Showing 96001 words to 99000 words out of 110493 words
Chapter 33 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa.docx
fadan hakan gareshi.
Sai naga ya dan juya gun abokan tafiyan shi suma sunji metake fada a lokacin don haka dariya sukai mashi da sauri yace.
Look daughter next time idan mun dawo zamu shiga akwai inda zamu yanzu amma ga wanan ki shigawa mummy dinki dashi ciki hjy ce ta bayar akawo mata tsarabansu .
Naji ya kira kaninsa da sunan Nazir bude boot din nan ka tayata daukan zuwa ciki ka gaidasu lokacin idan ka shiga don Allah .
Lokacin nayi magana nace ai daga mamata sai mu da antyna ne a gidan Abbu ya tafi kasuwa tun safe sai dare zai dawo yace next time don Allah .
Next time idan mun dawo zamu shiga ya sake fadan hakan na dauka dan leda zan gani sai naga sabanin hakan don ko kayane sosai a bayan motan ake fitarwa a lokacin.
Su drinks su galon din turkey taliya macaroni kayan shayi sabule omo da dai tarkacen daba zance gasu ba a lokacin a cikin ledan suke ban san meye a cikin shiba.
Nace wai duk wanan tsaraban mune haka amma kasa hjy wahala da yawa aimin godiya don Allah wajen hjyn mu din duk da nasan yadai fada ne kawai kilama bata sanda kayan ba ita.
Can Asmau ta kara fitowa da basket din da aka shirya abinci a ciki tace Ammah tace nafito maku da abinci kuje kuci a mota tunda kunki shiga ciki kuci .
Kai mama nason wahala haba dai har sai an biyo mu da wani abinci kuma haka ya zama wahala ai nake gani .
Na tare da fadin amma kasan ba zakuzo ku tafi hakana ba bakuci abinci ba fa a gidan mu gaskiya duk da baka sanar damu ba balle a shiryawa zuwan naku ?
Amma kince baki san da zamuzo ba yau nace wallahi kunyi sa,a an dafane daidai da zuwanku ai shi Nazir din ya amshi basket din daga hannu Asmau yana fadin angode kinji.
Zata tafi samira ta fito da kayan drinks tana gaidasu itama ya amsa cikin kulawa mun dan taba hira kafin ya kalli agogonsa yana fadin a fadawa Nusaiba ta fito mu tafi.
Kada muyi dare a hanya don hajiya taja min kunne na dawo mata da yayanta kafin magariba yanzu fa two ke batun yi matazun .
To ya na iya zamu gidan wata sister din hjy daga nan shima wanan abokin nawa yana son ganin wani abokinshi ne .
Sun takura min da banzo dasu ba kinga ina nan har magariba ina kallon sahibata don ba gajiya zanyi da kallon ki ba ai.
Muka dan kara taba hira dasu nake fada mashi zancen zuwa IT da zanyi abuja ya nuna jin dadinsa har kanin nasa na fadin aida kaduna nazo in zauna gidansu.
Nace haba dai Nazir gara dai kada ai hakan nashiga na samu wanan yar uwar nasa har tayi sallah muka dan taba hira don suma sun tafi suyi sallah din a lokacin.
Nan na daji wani labarin shock a bakinta take fada min ai wanan yar da suke tare diyar S matazunce amma basu tare da mamanta a yanzu.
Nayi ta satan kallon yar tana da dan kama da mahaifin nata gaskiya da zata tafi na dan hada mata abinda Allah ya sauwaka min a lokacin tana ta murna muka rakosu gaba dayan mu kofan gida.
Nazir din yana ganin mu ya fito da kayan abincin ya mikawa Asmau yace ga goro nan yayana yace a baki agaida mama kuma mun gode.
Suka ja motarsu suka tafi kafin nayi a jiyan zuciya mu koma cikin gida ina shiga anty safiya tana bude kayan tana fadin wai wanan yar da sa,an samun maza kike saidai matsalan abin da sunji kome ke nan sai su gudu.
Mijin daine baizo ba ai idan lokaci yayi mijin na gaskiya yazo kome ake fada akanta ba gudu ba saida ya matso wanan cikin jerabawanta yake haka a rubuce.
Wani yana da komai din a rayuwansa amma kare ma baija balle ya sunsuna ai abin baiwane daga Allah Ammah naji ta bata amsa hakan.
Ta dan tsuke fuska kafin tace niba wani abune nace ba ai mama ganin dai wanan abin kamar za a bude shago dasu yasa na fadi hakan ai.
Shine ai na baki amsa daidai da maganan ki laifine kuma yanzu kai don Allah waga maganan ai baiko dace ba wallahi mi ar ranan shi yanzu karshe fa duk mu zamu amfana da kayan da a wuringa to mezaisa ki fadi waga magana don Allah ?
A ikon Allah kuna dai son ku juya min zancen da wani ma,ana ni yanzu gidan nan banfi kowa moriyan Aeesha ba tunda komai nata bai wuce yaranga ?
Hanyan daki na nufa kai tsaye kafin inji Asmau tana magana kasa kasa tana fadin mi da kika waga tabi,an ne mama wallahi dai wanga abu baiyi ba wallahi.
Kayan bukatuna ta kwaso a cikin kayan irin su manshafi sabule turare da wasu abaya da english wear dake cikin wasu ledoji ta shigo min dasu dakina.
Koda ta shigo ta samu nayi alwala na fito daga bayina bayan na kara wankewa take fadin mummy ga kayanga da naga kanwarshi a daki na ajesu a gefe daya falo dazun .
Sallah zanyi Asmau banyi sallah ba tun dazun ga la,asar ya gabato jiki na fara harama tayar da sallah hakan yasa ta dora min kayab saman gado tafita.
Koda na idar tagama sabon abincin data dafa jeloup din shikafa tayi muna sai sauran ganyen data zuba muna a sama tare muka zauna mukaci da ita lokacin samira ta shigo.
Take fadin wasa tare ci bambanko gara da Allah ya kawoni nishigo ke kwasowa mummy na sama ke barmu da gaya can zama tayi muka hada hannu da ita.
Can naji samira din tace mummy an kiyi hakkuri don Allah da maman mu kesan halin mama haka taka hwadin magana kai tsaye bata taunawa wani lokacin.
Samira yau idan ba Ammah wa nike dashi bayan su anty safiya daku a duniyan nan ni naga gaskiya ta fada ai ba karya a cikin zancen ta.
Haka mazan suke kwana biyu daka sake da mutum yanzune zakaga ya gudu kuma bai sake dawowa ni banga abin haushi ba a ciki ?
Amma mummy ai bai kamata haka ya fito bakin mama ba ko yau duniya ita damu wa muke dashi da zai muna waga abin da muke samu ta sanadinki haka don Allah dai ?
Yanzu fa zancen karatu kike muna waya tuna damu duniya har yasan da haka garemu inba keba ai fatan alheri ya kamata yanzu ya fito a bakin mama wanan lokacin gareki kuma.
Ke gani nan duk abinda wani zai fada kan mummy a yanzu ni baya shigana ko yaro na goye yasan mai kyautata mashi ai balle mama halintana haka kawai.
Mummy ma bata damu da waga zance ba ai haka dai mukai ta magana har muka gama kafin mu koma kallon kayan daya kawo muna din .
Naso in kwanta bayan la,asar sai kuma naga rashin dacewan hakan yasa nake gyara daki mu shiga gidan akwai wajen su maryam da farida.
Muryan yaro daga waje yake fadin wai ana sallama da Aishan gidan nan inji Auwal cak na tsaya ina maimaita sunan nace Auwal Auwal fa ?
Filon dake hannuna na aje na saba gyalena na fito Auwal din ne kuwa cikin wata farar mota mai kyau yana ganina ya fito yana washe baki na daure fuskana lokaci guda.
Haka ya karaso yana fadin ni dama ai nasan mai laifi nake a wajen ki Aisha tun wacan lokacin ban kara lekoki ba zakice don oga Bash baya kasan ne yasa hakan ?.
Ummm,humm Auwal ke nan ina gajiya ya amsa da lafiya kalau ya kwana biyu ya karatu kuma nace Alhamdullahi .
Yau dai nasan in nazo ai dole na jiki tunda shirun yayi yawa haka Auwal na katseshi da fadin kaima kazone ka ci min mutunci ka fada min magana yadda Salma ya fada min kwanaki ?
Salman salman fa kikace Aisha nace kwarai ya fada min maganan dako makiyina banyi tsamanin zai iya fada kallona ido da ido yafada min shi ba .
Yayine don yana ganin banda gatan da zan iya kwatarwa kaina yanci kome saukin abin dai koda yace kwadayi yasa na bawa Man Bash kaina yayi amfani da daman shi akaina.
Saukin abin ba amfanin iskanci yayi dani ba daiko amfani na hikima irin nasu na mayaudara yayi min a lokacin ?
Saidai duk da ban fahinci amfanin da yake nufi yayi dani ba abindai da sauki bisa a ce yau iskanci na shashanci yakeyi dani ai a karshe ya gujeni kuma.
Wanan wani zance da wani dalili nasa can da ban sani ba kuma hakan ya faru danine a cikin,,,,,
Don Allah dakata Aisha shi salman din da kansa ya fada maki wanan maganganu irin haka ya tsureni da kallo nace zan masa kazafine ?
Tunda a girme dai salman ya girme ni nisa ba kusa akan me zan masa karya don naga baya nan yanzu kome zaisa nayi masa karyan hakan ko kazafi ?
Zancen kazafi ai bai taso ba zancene naji kaina ya daure da jinsa don yanzun hakama ogane ya turo ni inzo in kawo maki sako wallahi Aisha .
Sai shekaran jiyan nan na wallahi na dawo garin nan ina can oga ya turamu wani aiki a cikin kwanakin nan da kika jini shiru .
Au yanzun ma ya dawo ke nan yayi amfanin dani a karo na biyu ke na ko me ?
Saidai niko a yanzu sako na fito in baka ka isar masa da cewa ashe dan tallakama yana da ranansa don shine na fito a yanzu din daba zaka taba ganina ba kuma again tunda na gane yaudarata kukeyi ashe ?
Sai naji yace dani dakata Aisha ki saurareni don kina kara ban mamaki a cikin zancen nan a yanzu .
Yadda yace din dani na daka nayi cikin kura masa ido inji me zai fada min lokacin sai naji yace zancen yaudara ko wani abu a tsakanin mu kinsan wallahi babu shi alkawari na daukarwa kaina da hakan.
Kema kin sani tun farko wallahi balle shi oga bash a rayuwana tunda na sanshi ban taba jin wani mahalukin da yace bash ya cutar dashi ba tun tasowan mu har yau din nan sai ko yau a bakin ki da kika fadi haka har naji kuma ban yarda ba.
Duk da nasan ba halinki bane akasi aka samu ko a yanzu din sai dai abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankali don Allah.
Har zuwa lokacin da zamu gano gaskiyar wanan maganan me Salman ke nufi da hakan da yayi a gareki ?
Shiru na danyi cikin nazarin zancensa kafin in nisa nace abin mamaki wanda ban tabo tunane ko zato ba saiga malam salman a gabana yana fada min wayan nan maganganun haka ?
Audi ai bai fadawa talle hakan dake dashi dani da kowama yasan waye Oga Bash yasan mutumin kirkine akan meke zai damfareki karamar alhaki a dake wajensa .
Idan ya damfareki Aisha yaci riban me ga yin hakan idan yayi maki yaudara ?
Yaja wani huci yana fadin lalai Salman inda wani manufa ko wani ya turoka ka tafka babban kuskure a nan wanan karon don har Man bash yaji wanan akwai rigima a tsakaninsu gaskiya .
Wallahi koda ya kirani jiya yana fada min sakon nan zai iso na tabbatar da kuma ya iso hannuna na kawo maki shi don zaki bukaceshi a yanzune.
Saida nace a zuciyana lalai kina da wani kima da daraja da nauyi a zuciyar Oga Bash yadda ya ke magana dani a jiya din.
Don haka har in kin yarda kibi wanan shawaran tawa ki bari mubi zancen nan a sannu mu gane meke faruwa dayasa Salman yin hakan .
Amma kuma nafi kyautata zaton kamar dai wani ya turosa yai maki hakan don cin ma wata manufa na a raba alakan da ake tunane akwai shi tsakanin ki da Oga Bash.
Na katseshi da fadin wace halakace banda kyautatawa da mutuncin dake tsakanina dashi da har za a iya turo salman yai min hakan.
Yace ke kike ganin hakan Aisha kibar abinda baki sani ba akan baki sanshi ba tunda ba,a taba ganin ya kula wata ya mace ba a cikin garin nan saike a karo na farko.
Ai koda ya kulani Auwal tsakanina dashi mutuncine kawai da girmamawa dan bai taba nuna min wani alaman so ko wani kalman banza daga gareshi ba.
Asalima duk zan shiga wurinshi shi malam salman din yana a office din mafiyawan lokutan suna tare koda nake shiga din .
Amma sai cewa yayi dani wai daga taimako na dauka man bash yana sona ne idan haka nake tunane na yaudari kaina.
Har Inma wani abune nake tunane ai Man Bashi din ya biyani amfanin da nayi mada don haka kada in sake nemansa da sunan son jin labarin Bash a bakinsa.
Alhali ni kuma naso in fada masa zuwan wasu manyan mutane da sukazo gidan mu wani rana suna tambayana wai lamban Man bash suke nema da ake samunsa a waje na ?
Wanan naso fada masa amma saiya tare da wanan kalaman marasa dadin ji daga bakinsa har yana ikirarin cewa haka mu mata muke da munga wani dan oppotunity yanzune sai mu lakewa mutum don kwadayi.
Sunana ya kira da Aisha na dago na kallesa kafin yace kiyi hakkuri don Allah zanyi bincke kan wanan zancen .
Do min ina ganin akwai wani abu a kasa wanda bamu sani ba koma meye zamu sani insha Allahu nan gaba.
Don maganan nan da kikayi a yanzu cewa anzo wajenki neman number Oga Bash yasa na danyi tunane su waye zasuzo gidan nan wajenki neman layinsa.
Waya nuna masu gidan ku har sukazo dole akwai dai akwai akwai abinda ya faru har salman din yayi hakan gareki?
Yanzu kiyi hakkuri don koshi bash din banson yayi saurin fahintar da matsalan saboda yadda suke dashi salman din don banjin yasan da wanan zancen ayanzu .
Ya juya zuwa wajen mota da sauri ya bude baya ya fito min da wani babbab jakka haka irin na kasan waje din nan da ake tura sako dashi .
Ya dawo inda nake tsaye yace ga wanab in kawo maki kayan aikine a ciki zaki bukacesu a yanzu wajen da zaki iya bayanin da yai min ke nan.
Murmushi nayi na kalli jakkar a lalace nace Auwal na fada maka sabon yaudarane wanan kuma me zan bukata dani ban sani ba sai shi zai aiko min tun daga can ?
Ki karba don Allah Aisha kada daman nan ya wuceki oga dai ba zai taba yin abinda zai zubarwa da mutuncin gidansu ba kin sani.
Wanan kalamin yayi kama dana Asmau yasa na karba sai naji abindake ciki yana da nauyi kara kallon jakkar nayi nace kace nagode na juya na shiga gida kai tsaye.
ZAINAB IDRIS MA
[9/2, 5:17 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Duk da Auwal yace dani urgent ne sakon hakan baisa na bude a ranan ba saboda ina zargin wani tarkon irin yaudaran nasu suka hada min kuma.
Takaicin hakan ya hana in bude inga meke cikin jakkar alokacin saboda gudun sabon yaudaransu gareni.
Hakan yasa sai washegari da asuba bayan na idar da sallah lokacin ba wanda zai iya shigo min daki na jawo jakkar na bude.
Idona ya fara tozali da na,auran bincike irin ta siri wanda ban taba mafalkin mallakanshi a duniyan