Showing 108001 words to 110493 words out of 110493 words

Chapter 37 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2285

jona system din aikina don binciken da nakeson yi kafin ogan mu ya iso sam bansan zan iya ba sai gashi da gwaji ina bin yadda mam bash ya taba fada min har na shiga wani na,uran wata kasa ina bincike akai.

Inda na shagala sosai da abinda nakeyi har ogan namu ya shigo office din ba tare dana sani ba hakan yasa dayaga na shagala ya kewayo zuwa inda nake din a duke.

Sai ji nayi an duka a bayana ya duko yana duba binken da nakeyi din a computer yabi da kallo kafin ya zaro ido yana kiran yan uwanna da sauri suka karaso wajen sit din nawa.

How do you do these yake tambayana a cikin mamaki na dan tsorace na fara inda inda ina masa bayani sai kuma nayi nayi shiru ya tsurawa seching din nawa ido na dan lokaci kafin ya furzo iska daga bakinsa.

Juyawa yayi ba tare da ya furta komai ba akaina yace kowa ya koma wajen zamansa kuma yanayin yadda ya zauna yasa na shiga tsarguwan kaina har na tashi naje gunshi ina fadin sir nayi wani abinda ba daidai bane ?

Yake fadin yayi mamakin da yar traning ta iya kai hakan a bincike ba tare da jin komai ba wanan matakine da wasu manyansu suke amfani dashi na nuna don kosu basu san yadda zasu zakulo wanan hanyan ba a yanzu don,,,,,,,,,

Shiru yayi yana fadin quit sure you are braved as you know these method now don sai wanda suka samu training din hakan a turaine suka san yadda ake wanan abin.

Have you been there before ?

No nace da sauri yace a,a abin yana da mamaki fa ace ke tun a yanzu kinsan wanan din ba matsala ki koma ki zauna ya fada tare da nuna mun wajen zaman nawa.

Nabar computer yana loding dama karan da yakeyi kafin inkai na nuna bukata ya shiga yasa ya taso da sauri zuwaga computer nawa har ya rigani isa wajen .

Saida ya gama dubawa ya juyo yana fadin miss how do you manage to do this serching please ya tsureni da idanuwan shi cikin dan daburcewa na bashi amsa da i just try it now.

Yadda ya kalloni naga alaman kamar bai yarda ba nidai na share kawai nayi tsuru tsuru da idanuna kafin ya gama binciken shi ya mike da sauri ya fice daga office din.

Zama nayi cikin karfin hali inda abokan aikina suka taru a kaina da tambaya na share kowa a wajen ba kawai saiga ogan mu ya shigo da manyan officers din mu ba.

Sun taru suna ta magana kafin a dauki computer nawa gaba daya su fice dashi dama na ma,aikatane abinda na sani kawai shine yau najawa kaina sabuwar matsala kuma Allah kadai zai fitar dani wanan kuma .

Shiru shiru ina jiran inji anzo an fitar dani sai naji shiru wanan yasa na dan samu sauki a zuciyana har time din zuwa mosque yayi musulmai suka fice zuwa ibada ya rage wa yanda basa sallah a wajen sai mu mata sai kuma wa yanda basu damu da ibada ba sosai tsirarunsu a ma,aikatan .

Ogan office din mune ya tsure ni da tambaya ban yarda na fadi komai ba duk tsoratanin da yakeyi bance kala ba na kafe da gwadawa nayi kawai.

A haka har muka tashi daga wajen aikin lokacin ina ji kamar na gudu in koma kano in fasa karatun ga baki daya don halin dana shiga ciki.

Ashe bai kare min ba don ko zan samu wani a gidan yaya kuma dan kayan makulashe na soyowa Amira dake murna idan ta ganni.

Ina jin nauyi da kunyan komawa ban rika mata komai ba don yanayin dana shiga a office yasa nake jin kasala na sauka min a lokacin.

Da sallama na shigo gidan da muryana dake nuna gajiya a tare dani lokacin na hawowa samansu kuma da nayi a falonsu na samesu da kannenta .

Kamar kullum ina sallama Amira tasheko tana tarona na rugumeta nima ina nuna mata jin dadin ganinta a lokacin yayin da uwarta ke faman waya a cikin yare.

Tsaraban na mika mata sauran na mikawa dayan budurwa don yayiwa amira din nauyi hankalinta kuma ya koma ga chis ball din dana mika mata.

Anty Basira sannu da gida na kara furtawa a kasalance ban tsaya jin amsanta ba na nufi daki don in rage kayan jikina .

Ina shiga idona ya sauka akan kayana dana aje da alaman an taba kayan a lokacin ban damu ba tunda gidan yawane nake zaune a gwamatse dama haka na cire abayan na kai hannu in dauki zanina na samu an balla min hannun jakka gashi anyi kokarin bude wajen key din ankasa hakan.

Cikin mamaki nakai tsugunne ina dubawa saidai ban fahinci komai ba hakan na dauko zani da riga na sauya na fito falo inda suke zaune a lokacin tagama wayan ko.

Na kara gaida ita ta amsa da Aisha kin dawo nace eh nashigo kina waya tace wallayi zama nayi a saman kujera kafin nace anty na samu wani yayi kokarin balla min jakara a daki yanzu da nashiga don har an balla hannunsa ma.

Cikin mamaki tace sani jakarki kuma sai ta kalli kannen nata tana masu yare ko da banjin yarensu na gane amsan da suke bayarwa na a,a a lokacin.

Ina jin tana fada a cikin yare nace ki barshi anty amma mashi ya daina don Allah hakan ba kyau tace shine ai nake tambayansu ?

Don mu dai gidan nan ba,a taba yin irin hakan ba akan me yau zai faru dake kuma mafarin akaimu kano ana fadan nida yan uwana barayine .

Na kallota cikin mamaki kamar zance nice zan kaiku kano kowa sai kuma nayi shiru don tuno da abinda ya faru zuwan su kano buki karta dauka halinane dafawa mutane sata kuma.

Har na daure sai kuma naga ban iyawa nace idan da ba aimin ba ba zan wa wani sheri ba anty kuma na fada makine don ni bakuwarkuce kada a maimaita hakan .

Zancen wai inje kano in fada bai taso ba ki daiyiwa yan uwan naki fada kar akoma min hakan don Allah.

Da alaman taji mamakin amsan dana batane a lokacin yadda ta kalloni sai naji tace inba hakama Aisha suwa ke gidan nan iba muba da zakice wai kin samu kayanki ba daidai ba ?

Sam banji tsoronta ko shayi ba tsoro ya dade da fita raina ga duk wanda ya kawo min rainin wayau a yanzu nace idan ba lalura ba baki ganina nan ai.

Ko a kano kin sani ba gidan kowa nake shiga ba an min ba daidai ba ba zanyi magana ba ko me anty ai kamata yayi ki bincika ki kuma tsawata amma ba kice za a kaiki kano dake da yan uwanki ba kuma.

Sai naji mai karamin cikin mazan yana mata yare hakan yasa tayi shiru na kai second biyu a zaune falon saina mike na koma dakin na fara gyara.

Na gama na wanko bayi don shi nafi tsana kaf zaman gidan nasu gareni Allah ma yasa suna da ruwa ko yaushe sai hakan bai mun wuyan gyara.

Nagama na fito na gyara har falon tsab lokacin mazan sun fita sai matan dake aikin girki bayan na gamane nayi wanka tare da alwala na koma daki.

Miss Called na samu a wayana maryam ce ta kirani na dauka muna waya hakan ya shagalal dani har na manta da komai ban dai sake fitowa ba har washe gari.

Da safema na sake maimaita gyaran gidan dama waje gyara yake so don gaskiya gidan ya fara komawa daidai a yanzu.

Abinda na lura dashi ta dauki zafi dani kan zancen don koda ta fito da safe ta sameni ina wanke wanke na gaida ita da kyat ta amsa min gaisuwan.

Bayan nagama nayi wanka ina zaune daki naji muryan yaya dake gida ranan yana kirana daga falonsu na amsa na fito.

Gaidashi na fara yi ya nuna min waje in zauna na zauna ke nan sai gata ta fito ta zauna itama yace kwana biyu bamu hadu ba kina rigani fita da safe nace hakane.

Yace Aisha yaya akayi kuma keda mutumiyar taki daga zuwanki za ace har kun fara samun matsala haka meyasa jiya na dawo take fada min maganan da banji dadinsa ba why ?

Zaki dafa masu sata da ita da yan uwanta kai na dago na kalleshi cikin mamaki nace banyi zaton jin hakan ba son kamar ka dauki abinda ta fada ma shine gaskiya.

Na mayar mai da yadda mukayi sai ta tare da fadin dole ince hakan mana wake gidan nan idan ban dan da yan uwana .

Ai ko fati da tayi zama a nan tare damu gidan nan har mukai ta samu matsala bata dafa muna sata ba duk iskancita kuwa na dago kai na sake kallonta cikin mamaki taci gaba da fadin.

Haka kikazo muna da sallo iri iri gidan nan na kawo ido nasa maki Aishy tunda nasan bariki nima sai mijin ya daka mata tsawa da fadin Basira ki san abinda kike fadi kada ki manta she is my sister.

Yaci gaba da fadin wai me yasa hakane why duk wani dan uwa nawa yazo garin nan ya sauka gida sai kun samu matsala dashine Basira ?

Wanan ai ita taja mu samu matsala da ita akan me zata dafa muna sata nida yan uwana yace amma yanzu ta mayar da yadda kukayi a gabanki .

Kuma kokece kikazo kika samu abinki ba daidai ba dole zakiyi magana kamar yadda tayi yarinyar nan tana da kokarinta akan,,,,

Oh oh oh oh haka zakace min ke nan dama na gane take taken ka akan Aishy dama neaboughs sun fada min na saka ido a kanku da ira.

Tunda sun sanka da bakin son mata tunda ba uba daya ko uwa dayace ta haifeku ba zakayi halin dan akuya kaga mace haka dole fa inyi magana habib.

Munafuki nagane ka ai tunda tazo kake rawan kafa da zuwanta din wallayi kasani sarai ka gwada ka gani kaga yadda zamu kwasa dakai gidan nan har ita .

Sai naji yace basira kina da hankali kuwa da kanwar tawa zaki zargeni yau kuma ke wace irin dabbace mara hankali wai ?

Kanwar ka for where idan ka samu sister in bed ko ai nasan irin halinku idan kunga mace haka nan suka fara yiwa juna tonon asiri a tsakaninsu ba dadi .

Daga yarinyar dake jikina nayi yana kiranta da karuwan banza mara mutunci zaiyi magani ta ai bada dadewa ba.

Amira na lafe a jikina ta kankameni cikin tsoron abinda iyayyen nata keyi har sukaci suka sude ba makwabcin daya shigo gidan da sunan rabonsu fadan.

Tsam na mike tare da yarinyar zuwa dakin mu don ba zan iya ji ko ganin wanan abin ba saboda sunyi nisa gashi ban saba ganin hakan nayi ba garin mu f.

Fada da tonon asiri haka tsakanin mata da miji na tujara tana wani bugun bango fafafa da karfi kamar zata fasa bangon ginan gidan wai duk a kaina haka ke faruwa.

Wai sara akan gaba ina shiga dakin na samu waya nata ringing na dauka faridace ta kirani tana tambayana ya Abuja.

Na amsa da Abuja kalau dama kiran karafin haline tayi min naji wayan ya dauke kuma banda hankalin kiranta a lokacin don haka na aje wayan.

Ina gyarawa yarinyar kwanciya don sai faman ajiyan zuciya takeyi a jikina yadda tayi barci a kife gashi ko karyawa banyi ba ranan .

Ga wanan abin kuma da yanzu ya faru sai kuma wayan ya kara ringing da bakuwar layi nagani haka na daga don banda wanan layin ina dagawa tana jin hayaniyarsu tace wai Aishace ?

Na amsa da ehh wake magana ?

Ke Anty Fati ce fatin kuce ashe kinzo abuja shine baki nemi ba nace anty fati cikin farin ciki muka gaisa

Hello nace ta amsa da fadin Aeesha meya kaiki sauka wanan gidan ke baki san halin wanan matar bace ga muryanta ina ji dawa take fada hakane wai ?

Nace bari anty nan na kwashe komai na fada mata tace ai wallahi tunda umma ta fada min kina nan Abuja kuma gidan yaya sai ankwasa da wanan matar.

Tun shekaran jiya naso na kiraki ban samu time ba sai yau nasan kuna gida shine nakira wallahi har yanzu bamu dawo ba sai next month ina ganin zamu dawo.

Muka dan taba hira kafin mu kashe wayan nikan damuwa yayi min yawa a ranan ga amira lake dani har tayi barci a hakan cikin tsoro.

Da alama sun saba da hakan dama don su suka gaji suka raba kansu bayan ya daki banza matar bariki ke nan ko gezau ta gaji ta daina ihun don ba maceci.

Sai ince ya gadane ke nen gun mahaifinshi ko don haka akace mahaifinshi yake da uwarsu saratu daya auro shima a bariki.

Ganin Amira ta tashi yasa na shirya na fice da ita koda muka fito babu kowa a falon lokacin taxi na tare ya kaimu wani restaurant na hado muka take away din abinci har wanda zai kaini dare muka dawo a falo muka samu uwar bakinta ya kumbura saboda bugun da yai mata din.

Yarinyar na ganin uwar kuma ta nufe da sauri ta danje kuma sai gata wajena ina shiga daki muka shiga tare abincin na mika mata nata ta juya zuwa wajen uwar.

Na zauna naci nawa na kwanta daga tunanen rayuwar duniya barci ya daukeni a wajen mai nauyi da mamakin basira a raina don kalamanta sun tsaya min a rai sosai lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login