Showing 36001 words to 39000 words out of 110493 words

Chapter 13 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2280

ta daina shigowa gidan nan .

Menene matsalanki da Aeesha bayan iyayyenta basu raina muna ba Aimana, fada sosai tayi mata ta fito zuwa dakinta.

Hankalina bai tashi ba said a na fitar da kayan naga yawan uban kayan da muka kwaso shagon duk da kudin man Bashir akai wanan uban sayayyan haka dolene nasan yayi fada idan ya farga.

Amma saime da gamma saiga Auwal naming sallama har ciki ya shigo don yana ganin ya zama dan gida yanzu shi da akwati baba niki niki a hannusa da wasu tarkace ya kawo min don't gulma har daki ya shiga min dasu ranan kamar an kada kan yan gidamu sun fita wai sunje talla da uwarsu.

Tare muka fita kofan gida dashi bayan nayiwa kofana key nan yake fada min yana gida aka kirashi yazo gidansu kharat ya dauki wanan din shine yaje ya dauko.

Ai hjy Aeesha in fada making harka da masu kudi akwai dadi wallahi don nima yau a cikin farin cikin jimma,an nan nake don na samu alheri ba kadan ba gaskiya.

Tun banson sakewa dashi da farko har yakai yanzu na soma sakewa dashi don ko yanzu dana jingina da mota INA saurarenshi nace malam Auwal yace that's my name koki kirani da Awilo lo gomba.

Hakan ya dan ban dariya kafin ince dashi tsoron abubuwan dake ta faruwa nake a zuciyana Auwal ina jin tsoron idan ba wani tarko aka hada min ba don ina yar talkawana nazo na fada ciki a karshe.

Dan shiru yayi yana tunane kafin yace dani to gaskiyane amma kuma banjin hakan gaskiya ni dai abinda na dauka shine yana son ki fito kamar kowa tunda kina tare dashi ta yadda babu inda wani ko wata zai iya rains masa akanki.

Kinsan fa yaran masu kudin nan dason jan aji nidai gaskiya abinda nafi tunane ke nan amma duk da haka hakan zan saka maki ido akan komai wanan alkawari na daukar maki na hakan.

Kinsan mu a barga aka haifemu anan kuma na taso cikin gidan sarki don iyayyena anan suke rayuwa har yanzu mu daine diya maza idan mun tasa saimu koma gidan mu nagado mu zauna ciki amma har gobe ina shiga gidan duk lokacin da nake son hakan anan ma muka shaku dashi idan yazo har sabo ya shiga tsakanina dasu tun muna kanana.

Na tare da fadin ashe dai duk ku din ne yan saka masa ido kan komai yace gaskiya ko wanan aikin cancantana aka duba aka dorani a kai kuma ina jin dadin hakan wallahi.

Saboda kina da mutukar saukin kai da sanin darajan dan adam Aeesha hakan yasa nake maki fatan ku kasance a tare duk da naji yana fadan ke din kawarshine kawai na dan lokaci.

Naso ya fada min wani abu fiye da hakan amma sai yace yamma yayi zaije ya faka mota kada ya makara ko a hakan na fahinci wasu hiran da yai min din game da shi man bashir din kamar yadda suke kiransa malam bashir amma sai suka sauya da man bash ko man bashir.

Saida dare na zauna na jera komai yadda ya dace haka kuma na ware wanda nazabowa yaran gidan mu dama iyayyena na kuma fitar da tsofin kayana da nake amfani dasu wanda Abbu yake min zanbawa su samira su duk da ban sani ba ko zasu karba din.

Kayan kwalam dina kuma na hada su waje daya bayan na ware wanda zan ba iyayyena suyi amfani dashi don kome na zama banda kamarsu a duniyan nan koda kuwa yau ga uwata da ubana suna sani don dasu na bude ido nayi sabo.

Washe gari weekend ne don haka na tiki barcina don ban fito wani aikin girkin abinda zamuci ba dama Abbu ya hanani hakan nice dai naga ya kamata in fito inyi din.

Don in banyi ba haka zai fita da yunwa bai karya ba don Anty dai ko yaranta ba fitowa zasuyi ba suyi tunda ance wai insuyi bai kyau koba dadi yasa tace daga ita har yaran basu kara taba abinci da sunan yi kaji sakarai.

Nasan kawai dai don ganinane yasa hakan duk da yanzu ba kullum nake girki ba wani lokacin idan na dawo sai in zama saboda gajiya.

Duk da nasan dan sauyin rayuwan dana fara samune yake son jawo min hakan a yanzu idan ban girka ba Abbu zai fitane ya kawo min abinda zanci nida sama,Ila dashi da yakan hado da Aimana sai taking karba.

Saina fada mashi tana girka abincintane kada ya damu da rashin karban nata yaso yin fadan hakan kome ya tuna kuma yayi shiru aka tafi a hakan.

Yanzun din ma muryansane ya falkar dani daga barcin inda yake fadan rashin fitowa a girka abin karyawa a gidan shine na mike na fito da wanan ledan kayan shayin ina fadin Abbu ina kwana daga bayansa.

Nana kin taso ke nan an tashi lafiya na amsa da lafiya kalau Abbu jiya nayi barci koda ka dawo yake fadin munjimane bamu shigo ba jiya mun samu aiki sosai wallahi ya kaimu har dare.

Ledan na aje a gabansa ina fadin kayan shayine Abbu jiya muka shiga kasuwa da kanwar mutumin nan shine tayo min sayayya masu yawa ta kumace in dauki duk abinda nake sai na dauko maku kayan shayi da wasu kaya suna daki.

Baki Abbu ya bude cikin mamaki yana fadin kanwarsa ma Nana bako shi ba ta saya maki wanan kaya haka nace wallahi Abbu tare wanan drivern nasu ya dauko mu shine tace a tsaya zatayi sayaya a wani shago .

Karyan dana shatawa Abbu ke nan ya hau ya yarda dani akan ba zan masa karya ba don ya sanni farin sani kuma ban iya karya ba saidai kash Abbu bai san da na fara shiga system ba nima a yanzu.

Na sake dawowa dauke da kaya niki niki a hannuna kafin na soma bayani da tace in dauki duk abunda nakeso kada inji nauyi ko kunya Abbu shine na dauko maka wanan jallabiyar don naga kanaso wanda Nana ta aiko maka ya tsufa.

Ammah kuma turmin zani gashi gana su anty safiya da yan matanta juyawa yayi ya kalli Ammah tace to nima dai jiya ina nan nagansu da kaya niki niki ita da yaron nan dake daukanta yanzu sun shigo ashe ba karamin kaya suka dauko ba.

Anya Nanata wanan kayan sayayyan mace be kuwa bafa karamin kudi aka kashe wajan nan ba wallahi Abbu macece ta saya min idan baka yarda ba muje dakai gidansu ka tambayeta kaji.

Baba mekakewa mamaki indan ance macece ai idan mace nada kudi tafima namiji kashewa kawa abu don ta burge mutane.

Allah ya kyauta yau Nana ba don ke bace wallahi ba zan taba yarda cewa mace tabaki wanan alherin ba haka to nasanki Nana ta baki iya karya ba tun kina karamar ki wanan yasa na yarda.

Ita kuma inda niyar alheri tayi maki Allah ya saka mata da alherinsa ya biya mata bukatunta na alheri.

Muka amsa da amin kafin anty safiya ta matso tana fadin mukan waga mata Allah ya saka mata da alheri wallahi nace anty ba matan aure bacema fa dalibace itama kamarni kudin daine akwasu kawai.

Kinji arziki ba anty din ta fada nace ni ai jiya naga duniya banza da wofi haka zata dauka sai matsamin da take ki dauki duk abinda kikeso fa Aeesha kada kiji nauyi ko kunya Dana zabo was yan nan dariya ta saka min shine ta zaba min wasu riguna masu kyau da takalma da jakka.

Bayan wanan kuma nace wallahi Ammah saida muka sauketa min kamo hanya wanan driver yake fadin ai haka take da alheri ita.

A,a ashe haline yanzu naji magana Abbu ya fada nan aka sayo bread ga murnan kaya ga kuma murnan shayi da bread da za,asha ranan Allah sarki tallaka.

Sai bayan fitan Abbune na kira Asmau yar anty safiya nace su kwashi kayan dana ware masu na kara masu son ina son in kara gyara dakin mu din kafin Aimana ta dawo na shirya komai yadda nakeso.

Hakan ne ya faru kuwa dakin ya fito tsab kamar yadda na keson sa matsala dayace katifan kwarai da bandashi a dakin har yanzu.

Amma dakin ya fito min tsab dashi ba laifi ranan yan arzikin yan gidan mu yana kai yar anty safiyace Samira tayi min kitson kalaba manya masu kyau da suka fito min da fuskana shar a lokaci.

Wanan yasa muka fara shiri da samira ba kamar yadda muke kamar Annabi da kafiri ba don wayata yana hannuta suna kallon carton saida caji ya kare suka dawo min dashi.

Tsohon wayata na bata a ranan don su samu na kallo a ciki tunda gidan mu ba kayan kallo yaro kuma akwai son kallo ko can haka uwar tace tana fama dasu kan kallo.

Washegari ma tare mukai abin karyawa da ita din saidai ni ban maci ba na kwanta don in huta kafin rana lokacin ne Ammah ke masu fada tace koke fa da kika shirya da yar uwarki bakiji dadin kanji ba don't Allah ?

Amma haka kawai kin dauki bakin rai kin sakawa kanki ga year mutane dubeku yau gwanin ban sha,away daku na fada maku run farko Aeesha bata da matsala yanayintane na shiru shiru haka ita.

Zaku iya kai dare da ita batayiwa kowa magana ba gidan nan sai task to ai na fada mata a daki nima mai son ka shike damuwa akan ka dama shi sama,ila ai kinga tuni ya watsar da shirmensu dama anty sama anty kasa kuma yana samun alherinta .

Daren Sunday din muna zaune tsakar gida muna shan iska kwance nake saman shimfidan Ammah Samira tana gefena a zaune da yar wayan dana bata tana kallo.

Sai su Asmau dake bayanta sun gwagwafe sums kallo sukeyi a lokacin mukaji sallaman Aimana kamar an jefota a lokacin gashi munsan ka,idan dawowanta sai safiyan Monday idan ta shiga school daga can muyo gida.

Ranan zumudi yasa ta dawo tun lahadi a cikin dare inda ta fake da karyan ta dawo tayi assignment ne ta manta bataje dashi gida ba .

Nan ko zuwa tayi da safe ta nuna min ita din ta wuce sanina kan komai don taje ta shiryowa hakan a yanzu saita ban mamaki da safe idan zamu fita.

Nikan tunda muka gaisa na mayar da kaina saman tabarman naci gaba da charting da nakeyi ban koma ta kanta ba ta nufi ciki da jakar vaccon data shigo dashi din.

Ganin dakin a rufe yasa ta juyo tana fadin Aeesha key yana wajenkine nace Asmau ta mika mata key din ta karba ta tafi ta bude dakin.

Saida ta kadu ganin saitin akwatuna a jere gefe daya ga sauran yan tarkace dana aje a gefe daya she was shock da abinda ta gani din.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/16, 9:16 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc

LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

2️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp

Tunda muka tashi sallah ban koma na kwanta ba ina waje ina rage yan aiyukan gida kamar yadda na saba yi duk safe irin shara wanke wanke da hasawa Ammah wuta.

Sai bayan nagamane na debi ruwa nayi wankana can ban dawo daki ba bayan nafito na kara gyara wutan na nufi dakina na samu Aimana da ta koma cool tana kokarin saka wasu tufafi a jikinta a lokacin.

Jakata na jawo na dauko maina na fara shafawa katon rubane da aka hadashi da yayan itatuna na asali mai suna naturalseness .

Yana cikin manda Kharat ta zabo min bai kara haske saidai jiki ya kara sumul fata na asali ya murje ya kara baiya ga mutum shine aikinsa ga kamshin diyan iccen da aka hadashi yana tashi sosai don a take ya hade dakin lokaci guda.

Brezyer na saka sai dan short tiet da pant fuska na tsaya gyarawa lokacin Aimana dake nuna tana fushi dani na ba gyara ba dalili a yan kwanakin nan naji muryanta tana fadin Aeesha ni zan tafi.

Ashe ta fadi hakan ne a gareni don in juyo inga shiganta a lokacin sai kuma aka samu akasi ban juyo din ba na dai ce da ita ki bari Auwal yazo ya sauke mu mana.

Ta maimaita sunan Auwal nace eeh har lokacin ban juyo na kalleta ba a zatona zatayi gardama ta wuce sai gashi naga ta koma ta zauna tana wani tsabga kuma.

A tsanake nake shirina tsab already kayan da zan saka dama suna fili na ajesu wani charculet less ne dinkin remade bubu da akabi da stone shina saka na dan lakato oud na murza ga gyale da dan kwali kafin in tsaya daura dan kwalin da baso nakeyi ba amma idan na daura zakice na koyi daurine dama a wani wajen koyon daurin.

Takalma na jawo half cover da dan jakar hadasu har inda nake naji sautin ajiyan zuciyarta a kunnuwana hakan yasa na juyo lokaci guda ina kallonta.

Wani iron kaduwa da razana nagani a fuskanta lokaci guda kamar ma ta manta a zaune take lokacin data ja baya kadan tana gyara zamanta.

Karamin dan kunne na manna a kunnuwana lokaci wayata ta dauki kara nasan Auwalne ya iso ke nan nace da ita muje ko ?

Ta mike kamar zonbi muka gyaro komai muka fito saidana tsaya wajen Ammah dake bakin murhu mukai magana kafin in mata sai mun dawo muka tafi.

Zaune muka sameshi wurin Abbu suna hira shida Abbu dake zaune yana jan tasbaha a hannubsa na zagaya zuwa wajen Abbu na tsuguna ina gaidashi da kwana tare da fadin zan tafi Abbu.

Nanata har an fito to akula da kai da mutunci kinji Allah ya tsare muna ku yana magana yana kokarin ciro dan kudin daya saba aje min duk safe ya miko min.

Kaina kada nace a,a Abbu yanzu kuma in ban taimaka maka ba ba zan karbi naka ba kuma Allah ya rufa wanan asirin cikin hikimarsa ya kawo muna sauki a saukake.

Hakane tabbas Nanata Allah ya kara tsare muna ku dama ance garin kwarai baya ruwa wajen damashi balle ya sake ki dai rike Allah da Annabinsa a zuciyarki kiga fiye da hakan a rayuwanki.

Aimana dake tsaye ta daskare tana kallon motar da Auwal Awilo ya bude yana dan gogewa saida Abbu yace Aimana yaya wajen su baban naki kuma ta juyo tana sauke ajiyan zuciya tace suna gaidaku Abbu.

Muka mike kafin ma mu iso Auwal din ya nude baya inda zan zauna ya kallota yace ke zauna gaba ko kibar hjyn mu a baya ita kadai.

Hakan tayi nidai ce mai nayi Auwal sister dinace fa don Baku taba haduwa bane gidan mu daya dakin mu daya da ita itama a nan Jami,a take karatu ai.

Oh ita wanan din amma gaskiya ba za ace ba don ba hadin kifi da kaska ko daya tsuki taja tana kawar da kai sai lokacin nace indai Auwalne ki gani ai Aimana wanan sarkin barkwancin.

Ai hjyta in fada maki jiya ogana ya dawo kinsan me a cikin daren nan ya saida ya tambayeni ke wallahi duk da gajiyan daya debo kuwa.

Duo hiran da mukeyi Aimana tana can ta lula a cikin duniyan tunane ba jin mu takeyi ba a lokacin don ita abinda take gani kamar a mafakine yake zo mata.

Ita da tayo dinke dinken da zata razanani sai gashi nina zaranata a karshe bayan hakan kuma wai har mai kaini school ke gareni yanzu cikin wanan uban motan mai bala,in kyau.

To wanan da taji ina kira Auwal shine saurayin nawa ko kuma wanine can na samu mai kudin da shine mafalkinta koda tsohone ko mumuna.

Tsab ya shirya ya fito yana kallon lokaci jikin agogon fake daure a hannusa kofa yaji an turo ko bai dubaba yasan salman ne don shi kadaine wanda ke shigo masa daki haka kai tsaye ko wani lokaci yaga dama.

Saidai muryan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login