Showing 105001 words to 108000 words out of 110493 words
Chapter 36 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx
ID card dina sun gani na mika masu tun a nan na fara samun matsala.
Duk inda nabi idone yasa na tsargu ina tunanen ko nayi wani shigan banzane kuma nidai nasan bujene da riga na lece a jikina sai dan gyale pink kalan fillawan lace dake jikina da wasu half cover masu kala daya da gyalen sai dan jakka karami shima pink mai sarka ba belt ba na dan rataya a kafadana.
Hakana dana shigo office din mu na samu kowa yazo lokacin don na tsaya laundry na bayar da wankin uniform dina da kayan barcina a ranan hakan yasa na dan makara.
Oga thomas yana duke yana faman aiki a computer office ya dan juyo yana amsa min ya mayar da kansa sai kuma naga ya sake juyowa da sauri ya sake kallona karo na biyu.
Kansa a kasa yace miss Aisha is that you ?
Nace yes sir na waw woo so is the uniform that hiding you before na kalli abokan aikina da suma kallon nawa sukeyi a lokacin .
Sai kawai na tsargu na samu waje na zauna ina fito da laptop dina da ranan na fara zuwa dashi office din tunda na bude gaba daya hankalinsu ya dawo kaina.
Enkechi ce farkon fadin ewwerr Ayasha na you get this laptop wanan fa bai shigo kasan ba tukun last month akai lunching dinsa.
Hankalin mr Thomos din ya dawo a kaina yana fadin unbelievable you this Aisha you hinding something for us nifa na fara tsoron ki yau ?
Tsoro kuma na fada yace duk zaman mu office din nan kusan kwana nawa sai yau din nan muka san kalar ki haka kuma kinzo muna da abin mamaki tare dake da yawa.
Nan dai akai wasa da dariya na mika masa laptop din ya shiga ya fita yana mamakin akan kyawonsa.
Tunda suka fita zuwa break nake ganin manyan mu suna shigowa suna fita office din nidai ina duke ina faman tura bayanaina a cikin computer din.
Barka da aiki hjy aka fada a bayana hakan yasa na dago ina sawa da yauwa sannu don jin maishi yayi min hausa kai tsaye a lokacin.
Idona ya sauka kan MD din wajen da sauri na tura computer din gaba kadan na mike tsaye ina sake gaidashi ya amsa tare da matsowa table din nawa yana fadin.
Ba mamaki wani nakine a waje ya saya maki wanan simple din duk da bamuyi zaton ganin wani dashi ba nan kusa sai gashi yanzu nake jin angasa a hannuki kina amfani dashi.
Kaina kasa nake fadin daga U S aka turo min shi da zanzo nan hannu yakai a hankali yana duba system din na dan lokaci ciki har baya kafin inji yace.
Gaskiya hakan yayi kyau sosai wallahi saiki maida hankali ga koyon aikin yadda ya dace zamuyi alfahiri daku sosai don matan mu na arewa basa son yin course din nan amma ke gashi naga kin dauki abinda muhinmanci sosai Allah ya bada sa,a.
Nagode Sir na fada yace ba matsala daga kano kike ko na amsa da ehh sir amma kamar ke ba ,,,,,,sai kuma yayi shiru ya dora da fadin anyway indan dai da matsala zaki iya samuna you are wellcome anytime .
Nagode na kara fada yayin da lokacin mr Thomos ya dawo office din sai kuma ya tsaya wajenshi suna magana dashi kafin ya fice daga office din.
Ajiyan zuciya na sauke ina kokarin kaiwa zaune naji mr Thomas din yace kiyi hakkuri fa bawai tsegumi na kai ba na fada masune ko za a samo muna irinsa a nan.
Ba komai sir na fada naci gaba da abinda nakeyi sauran suka dawo mukaci gaba da abinda mukeyi akwai wata Meenat dake yawan shigowa office din mu daukan bayanai.
Wata mai jiji da kai haka irin wayayyu din nan dai itace ta shigo a karshe take tambaya wacece kake zancenta dazun ?
Ya nunani can karshe ta dan kalleni tace wanan ne new product din da yake fada kafin in bata amsa khalid yace no gashi nan ta aje ya zagayo yana nuna mata ta jima tana kallo harda dauka hoto tayi tagama kaudinta ta fita.
Lokacin sallah nayi na mike na fita zuwa mosque din mu inda na samu ba kowa a sashen matan hakan ya bani daman aje kayana don inyi alwala .
Ina duke ina alwala suka shigo su biyu daidai ina shafan kai naji wace suke tare mai dan shekaru tace tubarkhalla masha Allah.
Hakan yasa na juyo ina kallonsu ni dai suke kallo a lokacin ban fasa alwala naba na gama na mike don zuwa sallah lokacin suka shiga yin alwala su kuma.
Hijjab dina na sallah na fitar na tayar da sallah koda na sallame na dan bude jaka na dauko mai ina shafawa kafana karya bushe.
Naji wanan matar data idar ta kura min ido tace don Allah yar uwa in tambaye ki yasa nace tambaya mana anty a cikin hausa na bata amsa.
Ke yar inace wai nace kano ikon Allah har da iyayyenki a kano suke nace ehh baba dan kano ne tace gaskiya da bake kika fada min ba sai ince ke balaraniyace.
Kai na girgizs nayi murmushi ta sake fadin kunne wa yanda sukazo traning ko nace eeh ina kokarin mikewa don ina son biyawa in sai wani abinci nashiga dashi.
To yar uwa baki fada muna sunanki ba zaki wuce nace Aisha amma da Aeesha ake kirana a gida nagode kada in makara na fada suka bini da kallo.
Restaurant muka haduwa da Enkechi tare l
muka jera muka koma department din mu muna hira take fada min tana son dress din mu na hausawa amma matsalan bata iya sakawa ta dade dashi a jiki.
Amma baida matsala kafinta koma zatayi kokari ta dinka ko kala biyune ta gwada ta gani take fadin kayan sunyi min kyau sosai wallahi .
Nadago ina mata godiya naga wasu tawagan manyan mu zsu shiga office din gagawa da sauri take fadin inama ace tana cikinsu nace ta roki Allah dai ya bamu sa,an karatub mu a yanzu.
Mr Thomas baya office din hakan ya bamu daman zama yin hira na bude abincin na bada baya zakice bafulatan dajine yadda na juya daga garesu ina cin abincin.
Ya jima baidawo da ya dawo kuma ya sallamemu take fadin in rakata kasuwa don Allah nima ina son zuwa don haka muka garzaya zuwa kasuwan .
Abubuwa da dama nagani da nakeso saidai ba halin saya a yanzu don kona saya din zasu zamo min wahala don kayana ma a gidan yaya a rabe suke gefe daya.
Don haka banyi sha,awan sayo wani abu don kaina ba nadai sayowa Amira kayan masu kyau da teddy na yara.
Sai kayan kamshin gida dana sayo tare da kayansu fresh tomatoes daya ban shawa har nama da ice fish na kwaso donshi taje saya a wuse market.
Saboda ita haya aka kama mata a wani side nan cikin girki mota daya muka shiga muka fara sauketa don motan gaba daya muka dauka sai ni yakai har kofa a karshe.
Falo na samu madam Basir zaune da kawarta suna hira nashigo da sallamana Amira na ganina tasheko da gudu ta rungumeni .
Gaidasu nayi da gida kadin na nufi kitchen dinsu na aje kayan dana sayo masu din don ganin bakuwar muka shige daki nida Amira da dayan ledan.
Ina jin matar na tambayanta a cikin hausa da wanan fa tace sister din mijinane tazo pratical daga kano take zaune damu.
Uwarsu dayane tace a,a not the same father ma kawai dai a family din take humm amma kina da sakaci maman Amira shine kika yarda ta zauna maki gida ?
Meye halan iya abinda naji kenan muka shiga dakin ina fadi a raina wai gida gidan kazanta shine har ake tambaya ta yarda na zauna kome ?
Har na sauya kaya Amira na dakin tare dani don kafin na dawo tayi barci idan zan fita kuma lokacin bata tashi a barci ba.
Banyi na shiga na wanke kafin na fara sharan gidan lokacin matar tayi sallama ta fita sun dade a waje tare da matar kafin ta dawo cikin gidan.
Sai lokacin naba Amira kayan dana sayo mata ita kuma nace madam yau kasuwa muka shiga nina rasa abinda zan sayo maki shina na kwaso maki wanan.
Saiga Amira din da nata tana nuna mata tace wai,wai,wai ashe yau ba barci a gidan nan abinda takeso ke nan daddy ta ya hana a sayo mata.
Ta karbi ledan yarinyar tana budewa taga riga maikyau ta bude na juya naci gaba da aikina saida nayiwa gidan fes kafin yan uwanta su dawo na saka kamshi ko ina.
Sai can naji tana fadin ashe ke ba karamin sayaya kiyo muna ba to angode ta fada ta kara shigewa kitchen din nagama nayi alwalana kafinsu dawo su bata gidan nagama nashige daki ban kara fitowa ba kuma sai washegari.
ZAINAB IDRIS MAKAWAJA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
4️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ONLINE TRAINING!*
*ONLINE TRAINING!!*
*ONLINE TRAINING!!!*
*Are you looking to level up your game with traditional spa?*
Whether you are married woman, bride to be or some one who loves to master the art of *traditional spa*, *natural aphrodisiac* and *Traditional incense* asalin kamshin shuwa look no further in this article *@sady_aromamist_and_spa* have got you covered
Imagine you know all the ingredients used on your skin to moisturise, nurture and revitalise it, *intimate confidence* and a good long-lasting Traditional scent.
Transform your space
Transform your skin and have that intimacy confidence. Join our online training
Wa.me/9048763046
learn the connection between *skin care,* *Traditional incense* irin kamshin nan mai kama jiki and *natural aphrodisiac* masu matukar kyau with zero side effects 😍
Sign up now to join the waitlist(https://chat.whatsapp.com/EDJan6LcDjGDrh6geC0Bk5)
Early birds 7500
Actual price 15k
Follow our IG handle for free recipes @sady_aromamist_and_spa
Start Transforming your body
Ya kasance jumma,a don haka na saka farar abaya a jikina normaly hakan dabi,antace ko a gida saka fararen tufafi a jikina ranan jumma,a don karrama ranan ga musulmi.
Wanan kuma ya samo asaline daga Abbu da naga yana yawan fada idan har jumma,a tazo ba a tsabtace masa fararen tufafinsa da zai saka ya fita ba saina maida hakan dabi,ata nima.
Abaya din farace sol daga bayanta sai ta gabatane aikai mata kwaliya har zuwa kasanta da hannayenta da silver din zare aka kuma dagwara mata wasu yan filawowi na farin kyalen rigan ta gaba zuwa dan kasanta kadan.
Kayan aikina na dauko bayan na gyara kayana tsab har dakin don da yarinyar taga dana tashi abinda nakeyi ke nan itama saita fara tayani gyaran daki da gidan kafinsu fita.
Sai dakin namu da muke kwana ya danyi space a yanzu ga kamshi ko yaushe a cikinsa ni dai banace na taba ganin wani a cikin su yana sallah ba gaskiya tun zuwana garin.
Ahakan yasa na kara taka tsantsan da kayana dama kaina dasu tunda hakan ya nuna ba alkibilan mu daya dasu ba ke nan harko ita uwar gaiyar Basira bazance tun zuwana na risketa tana ibada ba gaskiya.
Na fito cikin shirina suna zaune a falo da yan uwan nan nata magana sukeyi a cikin yare ganin na girshesu yasa nace a anty basira ashe kin tashi ko ina kwana ?
Aisha har an fito na amsa da ehh ya kwanan Amira da yayan mu tace lafiya a takaice gidansu nazo na sameta da yan uwanta don haka na kallo sauran nace ina kwanan ku cikin jam,i garesu baki daya.
Suka amsa min nikan nasa kai na fita abinda ba komai a zuciyana lokacin game dasu saidana fitane dayan namijin yace.
Sister ke kinga wani abin daya nuna tana tare da mijinkine a yanzu tunda gata dai ba ruwanta da kowa har shi banga ta damu da zuwa wajenshi ba ai.
Lukas nima nayi wanan tunanen kan hakan amma kuma madan Ladi tace dole saina saka ido sosai a kanta inson samune kuma in mayi sanadin barinta gidan nan kawai zaifi.
Damani gaskiya ba wai son yan kano din nan nakeyi ba tunda gulma ke kawosu itama wanan abinda yasa na yarda don akwai mutunci a tsakanin mune yasa hakan aina fada maku.
Jiya duk abin nan da kuka gani itace ta sayo muna wai tashiga kasuwa da kawarta ta gani ta sayo muna shi muyi amfani Amira kuma tayo mata sayayya dama mutumiyar tace.
Sister nifa banga abin damuwa ba a nan tunda dan lokaci zatayi ta koma gida ba wai zama zatayi nan ba dindindin damu why not dai ki kara sa ido ki gani a tafiyan ta.
Macen da komai bai hadani da ita tace a,a,a tabar gidan nan kawai mace mai kyau a waje hatsarine gaskiya ga brother da son mata balle wanan yadda take din nan.
A sanyayye wace muke kwana da ita tace eyya sister sai naga kamar kunyi mata fahinta ba daidai ba bata komai sai karatu da duban computer dinta ko yaushe.
Ban taba jin tana waya koda wata mace ba balle namiji tunda ten tayi barci suka kallota don abinda ta fada dayan tace kin sani ko yana binta can wajen aikin nasu ta dawo tana pretending basu hadu ba.
Saida karamin namiji ya mike kafin yace wanan duk shirmene don Allah me wanan zata tsaya yi da mijinki yarinyar dake kyamar kowa bata da lokacin wanan ki dai bari ku rabu lafiya da ita is not good mutum bai maka komai ba tana kokarin kyautata maku kuma ku tsaneta.
Dama kai haka kake ai don ka ganta haka kadai san ba ajinka bace kaje kaji da yan matanka masu warin gwajo can ita wanan dayan mai suna Bidi ta fada.
Na isa wurin aikina ina sauka taxi motan wanan meenat din tazo ta shige ni tayi min horn hakan yasa na juya tayi min hannu na sake juyawa ina bawa mai taxi kudinsa kuma.
Saiga wani mota mai kyau zai shiga ya danyi gaba kuma sai naga ya tsaya kadan bayan na tsalako na sameshi har zan wuce ya sauke glass yana fadin.
A,ya akayi yau kika shigo taxi ko dama da ita kike zuwa shigo na karasa dake ciki jin hakan yasa na dan waiga don ban dauka dani meshi yake magana ba.
MD din nan namu nagani ya sauke glass din motan yake min magana a lokacin kasan cewa ranan jumma,ace ya sawo shedashi mai kyau sai sheki takeyi ga kamshi na tashi har inda nake daga cikin motar nasa.
Sorry sir ina kwana na fada tare da dan tsayawa nake fadin aiba nisa nagode zan karasa da kafa ma .
No no shigo don Allah ko kina tsoro kada in sace kine ne ya fada a wajen yasa na danyi murmushi na zagaya na shiga gaban motan.
Tare da gaidashi da kwana ya amsa min yana fadin lafiya wai dama da taxi kike zuwa ne ko yaune nace ehh sir drop nake dauka zuwa nan.
Naji yace kai daga wani unguwa kenan fa ?
Na amsa da erea ten sir
Yace ohh Garki ke nan ko na amsa da ehh sir naji yace ayya sorry amma ke ba yar nan bace ?
Daga kano nazo sir na bashi amsa a gundure don tambayan yayi min yawa yace No wander you look different sai naji yayi shiru koya kula da irin hade fuskan da nayi a lokacin duk daba kallona yakeyi ba shima.
Inda senior staff suke parker motarsu ya faka nayi masa godiya na fita zuwa hanyar da zai kaini office din mu.
No ga hanya kibi mana ya fada kuma don haka a ranan ta kofan manya na shiga haraban ma,aikatan zuwa office din mu.
Na samu senior staff din mu bai shigo ba tukun sai mutum biyu a office din namu na gaisa dasu na wuce wurin zamana don kowa yasan inda wajen zamansa yake.
Banyi sanyi a gwiwa ba na fara