku anty ya kuka dawo kwanaki kuma ?

Kai bari bari duk a cikin hausanta da harshenta keda surki da yarensu take fitar da harafinta amma ina ganewa tsab don hausane amma fitan harafi ne ya banbanta.

Kano kan wai badai kuma yanzu ba gaskiya wanan bukin ma don na fatine naje wallahi ban iyawa da banje ba .

Irin ginan nan ne mai hawa hawa ta tsaya gabanshi muka fito na dauki babban jakkar tawa da karamin ita kuma ta dauko min dayan dayafi karanta.

Tana gaba ina baya da kyat na iya hawa saman na biyun da suke da kayan hannu ta sanya ta danna bell ba bata lokaci naji ana kokarin bude kofan ta ciki.

Wata nagani mai dan buje da kitson attach akai tayiwa yarinyar yare tare da dan gusawa ta jaye naji tace min you are wellcome tana mika hannu in bata kayan na mika mata dama a gajiye nake lokacin.

Abunda mummy gidan Rabakaya maman yaya habib ta fada min da naje sallamanta dashi na fara arba don cewa tayi Aeesha zaki iya zama gidan yaron nan don na sanki da yawan addini.

Shiko gidansa kamar gidan kafirai yake don yan uwan matan nasa dake zaune taba agidan ba sallah ba salati sai kafirci.

Zan iya mummy na fada a kunyace tare da nuna mata ba komai a zuciyana don yadda tayi maganan cikin yanayin damuwa fam a zuciyarta .

To ki hada da hakkuri kije kiyi abinda ya kaiki ku rabu lafiya kinji don basira bata da dadi wallahi duk da farfar din da tazo nan tanawa mutane na karya .

Abinda ya hadasu da fati ke nan lokacin har muka samu sabani dasu saidai ke nasan kinfi fati hakkuri saukin abin ke nan .

Sai gashi suna gusawa daga kofan nayi arba da wasu katan maza biyu dagasu sai wani dan gajeren wando dayan yarinyar kuma cikin ta ukkunsu itama da nata dan buje ajikinta iya cinya.

Duk da ana ruwan sama hakan baisa sun daina abinda sukeyi ba watau karta don cards ne a hannunsu suke bugawa a lokacin da ake son bawa ya natsu.

Wa,iyazu billahi na fada a zuciyana ina kawar da kai daga kallon tsiraicin da nake masu lokacin don dasu da tsirara duk daya nake ganinsu a idona.

Yarensu tayi masu duk suka dago suna fadin you are wellcome sannu da hanya na amsa da hausa yauwa sannun ku itako sai cewa take Aisha Aisha yau gaki Abujan mu ko ?

Saidai kiyi hakkuri da dan gidan namu fa ba girma nace haba dai ba komai anty ta nuna min kujera na zauna ina mamakin wanan bakin rayuwan dana fara sama a cikin zuciyana.

A cikin yare ta dakawa wace muka sama ta bude muna kofa tsawa kamar fada naga ta mike zuwa kitchen dinsu sai gata da wani farin goran da aka durawa ruwan sha a gida yayi sanyi a ciki tare da cup ta aje a gabana.

Tun kan budurwan ta dago nace a,a yau akwai sanyi ai nagode ki mayar ina Amira ban ganta ba na fada ina dan dube dube naji uwar tace dani tayi barcine yau zata sha mamaki idan ta tashi ta ganki gidan nan ai zamuga zumudi.

Sai naji dayan na mijin na irin yarensu da ita ta bashi amsa a gyatsire tace emba.

Wai ashe ya tambaya nima sister din baban Amira ce tace dashi eeh hira take jana dashi niko hankalina duk a tashe yake lokacin da mamakin wanan rayuwan kamar na kafirci da nagani a gidan yaya habib .

Ba Abinda ke raina sai kyankyami wanan gidan da zamu gaurayu a cikinsa muyi rayuwa har tsawon wata uku dasu haka wai ?

Maryam ce ta kirani a waya suji kona sauka lafiya nace gani ma a gidan su anty Basira tare da ita zaune muna hira na mika mata wayan suka gaisa kafin ta miko min.

Tun wanan lokacin dana fito da wayata naga irin kallon da sukai min yasa nasha jinin jikina da lamarinsu can na kalleta nace ina son inyi sallah anty .

Cikin irin yadda suke magana kamar tsawa ta dakawa wata tsawa tana yare ashe tace taje ta gyara bayine lokacin koda na shiga yin alwala din haka nayisa cikin kyakyami na fito dakinsu tace in shigo inyi sallah.

Saboda naga kayan yaya a dakin wajen gadonta yasa nagane dakin kwanansa nan nan nayi sallah har la,asar kafin na fito .

Lokacin Amira ta tashi daga barci nafito daga kofa na tsaya na kira sunan ta tayi wani irin juyowa don jin muryana da tayi a bazata.

Ta mike tabar abincin dake gabanta da sauri zuwa wajena haka kawai Allah yasa muna kaunan juna nida yarinyar hannunta naja zuwa wajen abincinta nace ta zauna taci saida kyat da taga na zauna kusa da ita ta yarda ta zauna itama ta soma cin abincin tana dan waigena.

Saiga namijin ya kawo min wani farin dafa duka a cikin plate da gutsiren kifin teku ta tsakiyan nasan taji nauyin hakan ne yasa tace kici abincin mu da manage anty Aisha haba dai ai nagode.

Idan na kalli wanan abincin sai naji bakina ya cika da miyau ya cika min baki hakana dai nake zaune ga kayana har lokacin aje a falo gefe daya kafin su gama cin abinci tana fadin bari mu gyara maki dakin da zaki zauna a ciki.

Dakuna biyu kacal nagani a gidan kuma haka suke zaune da wa yan nan katan mazan da basu da tarbiya a ido don rashin kunya zaku zauna a haka cikin gida.

Ni dai har na shiga dakin nawa inyi sallah magariba yaya bai dawo gida ba a lokacin wa iyazu billah na fada a raina dana shiga dakin don ko wani tsami da bashine irin na kaya sun hadu da sanyin dama ga kuma tsamin dauda din nan shine ya daki hancina a dakin.

Ba yadda na iya haka nayi sallah cikin kyankyami kafin na mike na dauko rigan barcina wando da riga sai zanin dana daura sama na haye gadon da katifanshi duk yayi laushi kana jin katakon gadon na sukanka har gara tsohon katifana na gida da aka cire a dakina yaran anty safiya yanzu ke amfani dashi falon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login