Showing 3001 words to 6000 words out of 231198 words
Chapter 2 - TAKARI Book Complete by Zainab Makawa .txt
ido tana kallo tana wani yatsune fuska azuciyar ta tana fadin ,,,, kai dadina da kauye kenan wlh,.
Komai nasu na tsafta ne ji randan ruwanta duk da sun tsufa amma an wani lulube shi da wani marfi mai fadi gidan gashi na lakane amma jiko ina tsab,,
In a gida nake aiko tashi banyi ba yanzu balle har inyi gyaran wuri.
Motsin dataji shi yasata dagowa da sauri takai diban ta akofar dakin .
Hakan yai daidai da fitowar inna a,daki a,a,a lalai marhabin mutanen birni ne yau a garin namu .
Cikin sakin fuska da murmushi suka gaisa cikin natsuwa.
Inna ta koma daki tashinfida tabarma mai haske tace bisimillahgag shigo daga ciki,,, batare da bata lokaci,ba Gajiye ta shiga suka kara gaisawa abisa al,ada irinta bahaushe idan kai bako gaisuwa kusan biyu akeyi,,,,,
Hira sosai sukeyi na yanayin lokaci,,,,,,, A cikin hiran tasa Gajiye ta sako zancan daukan yara.
Saida inna tanisa sanan tace, a gaskiya Gajiye bawai bani son yaran nan su, gusa, kusa dani bane,aa,Kinsan amana suke gare ni Allah yai ma mahaifin su rasuwa, batare da nasan asalin gidan su ba,. saidai zuciyata tana fada min cewa insha Allahu zasuga danginsu koda kuwa bani raye ne.
Saboda hakane yasa nake kokarin ganin nabasu ingattancen rayuwa,.
Saida gajiye ta gyara zama tace inbada abinki yar kulu ai zuwa kawai zamuyi sudanga inda nake kwana biyu indawo dasu.
Kinga aiko watan wata rana su zasu kai kansu inda nake don zumunci ko?
Shiru inna, ta karayi tana nazari maganar gajiye acikin ranta.
Gajiye kibari sainayi shawara da yaya na malam sale duk abinda yace zakiji kafin ki wuce. Nakuma gode da kulawar ki,,,,,,
Malam sale yayane ga inna, "Saboda haka kamar yadda inna tace haka tayi tasamu malam sale ta fada mai duk yadda sukayi da Gajiye shiru malam sale yayi yana nazarin maganar da yar kulu tazo masa dashi .
Can ya nisa yace tau yar kulu mutum yazu ba abin yarda bane , Saidai kuma ita Gajiye din ai ina ganin ta gida ce koma dai maiye aibazata wuce nan ba.
Cikin murya mai rauni Inna tace tau yaya duk abinda kace insha Allah haka za,ayi.
Malam sani ya lura inna batason tafiyan kokadan,,, Sai yace kiyi hakuri diyar kulu addu,a zamu Allah yakai su lfy yadawo muna dasu lfy tace ameen
Inna tace zata koma sukayi sallama ,Sai dai shi malam sani yasan cewa inna bata amince da wanan tafiyar ba,,,,, tausayi Gajiye da bata taba haihuwaba yakeyi kuma gashi har ta taya diyan " yar uwan shi idan har bai bada baki ba Gajiye bazataji dadi ba,,,
Dasanyi gwiwa inna ta dawo gida .
🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 16:28] +234 703 602 1388: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
5⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
Inna yar kulu zaune a dakinta cikin dare bayan ta idar da sallah dare kamar yadda tasaba, Tana kai kukanta ga Allah akan Allah yasa wanan tafiyan da za,ayi yazama mata alheri,
Allah kuma tsare mata yaranta aduk inda suka shiga.
Duk wanan addu,an da takeyi a cinkin zuciyar ta takeyin shi, ,,
Shin wai ma wazata tura wanan tafiyan cikin hafsat da fadima .
Duk iya tunanen ta takasa tantance wacce zata bari a,tafi da ita,,,,,,,,
Washegari karfe takwas na safe sai ga Gajiye acinkin shirinta na,tafiya,,, A,zuciyanta tana fadin ai,tunda malam sale ya yarda bazan kara kwana ko guda ba kada in,zo in samu matsalar tafiya,,, Don ita ga haukanta duk yaran biyu zata tafi dasu saboda samun banza.
Da sallama tashigo yar kulu ta, tare ta da mutunci, Saidai acan cikin zuciyar ta addu,atakeyi ,,,,,,
Bayan sun gaisa cikin gimama juna,,,,, Sai yar Gajiye tace tau ina fatan yaran sun shirya ko ?
Innna dake shirin mikewa ta dauko mata koko tadakata tace yaran kuma ,"eh mana inji Gajiye bada hafsat da fadima zamu ba ,,,,,,,, habadai Gajiye idan na,bakisu dukka nidawa zan zauna au baga Maryam da DATTIJO ba,,,,, a,a gaskiya hakan bazai yiba , ai,ko mutun gudan dazan baki kawai dai don kece an riga anzama daya
Duk da ran Gajiye ya baci amma sai tadake tanuna ai ba komai ko hakan ma ai, ta gode tunda an,yaba da ita har anbata,,,,,,,, Saidai acikin zuciyar ta fada takeyi,,,, yo ga matsiyaciya nizaki kulla ma tsiya inga samu inga rashi haba wanan wata irin shu,umar mace, ce
Muskudawa tayi tare da gyara zama dan taji dawa zata tafi,,,
Juyowa inna tayi daidai lokacin tai ajiyan zuciya gami da cewa,,,,,,, Ban riga na gama shawaran ko dawa zaki tafi ba tukun ,,,, au mutafi da hafsat ma tunda itace babba.
A,aa gaskiya hakan zaiyi wuya donkin ga itace maidan wayo daga cikin su. Kinga ko zaiyi wuya inbari tayi nisa dani . Duk da yake fadima itace kusan ke taimakawa hasfsat din, kinsan abu ga tallakka ai sai a hankali.
Acikin zuciyar gajiye tace duk kigama tsiyar ki sai naci riba dake,,,
Inna abu yasha mata kai tara wace zata tura birni,,,,,,,,Caraf fadima da ke da saurin wayo da fahinta tace inna nizani abar hafsat dasu maryam
Aiko inna taji dadin hakan don dama tana shakar zuwan hafsat, Saboda shiru shirunta yai yawa za,a iya cuta mata batare da ta dauki wani mataki ba.
Fadima duk da yarinyace amma ta gane cewa inna batason zuwar hafsat din don ko cikin dare , da ta, farka taji inna na,maganar ,,,,,,,
Duk zancen da inna tayi cikin dare fadima naji ,,, A ,hakanan ta kwanta zuciyar ta fam da tunane tana fadin,,,,, Kiyi hakkuri inna tunda kin riga kinyi alkawari ,, nayi alkawarin ni fadima nizanje koda kuwa zuwan nada illar kamar yadda zuciyar ki ke fada maki ,,,, kuma gashi kinyi alkawari baki son fasawa,,,, kada Gajiye taga rashin cika alkawarin ki.
Kuka inna tasaka tana fadin Allah yaimaki,albarka fadima ,,,saboda ta fahinci fadima tagane manufar ta.
Kiyi hakkuri zan maki addua ,,, Sanan kuma ina son jan hankalinki duk da nasan tarbiyan da nayi maku, amma dai inason kisan yanzu birni zaki ba kauye ba ,,,,Don Allah ki kula ki kauda kai ga abin duniya ba ruwanki da abin mutane kiyi abinda yakaiki watau zumunci ki kulada rayuwar kamar kina a gabana,,,Don Allah ki kiyaye ki kare mutuncin ki,,, Sannan nasan ki da rawan kai to ki rage don Allah,,,, Allah yayi maki albarka yakare minke daga duk wani abinki ya azurta min ku da ilimi mai amfani ,,, Zancigaba da yi maki adduan alheri har randa akadawo min dake ,, Allah ya kaiku lfy
Da kyar ta kai maganar ta da kuka a fuskanta.
Gajiye ta mike tsaye tana fadin haba yar kulu sai kace wani guri zata haka.,,,,, aiki kwatar da hankalinki fadima gida zata.
Hmmm Gajiye aikin san danyau saida fada ,,, tau hakane kuma
Gajiye tace ina kayanta akadauko wasu yan tsumakara da duk basufi huduba acikin wata tsohuwar leda bage baka aka bata
Kuka fadima keyi ta kankamay yan uwanta tana kuka kamar bazasu kara haduwa ba,,,Gajiye tace haba fadima ki yi hakkuri daina kuka ba wai dadewa zakiyi ba ai idan zan dawo tare zamu dawo, ba wai an rabu ne gaba daya ba . Wanan kuka haka ai sai yasaki ciwon kai.
Gurin inna takoma ta kara riketa tana fadin inna ki yafe min dan Allah ,,,, ita ma inna fadi takeyi cikin kuka baki man komai ba fadima Allah ya kai ku lfy.
A waje suka tarar da,su Ramatu da wasu yan uwan gajiye suna jiran fitowar su,
Haba shiru haka inji Ramatu ai mundauka kun fasa zuwa yaune,,,,
A,a ,a haba dai mun dai tsaya adan kintsa ne kinsan rabuwar da da mahaifi da wuya tun dai irin wanan da ba,a taba zuwa ko ina ba.
A haka suka samu motar da zata kaisu sokoto nan bakin hanya ,,, Ana daga masu hannnu fadima ma tana daga masu hannu tana kuka har saida ta daina ganin su,,,,,,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
[10/3, 16:34] +234 703 602 1388: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
Girmamawa Gareku masoyana👏👏,👏
ANTY Mariya SB
Hafsat yusuf
Safiya mai Huguna
Fatima Garba Teema luv
Maman Rufaida
Maman Ihsan
Anty Amal.
Nagode maku sosai,,,,
( FARKO )
Allah sarki ,,,, Yau litani itace rana ta farko da ni fadima nafara fita nabar kauyen mu dogon daji dake cikin jahar sokoto ,,,itace kuma rana tafarko da na fara shiga mota.
Tun ina kuka har nadaina gabana ko yanata faduwa ina ta rintse idona ,,,,,, anawa haukan wai,na ga itace na ta gudu .
Ba ai wani dadewaba muka shigo garin sokoto .
Muna isa tasha muka samu motar kano saura mutum uku, Gajiye ta biya kudin mutun uku din wai batason a matseta a mota.
Tun a sokoto nafara ganin canjin fuska a wurin Gajiye. Cikin hali irin na yaro nadan sa guiwar hannuna bisa ciyar ta haba aikawai naji ta fisgar min da hannu ta hankadeni gefe guda . tace kada ki kawo min sakarcin nan irin wanda uwar ku ta koya maku,,,,
A, hankali nadaga idona na kalleta idona tab da hawaye,,
Wani irin a jiyar zuciya nayi na maida fuskata hanyan titi,,,,,,, Ga fitsari ya cika min mara amma tsoron Gajiye ya hanani magana saida naga fitsari na batun balla min mara nasa , ihu cikin kuka nace wayyo Allah fitsari nake ji
Driver yataka burki da sauri yana fadin subahanallah shine baki magana,,,,,, Gajiye takai min rankwashi akai tace ja,ira fita da sauri kada ki min ajikina. kafin in tsuguna har yafara fita ko.
Karfe uku da rabi muka shiga KANO, zokaga kallo wurin yar kauye in waiga nan in waiga nan . muka sauka a saman hanya Gajiye takara tsaida wata a daidaita sahu sukayi jinga akaita Tarauni.
Mun isa tarauni cikin dan kan kanin lokaci, Gajiye ta biya mai adaidaita sahu kudin shi yatafi
Wani gida muka dosa gidan akusan tsakiyar layin gidan yake, saidai yanayin wurin yaimin kama da kasuwa a gurin saboda yawaan mutane da kuma abin hawa.
Gidan yana darumfa ga katuwar baranda an shimfida tabarmar roba babba ga benci kuma an jera su kala kala
Muka zagaya ta baya naga wasu yaran mata suna ta gaida Gajiye,,,,,, HAJIYA tana ciki ne inji gajiye tana tambayar "yan mata wata gutuwa tace mata eh tana ciki,,,, Dakata nan kijirani inji Gajiye .
Daya daga cikin yan matan tace Allah sarki Yumma dibi wanan yar yarinyar don daukar alhaki wai itama ankawota aikatau ko bauta,,,,,,, Yarinya da uwar ki tasani da bata barki kinzo ba .
Duk da yarinya nake saida cikina yabada kara naji wata iri don, Kande mai aya tagarin mu tana muna hiran yadda turawa suka dinga bautar da mutane da yadda shehu yazo ya dinga yaki da kafirai,,,,,, wanan zancen na kande na tuna.
Wata murya ta katse min tunane na tace Sukaina ance kiba wanan bakuwar yarinyar abinci taci inji hajiya
Saida nagama cin shinkafa da miya sai wani ganye da aka zuba sama,,,, bantaba cin ganyen ba sai na yayeshi gefe naci shinkafar kawai mai shegen dadi da nama guda uku aciki, aka kawo min ruwa masu sanyi nasha nayi hamdala.
Ina gamawa na mike naje gurin wacce akace tabani abinci nakai mata kwano takarba tana fadin kin koshi ko nace mata eh,,,,, saidai don Allah inason inyi sallah ne .
Tadafa min kai tace Allah sarki zoto in gwada maki wuri, wani dan daki takaini ansa wata tsohuwar kwali agefe tace min yi nan, muma anan , muke dan labewa muyi,,,,, dam sallah kuma ake labewa ayi nafadi haka a zuciya ta.
Ina cikin sallah naji ana fadin hajiya tace wai a,shigo da bakuwar yarinyar da tazo yanzu
Akace mata ina sallah takoma tafada masu,,,
Bayan na idar wanan Sukainar tace min inzo muje gurin hajiya,,,,Da sallamata na shiga su,biyu ke cinkin dakin maikama da shago, GAjiye tana zaune samar tabarma, itako, hajiya mai sharwali na saman wata kujerar roba fara.
Cikin gimamawa naje har gabanta na rusuna nace ina wuni hajiya takarba min ba yabo ba fallasawa, najuya na gaida gajiye itama,,,,Ido matar ta kuramin ina nan a tsugune har nadan wani lokaci,,, ina ganin matar nazari takeyi akaina.Dakin yai shiri nawani dan lokaci, kaina yana kasa duke, naji muryan matar tana fadin a,gaskiya Gajiye don dai kin fada min matsalar ki data uwar yarinyar gane da bazan dauki karaman yarinya irin wanan ba .
Ai wanan wahalar rainonta kawai mutun zaiyi Ita, ko Gajiye tana fadin ayi hakkuri hajiya , ataimaka muna.
A,zuciyata nace taimako kuma ashe dama inna sayar dani ta hada baki da Gajiye suyi shine ban sani ba ,,,,,, Allah sarki inna har talaucin da ake kira muna yakai hakan,,,,,, wasu kwalla masu zafi suka sulalo min ga fuskata na share hawayena na dan, gyara tsugunawa na,sake cewa, Allah nagode ma da ba hafsat tazo ba don ita bata kaini lfy ba ance tana da shawara ajikinta kuma inda tazo ya saurayinta I,Lu zaiyi yadda suke son juna,,, kusan mu kauye da yarinya takai shekara goma zancen aure yafara ke nan duk wani abu na mata zata fara iyawa....
Ina cikin tunane naji hajiya nacewa to amma gaskiya bazan baki kudin taba duka sai naga yadda yanayinta yake . Ai ba matsala inji Gajiye nasan insha Allahu zakiyi alfahari da ita.
HAJIYA taba Gajiye kudina ina kallo tanata washe baki har kune ita kakanta ya yanke saka.
Hajiya ta waigo tana fadin maye sunanta ne Gajiye ta ansa da fadin FATIMA saidai mu can kauye muna ce mata FADIMA ai, to shike nan sunar yayi kinsan mu nan muna canza ma mutun suna saboda bat,da, kama,,,,
Da Gajiye zata tafi tajawoni gefe taja min kune tana fadin to fadima ki kula da duk wani aiki da a,kasaki kuma banda kwadai don nasan kinga abinda baki saba gani ba don Allah ki kula sosai
Wanan kudin kuma zan je dogon daji in kaiwa mahaifiyarki su tasan abinda zatayi dasu,,,, (kaji makirci) irin ta tsofin kilaki,,,
Har ta fara tafiya cikin muryan kuka nace Inna nan zaki barni tace, "eh fadima amma zan rika zowa ina dibaki ke kuma dan abinda kika tara saiki bani inkaiwa maman ki.
Wasu hawaye masu zafi da kunar rai suka kara sulalowa a idona nace to kigaida su hafsat,,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITES🐎
[10/3, 16:40] +234 703 602 1388: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
7⃣
BY
🐎ZAINAB MAKAWA🐎
🐎HUGUMA WRITERS🐎
Akullun ina gode maku yan Huguma groups gaba daya da kuma TEEMA Luv Hausa Novels
Anty mariya sb
Anty hafsat yusuf Ali
Godiya dubu dubu gare ku.
Tun wucewar Gajiye sai nasamu wuri gindin wata bishiya na zauna nayi ta gumi,,,,,