Showing 69001 words to 72000 words out of 110493 words
Chapter 24 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx
ai nace ni kuma na koma Aisha yanzu ko ?
To mu bar zancen Allah na dauka ba zaki fito ba nace saboda me wai yaya koma zaki fitowa wani ai banda kai dan uwana da muke ta jiran dawowan ka kullum.
Yayi murmushi tare da fadin haka dai kikace Aeesha ni dazun ai na kasa gaskata idona akan kece nake gani a jikin mota zaune.
Haba yaya har na wani sauya maka da idonka zai kasa gaskatanine kuma yanzu wai da yaushe ka iso ne don Allah ?
Dazun da yamman nan isowata ke nan ban jima ba na fito in samu jam,i har kika gani nace to yaya kaduna ya aiki da mutanen can kuma ?
Saida ya nisa yace komai Alhamdullahi ya Abbu dasu Ammah ina Aimana nace duk suna lafiya Aimana na ciki tace zata fito ku gaisa idan ta karasa cin abinci.
Ashe na saura da muka mi a gunku irin haka wallahi cikin shaku nazo nan don ban dauka zaki fito har ki saurareni ba a yanzu.
Saboda me kace haka yaya ko ance ma munyi wani abune yace a,a ban hadu da kowa ba balle a fada min amma gaskiya Aeesha kin sauya min sosai a yanzu kasa gaskanta hakan nake a zuciyana har yanzu.
Dawowan Abbu yasa muka tsaya gaidashi din ya taka har zuwa kofa ya tsuguna yana gaida Abbu naji Abbu yace wai Suleiman ne yaushe garin namu ?
Yace da yamman nan nazo baba mun sameku lafiya Abbu ya amsa da lafiya kalau ya aiki kuma yace Alhamdullahi baba sai naji ya ban wani irin tausayi.
Don yanayinsa da gaba daya ya nuna yana cikin duwa a lokacin saida Abbu ya shiga gida ya juyo zuwa wajena na taresa da fadin ga Abbu ya dawo barin koma gida da safe mu hadu ko yace to Allah ya kaimu yadda kikace dai din ai ko hakan nagode tunda kin fito na ganki .
Muka dan taba hira mai kama da ba,a ko zolaya ga juna damashi sarkin son wasan barkwancine saidai wanan karon yana da damuwa ko wani abu don duk da duhune amma bai hana min ganin ramansa ba da duhun daya danyi.
Mukai sallama ya tafi har lokacib Aimana bata fito ba sun gaisa wanda banji dadin hakan ba gaskiya a lokacin .
ZAINAB IDRIS MAKAWA[8/25, 10:06 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN waning A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Tsaye take rike da labulen window tana shakar iska yanayi na subbahanahu wata,ala a dake saukar mata da ni,ima a lokacin cikin jikinta tare da saukar mata ds natuwa a tattare da ita.
Hakan ya farune saka makon yawan msfalkin da takeyi cikin yan kwanakin nan wanda a sanadi hakan ta kasa samun natsuwa.
Hasken ranan da yaiwa fuskanta yawa a yanzu yasa ta koma ta zauna tana mai bin dakin da kallo kamar tana neman wani abu a lokacin.
Idonta ya tsaya cak saman drower saidai kasala yau ya hana ta jin dadin jikinta ga baki daya ga wani yanayi na bakin cikin haka kawai da take ji ya tokare mata makoshinta a lokacin tare da hanata sukuni.
Ido ta runtse a cikin yanayi take abinda ya shude shekara da shekarune ya biyo mata a rai lokaci guda wanda bata san lokacin da hawaye ya sauko mata ba jin karan bude kofa yasa ta bude idanu mai aikinsuce wata yar togo ta shigo dakin dauke da shayin da ya zamo masu al,ada sai kasha shayi kafin komai tunda farar safiya don watsake jijiyoyin jiki tare da samun kuzari.
Ta aje shayin kafin tace da ita Oummu Banna Kaifa Subbhi ta dago cikin yanayin kasala tana amsa mata da Subbhi bil hair ya bintu kudirat
Ga shayi na hado ko zaki bukata kafin abinci tace Shukuran bintu kudirat ya kwanan yaran kuma ina dai ba matsala komai ko ?
Tace Alhamdullahi lafiyansu kalau sun tashi suna shirin school driver kawai muke jira a yanzu yazo masha Allah sannu da kokari ta fada karo na kusan uku ga matar dake duke tana tsiyaya mata ruwan shayin da zalla ganyene akai amfani dashi sai kayan hadin kamshi da ya dan bashi dandanon dashi ba zaki ba shiba dandanon ganyen nasa ba don basu damu da sugar ba su.
Wani gaisuwan karo barkatai tayi mata ta fita cikin jin dadin yadda uwargidan nasu take kula dasu tankar a gidajensu suke zama.
Ajiyan zuciya ta sauke bayan fitar matan daga gidan ta mika hannu ta dauko ruwan shayin dake turiri a cikin cup saman table.
Baki takai da zumar sha yadda ta saba kurbi daya taiwa ruwan ta sauke da sauri daga bakinta don gabanta daya fadi ajewa tayi tare da dora hannu saman goshin ta ta dafe na dan lokaci .
Ta jima wajen zaune kafin karan wayarta ya dawo da ita cikin yanayinya firgigita sauke hannu tana bin wayan dake faman ringing saman gado da idanu har ta samu ta mike da kyat ta dauko wayar nata.
Wanda take zaton ya kiratane shi din ya kira kuwa ta dauka tana karawa a kunnenta muryansa mai taushi na larabawa ya sauka mata a kunnenta lokaci guda.
Ido ta lumshe tare da fara gaidashi ya amsa cikin jin dadi tare da tambayan lafiyansu dana sauran jama,an gidan.
Sundan jima suna magana kafin suyi sallama ta kashe wayar nata a cikin kundura da zancen zakice ba ita bace akoda yaushe takan zauna a daidai wanan lokacin zaman jiran wayasa ba sai gashi a dan kwanakin ko wayar nasa bata kaunar taji yanzu.
Hawayene masu dumi ya gangaro mata a saman fuska wanda tasan da zuwanshi don hakane batayi mamakin jinsa a fuskanta ba lokacin.
Yar uwarta da take tankar uwa a gareta da wani bangaren rayuwa take mata gizo akoda yaushe a yanzu yanayin da take ganinta a mafalkin suna magana ya tsaya mata a rai ya hanata sukuni da jin dadin rayuwa a yanzu din.
Kwance yake don ya kasance weekend hakan ya bashi daman hutawa a gida tun bayan sallah asuba daya samu yayi ya koma ya kwanta barci saida ya gaji ya tashi.
Wayansa ya lalubo ya kunna ta bayan ta kawo ya fara neman mahaifinsa don yasan yanzu gari ya waye masu a nan saidai safiyane sosai cikin irin wanan lokacin yakan kirasu su gaisa dama.
Saidai yau ya kira har wayan ta katse bai dauka ba hakan yasa ya hakkura da kiran ya fara shiga wajen sakonni kafin ya danna WhatsApp dinsa da bai damu da shiga ba ko wani lokaci.
A gurguje yake bin sakonnin kafin ya kai kan wani photo daya dauke mai hankali tabbas Aeesha ce jikin photon babu tamtama itace a wajen buki akai hoton kuma bai tantama da cewa ba a cikin satin ake bukin ba.
Photon ya kara zooming yana karewa yarinyar kallo kafin ya fara karanta abinda dake kasan photon na dan lokaci ya runtse idanuwansa a hankali.
How comes suka samu photon yarinyar nan haka ya tambayi kansa kafin ya kara zooming ya kurawa photo ido na dan lokaci kuma shigar ba assha a cikinsa gashi kuma alama ya nuna tana cikin farin ciki alokacin.
Kodai yarinyar nan ce take aure ya tambayi kansa bayan ya gama kallace hotunan kaf da sauri ya ba kansa amsa da no bai yuyuwa ina ya mike zaune zubur lokaci guda.
Wani zufa da baisan daga ina bane ya feso masa a goshinsa duk da sanyin da dakin dayake yake ratsa jikinsa amma wai munafukin zufa yaji a jikinsa yanzu kuma.
Ya jima zaune kafin ya mike ya shiga wanka bayan ya fito yana tsaye yana goge ruwa akansa ya dan tsaya kamar mai tunane kafin ya aje tawul din ya dauki wayar har lokacin tana kan photon daya tsayar da wayan nasa photon ya kurawa ido na dan lokaci kafin yaja tsuki yana yarda wayan saman gado.
A gurguje ya shirya ya sauko kasa abinci ya samu an shirya masa zama yayi don yaci abincin amma zuciyarsa ta kasa samun natsuwa sam.
Wacece ita yar waye agarin nan ko acikin kasan nan waye ubanta ita din kayi bincike a kanta bata kasance cikin tsaraban takaranci ba.
Don babu balaraben arziki da zai jefo yarshi Nageria ta zauna haka cikin wanan kasan tare da wasu tarkancen dangin kala.
Zancen shi dasu mami a falin mai babban daki na karshe akan Aeeshane ke masa yawo a kwakwalwansa lokacin haka kawai hjy kura tasa aka tarasu take masa wanan yankar kaunan a gaban iyayyensa .
Hjy meya kawo wanan zance kuma yanzu magaji bai taba kawo wata yarinya ba da sunan aure a gaban mu har yanzu.
Ai kuma hjy naga koda ta kasance ba yar kowa bace indai tana da hali walillahi,hamdu inji daddy tunda shiya ganta yace yana son abinsa ko.
Matsalan ku ke nan maza da kuma iyayyen yanzu son diyanku sai ya rufe maku idanu kan halaka baku damuwa .
Haka kuma da zaran kuna son mace idon ku sai ya makance ku kasa tunanen abinda kaje ya dawowa rayuwanku gaba sai idan kukai kwadan ku ya fada kuke komawa da kun sani wani lokaci hjy mai babban daki ta fadi hakan ga mahaifinshi da yai magana yana kokarin kare yarinyar da take zance a lokacin.
Hjy naga in ma abinda kuke tunanene inhar hakan gaskiya ne meye laifin yarinyar a cikin zacen nan tunda ba itace ta aikata wani sabo ba balle a kyamace ta ?
Kaiyya naka tunanen ke nan Ahmad na zata a shekarunka zaka san illan wanan abin a yanzu ba sai anje ba wata rana me zaku fadawa yayanta idan ta gauraya daku ta haihu da danka ?
Hjy ai duk wanan abin baikai can ba ayi tunanen mafita a yanzu a gano ita din yaya take kafin a fara tuna zurian da zasuzo gaba.
In ma har bata da gata aishi magaji sai yai mata gata Allah yai masu baki daya ina dama ko wani namiji shine gatan iyalinsa dai.
Rufa min baki Ahmad da zancen kana banza na fahinci son dan ka yasa kana kokarin abinda zai zubar muna da mutuncin mu da kimar gidan mu nan gaba .
Na fahinci Idon ka ya gama rufewa a yanzu kan son kai irin na nasara da ka koyo zamanka cikin su ni zaka jawa abin gori cikin zuria ta don kawai kada ran dan ka ya baci ?
Ga yar asali jikan asali wace asali ya haifa ka tsaya kana son yiwa mutane wasa da hankali Hindu ce na zabar masa ita kuma zai aura nagama maganata ta fada tana wani kaiwa kishingide saman tintin din gefenta.
Mikewa man bash yayi don ya fice daga falon saboda bai iya jure jin zancen tsohuwar nan na shirme a kunnuwansa donshi a shirme ya dauki duk zancen ta.
Har ya kusa kai kofa zai fita din yaji tana fadin kaje duk inda zaka magaji sai ka dawo nan ka sameni indai nice.
Aure da hindu ba fashi tsakaninku don na riga dana yanke wanan hukuncin babu kuma mahalukin da ya isa ya tayar da wanan zancen a cikin iyayyenka.
Har yakai kafa zai fita din ya juyo ya tsaya don jin abinda ta fada ya kalleta yayi murmushi kafin ya kara tako biyu zuwa gareta ya nunata yana fadin .
Gara dai da kika gyara zancen ki hajjaju don su kika haifa ba niba ya nuna iyayyen nasa dake zaune a gefe tsit kamar ruwa yaci su wajen.
Don sunsan kwanan zancen duk wanda ya motsa cikinsu zata hada dashine tayiwa mashi rashin mutunci don haka kowa ya kama bakinsa yana kallon draman da sukeyi tsakaninsu ranan.
Akidan nasara kuma da kikace munayi ni da ubana yanzune zan nuna maki an haifeni cikinsu da nasan akan wanan shirmen naki kika taramu don ki yi hakan wallahi da ban zan zo ba.
Haka kuma indai Bashir ne ki sani ba zan kara zuwa nan don ke ba bance gidan ba a,a nan dai matukar kina raye a doron kasan nan mubar haduwa dake har abada tunda nagane son kai yayi maki yawa.
Don ko a cikin yayanki dukkansu diyan kine amma kina zabe a kina nuna masu son kai balle wani.
Tau ba zan dauki wanan ba zan kuma fadawa mijinki ya tsawata maki karo na biyu a kaina ko na dauki mataki da kaina.
Ahmad's kana jin yankan kaunar da danka ke kallona yana min kuma a gabanku kuna kallonsa .
Ai basu sukace ki kirani ba kuma ban yake maki kauna da kikace na yanke maki a gabansu
ba, sai nan gaba .
In har kikai gigin daura min bakar yarinyar can da sunan aure zaku rainawa kanku wallahi.
Kai waye dan iska yaro me kake daukan kankane cikin mu Bashir hjy kura ta mike tana fadan hakan gareshi.
Ta nunashi tace kana dauka kafi wanine a cikin mu nan kome hjy zata fadi magana ka ketare a gaban mu ?
Har kana kokarin fadin maganan banza ko ita hindun ka fitane data yarda, saima ince taimakonka za ayi har hindu ta zauna dakai ai
Ooh soryy aunts zancena da tsohuwar nan ne a yanzu ya shafeki ko don Allah kiyi shiru ba daku nakeyi ba a yanzu ina zance da kakatace wanan da tayi zamaninta take son ta shigo na wasu nake magana ban kawo gareku ba tukun ya hada hanayesa waje daya lokaci guda alaman ban hakkuri a gareta ya juya zai fita.
Hakan yasa hjy kura fadin tabbas ya tabbata kana shaye shaye bashir wanan iskancin har ina kai kuma yaya ka zuba masa ido yana ciwa hjy mutunci haka a gabanka ?
Babu mai kallon bashir ya kira sa dan shaye shaye yarki daice yar shaye shaye kowa kuma ya sani wajen nan mami ta fada.
Shima saida ya kallo uwar balle su da suke ganin abin mamaki a yau don sunbar zancen bashir sun koma mamakin mami da ko hannu kasa mata a ido bata taba cewa don me ?
Yau sai gashi a gaban kowa tana fada akan danta da akai wanan zaman donshi ba tsoro ko shayin idon kowa ta tarewa danta fada karo na farko a rayuwanta.
Af hajiya yau dai kinji kin gani da idonki kuma hjy maryam tana kokarin kare danta ta aibanta min tawa yar a gaban kowa.
A,a Kura inza a fadi gaskiya kowa yaji sanda kika fara aibanta mata da kafin ita dan galadima ya fada don shima yana zaune tunda taron na dakinsune iya su kadai aka kira a lokacin.
Au kun yarda ke nan zaku hade min kai su aibanta mi ya anan a,a fa ya kara fada zaici gaba da magana hjy mai babban daki tace kuyi min shiru don Allah da wanan abin kunya da kukeson jawo min a yanzu.
Duk wanan abin ke kura ke kika jawoshi bayan nagama magana meya kaiki tofa wani zance kuma a baya koma meye yanzu ai yarki taja komai ta dauka duk tabar gazan da tayi a can wajen karatunta kafin su korota ba a sani bane ?
Yanzu anbar kiwon dabbobi an koma kiwon mutane yan adam duk abinda kakeyi da masaniyar mutane akanka don haka ku kama min baki anan.
A haka suka watse saidai ba a san a inda zancen hadin ya tsaya ba a yanzu don hjy kura ba kyalewa tayi ba asalima tana ta faman shiri a bangareta yadda hjy Nasare ta kyankyasawa su umma labari.
Dad ya fada mai komai hakan yasa ya murmusa don tuno da rabuwan nasu da tsohuwar kakansa fitinana tare da fadin trouble woman ya furzo da iska.
Kafin ya koma tunane anya hukuncin daya daukarwa rayuwansa yayiwa kansa adalci kuwa bafa Allah bane ya haramta tsakaninsu camfi ne kawai na yan adam hakan.