Showing 6001 words to 9000 words out of 110493 words

Chapter 3 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx

02 Nov 2025

2274

gidan kamar sabuwar mahaukaciya in na gaji in fashe da kuka inyi kuka saina gaji kuma in cigaba da magana.

Har nagaji nayi barci a wurin saida almajiri yazo yana bara na falka sauran tuwon dana zubawa Abbu ya rage shina raba biyu na kirasa nabashi ya shiga jero min addua.

Nan kofa na zauna bayan na debo ruwa a randa nake zauna na tasa abincin a gabana na kasaci da kyar nayi loma biyu naji tuwon bai wucewa hakan yasa na mike zuwa alwala nayi sallah.

Haka na wuni ko wanka banyi ba a ranan sai zuwa yamma na dan samu zuciyana ya sake har na samu na dinga yan aiyukan daya dauke min hankali.

Sauran garin tuwon daya rage na tuka muna don zai isa saboda daga bakina saina Abbu har miya na hada koda Abbu ya dawo da wasu kayan cefane yasanu ina kwasan tuwo.

Tun daga kofa yake fadin nana ikon Allah a ina kika samo kayan girki na juyo ina fadin Abbu sannu da dawowa ya amsa da yauwa har lokacin da mamaki a fuskanshi.

Ya sake maimaita min tambayan dayayi min da farko na bashi amsa da fadin Abbu sauran na jiyane daya rage na tuka muna.

Allah yayi maki albarka nana ya fada nakanji dadi idan Abbu da Ammah suna min wanan adduan don duk sukai min nakanga fa,idan wanan abin

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/23, 10:14 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

0️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Kwanan Ammah uku ta dawo cikin bacin rai hankali tashe na gane hakan ne ga yanayinta duk da hakan bai hana ta hango yar rama da nayi ba.

Keko Aeesha wanan rama fa ko bakya cin abincin ne bayan tafiyana lokaci daya duk kin zube haka meke damunki haka ko kinyi ciwone a bayana take tambaya cikin damuwa ?

Lafiyata kalau Ammah kawaidai kila kewanki ne yasani rama nake gani tafi can ja,ira saboda tafiyan kwana biyu ki zube haka ?

Kodai malam ne baya kawo abinci ki dafa maku ta tambaya cikin nuna kulawanta a gareni nace abinci kan har sai mun ture ai.

Gefenta na karasa isowa na zauna ina fadin da alama dai a gajiye kike Ammah ko in fita in nemo maki wani abu kici ta kalloni tana kako murmushin dole a fuskanta tana fadin dadina dake Aeesha tausayin da jinkai.

Yanzu har kin fahinci damuwa a fuskana to kwantar da hankalinki gajiyace kinsan hanyar namu bakyaune dashi.

Ina maman gwarzo don naga tare suka tafi ai da ita take fadin tun acan kowa ya shiga motar garinsu don tafiyan zai zama wahala idan tace sai ta biyo ta nan kuma.

Nidai ban matsa mata ba naci gaba da aiyukana da nasan nice zanyi idan tana gida har lokacin Amma din tana zaune a inda take .

Har lokacin Ammah na zaune a inda na barta cikin damu saida aikai kiran sallah la,asar na kawo mata ruwa a cikin buta a nan inda take din don tayi alwala ta samu ta mike ta zagaya ban dakin ta dawo tayi alwala ta shiga daki.

Nima shinaje nayi bayan na idarne na fito a hankali nake jin sautin kukan Ammah din yana tashi daga dakinta na dan dade tsaye a cikin damuwa kafin na yunkura na shiga dakin tana ganina tayi saurin share hawayen dake fuskanta tana saita kanta.

Don kada in gane halin da take ciki a lokacin da wayauna dole in gane ko ace ni karamace yau naga uwata tana kuka haka dole in shiga halin damuwa da tashin hankali.

Balle a shekarun da nake lokacin ya kamata in fahinci wani abu yana damun Ammah din a lokacin kuma koma meye ba karamin abu bane wanan.

Zubewa nayi akan gwiwana ina fadin Amma saboda nice kike kuka ko nice bacin ranki a yanzu na sani sani itama ta sani don tasan haka zai faru ta gudu ta barku dani kuna kumsan bakin cikin da ba laifin ku bane ya kawosa.

Wani irin kallon mamaki Amma din ke mun a lokacin don bata taba zato ko tsamanin jin makamancin hakan a bakina ba don bata taba tsamanin har zansan ba ita ta haifeni ba.

Ga irin nata hikimar fada sosai ta hauni dashi tana fadin wani zancen banzane haka nazo ina mata in tashi in bata wuri tunda bansan meke damunta ba in barta da abinda ke samun zuciyar ta.

Simi simi na mike nima ina sharab kwala zuciyana a cunkushe ji nake dama na mutu in huta da wanan bakin ciki da nake gani a rayuwata tun ina kankanuwa dani haka .

Itama Ammah din fitowa tayi tana fadin in bata aikin in wuce islamiya kada in makara hakan yasa na bi umurninta na shirya na nufi islamiya.

Mai karatu da zaki hadu da ire iren mu diyan watsin kano da ake haifowa a saudiya a watso nan gida Africa a jibgemu zakiji labarin dayafi nawa daci a kunnen ki

Don saikai da hakan ya shafa kasa abinda kake fuskanta daga gida da kuma wajen jama,an gari don kiri kira za a nuna maka rashin gata ko wani cin fuska a bainan jama,a.

Haka na nufo makaranta na samu hat an soma karatu ka,idane ga duk wanda ya makara irin hakan a hukuntashi a kwaini da tsoron bulala duk da ba wani bulala bane mai yawa biyune zuwa ukku.

Saidai nayi sa,a ina isowa malamin namu ke fadin yau ya akayi kika makara nan na marairaice ina fadin mahaifiyatace bata gari natsaya aiki na makara.

Karyana ya karbu don cewa yayi ban sanki da halin makara ba don baki da wasa shige ki shiga ciki har da dan rusunnina ina godiya na shige da sauri cikin ajin na jona tare da sauran yan uwa akaci gaba da karatu dani.

Koda muka taso na iso gida na samu har Abbu ya dawo yana waje yana yan gyare gyren wurin da suke zama karba naje yi da sauri yace barshi nana shige ciki ki huta kinji.

Ammah na tsakar gida tana kawar da kaya nayi sallama idona kyam a kanta ina karewa yanayinta kallo tare da gaida ita da kallo.

Cikin sakin fuska kamar ba ita na bari cikin wancan yanayin na damuwa ba tace Aeesha kin dawo ke nan ya hanya na amsa da lafiya Ammah .

Ki dauko ledan can ki bude akwai dan tsaraba dana sayo maki a hanya da sauri na karasa ina fadin to mama na karasa wajen ledan.

Na jawo ledan na kawo gabanta tace bude ki diba mai isan ki kije kici na duka na fara bude ledan da dan saurina ledan yalo na fara cirowa cikin murna da ganin yalo don ina son cin yalo arayuwata naci gaba da tona ledan nan ma naci karo ayya soyayya da gyada suya ruwa ko wani kuli daya na dauka sai yalo guda ukku.

Na tura ledan agaban Ammah ta dago ta kalli hannuna kafinta maida kallonta ga ledan tana fadin kara mana donki na sayo kinsan malam in yayi ya debe yalo kawai a ciki.

Nace Ammah bari inci wanan in Abbu ya dawo ya diba sai inzo in kara anjima batayi magana ba kai ta kawar daga gareni kawai Abbu bai shigo gida ba saida yazo daukan abincinsa.

Bayan ya shigo din ina jinsa yana fadin ni zancen nan ya daure min kai mutane yanzu basu da tsoron Allah a zukatansu kiri kiri ku dannewa mutane hakkinsu saboda wani dalili naku can dabana addinini ba sai zalla son kai.

Naji Ammah tace ka barsu kawai ai inba nan akwai can zasu bamu inda basu dashi hakki dai kowa yasan namune don muna da iko a acikinsa.

Ba wanan bane damuwana ba malam yadda suke muna bugun kadanya baki dayan mu damu muka kashe mahaifin mu saboda bakin cikin dakin mu har mahafin mu ya mutu ai.

Wanan ba hujja bane Amamatan koda hakan gaskiyane kuna da hakki akan dukiyasa ai abu daine son kai da rashin imani yaiwa mutane katutu a zukata yanzu.

Idan ita nana bata kusa ku baku kusane ko ance kada aba diya mata hakkinsune ?

Dama nasan komai dadewa sai irin hakan ya faru don mutane yanzu kiris suke jira su samu dama saisu fake a nan su zallunce ka don zalunci yanzu ya bar birni ya koma ga mutanen kauye garama na birni suna jin wa,azi yanzu daidaikune marasa imani kowa yana tsaye yana neman na kansa.

Nana dai komai daren dadewa muddin tana raye zata dawo kasan nan wata rana dole ko su fito da dukiyan nan kamar kada ya fadi hakan naji Ammah din na fadin.

Kaiya malam da zata dawo gida aida yanzu ta dawo din haka dai ta zabawa kanta rayuwan nisa damu naji yana fadin kaiya nakan rabaki da irin wanan zance Ammah .

Idan haka ta zabawa kanta me zakice ga wa yanda sukayi sanadiyar fitanta gida tun tana kankanuwanta ko shima duk har lokacin abinda ta zabawa kanta ke nan a rayuwa.

Sam banganin laifinta har gobe a idona don yarinyar nan ba itace ta jefa kanta cikin wanan halin ba kiyi tunanen hakan ko wani lokaci abin saidai istigifar kawai za a yi don shiya dace kawai yanzu.

Gareku iyayye masu tura diya aikatau kada kuce baku da kamishon duk halinda yarinya ta shiga ku Allah yaba amanan rikonta ba wani ba.

Yalon dake hannuna nake zumudin ci naji kamar ina taunar tsakuwane a bakina lokacin don yanayin dana shiga a lokacin.

Saboda zargina ya zamo gaskiya duk abinda Ammah kewa kuka bai wuce zancene daya shifi mahaifiya ta wadda ta kawoni duniya ba a lokacin.

Muryan Ammah ce ke fadin Aeesh me kikeyi a cikin daki daba zakizo ki dauki abincin ki ba sai yayi sanyi na fito jiki a sanyayye ina fadin na koshine Ammah.

Dagowa tayi ta kalleni kafin tace har me kikaci kafin ta rufe baki nace yalo ta tabe baki tana fadin yalo abincine banda shirmen ki nidai dauko min kwanon can ki mikawa tabawa tsaraba.

Kwanon data nuna min din na dauko nakawo gabanta ta bude ta diban masu lokacin na dauka zuwa gidan tabawa din dashi tunkan na shiga nake jiyo hayaniyarsu don haka sukesu da haniya kamar gidan dambe ko yaushe.

Tana zaune tana raba abinci nayi sallama tare da gaida ita na mika mata ina fadin Ammah tace na kawo maki yan tsarabanta tace dazun nake jin ai ta dawo a wajen yaran nan.

Juyewa tayi cikin wani kwarya dake gefenta tana fadin ai zan shigo yi mata sannu da safe ki gayar min da ita da dawowa na amsa da to na juya na fito kawai.

Anan waje din na wuce su Abbu sunata hayaniyarsu ta maza akan siyasa kamar fada da yake akwai duhu a lokacin ban tsaya gaiyar dasu ba na shige gida ina mamakinsu.

Ammah na daki lokacin don haka daga kofa na tsaya na fada mata nadawo da sakon ta bawa din na juya zuwa dakina.

Kwanciya nayi don banda katabus a lokacin banda tunane da ba amsa da zuciyana ketayi akan zancen daya shafi mahaifiyata din.

Wace fuskata yake min tsaye a hotonta dana gani wanda ban gajiya da kallo a ko yaushe ina faman ayyana abubuwa da yawa a zuciyana game da ita.

Ina kwanciya naji Abbu ya shigo yana fadin kinga ikon Allah ko hadarine aka hada tako ina garin nan da alaman bana ruwan sama zaiyi saurin sauka garemu insha Allahu.

Nima yanzu nake fadar haka a raina ai ganin yadda ko ina walkiya kawai ake sakewa sama makin ya shiga daki anan suka zauna suna hira a zatonsu nayi barci ko a lokacin.

Tiryan tiryan Ammah din ke koro masa duk yadda sukayi acan din da abinda kowa ya fada akai sai faman fadin umm,umm ikon Allah dama shirinsu ke nan Abbu ke fadin.

Kafin naji yace abinda nake so dake shine daga yau ki kawar da idonki acikin wanan zance don Allah ku bar masu suje suci in zasu iya in ba yau akwai gobe ai a wajen Allah.

Kin ganni nan Ammah banson fitinan daya shafi gado ko kadan badai sun sayar da wajen ba to kuyi hakkuri kusa masu ido kuga ikon Allah ai inku matane suna ganin baku da yadda zakuyi akwai maza a cikin ku donshi dayyabu ba zai yarda ba haka kuma ba,a sab abinda gobe zai haifar ba ai ga bawa.

Jikina ya kara sanyi da zancen su kamar ranan haka na kwana banyi barci ba duk iskan da akayi har aka gama ba ai ruwan sama ba idona biyu.

Haka na shirya washegari na fita zuwa school kwana biyu sai rama ya shigeni na fara ramewa a tsaye don damuwa dana saka kaina.

Saukin abin karama nake a lokacin amma ibada ya shigeni sosai a zuciyana haka nake fitowa a tsakar dare cikin sanda nakan fito nayi alwala in raba dare ina gaida Allah ina neman daukaka a wurin ubangiji.

Yadda malaman islamiyan mu sukr koyar damu a kullum wanan sai banyi wasa da hakan a rayuwana ba na rike hakan sosai a zuciyana duk da bansan amfani hakan ba gareni.

Aeesha nayi firgigit ina dagowa dagawa tare da kallon Ammah din ina fadin na,am Ammah itama kallon mamaki take min a .

.

Keko me kike tunane haka har kira ukku bakiji ba lafiyan ki kalau kuwa yar nan tunfa dawowana naga sauyi a gareki kardai wani abu ya faru dake a bayana kika kasa fada min Ammah din ta fada.

Cikin damuwa da kulawa take min maganan tare da maida hankalinta gareni lokaci guda nace cikin sauri Ammah wallahi ba komai daya faru dani bayan ki .

To meke damunki haka yar uutana yaki zo nan ki fada min ta fada tana nunamin kusa da inda take zaune a lokacin.

Hakan yasa na karasa ina sakin hawaye nace Ammah a cikin muryan kuka sai kuma na kasa karasa maganan dana so fada saboda tuna gatgadin da Abbu yai min kafin ya ban tarihina din a ranan.

Hankalinta ne ya tashi gashi kuma ina fadin ba komai saina fake da fadin mafalki kawai dai nakeyi akan wata mata.

Mata kuma na gyada mata kai wace irin matace haka kuwa nashiga uku ni Ammah nidai inba manya bace ta sa min ke gaba haka ?

Bari malam ya shigo ya bamu hayaki ayi insha Allahu inkin tirara ba zaki daina ganin ko wace muguwa ba cikin mafalkin da yardan ubangiji.

Haka kawai ban damu da dan kowa ba balle wata muguwa tasa min ya a gaba don hassada da bakin ciki kurwanki kurrr wallahi.

Sai ta jawoni tana shafan kaina tare da tambayana kanki dai bai ciwo ko na girgiza kai alamam a,a gareta.

Nayi kukana ma,isha a saman jikinta kafin na tashi na fara aiyukana nagida don kada ta kara jefa kanta cikin firgici.

Da Abbu ya dawone take fada mashi shidai murmushi yayi ya dauko hayakin ya bata ta tukaka min ina ji ina gani ba yadda na iya da Ammah don nina jawa kaina hakan a lokacin.

Abbune ya zaunar dani yana min fada akan na natsu na cire tunanen komai a raina a yanzu in dai mayar da hankalina ga karatu in samu inci jerabawana yayi min alkawarin ina gamawa insha Allahu gaba zai kaini in karo karatu gaba da secondary da yar gidan malam iro ke zuwa.

Wanan magana da mukayi da Abbu ya karfafa min gwiwa yasa har nasake na koma normal na watsar da zancen Nana a zuciyana ban mason in tuno da inada wata mahaifiya bayan Ammah.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[7/25, 9:54 PM] Zainab Idris Makawa Writer: JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

0️⃣4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login