Showing 63001 words to 66000 words out of 110493 words

Chapter 22 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2284

gashi a wanan bukin na gidan nasu bayan shekaru mai yawa muna ta hadu dashi wajen shagalin nasu.

Niko da bakin riko irin na larabawa ban yarda ko gaisuwa ya hadani dashi ba a yanzu ma dana hangonsu dai din kaina kawar gefe daya ina cigaba wayata.

Don sam ban so hakan ba sai gashi haduwa din dasu wajen ya zamo kamar wajibi don yanzuma dai mun kara hadewa sai nayi saurin kawar da kaina gefe daya.

Fuskansa dauke da murmushi dana sansa dashi ya amsa gaisuwan da maryam din tayi masa cikin girmawa kafin yace wai wana ba yar gidan baba umar din nan bace mai yawan tsale tsale din nan ni meye ma sunan ta?

Itace Aeesha ko yace exactly sunan ta kenan kuwa ke kin girma yanzu bakya iya gaida mutane ko ?

Maryam ce ta zunguroni alaman dani yake fa na juyo mukai ido da ido dashi kafin nace ina wunin ku ?

A sake ya amsa kamar bashi ba da ada yake cikin daure fuska ga kowa don har manya gidan wasu na tsoronsa a lokacin.

Matar naji tana fadin muje mana D gasu can suna jiran mu fa sunyi gaba hakan yasa ya juya suka tafi ba tare da ya tsaya amsa min ba.

Allah maryam yau kin cuceni wanan mugun mutumin mai mugunta aini ko sunansa banso a kira a gaba don ban manta muguntansa a kaina.

Ke dane fa yanzu ai kila koshi baison a tuna masa hakan bakiga duk yayi laushi ba kamar ba yaya habib ba ko jiya da akace zasuzo naji umma na fada sam bata son wanan matar nasa bansan meyasa ba wallahi.

Ina ya aurota ne gata kamar kabila na fada ina jingina jikina a motan da muka tsaya bayansa tace naji kamar ance yar lokajace ita irin dai kabilu din nan ne dake tarewa Abuja.

Sune ai daidai dashi na fada ina dago kai nagansu a tsaye da alaman yar tasu suke saurare don tana nuno inda muke tsaye din sake kawar da kaina nayi daga kallonsu.

Nama mayar da hankalina akan waya ga baki daya na juya masu baya saida mukai sallama da Auwal ne na juyo garesu.

Ke din nan yar iskace Aeesha yarinyar can fa da alama akanki takewa iyayyenta magana amma kika sharesu kamar baki gani ba.

Nace ke bakiga uwar yadda ta nuna bata ma ganmu a wurin nan ba wa tafi da zamu kama binta gata kamar guntun doya.

Samira tace irinsu ko sai masifa ba rabu da gajerar mace guntuwar mara kiba irinsu masifa na nan garesu wallahi nace ai maganin mazan ke nan yanzu wa zaice wanan abin matarsace ?

Sai muka hango Aimana zuwan Aimana din yasa muka canza topic din zancen tazo muna da labarin an daukewa amarya sarka a cikin taro.

Kinga mu bar wajen nan don Allah ina farida da Asmaune tace suna can ni ban iyawa naga ana kokarin daga hammata yasa nafito.

Ina ganin Asmau tafito itama wuri duk ya yamutse da hayaniya nace muje mota gara mu bar wajen nan yanzu ba wanda ya musa muka shiga ina kokarin ribas muka hadu da tawagar yan gidan Rabakaya sun riko anty Fati amaryan sai kuka takeyi.

Dole naja na tsaya don dole tagabansu zamu wuce wai meke faruwa hakane maryam ta fada itama tana lekowa taganewa idonta.

Ina dan ribas a hankali ya iso wajen shi ya tsayar dani da hannu dole na sake ja natsaya yana fadin suwa kika kwasone a ciki.

Yana rike da hannun anty Fati ya tako zuwa inda nake yana fadin suwa kika dauko ya leka motar saukesu don Allah ki dauki Fati dasu mama ki fara kaisu gida kuyi hakkuri ku don Allah a kaisu ta dawo ta kwasheku wurin nan is not safe a yanzu.

Dole yasa suka sauka su suka shiga na tafi dasu amma ban yarda Asmau ta sauka ba don na fake ga bansan hanya ba idan zan dawo tace tasani dole muka tafi da tare da ita din.

Tun a hanya nake fahintar mafarin fadan yadda wata gwaggon mu ke mayar da magana anty fati har lokacin sai kuka takeyi murya duk ya dakushe mata saboda kuka.

Nikan tun a nan sai bukin ya fita raina bayan mun ajesu muka dauko su maryam da muke waya don sun sanar dani sun bar wajen muka dawo gida.

Tun a hanya na fara tunane dan camera dana ba Asmau tai muna dauka dashi ko zamu samu wani abu a cikinsa saidai ban fadawa kowa ba saida muka saukesu muka nufo gidan mu kai tsaye.

Kaya na fara ragewa a jikina kafin na saka riga ta mai dan free da nake zama gida na kara gyaro dakin na fesa kamshi na rufo na dawo falon mu tare da alwalana don magariba ya kusa a lokacin.

Har lokacin suna ta hiran abinda ya faru ina dai saurarensu tare da nazarin zancen kowa a wajen sallah da aka kira yasa Ammah fara mikewa tana fadin Allah ya kyauta da wanan abin.

Dakina nakoma nayi sallah ina wajen ina adduoi kamar yadda na saba ka kira isha,i ina idarwa har shafi da wutir Aimana tashigo muna da abinci kadan naci na haye gadona na kwata don na gaji kamar nayi wani aiki a wajen dan zuwa da dawowan da mukeyi wurin bukin kawai yasani wanan gajiyan.

Sai barci ban tashi falkawa ba sai missalin ukku na dare na tashi nayi alwala nayi sallah don haka Abbu ya saba min dayi tun ina karama idan ya tashi sai ya tayar damu lokacin mu kadaine a gidan mu ba wanan taron irin na yanzu.

Bayan na idarne na koma na kwanta sai yan tunane nake famanyi Aimana na gefena a kwance tana barci lokacin na mike na dauko wanan wayan da Asmau tayi recording din taron ina bi da kallo.

Can na hango wata mace lokacin da taro yayi taro tana bin bayan anty Fati duk inda tayi har cire sarkan da wanda ta mikawa duk Asmau ta dauka cikin rashin bata sani ba.

Murmushi nayi na kashe yar wayar ina ajiyan zuciya Aimana sai kwasan barcinta takeyi wajen hankali kwance.

Mamakin yadda a yanzu mutane suka sauya nakeyi duk kuma kan abin duniya ido na runtse ina godewa Allah don haduwana da bawan Allah nan man Bashir ba karamin rufin asiri Allah yai min ba ga hakan.

Don kawai mutum yai playing din game dakai sai ya zauna yayi ta kashema kudi irin haka kamar baisan zafin kudi ba ni wani lokaci idan ina tunane nakan ce kodai akwai wani hikima cikin wanan abin nasa a boye.

Amma kuma yadda Auwal ya nuna min shi mai alherine ko yaushe ga duk wanda ya rabeshi saidai kafin ya yarda dakai saiya auna hankalinka.

Don kawai yayi playing game sun zata muna soyayya dashine wanda ba haka ba Allah ya ciyar dani wanan alherin gareshi daga ni har iyayyena.

To wai akan waye yayi wanan abin akaina haka babu amsa har a zuciyana karshe nace koma waye ni dai gaba hakan ya kaini a yanzu tunda mun rabu lafiya bayan alherin dana samu garesa.

Saidai kalaman da muka rabu dashi tsakanin mune suke daure min kai don har yanzu na kasa warewaresu balle in fahinci zamcensa including me din nan daya fada.

Can zuciyana ta halbo min yadda Aimana ta gigoce ga abinda idonta ya gane mata a kaina don ga baki daya bata sake jiki ba tun zuwanta haka kuma mamakin shirin mu haka yanzu gida a fili a fuskanta.

Washegari saboda barcin da ban samu da dare bane yasa ban tashi da wuri ba kodana falka rana tayi wajajen sha dayan rana lokacin .

Wanka na somayi kafin na fito falo inda nake jiyo hayaniyarsu gaisawa muka fara kafin na tambayesu Aimana suke fadin dazun tace zataje ta dawo amma bata dauki kayanta ba ai samira ta fada.

Ammah fa na tambaya tafita zuwa gidan Rabakaya yin tanzanko kan abinda ya faru jiya don har yanzu cikin rikici suke yan gidan ango sunzo tunda safe wai zasuyi kara.

Banyi magana ba na juya na nufi kitchen don samun abinda zai kore min yunwar cikina don rabona da abinci tun shabiyun ranan jiya.

Ban samu komai ba sai guntun dumame na dauko na hado da kunun ayya nazauna nayi nak na kora da kunun ayya kafin nace Asmau taso ki rakani gidan Rabakaya.

Duk suka kalloni nace a,a ba komai zanyo bafa kawai zanje in tambayi wani abune wajen wata Asmau ta taso tana fadin .

Itama Ammah tun dazun taje ta zauna bata dawo ba Asmau ke fadin hakan nace idan ta dawo wani abu zatayi maki ki dai taso mu sameta a can din.

Koda muka shiga gidan ya dam da jama,a ana harkan buki dakin yan matan muka nufa muna neman anty Fati sai wata kawarta ke fadin tana can dakin ummanta tun dazun.

Dakin muka nufa saidai muna shiga kuma nayo baya saboda arban da nayi da yayyunta maza a zaune falon umma din ina kuma zaku ku shigo mana umma ta fada.

Hakan yasa muka juyo muka fara gaidasu da wuni nikan madangalin kujera na dafa kawai ina fadin ina wunin ku a cikin jam,i.

Kamar kullum wanan kallon nasa na nakasa cikin yaudararen idanuwasa yana nan wanda tun ina kankanuwa nasan shi dasu.

Wai ita wanan yar har yanzu tana kasan nan ashe uwar naji tace dashi ina zata inda yafi nan kuma yanzu habibu ai me raba Aisha da kasan nan kuma sai Allah yanzu kuma.

Umma anty fati fa na katse masu zancen da ba dadin sauraronsa nake ji ba a lokacin ko ina yake son in tafi ban sani ba.

Gata can ciki kwance kukan data sha yasata ciwon kai tadai sha magani ta kwanta tun dazun jin hakan yasa muka mike zuwa ciki ina jin matarsa na tambaya wanan fa wai ?

Yana fada mata sister din suce da harshen turanci sai naji tace but she is different know yace mata halittanace hakan dai ?

Yadda muka ganta kwance yasa na dauka barci takeyi a lokaci yasa nacewa Asmau tana barci mu tafi sai naji tace damu karaso mana Aesha idona biyu.

Hakan yasa muka dawo ina fadin anty fati ashe bakiji dadi bane kuma tace wallahi Aesha tana mikewa zaune tace kukan da nayine yasa kaina ciwo.

Dazun dai yan gidan su yusuf maza sun zo sunce abar zancen sarkan tunda ya bata maishi ita da Allah ai a daina zancen .

Amma gaskiya maishi batayi min adalci ba Aeesha sarkan nan yana da kyau matuka hjysa ce ta sayo min shi dataje saudiya amma an sace a karshe.

Kiyi hakkuri anty fati dama wasu da biyu suke zuwa wa mutum taro ai amma idan na nuna maki wani vedio zaki rufani koda yake ance abar zancen ido ta waro waje tana fadin Aeesha kinsan wani abune don Allah nace kamar haka dai amma tsaya umma tazo.

Nan ta sakawa umma kira umma din tazo da sauri sai mukaji na falon sunyi tsit nace su yayane ai baida damuwa wani abune umma din ta tambaya ?

A,a umma dama dai muna son mu san ko wacece wanan matar ne don itace ya kamata a fara tuhuma yanzu kai Nasir rufe min kofan dakin nan da sakata.

Sakata kuma umma tace don ubanka yi yadda nace hakan yasa sauran tasowa zuwa uwar dakin inda muke zaune a bakin gado a zatonsu wani abune ya faru damu.

Dan camera din na ciro na dan yi forward zuwa inda matan ta fara bin anty Fati din sai naji tace wanan ai Lami ce ko ?

Can ta fara dan yi kamar tana daukan kudi ko gyarawa anty din mayafi kafin ta ballo sarkan ta mikawa na bayanta da hannun tufafinta kawai muka gani tace hannutu.

Salati umma din ta fara kafin tace lami da hannatu aiko dazun suna cikin gidan nan kuwa wai meke faruwane umma ya habib din suka tambaya daga falo don su basu shigo daga ciki ba .

Ummace ke sanar dasu abinda ke faruwa sun jima suna nazari kafin su tsayar da yadda zasu fitowa zancen kai tsaye.

Wacece ita Lamin din wai Nasir ya tambaya nan umma ke masa bayanin wace ake kira da Lami din tace kawar hju Aginatuce kuma tana hurda da hjyn karama yanzu a cikinsu ba a san dawa ta hada kai tayi hakan ba.

Ita dai gata compound itace ta cire sarkan da taro yayi taro kamar abin tsafi saidai an kasa gane wace ta mikawa don hannunta kawai akagani a wajen.

Umma me zai hana mu kira wanan tsinanar matar mu kulle a daki saita fadi gaskiya da sauri wani yace ba zata fada ba .

Uwar yasawa kira yace umma nace kubar zancen sarkan nan zan saya mata wani abarshi don Allah kada a tayarda wani rikici kuma yaya habib ya fada daga falo cikin takaici.

Wallahi yaya ba zaka biya ga abu dai angani itace ta cire sarka babu gardama illa asan wata mikawa shine yanzu.

Suka kwasa sukai falon har anty Fati din sai yadda za ayi suke tunane daga can na mike nafito falon nace .

Ya Nasir ai gane ko waye baida wuya na farko a duba hannunta akwai zobe sai kuma wanan kayan mutum biyu keda dinki shigen hakan a wajen.

Zooming din photon nayi masu yadda zasu gane da kyau naji umma tace innalillahi hannun hjy Aginatuce wanan babu tamtama wallahi.

Ke ya fada hakan yasa kowa ya kalloshi don ba a san da wace yake ba me kike karantawane ya fada cikin tsureni da idanuwansa .

Saida na kawar da kai ina mikewa nace dashi software enginering no wander kika iya wanan kwakwafen haka yanzu ku bari a anjima idan an rage sai a samu Abba da zancen kada yace an lakawa matarshi sheri.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/24, 10:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc

LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

3️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp

Daga inda nake zaune na juya ina bayani naji yarinya ta rike min hannu tana fadin i know you na dan juyo na shafa mata kai kadan naci gaba da magana a tsanake.

Ta kara makale min jiki tana fadin wait ta sanni uwarce cikin murya irin na kabilu tace a ina ta sanni ?

Wai a cikin tv gidansu har tanawa uwar kwatance da film din hakan yasa na dawo da hankalina gareta bani ba duk wanda ke falon ma yana kallonta a lokacin ana sauraren shirmenta da uwar ke fassara muna.

Gashi sai kwantan fatan jikina takeyi ta gani ko zai fita can tace wait zan mayar da ita irin jikina nace ehh na shafo mata kai Ina karba yar wayata daga hannun yaya Fahad days gama tura recording din vedio a wayarshi.

Umma ke fadin sannu yar gidan Ammah mun gode da wanan taimakon naki garemu ba komai umma naga in ban kawo an gani ba sai anyita zargin Wanda bashi ba.

Hakanefa umma din ta sake fadin kafin anty fati itama ta mike zata biyo mu lokacin uwar take fadin Fati kada inji kinyi zancen nan da wani harsh gane ansan sarkan nan na hannusu su juya zancen nan.

Ba zanyi ba ai umma ta fada nan yar nan tasa rikici wait zata bimu uwar ta rike ta nidai na samu na fice daga dakin tare muka fito da anty fati har kofan gida ta rakamu ta kama ciki.

Amma mummy kina da kasada Asmau ta fada nace aikina ke nan dama kasada ai karatuna ya shafi hakan yanzu kinga kowa ya fita zargi ai Asmau don ko mu ba zamu fita cikin lissafin zargiba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login