Showing 72001 words to 75000 words out of 110493 words
Chapter 25 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx
/>
Duk lokacin da irin tunanen nan yazo masa abinda yake tambayan kansa shine meye laifin irin yayan da aka haifa ta wanan tsigar da sune ke ganin ukuban hakan a karshe.
Don gashi kai tsaye yarinyar nan take fada mashi bata da asali wani irin rayuwane wanan itama mahaifiyar nata ina ta shiga ta gudu ta barta kamar uban.
Photon yayi zooming ya kura mai ido na dan lokaci kafin ya sauke wani irin zuciya acan kasan zuciyarsa ya furta Allah ya zamo gata a gareku baki daya masu irin laluran nan shikan a nasa irin tunanen baiga aibun kulla wani halakan arziki da irin yayan nan ba gaskiya.
Kamar yadda hjy mai babban daki da hjy kura suke kokarin kushe yar mutane akan asalinta duk da basu san halakan dake tsakaninshi da ita ba amma su suna daukan hakan da wata manufa wanda bashi ba.
Karshe dai haka kawai yaji kasala na sauka masa sai faman tunane yakeyi shi kadai a gida ya kasa fita.
Ranan sai ya ji gaba daya kasa fita ko ina abu daya ya tsaya mai azuciya shine zai taimakawa rayuwan yarinyar nan kota halin kaka.
Kada ta nakasa tazo ta wullakanta a banza duk yadda zaiyi alkawari ya daukarwa kansa kan hakan tun farko tun daga ranan da hjy umman su salman tayi masu sharhi akan irin yadda rayuwan hakan sukan kasance a karshe.
Balle wanan din da yaga tana da kyakyawan niya zama abin kwarai a rayuwanta don haka yayi alkwari zai taimaka mata tun daga wanan ranan sai daddy shine yasan wanan niyar nasa tun lokacin.
Bayan haka yana son ya taimaka masu ako wani bangaren rayuwa yadda iyayyen rikon nata ba zasu taba jin sun gaza da ita ba irin tunanen da yayini yanayi ke nan shi kadai a gidanshi.
Aike kan muzo gidan Rabakaya tun aika Asmau da nayi da kudinsu na amarcin su ita kuma iyayi yakai ta ga fada masu ba zan sake zuwa ba Abbu yace har dani don yawan takuran da saratu take min.
Shine hjy su Anty fati take ta min aike har wurin Ammah ayi hakkuri abarni inzo dan Allah amma naki fita saida akai sallah azahar na shirya na shiga gidan a lokacin yana dam da yan buki .
Ko kwaliyana ma abin kallone ga mutane don haka na zamo masu abin kallo dakin hjy umma muka fara shiga muka gaisheta nan take min fada da nan gidan mune saboda da saratu ba zan daina shigowa ba.
Karshe dai muka mike da wanan yar ta yaya habib data leke min tun shigowana dama suna falo ne ita da uwarta dake kwance tana ganina tazo ta rikeni muka danyi hira da ita tana fada min sunan ta da sunan makarantanta irin dai hiran yara.
Da zamu fita zuwa dakin amare kuma ta lake saita bini uwar tana riketa umma tace ki barta mana yarinya nason bin yan uwa kin riketa ?
Idan ta zauna a nan wani abu zatayi maki ai gara dai tabisu taga gari tunda Aeesha ba bakuwa bace yar gidace sam banso zuwa da ita ba yadda uwar ta kankame abinda cikin daki.
Amma maganan umma yasa na kama hannun yarinyar muka fita tare zuwa dakin amaren samira na fadin walle da bakizo da yar shigiya ba ta rike kayan ta mana waddamu da ita ?
Ni dai dariya take ban haka muka shiga dakin yana dam da yan mata sun baje suna cin taliya group group mukai sallama muka shigo.
Yauwa ga Aeesh din ina zubaida da tace bata gane Aeesha ba wai ita bata sanki ba saudat ta fada anty fati tace da ita aiba kowa yasan Aeesha ko unguwar nan saboda basu wani dade da dawowa nan ba.
Ai yar gidan yaya Habib ce ashe saudat din ta kara fada wai ya akayi uwarta ta yarda ta biyo ku wanan yar da ake rowanta kamar tafi kowa.
Sunga wace tafisu class mana wata ta fada kafin su fara min bissimillah muzo muci abinci ana faman kus kus kus a kaina duk da gamu a cikin dakin lokacin.
Yauwa Aeesha zance dinner nefa akeyi kinsan wurin special ne ba kowane zai tafi ba ga yan gida sun nace kowa na fadin shi zai tafi.
Zaune nakai ina fadin ai sunsan wanan ba tsarin mu bane gidan ango keda wanan tsarin don haka ku kyale kowa kawai idan sunje an hanasu aisa dawo kawai.
Yau akwai butar kashi saratu ta fada daga inda take zaune tana fama loda taliyan a cikinta kai kanawa akwaisu da son filawa Asmau ta fada.
Kuko dawo ko wata ta fada tace aigara dawo hatsina yana kara lafiya a jiki shiko filawa fa ko can dinner kuka tai shi za a zuba kuyi ta kwasa daga nan in kunga taliya kun rude barauniya ta shiga harka ta hade sarkokinku dana amarya duka ta nade tayi tahiyar ta kuna can kun rude kan hilawa.
Dan hausa ba haushene rabu da bassakwacen mutum duk abinda ka fada yasan mai kake nufi amsan tabawa saratu a take da take fadin akwai kaza yau.
Nan sukaita cacan baki nikan surutunsu yana hawa min kai hakan yasa na riko hannun yarinyar nan muka fito da maryam wajen gidan.
Wai bakizo da motarki bane maryam ta tambaya nake fadin haba dai nan da nan zan wani dauko mota kuma ?
Wai me Asmau nan naku ke fadane naga saratu tayi shiru nace koma me take nufi Asmau ta fita dabanci wallahi nima nan tsoronsu nake ji dukkansu biyun.
Suka kwashe min da dariya Aimana ke fadi nima nayi mamakin ganin yadda kuka shirya dasu yanzu wallahi ?
Haba dai yau da gobe basai Allah ba ana waje guda kuma yan uwa sai tayi shiru bata kara tofawa don ba zan bada kafan da zatayi tsegumin yan gidan mu dani ba.
Photo suka farayi da waya kafin nima in shiga muyi tare harma da wasu suna shigowa nayi da yarinyar nan sosai don tana lake dani ko ina sau biyu uwar na turowa ana fada mata muna tare
Can naji wanan yar na kokarin fisge hannunta daga rikon da nayi mata don kada ta bace min a cikin taro nawa ya sameni ashe babanta ta gani saida na waiga naganshi ya faka mota gidan massalaci yana zaune a ciki abinka da naka wai har yarsa ta gashi ita.
Asmau nayiwa magana ta mikata wajen uban ta rikewa yarinyar hannu ta nufi inda yake tsaye takai masa yarinyar nan yarinyar ke fada mai cewa tayi photo da sabuwar anty din can.
Nan ta dinga masa hira wai zatayi photo da uban dole yasa azo a kira mu sam ban dauka mu duka yake kira ba saina tura Asmau taje.
Sai gata ta dawo tana fadin yace muzo na nuna kaina irin na mamaki kafin nace muje din a zatona zaice wani abu ya faru da yarsu ne.
Saidai muna zuwa yake fadin tace kunyi mata photo take son nuna min sannu wazan baka so a jikinka kaga murde muna kunnuwa yanzu zaka nuna muna son yar cikinka a fili na fada a zuciyana
Yar bakin nan Asmau ke fadin da wayan mummy Aeeshace akai mata photon kawo mu gani mummy tana karba wayan a hannuna cikin zumudi.
Ba mus,su na mika mata wayan juyawa nayi na dan gusa nisa dasu kadan ina kallonsu don irin kallon da yake min na fara tsaguwa da hakan tun farin ganina dashi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Wani gida babba mai kyau duk da ginan dane amma gidan ya tsaru iya tsaruwa don da gani ba sai ka tambaya ba a zaman baya gidan na ciki jerin gidanjen da sukai tashe a garin.
Don yanayin ginan ya nuna hakan har yanzu kuma ko yanzu din ba,a canza fasalin ginan ba gidan yana da dadin kallo don komai a tsare yake amma yasha gyara da kayan alatu na zamani ginan daine yan gayu a yanzu zasu daukeshi a old mordel saidai ko yanzu din dubban mutane suna kwadayin ace nasune wanan gidan.
Sannu a hankali wani babban mota ya tsaya a kofan gidan kafin a bude mutanen cikin motar su fara fitowa a hankali.
Anty Ummi ce da yan uwanta ta kawowa kakanin nata ziyara kada ta koma ghana bata samu zuwa wajensu ba shine dalilin fitowanta ta fara zuwa wajen kanwar mahaifiyarta mami suka gaisa daga nan tace zata wuto gidan kakar tasu shine yaran mami din sukace suma zasuzo suka hade su hudu da yaranta zuwa gaida kakanin nasu sai ince wanan ahalin sunyi dace da gadon tsawon rai don uwa raye uba raye harda kakani tako wani bangare irin hakan dace ne da baiwa daga Allah.
Don ba kowa Allah keba wanan falalan haka ba wani ya taso ba uwan ba uba wani uwace kawai a raye wani ko ubane kadai a raye wani kuma rabuwan aure yashiga tsakani haka zai taso koda suna a raye ya koma kamar maraye haka dai abubuwan tsarin rayuwan sukan zo wa bawa wani lokaci.
Tosu wa yan nan ahalin har wace ta haifi iyayyensu din mata bata jima da rasuwa ba don a lokacin baifi shekara ukku data rasu ba.
Tana tsaye cikin kulawa saida kannen nata kaf suka gama sauka a motan kafin su nufi cikin gidan kai tsaye kharat ce tace ga sabbinani a zaure fa mu fara shiga.
Hakan yasa suka shigo ta kofan zauren gidan mai kama da falon mutanen da zauren babbane ga kujeru ga fankan sama data kasa agefe daya.
Ga tarin littafai na addini gefe daya duk da kujerun dake akwai a falon ga shimfida irinta alfarma mai nuna jin dadin rayuwa ga mutum inda tsohon ke kishingida ya huta ko yayi karatu saboda zama dake masa wuya a yanzu don tsufa.
Sallama sukai masa cikin girmamawa kafin ya dago yana fadin su waye yana mai kura masu ido kafin yace au yau kuce in shirya ina da baki tafe ai.
Suka kwashe da dariya kafin anty ummi din tace wai tsohon nan kana gani haka har yanzu yace ko zaki ban aron idonki in kara da nawa nina fiki gani a wajen nan suka kwashe da dariya .
Kafin sukai kasa cikin ladabi suna gaidashi yayinda suka mike kuma suka dane kujerun aka fara jero ba,a a tsakaninsu.
Mai karatu kada in kaiki nisa wa yan nan tsofin sune mahaifan iiyayyen su Man Bashir da Salma dasu khairat su Ummi.
Na fada maki a baya ds uwarsu kharat da uwar Man bashir mami ya da kanwace suma asalinsu dai yan bauchine mahaifansu amma zama ya mayar dasu yan asalin kano don kowa nasu na kano amma ruwan fulanin nan yana yawo a jinin ahalinsu har yanzu.
Ainihi karatu ya shigo da hardo garin kano saboda hazikancinshi da zati na iya yaki da sauran dabarun sarauta sai ya zama malamin cikin a masarauta a lokacin .
Yayasa mata sune su mai babban daki da hjy Umma mahaifiyar su ummi da salman dama na taba fada cikin labari inda Man bash ya nuna salman ma jikantane ta nuna mashi ai tafishi sani amma jikanta na jininta take son ganawan siri dashi alokacin.
Sun gama gaisawa dashi tasa khairat su kwaso mai tsarabansa wanda tasan abinda tsohon keso dama kayan shayine shi nasa tsaraban suka shigo mai dashi falon nasa aka zube masa.
Yana faman saka masu albarka kafin su mike zuwa cikin gida su samu Yanti kakarsu mace itama suka zube mata nata nan su taliya kayan shayi man turkey maggi da sauran kayan amfanin gida haka tazo masu dashi don ummi din mijinta mai haline gaskiya.
Nan suka baje ana zuba hira yaushe rabo kaya kaya suka dauko zancen man bash a cikin hiransu suna koro masu yadda akayi da mai babban daki dashi man bash din kafin ya tafi.
Murmushi Yanti din tayi tana fadin shi dan adam a yanzu lamarinsa sai Allah sai ya manta mafarin komai ya rufe ido akan gaskiya.
Ita harta manta da lokacin auren mu kakan ku gashi ubansu daya da mai martaba kun sani haka nida ita uwarmu daya uban mu daya.
Amma yanzu tunda na fahinci mulki ya rufewa hjy hauwa ido ni kaina da nake kawa wajenta na rage shige mata.
Don a gaban kowa saita nuna kai bakowa bane ta nemi ciwa mutum mutunci ko a auren shi Ahmad da mami ai saida rayuka sukaso baci a lokacin don haka ta budawa idonta toka taso nuna ba zai auri mami ba sai yar sarkin zariya.
Shi kuma ya nuna mami din yake so dole maza sukasa baki ta yarda akai auren da yake rabon yaran nan ne bata isa ta kaucewa kaddara ba a lokacin.
Don yau tayi hakan ban mamaki cikin lamarinta kadan ke nan daga aikinta indai hauwa kulu ce zata iya yin fiyema da hakan wallahi .
Waiko shiyasa bata son mune Yanti wallahi ban kaunar zuwa gidan sarauta sai in wata nawa banje ba sai in mami ta matsa min nakan je kuma kaje da bacin rai zaka dawo gida.
Daya daga cikin kannen man bash din ta fada sai murmushi tsohuwa yanti tayi kawai husna din tace Allah hjy nakan zo nan sau goma banje gidan hjy ba.
Takan ce wai mu masu akidar nasarane bamu da kunya ko tace bamu samu tarbiya ba a rainon mu ni abin yakan bata min rai da ita wallahi.
Hjy dai batayi tunane ba takan mata da da yanzu nice a matsayinta donni mai martaba ya nuna yana so sai mahaifin mu yace ban isa aure ba a lokacin ga hauwa nan dai su shiriya tunda ta dan tasa ita saboda ita haka ta tashi da dan kuman jiki ga mazaune da yasa ake kiranta da mai babban daki wanda mahaifanmu suka saka mata kuma sunan ya bita ashe zata zamo mai babban dakin wanda bai sani ba saiya zata don ta auri maimartabane taci sunan .
Amma haka kowa yasanta dashi dama da shi kakanku ya taso kuma sai mahaifisu ya aura minshi wanda akaiwa hakan shi zai manta mafarinsa yace sai yan sarauta jininsa zai aura mu mun gaji sarautane da Allah ya bamu mazajen yan gidan sarauta.
Koshi mahaifinku ai bata so aurenshi da mahaifiyar kuba so tayi ta aura mata wani basaraken gobir bayan ga mahaifinku da kowa yasanta dashi zan iya cewa wanan ya kara hadamu fada da ba shiri tsakanin mu har yanzu.
Don lokacin mun nuna mata mu shehi muke son yarmu ta aura ba sarauta ba shine ta dawowa ubansu da uwarku wai yaje ya aura masa din.
Hjy Yanti kice dai anyi kwamacala a wancan lokacin anyi kan khairat an Allah dai ya kyauta sam ba halinsu daya da mai martaba ba don shi yakan taka mata burki kan wasu abu da takeyi a rayuwa.
Yanzu kan ai ta hadu da Bashir indai wanan mai taurin kaine anty ummi ta fada husna tace yace ko mutuwa tayi kada a kirashi tace miskili saikazo ka kasheni ai.
Suka kwashe da dariya Yanti din tace wanan yaron wanan yaron dama take takensa nasan zai rina donshi ba mutum bane mai ra,ayin saurata gashi kuma bai rage kakansa ba tako ina ya kwasosa saidai hasken mu daya debo kawai na halitta.
Idan ita yar rabosane kome suka iya zai auri abinsa amma kan sai ankai ruwa rana da mai babban daki nasani sai ya nuna namiji yake kafin ta yarde masa.
Yanti bakiga yarinya bace wallahi yarinya mai kyau da ita balabiya asali da ganinta kema zaki san ba jinsin nan bane ita gata kuma tana da iliminta an mace karatun ne ya hadasu nata.
Za a kai kan don hjy har sheri ta lakawa yayan mu ta kira daddy ranan tana fada mai wai