Showing 102001 words to 105000 words out of 110493 words

Chapter 35 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2278

mu da suke kwana.

Sannu a hankali nagama shirina tsab ina mamaki wanan rayuwan da nagani a gida yaya habib sam ban taba tsanmani ko zaton inzo inga hakan a tare dasu ba.

Mai karatu kada kice na raina da irin arzikin su a,a wani rayuwace ta daban da bamu taso a cikinsa ba na tsunta a nan din da yake jikina da gaji a haka barci ya daukeni bayan duk na adana kayana nayiwa komai security saboda gidan dana gani a watse.

Lokacin da ya dawo nayi barci don Basira tazo ta fada min ya dawo in kuma fito inci abinci ta samu nayi barci a lokacin donshi bata tasheni ba ta barni.

Sai cikin dare yunwa ya tayar dani ba abinda zanci a lokacin na mike don inyo alwala shine naga wanan dayan yarinyar cikin yan matan dake gidan kwance a kasa tana barci a dakin itama.

Nayo alwala na dawo na tayar da sallah lokacin ta dago tana gaidani na amsa mata ta koma barcinta ina idarwa na koma saman gadon ina danna counter dina sai wajajen asuba na fara jin buruntunsu.

Wai wanka sukeyi kada su makara zuwa wajen sana,ansu ta fada min saida suka rarage na mike naje nayo alwala nazo nayi sallah asuba.

Kafin nayi shirin wanka na fito na zauna ina shiryawa don nima ranan zanyi reporting inda zanyi aikin gwajin da aka turo muyi din.

Tsab na shirya cikin irin kayan da suka sa muka dinka don zuwa ma,aikatan dashi bujena har kasa nayisa banyi guntu ba.

Sama na kawo dan hijjab baki half sunna na dora akaina maimakon hula baki da sukace muyi amfani dashi idan zamu saka kayan.

Na fita falo don in duba lokaci naji wanan yarinyar ta kirani da anty na juyo ta tausa murya tana fadin na adana komai nawa ko ?

Nace ehh sai naga ta gyada kan ta alaman to shike nan har zan juya na sake jin tace dani in rufesu insa sheda koda an taba zan gane .

Wa zai taba na tambayeta tace indaiyi yadda tace min din don tsaro ina kallo ta dauki wanan zanin dana cire na dan baza a kofa shi ta dauko ta yafa min saman kayan nawa nace mata nagode.

Can aka kwala mata kira muryan Basira ce ta amsa a tsoroce ta fita ban sake jin duriyan su ba kuma wai ashe sun wuce kasuwa ke nan wajen neman kudi.

Allah ya kawomu nace na yunkura tare da saba jakkata da wanda na saka na,urorina a ciki na goya sai gata tace yayana ya fito inzo mu gaisa dashi.

Shikam tsab na gansa yana zaune yana shan shayi shida yarsa Amira nayi sallama ya dago yana fadin a Aisha harkin tashi ashe ko yaune zaku fara fita din ?

Nace ina kwana yaya saida ya nuna min wajen zama a gefen shi ya amsa min yace ni baba ya kirani yana min bayanin da bangane ba ?

A ina zakuyi aikin naku ya tambaya nafada mashi sunan wajen da sauri naga ya dago kai ya kalleni kafin yace amma kina da sa,a gaskiya.

Ko wanine yayi maki hanyar zuwa nan din nace a,a daga school din mu daine suka turomu nan kai tsaye yace gaskiya daku dasu kunyi sa,a kwarai da gaske don ba waje bane da ranke ranke ke zuwa balle ku yan koyon aikin .

Yanzu abinda za ayi ki karya sai in saukeki idan zan fita don kusan hanyan mu dayane dake saidai akwai nisa sosai amma dai ba matsala idan kikaga hanya daga yau zaki gane waje ai.

Nagode na fada ni dai naga matar tashiga daki ta kirashi ko me tace oho sai can ya fito da dan jakkarshi na zuwa wajen aiki yana fadin ok muje ko ?

Amira na jikina tana wasa na dagata zuwa kofansu ina fadin anty Basira ni zan tafi sai mun dawo ke nan ta fito tana fadin ok Aisha sai kin dawo .

Gashi bakima tsaya kin karya ba nace ba komai ai ina dariyan yake a fuskana don na fahinci akwai dan matsala da zuwana ya fara haifarwa a tsakanin su yazu yanzu.

Amira ta saka kuka wai zata bini nace tayi hakkuri na bude yar jakata na mika mata 1k ta karba tana murna ta juya zuwa wajen uwarta

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[9/2, 8:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc

LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

3️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp

Motan shigarsa gata dai mai tsadace gashi daka ganshi kaga hutu a wajensa amma kuma idan kaga mazauninsu saika raina mashi.

Yana gaba ina bishi a baya muka sauko zuwa kasa wajen da suke parker motocinsu wa yanda ke layin inda ya tsaya magana da wani makwabcinsa .

Na karaso ina kokarin bude baya in zauna ya juyo yana fadin inzo gaba in zauna hakan yasa na zagaya zuwa kofan gefen driver ina kokarin budewa.

Kamar ance in daga kai in kallli benen nasu Basira ce a tsaye tayi kicin kicin da fuska gabana naji ya fadi hakana cikin daurewa na bude motan nashiga shima ya shigo ya tayar da motan muka tafi.

Saida muka kusa fita daga unguwar yake fadin kingan mu a yadda baki tsamani ba ko Aisha ?

Jin hakan yasa na dan juyo na dubeshi ya mika hannu yana bude carvenet din mota ya dauko wani abu yana fadin sam mutumiyar taki bata da haline .

Yanzu haka ina gina a cikin garin nan amma ban taba barin ta sani ba kowa bai sani ba inbake yau da nake fadawa ba.

Don da zaran ta sani yanzune masifa zai tashi zatace me zamuyi da gida wai saidai inje garinsu in gina a zuba yan haya a ciki .

Jin abinda ya fada yasa na dan kallosa yace yes kinsan waisu haka suke saidai miji yaje can garinsu ya gina gida kafin yayiwa kansa komai.

Shine yanzu dana gane hakan nake wanan ginan a asirce ba tare dana bari tasani ba haka kona gama badasu zan zauna a ciki ba saboda kamar nabasu damane ita da yan uwanta wa yan nan da kike gani da sunfi haka yawa a gidan nan suda kansu suka rage yawa daga baya.

To balle wanan babban gidan da nakeyi a yanzu ai nace rabin garin nasu sudawo duka ke nan al,adansune haka sai daga baya nasan hakan bayan munyi aure da ita.

Aure nake son in kara in tare da amaryan a sabon gidab ita in barta nan don basira bata da dadi wallahi da kike ganinta nan halinta baida kyau wallahi.

Murmushi na danyi kamar na dole kafin ince sai hakkuri yaya tunda ga iyali a tsakanin ku an fara samu naji yaja tsuki kafin ya kawar da zancen yana min bayanin kan garin har muka kai ma,aikatan mu din ya saukeni ya ciro dubu biyu ya ban nace ya barshi.

Yace kin rainane Aisha don me zan baki abu kiki karba ko baki san zumuncin tsakanin mu bane wai ?

Abinda ya fada yasa na mika hamnu na karba ina godiya ya tafi bayan ya tambayeni zan gane gida wajeb komawa ko na amsa da insha Allah.

Da addua na karasa get din donshi bai shigo ba a waje ya ajeni na dago kai ina kallon dogon ginan dake gabana din kafin na daga kafata zuwa cikin haraban wajen .

Tun a get nasan nazo inda security suke saboda binciken kwaf da akewa mutum a wajen har na tashin hankali a haka nasamu na shiga har ciki duk ko da uban yunwan dake damuna tun safiyan jiya da zan bar kano Ammah ta ban abinci ban sake cin wani abu a cikina ba kuma.

Inje nan inje nan kafin in samu su bani accepted letter dinsu na sun yarda dani lokacin a wajen haka na wuni ina sintiri a wajen har nagama zuwa five na samu kaina.

Sai lokacin nake tunanen neman abinda zanciwa cikina na fito daga wajen wajen ina dan waige waige can na hango inda aka tubuta gidan cin abinci na nufi wajen.

Leda biyu nayi oda tare da abinsha na fito na tare drop zuwa unguwarsu yaya din kai tsaye duk da ya tsula min kudi ban damu ba ganin ni kadace a motar na bude abincin naci tun a mota na kora da drinks na danji na koma daidai.

Na sallami mai mota na hayo saman su saukin abindai na fada maki a hawa na biyu suke don benen mai hawa biyarne .

A kofan na tsaya na danna bell din kamar yadda naga tayi jiya wajen dannawa ukku ba a bude min ba sai can ina tsaye ina mamaki naji ana budewa daga ciki.

Itace ta bude tayi kicin kicin da fuska take fadin kin dawo nace eh sannu da gida ta juya tana amsa min nidai nabi bayanta zuwa cikin gidan nasu mai tsamin tsiya.

Mace ba gyara ba kamshi sai wani gahi da bashi na dauda daya hade da warin sanyi yana bada wani irin odo mara dadin shaka ahancin mutum.

Tunda naga yanayinta na canjin fuska nima ban tsaya ba na nufi dakin da aka saukeni a ciki yana ya mutse yadda muka barshi kafin mu fita.

Kayan jikina na debe naje bayi don inyi alwala aida sauri na like hancina donga abu cikin poh din nasan amira tayi ba a zubar ba hakama cikin masai din wani ya kewaya baiyi flushing ba saida na tsaya na tsab tace bayin na samu ya dansha iska bayan na fesa turare nayi alwalan na fito.

Na samu na sauke nayin sallah dake kaina ina jin har kuka nayi a ranan don takaici kaga mutum tsab a waje kaje gidansa ka raina masa wanan wace irin tayuwace haka wai ?

Ka zantan nata yayi yawa wanan shine tsabtan tsula majina a tsakar miya taje can tana muna kaudi da jin kyankyamin karya ashe gidanta ko ruwansa baka iya sha ?

Abincin ma dana sayo don inci da dare na kasa cinsa saiga wanan yarinyar da dan tuwon garin kwaki a dan leda da dan miya ta kawo min lokacin ina shirin kwanciya nace na koshi naci abinci wajen aikin mu dazun nagode.

Saida ta dawo na mika mata dayan take away din da nakasa ci tana ta murna tana min godiya nace ba komai ina jinta data dawo kwanciya ta bude taci.

Hakana kwana ko ranan kamar jiya cikin matsuwa gani Allah ya dora min kyankyami da saurin jin kazantan abu sai ga kuma zama ya kowoni nan cikin wanan irin rayuwa.

Washegari kan ina idar da sallah don a ranan na riga kowa tashi a gidan nayi alwala nayi wanka na fito na jira lokacin sallah nayi sallah asuba na fito na fara da kitchen dinsu.

Ai kamar zanyi amai duk abinda yai hunhuna na tara matashi a wuri daya bandai zubar ba na wanke komai na gyaro kitchen din tsab.

Zuwa lokacin mazan nan sun fita haka na gyara falon kafin na koma na kara gyara bayin na daureye jiki bakwai duk na shirya cikin uniform dina.

Na gyara kayana tsab kamar yadda wanan yarinyar tace dani inyi jiya haka na hada komai waje guda na fito muka hade da ita muka gaisa nace zan tafi.

Take fadin zan gane wajen ko da tace idan ta shirya saita saukeni ai nace a,a ai zan gane nagode na fice nima don yan uwan nata duk sun fice suma lokacin.

Yau kan bansha wahala ba wajen shiga kamar jiya don sun shedani ashe wanda basu san fuskanshi suke tsaurarawa bincike haka ?

Already nasan inda zanyi aiki don haka na nufi can kai tsaye a matsayina na yar koyo dole zan zauna kusa da wani ina kula da abinda yakeyi .

Don haka da wani ibo aka hadani aiki mu hudu ke karkashin kulawanshi muna training din banda fuskana baza kiga jikina ba ko fuskan ina saka face mask bazakice ga irina ba.

Ashe kamar yan banki muke akwai kwanakin da ba a saka uniform irin thursday friday kayan gida kowa ke sakawa a ranakun.

Ya kara muna bayani sosai da aikin mu baison wasa aikine dake son natsuwa da maida hankali don gudun samun kuskure akwai wata data zo daga Lagos da ake kira da Enkechi sai maza biyu mu yan arewa biyu suma su biyu.

Haka kuma duk friday zamu dinga kai bayanin abinda muka koya yana dubawa hakan yasa muka kara mayar da hankali ya nuna muna wajen sallah mu musulmai da wajen cin abinci.

Hakan naji dadi sosai don ko ba komai zan rage shiga wanan bayin na gidan yaya habib mai kazantar tsiya zanyi azahar dina da la,asar duk anan ke nan .

Abinci kuma zan iya karyawa a nan din kuma inci na rana haka inyi take away zuwa gida wani lokacin .

Don gaskiya hankalina gaba daya ya tashi da lamarin hidan nan kazantar a yanzu yafi tayar min da hankali bisa ga komai a gidan.

Don haka bayan mun tashi daga office na taka zuwa wani shago na sayi su Izzal dettol room fresh na tafi dasu gida.

Koda na koma gidan tun kan in karaso gida irin kidan na yan coci din nan kona yarensu ne shike tashi a falon a lokacin .

Don har kasa kana jin karan sautin kamar gidan kafirai ko wasu dai can inda ba kwabo din haka dai irin ba,a damu da addini din nan ba.

Nasa mu a lokacin duk sun dawo gida a ranan sai shi yayane kadai bai dawo ba daki na shiga ko kallon su banyi ba na aje ledan dana dawo dashi din na fito .

A kofan dakin Basira din na tsaya ina mata sannu da gida sai can ta amsa da Aisha kin dawo yau kin dan dade fa nace to indai ba kin bata bane ?

Murmushi nayi nake fadin aiban bata anty drop nake dauka daga can zuwa nan gidan tace what drop ke daya nace yafi sai a kaika direct baka bata koda safe shina dauka zuwa office din.

Nan na barsu suna yare da yan uwanta nikan nashiga na tayar da sallah don tun ina waje aikai kiran sallah shiyasa na shigo da mamaki jin kidan dake tashi a gidan lokacin.

Har yakai ina zargin anya ko suna sallah don duk dan musulmi yana girmama nauyin sallah idan lokacinsa yayi.

Ni dai ban fito ba wanan uniform din nake tunanen yadda zan wanke a lokacin kuma na godewa maryam data ban shawaran na dinka biyu mana har muna mata dariya.

Sai hakan zai mun amfani naga wasu masu loundry kafin akai saina yanke shawaran indinga kai wankina kawai a can baki alaikum zaifi min sauki don ba inda zance in wanke in shanya ba ataba min shi ba a gidan haka kuma gugan su ma aiki zai zamo min.

Kafin in kwanta saidana jawo computer dina nayi aiki a cikinsa da komai na gyara inda nake da kuskure banson inzo ranan friday ina inda inda gaban mutane.

Lokacin basira ta lekoni tana fadin dazun naga an gyara muna kitchen fes akace kece kikayi aikin nace eeh kinsan mun saba da aiki a gida tace hakane .

Nama kawai naci sai drinks dana sha na ajewa budurwan da bansan sunanta ba har lokacin sauran abincin na kwanta.

Washe garima dai kamar jiyan na riga kowa tashi na wanken bayin da Izzal na kowa dettol na zuba sanan nayi wanka tare da alwala na fito.

Ranan ma na danyi masu shara don kitchen din baiyi wani kazanta sosai ba na fito na shirya zuwa wajen aiki abina basira din ma bata ko fito ba a lokacin balle mijinta.

Ranan alhamis daine koda naje security din ma,aikan sukace wai sai na kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login